Dr. BOBBY COMPLETE HAUSA NOVEL

Dr. BOBBY COMPLETE HAUSA NOVEL

Tunda suka fita Lamido ta zube nan kasan dakin tana sakin wani marayan kuka…Bilkisu ma batasan lokacinda ta durkusa nan kusa da ita ba suka taru suka hada kai sunata kokawa abunsu…if you see yanda suke kuka zakayi tunanin mutuwa akayi musu…saida sukayi na sama da one hour Billy ta dakatar da nata snn ta shiga rarrashin ‘yar uwarta amma a banza…ta kwashi wasu 30 mins tana rarrashi ganin ba denawa zatayi ba ta mike tareda rage kayan jikinta ta fada bathroom…wanka tayo tareda alwala snn ta fito ta gabatar da sallahn azahar da akayi tun dazu basu tashi sunyi ba suna aikin kuka…har ta idar da sallahn Lamido bata dena kuka ba…ta karasa wardrobe dinta ta dauko dan dogon riga mara nauyi tasa snn ta sake komawa gun Aysha data koma kan gadonta ta kwanta tareda lullubewa da blanket…kawai ayyanawa take da ace daddynta irin easy going mutane ne da babu abinda zaisa ta sake kwana a FCNM saidai kawai su ganta a gida…to sanin da tayi kota fada mishi ma ba goyuwa da bayanta zaiyi ba kilan ma saidai ta janyo ma kanta fada yasa ba yanda ta iya haka nan zata hakura tacigaba da zama ko bataso…tun dazun wayanta ke vibration amma ta kasa tashi ta dauka…Billy da ta gaji da jin vibration din ta dauka tareda picking call din ta kara a kunne…a daya 6angaren Hamma Najeeb yace”Maama are you mad anata kiran wayanki bakya dauka?..”cikin voice dinta da bai gama warewa ba Billy tace”Hamma ba ita bace”..da sauri yace”Subhanallah Bilkisu what happened?.. you sound somehow..ina Maaman take? “..a hankali ta juya tana duban Aysha da har yanxun ke kudundune kan gado tace” Hamma gata…kuka takeyi tun daxu”..a dan rikice ya sake fadin”Ya Ilahi meya sameta?..bata wayan muyi mgn”..ba musu ta karasa ta yaye blanket data lullu6e dashi ta saka wayan a speaker snn ta ajiye kusada face dinta tace”Hamma gashi nan na bata”…da sauri yace”Maama can you hear me?..what happened?.. why are you crying?..”da sauri ta mike zaune tareda daukan wayan ta rike a hannunta har yanxun bata dena hawaye ba tace”Hamma bana son makarantan nan please..inaso in dawo gida dan Allah”..hankalinshi duk ya tashi yace”Aysha me yake faruwa ne wai?..me akayi maki?..”tana kuka tayi mish bayanin duk yanda sukai da proprietor daxun…yayi shiru har saida ta gama snn yace”to ki kwantar da hankalinki ina nan zuwa gobe kinji..first thing in the morning zan taho inshaAllah amma ki dena maganan dawowa gida kinsan daddy bazai yadda ba”…ta kai hannu tana goge hawayenta tace”Hamma to nidai kazo dan Allah…i really want to see you”..yace”ba damuwa zanzo inshaAllah..stop crying kinji”…gyada mishi kai tayi kaman yana kallonta…saida ya tabbata ta dena kukan yace”to bari in kaima Ammi zakuyi mgn dama itane tace in kiraki and karki nuna mata wani abu ya faru okay?..”a hankali tace”toh”…bai sake mgn ba ya fita zuwa parlor inda gaba daya suke zaune snn ya mikama Ammi wayan yace”yauwa Ammi gata”..Ammi ta amsa wayan tana fadin”kun gama sirrin naku knn?..”baice komai ba yayi daria ita kuma ta kai wayan kunnenta hade da sallama..a hankali tace”wa’alaiki salaam Ammi ina yini”..tace”lafia lau ya jikin naki?..”tace”naji sauki Ammi..ina Yusra”..Ammi tace”Yusra gata nan..kina jina?..”da sauri tace”inaji Ammi”…”wani mgn kika kira fiddausi kika fada mata?.”..lokaci daya Aysha ta wani zaro ido hadda su rufe baki tace”aunty fiddausi wai?..Ammi me zan fada mata ni toh?..”bata rufe baki ba Ammi tace”zakici ubanki wlh..kin kirata kin hadata da ‘yar uwarki shine yanxu kike tambayana me kika fada mata?..”ta marairaice tace”wlh Ammi kome Husna ta fada karya take..ya zaayi ma ki yadda na da mgnrta ni da nake babba baki yadda da nawa ba?.”dan tabe baki Ammi tayi tace”da kike babba ai ba hankali gareki ba har yanxun..kuma kome kika fada mata maza maza ki kirata yanxu kice mata karya kike dan ba cikakken hankali gareta ba itama fiddausin”..batasan lokacin da murmushi ya dan subuce mata ba tace”kai Ammi maman tawa?..”Ammi tace”Maman taki fa shiyasa duk wani rashin mutuncinta ai kikayi gado..lokacin da muna gida Fiddausi ai ba karamar fitinanniya bace”..batace komai ba sai daria da tayi…Ammi tace”iceko kina kiran daddy ki gaisheshi?..”tace”ina kira Ammi..ko jiya saida na kira ban sameshi ba”..tace”to ki sake gwadawa yau ko gobe..ya danyi tafiya ne amma nasan a yau ko goben zai dawo”..tace”InshaAllah zan kira Ammi..ki bawa habibty mu gaisa plss”..ba musu Ammi ta mikama Yusra wayan snn ta bar parlon…Yusra ta amsa da murnanta saidai kafin tayi mgn Husna ta kwace wayan tareda kaiwa kunnenta tace”to Adda ni da baki nemana sai me?..duk tsiya dai ni kika fara sani kafin Yusran”…wani murmushin Aysha ta saki tanajin yanda lokaci daya duk wnn damuwan data shiga na tafiya tace”kuma dana fara saninki ai ba cewa akayi dole sai nafi sonki ba”…Husna ta wani murguda baki kaman tana ganinta tace”kuma ko Hamma zaizo na fasa biyoshi wlh”..tana gama fadin haka ta ajiye wayan tayi gaba abunta…Yusra ta dauka tana murmushi suka fara mgn…duk abunda suke Hamm na zaune yana kallonsu…lokaci daya Aysha ta mance da wani 6acin ran proprietor sukaita hira da qanwarta…basu suka gama ba saida ya kar6e wayan da kanshi…sai a lokacin ta samu ta shiga toilet tayo wanka snn tazo ta shirya ta sake hayewa kan gadon ta kwanta sbd Billy bata dakin…tana kwanciya sai abubuwa da suka faru suka shiga dawo mata…ta tuna yanda ya daure fuska ya kuma tsareta da wnn shegun idanun nashi mai kama dana aljanu ta bakin na Billy…batasan wane irin magic ke gare idanun nashi ba da yana dora mata su taji kaman an tattaro duk wani rashin nustuwa da tashin hankali na duniyar nan an dora mata su akai…anya kuwa mutumin nan ba wani abu yakema idanunshi ba?..tana cikin tunanin Billy ta shigo dakin ta mika mata wayanta dake hannunta tace”kar6i ki ce masa ya dena kirana dan Allah..haba! tun daxun yaketa faman kira ko yanaso ya shanyemun caji ne?..”ba musu Aysha ta mike zaune tareda amsan wayan daga hannunta taga Lamido’s bestie ke kira…dariya ta saki sosai dan har gobe bata dena dariyan wnn sunan da tayi saving number besty dashi..wai Lamido’s bestie sai kace wani yace bestienta ne ita…har kiran ya katse wani ya sake shigowa bata dauka ba…Billy data kulu tace”malama idan bazaki dauka ba bani wayata dan Allah”..bata bata wayan ba tayi kokari ta tsayar da dariyan snn tayi picking tareda karawa a kunne…yanajin an dauka yace”Haba my Billy”..Aysha ta wani zaro ido jin abunda ya fada hadda toshe baki tace”besty ba ruwana wlh”..dan dariya shima yayi kafin yace”inata kiran wayanki bakya dauka itama kuma wnn ‘yar rainin hankalin sai wani jamin class takeyi taki daukan wayan sai kace saurayinta”..yana rufe baki Billy da taji kaf abinda ya fada ta daga murya tace”Allah ya kiyaye na rasa dawa zanyi soyayya sai kai…kuma a kashe a bani wayana sai ka kira wayarta ku cigaba da shirmenku”..dariya yasa sosai Lamido na tayashi…saida sukayi me isarsu snn yace”besty wai an fasa zuwa saloon din ne?..kin ganni fa tun dazu a bakin gate dinku ina jiranku”..tana dan girgiza kai tace”anya zuwa saloon din nan zai yiwu kuwa besty?..i don’t feel like going out”..tana rufe baki yace”kuma shine baki kira kin fadamin ba saida na baro gida nazo?..fadamin me yake damunki da zakice you don’t feel like going out?..na sanki da son yawo fa besty”…tayi shiru tanajin yanda 6acin ran dazu ke son dawo mata sabo fil…shi kuma jin tayi shiru sai yace”alright ki fito waje sai muyi mgn..ina bakin gate”..bata ce komai ba ta kashe wayan snn ta mike ta zura hijab tace ma Billy”taso muje”..tayi mata wani kallo tace”je ina?..”tace”wajen besty mana bakiji yace yana bakin gate ba?..”tsaki ta saki tana kokarin hawa kan gadonta tace”sai kin daw..”bata gama mgnr ba ta shiga janta suka fita daga dakin tunda already da akwai hijab a jikinta…har suka fito waje bata dena jan hannunta ba itama kuma bata dena kokarin kwatan hannun nata ba har suka karasa inda yake…ya bude mota ya fito yana kallonsu one by one kafin ya danyi murmushi yace”to a bani labari menene ya faru?..”Bilkisu ta daure fuska tana kawar da kai Lamido kuma tace su fara samun wuri su zauna first… duk basuyi gardama ba suka karasa wani dan wuri da aka zagayeshi da flowers tsakiya kuma cement chairs ne suma aka zagaye wurin dasu suka zauna…suka danyi shiru na wani lokaci kafin Aysha ta bashi labarin duk yanda sukayi da proprietor daxun…shi kanshi baiji dadi ba kuma suma yaga yanda duk Mood dinsu ya sauya dan haka yace ko baza’a je saloon ba shi yanaso ya kaisu wani wuri…Bilkisu ce ta fara cewa bazataje ba kunsan mutumiyar taku????sai da kyar suka samu suka lalla6ata ta amince ta bisu..daga nan basu koma ciki ba suka shiga motanshi suka wuce..kai tsaye Ten to Ten ya fara kaisu yayi musu ordern abinci mai kyau yace suci dan yasan yau da kyar idan sunyi lunch gaba dayansu…ba suyi musu ba kuwa sukaci dan da gaske ba abinda sukaci tun breakfast… suna barin nan ya kaisu park nan kuwa duk suka ware suna enjoying kansu…bayan sun bar park din suka shiga Ado Bayero Mall sukayi shopping snn sukai branching a gidan grandmother dinshi dake Tarauni…tana zaune parlor tanashan nono da fura suka shigo…ta dago tayi musu kallo daya tareda ta6e baki snn ta cigaba da shan furanta…saida suka karasa ciki suka zauna Sa’eed yace”Hajjaju baki ganni da mutanen naki bane?..”sake ta6e baki tayi ta kur6i furanta kafin tace”ai ni ba ruwana da mutanen nan yanxu…tsakani da Allah suna cikin garin nan yaushe rabon da naga kafafunsu cikin gidana?..”dan murmushi Billy tayi tace”Haba Hajiya kinaso Sa’eed yaji kanmu knn?..”tace”yo jin kai na nawa kuma Bilki?..ai saidai kar a kuma”…Aysha daketa murmushi itama tace”to munji mun dauki laifinmu Hajiya kuma mun bada hakuri inshaAllah baza’a sake ba..daga yanxu duk weekend sai bestie ya kawomu mun gaisheki”…harara mai kyau ta watsa mata tace”sarauniyar ‘yan dadin baki..to na hakura dai ba dan halinku ba..ya kuke ya karatun?..”sukace”karatu Alhamdulillah Hajiya..ya gida”..tace”lafia lau..ya wajen iyayen naku?..”Sa’eed dai na zaune yana kallonsu..lokaci guda i hira ya 6arke a tsakaninsu dama hajiya ba daga nan ba akwai labari su din ma kuma ba baya bane…a takaice sai da sukai sallahn magrib suka bar gidan…kai tsaye ya maidasu Hostel kowacce rikeda kayan kwadayin da suka siyo a shoprite..duk wnn kunci da 6acin rai da suka shiga daxun yayi disappearing..besty kam yayi kokari.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128Next page

Leave a Reply

Back to top button