Dr. BOBBY COMPLETE HAUSA NOVEL

Dr. BOBBY COMPLETE HAUSA NOVEL

Rano✨

Wnn littafin na kudi ne ban yadda wani ko wata ya fitarmin dashi ba…masu buqatan siya zasu tura 300 zuwa 2208991344 Aisha Ahmad Tijjani Zenith Bank…sai a tura evidence of payment via 07063800556.
54
Biki ya rage sati daya Aunty Fiddausi ta tattara su gaba daya suka wuce Gombe sbd preparation na biki da zata taya yayarta…zuwa lokacin sosai amarya Aysha ta canxa tayi wani 6ul 6ul da ita kaman ba amarya ba don ba wani stress na biki data daurama kanta..duk wani abu daya kamata ayi Billy ce takeyi tareda sauran cousins dinta sai kuma Aunty Fiddausi…sbd cika fa gidansu ya farayi da mutane na nesa da suka fara zuwa Ammi tace ita da Billy suje can gidan wani small uncle dinta da bai dade da aure ba su zauna tareda sauran friends dinsu da zasuzo idan an fara biki…haka kuwa akayi suka tattara duk wani abu da sukasan zasuyi amfani dashi har a kammala biki suka wuce can gidan uncle din nata dake few houses away from nasu gidan…sun rage yawan events da suka tsara zasuyi sbd Lamido ne yace lallai lallai duk yawan events dinsu kada ya wuce kwana uku dan haka sun bar Henna Party ranar Wednesday.. Thursday Cocktail party..Friday kuma Kamu da Mother’s Eve wanda Ammi ta shirya..Saturday ayi daurin Aure by 11 daga nan kuma a wuce da amarya Kano inda zasu gabatar da nasu events din a can.

Yau Tuesday tun safe sukayi shirin tafia saloon Billy na zaune parlor tana waya da Hamma bai Kai ga dawowa Gombe ba ita kuma amarya Aysha tana daki tana karasa shiryawa don su wuce saloon din da wuri..tana zaune gaban mirror tana kokarin parking gashinta kiran ango ya shigo wayarta..ajiye comb dake hannunta tayi tareda daukan wayan tana marairaicewa tayi picking tana cewa”partner dan Allah kayi hakuri mu tafi plss..wlh daga ni sai Billy zamu tafi ba wani ne zai kaimu ba”..girgiza kai Bobby yayi kmr tana gabanshi yace”baby i told u Sab is coming to take u guys ku Kara hakuri mana..ban yadda ki shiga motar wani ya fita dake ba wlh”..da mamaki sosai tace”u mean tun daga kano ka tasoshi sbd yazo ya kaimu saloon?..”girgiza kai ya sakeyi yana shafa kanshi yace”no yana Gomben dama tun jiya Mummy ta aikoshi bai dawo ba..yanxun yacemin ya fito daga gida so u guys should wait for him”..a hankali tace”partner kishinka yayi yawa mana..an kusa bikin ma bazaka dena wnn abun ba”..tun kafin ta rufe baki yace”duk abunda zaki fada ki fada amma da gaske bazan saki matata sakaka kowane Kato yana kallon min ita ba..ubangiji da kanshi yace ya tsine ma wanda bai kishin matarshi so bazan zama among wayanda tsinuwan Allah zai tabbata a kansu ba”..murmushi tayi tana girgiza kai tace”dukda haka naka yayi yawa partner..ya kamata ka rage plss”..shiru taji yayi kmr bazaiyi mgn ba sai can taji yace”kinsan wani abu?..”girgiza mishi before saying”aah”..wani munafukin murmushi ya saki yana shafa gemunshi murya can kasa yace”i can’t wait to be with you..Allah kadai yasan yanda nakeji kaman in janyo Saturday ya dawo yau”..ya karasa mgn yana lumshe ido kai kace a gabanta yake..Lamido dai diff tayi tana sauraronshi jin ya fara sauka daga layi..ita ta rasa dalilinda yasa ya dawo bashida kunya yanxu..gaya mata duk maganan da yazo bakinshi yake ita ya barta da jin kunya..turo baki tayi tareda mikewa daga inda take zaune tace”nidai tafia zanyi Ammi na kirana”..da sauri yace mata”hang on plss”..shiru tayi tana sauraronshi..shi kuma ya wani kwantar da murya yace”bakice kina Sona bafa”..murmushi mai kyau ta saki tana kallon kanta ta mirror kafin a hankali tace”Partner”..murya can kasa shima yace”yes partner”..sake kashe murya tayi tana wani kashe ido cikin wani irin siga tace”Ina sonka sosai..i love u”..lumshe ido Bobby yayi yana safe chest dinshi still smiling yace”i love u more wlh..son da nake maki Allah kadai yasan amount dinshi”..har yanxu bata bar smiling ba itama tana lumshe ido..batasan why har yanxu bata gajia da sauraron words din nn nashi ba..she loves him to the extent that duk wani word da zai furta mata means the entire world to her..she loves him to the core…kafin wani cikinsu ya sake mgn kiran Ammi ya shigo wayanta..tana dubawa taga itace sai tayi saurin maidawa kunnenta tana cewa”partner excuse me plss..Ammi naga ke kira tun daxu bansan ko nemana take ba”..gyada kai yayi tareda kashe kiran ita Kuma tayi saurin daukan call din Ammi tana cewa”hello Ammi”..a fusace Ammi tace”wai zaman uban me kukeyi a gida baku fito ba tun daxu?..”da sauri tace”yi hakuri Ammi cewa yayi ya turo Sab yazo ya kaimu shiyasa bamu fito ba”..tsaki Ammi taja kafin tace”to yana zuwa ku tafi and ki tabbata kin biyo ta nan don akwai baqin da zaku gaisa dasu”..a hankali tace”to Ammi”..daga haka Ammi ta kashe wayarta ita kuma tayi saurin karasa parking gashinta ta dauki bag dinta da veil dinta a hannu ta fita daga dakin..har yanxu Billy na nan parlor suna waya da Hamma..Aysha ta karasa ciki tana yafa veil dinta akai tace”su Laila da Majnoon har yanxu ba’a gama wayan bane?..”harara Billy ta watsa mata before tace”inace kema wayan kika gamayi da Romeo dinki yanxu?..”girgiza kai Aysha tayi tana karasa veiling dinta..daidai nan Kuma kiran Sag ya shigo wayarta and ko bata dauka ba tasan karasowa yayi dan haka a hanakli ta isa inda Billy ke zaune ta fizge wayar hannunta tareda kaishi kunnenta tana cewa”Hamma a dan daga mana kafa plss..zamuje saloon”..murmushi Hamman nata ya saki tareda kashe wayarshi..Billy da already ta gama shirinta kafin ta fito ta mike tana rataya bag dinta a shoulder dinta tace”to muje amaryar proprietor”..murmushi kawai Aysha ta saki tareda juyawa suka fita daga gidan..suna fita ta hango motar Sab Parke a gefe dan haka suka nufi can direct..yana hangosu ya fito daga motar ya bude musu kofa yana kallonsu da murmushi har suka karaso..Aysha na kallonshi with a smile tace”haka nan ya tasoka daga aikinka Koh?..”girgiza kai Sabeer yayi yana murmushi shima yace”duk aikin da nake ai muhimmancinshi baikai wnn ba aunty”..murmushi ta kara saki ta shiga cikin motar Billy ma ta shiga snn shima ya zaga ya shiga ya tayar da ita suka bar wurin..Saida suka hau titi Lamido tace”dukda haka nidai banji dadin tasoka da yayi kana zaman zamanka ba..Saida fa nace mishi daga ni sai Billy zamu tafi amma bai yadda ba”..Sab dake jinjina zafin kishi irin na dan uwanshi yace”haka nan fa yake aunty..tareda wani cousin dina da zamu zo yace bai yadda in tahoda kowa ya kalleki ba shine na saukeshi a gidan Waziri nace mishi yanxu zanje in dawo”..murmushi Aysha keyi tana girgiza kai tasan halin kayanta tsaf zai aikata hakan shiyasa batayi mamaki ba..har yanxu tana murmushi tace”ni kaina kishin Partner har tsoro yake bani fa..inaga shi baiqi ace babu wanda zai sake kallona ba har karshen rayuwa”..daria Sab ya saki yana cigaba da driving dinshi yace”zai iya aikata hakan wlh”..Billy dai na zaune baya tana jin conversation dinsu..tun bata sa baki ba har daga baya itama ta shiga suka farayi da ita..bayan ya saukesu yace idan sun gama sai su kirashi ya maida su gida shi Kuma ya juya kan motarshi ya koma gidan Waziri.

Lokacin da Sab ya maidosu gida was around 3..kofar gidansu tace yayi parking sbd amsan da kiran da Ammi keyi mata tun safe dan haka daga nan sukayi sallama dashi ya wuce su kuma suka shiga cikin gidan da yake nan taf da mutane…saida suka tsaya suka gama gaishe gaishe a parlor na baqin dake ciki kafin suka wuce bedroom din Ammi..daga ita sai aunty Fiddausi a dakin sai wata cousin dinsu suna lissafa cards din mother’s eve da dole Ammi tasa aka karo sbd wanda akayi da farko har ya kare..karasowa ciki sukayi suka zauna suna gaisawa dasu..cousin din Ammi mai suna Rahina tace”aah su amare an samu shigowa knn”..Lamido tayi kasa da kai tana sake gaisheta..Aunty Fiddausi ta debo cards kusan guda 40 ta mikama Billy tace”ungo wnn koda na hannunku zaku kare sai kuyi amfani dasu”..Billy tasa hannu ta amsa tana counting dinsu tace”wlh kuwa kmr kinsan wanda kika bani har sun kare”..Aunty Fiddausi tace”nasan za’ayi hakan ai shiyasa na kwasan maku wnn”..daga haka ta kwashi wasu da suka ware na ‘yan uwan daddy ta fita daga dakin don kai musu nasu..Ammi ta gyara zama tana duban Aysha tace”zauna muyi mgn”..ba musu ta zauna kusa da Billy tana kallonta..daure fuska Ammi tayi tana cewa”mgn dama zanyi Miki akan African time..wlh Aysha kika sake na tara jama’a a wuri kikaje kikayi zamanki bakizo da wuri ba da sunan make up zakiga yanda zanyi dake a gidan nan..dama da wuri ku fara make up dinku don bazan dauki a 6ata mana lokaci ba kin sani”..gyada kai tayi tana dan marairaicewa tace”wlh da wuri zamu fara Ammi”..Ammi tace”good..saura kuma kiqi nutsuwa kizo kina wnn raye rayen naki da kika saba”..sake marairaicewa tayi tana duban Ammin nata bata dai ce komai ba..Ammi tace”kika wani tsareni da ido ko bakiji abunda na fada bane?..”kasa tayi da kanta kafin a hankali tace”naji..amma to Ammi nidai dan Allah kice kar asa waqoqin gwanja kinga bansan sanda zanyi rawar bafa”..rai a 6ace Ammi ke kallonta tace”qanin ubanki ne Ado Gwanjan?..”da sauri ta girgiza kai tana turo baki..Ammi tace”to kije kiyi rawar kiga idan banci mutuncinki ba..ki bar ganin aurenki za’ayi wlh idan kikayi ba daidai ba Ina iya zuwa har gidan mijin naki inyi maganinki”..har yanxun kanta na kasa tace”to kiyi hakuri”..Ammi bata sake tankata ba ta dauki wasu cards cikin wanda ke xube gabanta ta mikama Billy tace”idan Kun fita ki nemi Husna ki bata..kuma kice mata idan batayi sauri ta kawomun abunda na aiketa ba itama zataci ubanta”..murmushi Billy ta saki tareda mikewa ta amsa cards din Aysha ta mike suka fita..suna fita cousin din Ammi dake sauraron draman nasu tana daria tace”yanxu Maimuna har yanxu baki dena wnn fadan naki ba..yarinya tana amarya kin wani sanyata a gaba da fada bayan ba laifin komai tayi ba”..murmushi Ammi tayi tareda mikewa daga kan gadon da take zaune tace”Adda bakisan halinta bane idan ba haka nayi mata kunya zatazo tana bani a gaban jama’a..shegen rawar kai gareta kmr ba bafulatana ba”.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128Next page

Leave a Reply

Back to top button