Dr. BOBBY COMPLETE HAUSA NOVEL

Dr. BOBBY COMPLETE HAUSA NOVEL

Ranan Monday tana shigowa school ta wuce office din Nur da safe…yana zaune yana signing wasu papers ta karasa ciki ta zauna bayan sun gama gaisawa tace”Sir dama alfarma nazo nema wurinka”…Nur ya ajiye pen dake hannunshi yana kallonta sosai yace”ohk ina jinki”…tayi kasa da kai tana wasa da fingers dinta tace”Sir so nake dan Allah ko mgn zai hadaku da Proprietor kada ka nuna mishi ni zanyi representing midwifery a presentation din nan”…kallonta Nur yake da mamaki karara a face dinshi yace”amma why?..”tana turo baki tace”cewa yayi wai ko anyi choosing dina ince banyi and ni kuma inaso inyi shiyasa banaso ya sani saidai kawai ya ganni kan stage”…gyada kai Nur ya shigayi alaman gamsuwa before yace”no problem ur secret is safe with me..he won’t know inshaAllah”..murmushi ta saki tareda mikewa tace”thank u sir”..yana mata murmushi yace”u are welcom”..daga haka tayi mishi sallama ta bar office din…Nur ya bita da kallo cikeda mamakin abunda ta fada…shi bai gane kan wani dalili Bobby zai hanata participating ba..dama these days ya lura kaman abu na damunshi and bai ta6a fada mashi ba…”ko dai son Lamido yake?..”ya fada a fili trying to figure it out amma ya kasa…daga karshe sharewa yayi kawai cikin ranshi yace”kilan idan tayi wari ni zan faraji”..da haka ya kaida tunanin daga zuciyarshi.

Bobby kam hankalinshi kwance yake sosai data ce mishi bazatayi ba…har wani nutsuwa yaji ya samu na musamman wnn dalilin yasa bai sake yunkurin nemanta sbd ya sake jaddada mata ba…ranan Thursday ya kama zaayi presentation din and tun safe Lamido suka shigo school sbd shirye shirye da ake…auditorium dinsu na nan a cike maqil da mutane participants kawai ake jira domin hatta malamai duk suna nan ciki…as usual Bobby da Nur tare suka shigo kowa ya samu wurinshi ya zauna…Nur ne ya danyi briefing jama’a yanda tsarin abun yake…kowane participant za’a rubuta sunan topics kaman guda uku cikin courses da sukayi a shekarar snnayi folding dinsu ya za6a and duk wanda ya dauka akanshi zaiyi presentation din…bayan dogon jawabi ya sake daidaita mike zuwa zaitin bakinshi yanda mgnrshi zai fito radau snn yace”and our two participants are Sa’eed Mukhtar Makarfi from Nursing department and Aysha Ahmad Lamido from Midifery department”…wani irin dammm Bobby yaji kaman saukan aradu a cikin heart dinshi…gaba daya saiya shiga rudani jin Nur ya ambaci Aysha Lamido and idan ba wai mancewa yayi ba da bakinshi ya ta6a fada mashi kta kadai take bearing da Lamido a college din…shi kuma yasan sunyi mgn da ita tace mishi bazatyi ba amma why zaizo ya kira sunanta kuma?..kodai watace mai suna irin nata bai saniba?…kafin ya samu amsan tambayanshi ya hangota ta taso daga inda take zaune zuwa seat da aka tanadar musu…sanye take cikin uniform dinta fari qal sai shinning yake sbd iron…dan hijab dinta daidai chest dinta sai gashin goshi da sajenta da suke nan waje as always…wani irin sanyi yaji yana lullu6eshi kaman fever zai kamashi…ya lumshe ido ya bude yana sake jin ciwon karyar da tayi mashi har cikin ranshi.

Rano✨

Wnn litafin na kudi ne ban yadda wani ko wata ya fitarmin dashi ba…masu buqatan siya zasu tura 300 zuwa 2208991344 Aisha Ahmad Tijjani Zenith Bank…sai a turo evidence of payment via 07063800556.
25
A hankali take takawa wanda Bobby kejin each taku kaman a kana zuciyarshi take yinshi…wani irin nauyi yaji zuciyar tayi mashi kaman wanda keda heart problems…sake juyawa yayi ya kalleta nan take kuma yaji wani abu ja sake tokare makoshinshi…ko baa fada ba yasan gaba daya mazan wurin nan kallonta suke…hakan kuma yasa yaji kaman ya harbi kanshi ya huta…finally ta karasa seat da aka tanada dominsu ta zauna kusada Sa’eed daya rigata karasawa…sake runtse ido Bobby yayi yanajin ciwon zama kusa dashi a tayi…ya ganeshi sarai shine yaronda tayi acting as his wife ranan da sukayi drama and shine the same yaron da ta bama ruwa ranar da akayi sports…yanxun nan din ma a rasa da wanda za’a hadata sai dashi?..kodai wani hu ke tsakaninsu dashi ne wai?…bayan sun zauna daya daga cikin malamansu mata ta taso da wani box a hannunta mai kyau ta kawo wurinsu tace Sa’eed ya dauki daya tunda shine first presenter…ba mus ya zura hannu cikin box din ya dauko paper daya cikin guda uku da suke ciki snn ya bude…sunan topic din ya gani a rubuce dan haka ya mike daga inda yake yana nuna mata ita kuma ta amsa daga hannunshi ta nunawa malamai then back to students snn ta koma wurinta ta zauna…dan matsawa yayi jikin white board dake ajiye nan wurin ya rubuta sunan topic din nashi snn ya fara presentation dinshi a tsanake…gaba daya hall din yayi tsit voice dinshi kawai akeji…Bobby dai na zaune kaman gunki sbd tsabar abubuwa da suka taru suka mashi yawa…yasan yanxu ko bindiga za’a zare ace ya fadi abunda yaron ke fada bazai iyaba as hankalinshi baya wurin gaba daya…kawai yanajin ciwon deceiving dinshi da tayi tace mishi bazatayi ba…ruwa dake ajiye gabanshi ya dauka yayi sipping ya ajiye tun yanxun yanajin haka idan ta fara nata kuma kilan zaucewa zaiyi…baisan meyasa Allah zai dora mashi wnn masifan a kanta ba…Sa’eed saida ya cinye 40 minutes da aka deba mishi snn yayi handing over mike din ya koma ya zauna anatayi mas tafi dan yayi kokari sosai ba kadan ba…bayan Nur ya gama praising dinshi snn ya sake kiran Aysha Ahmad Lamido data karaso tayi nata itama…kaman dazu wnn matarta mika mata box itama tayi picking one a cikin papers uku dake cikin box din snn ta mike a hankali zuwa inda board yake…kallonta kawai Bobby yake kaman bai ta6a ganinta ba sai yau…glasses data sa a idonta ya zauna daram shi sai yaga kaman ma bai ta6a ganin kyan da glass din yake mata ba sai yau…ya sake daga eyes dinshi zuwa goshinta da kusan rabin gashinta ke waje sbd ita ba gwanar sa dankwali ba hula bane..sam bata sonsu sbd suna takura mata shiyasa hijab kadai take zurawa ta tafi abunta…ciwo yakeji sosai yasan yau kaf wurin kowa saiya gama ganin gashinta..kowa kuma sai yaji voice dinta to his satisfaction…tunanin hakan yasa wani hadadde zafi ya kunno kai cikin sanyin da already ya faraji…lumshe ido kawai yayi ysna karanta duk addu’a da yazo bakinshi for he don’t want to loose it kamar yanda yayi ranan festival…sam bayason a fara zargin ko da wani dalili yake aikata haka while baya da wani dalili kawai dai yarinya ce Allah ya jarabceshi da ita da ko kusa bata son ya zauna lafia…idanun nashi a rufe yaji ta fara presetation din cikin sweetes voice dinta…sake runste idon yayi yanaji kaman yaje ya toshe kunnen kowa dake wajen yanda ba wanda keda daman jin muryan nata sai shi kadai…kwata kwata baya fahimtan abunda take fada shidai kawai yasan mgn take in a sweet tone amma ko za’a kasheshi bai iya fadin ga abunda take cewa…tsoron bude idonshi yake sbd gudun abunda hakan zai haifar amma daga karshe kaman idon nashi sunfi karfinshi ne dan ji yayi sun bude kansu da kansu basu fada ko inaba kuma sai a kanta…nan kuma ya tsayar dasu a kanta yana kallon yanda take mgn tana demonstration da hands dinta…gashi sai dan matsawa take from one place to another hakan kuma yasa jikinta ke dan shaking as if she’s doing it intensionally ga kuma gashinta koshi yana iya ganoshi daga inda yake…baisan lokacin daya rike kanshi da yayi mishi wani azababben sarawa ba…har wani jiri yaji yana daukanshi all of a sudden…addu’a kawai ya shiga jerowa dan samun sassauci amma abun kaman gaba ma yakeyi…ita kuwa Aysha presentation dinta take hankali kwance as ba wani sabon abu bane a wurinta…gaba daya tama manta da wani Bobby and his masifa abunda yake gabanta kawai takeyi…bayan ta cinye 40 mins dinta itama ta koma ta zauna anata aikin yi mata tafi wanda hakan ke kara ta’azzara yanayin da Bobby ke ciki…daya daga cikin malamansu ne ya amshi mike yayi ‘yan jawabe jawabensa kafin a sake mika musu box kowa ya sake daukan paper daya this time around 20 mins zasuyi instead of 40…kaman daxu Sa’eed ne ya fara yin nashi yana gamawa itama ta mike ta fara…zuwa yanxu abunda Bobby keji ya ninka wanda yakeji daxu kusan sau uku…har wani gumi ke tsatsafo mishi sbd azaba don zazza6i sosai ya rufeshi kaman wanda yayi kwana da kwanaki yanayi…bai sake gigin bude idonshi ba har ta gama snn yaji hall din ya kaure da tafi…kafin ayi announcing wanda yayi winning a cikinsu wani babban mutumi daya saba halartan taron duk shekara yace a fadawa Lamido ya bata kyautan sabon MacBook hade da 50k a matsayin tukuici na burgeshi da tayi…aikuwa ana fada hall din ya sake kaurewa da ihu da tafi…masu jin dadi nayi masu rashin jin dadi ma duk sunayi…Bobby da yaji abunda mutumin ga fada kaman saukan aradu baisan time daya bude idonshi ba…daidai lokcin kuma Sa’eed ya dan kai bakinshi kusada kunnenta yace”congratulations besty..seems baby ya samu new rival”…da juyawa tayi tana kallonshi ta dan saki murmushi kafin itama ta matsar da nata bakin dab da kunnenshi tace”ai mai iya takara da baby saiya shirya besty..i am his and his alone”…ta karasa mgn tana blushing as ta tuna da habibie noorul qalbinta…wani azababben tari Bobby yaji ya sarkeshi babu gaira babu dalili…numfashinshi har yi yake kaman zai dauke sbd azaba…ya rasa da wanne ma zaiji…da wancan tsohon banzan daya bata kyauta ko kuma da wancan karamin kwaron dake mata rada a kunne itama tanayi mishi…kuma don iskanchi hadda yi mashi murmushi kaman qanin ubanta…ita kuwa bata ma san yanayi ba wai kunu a wani gida…bayan hayaniya ya dan ragu Nur ya amsa mike yayi godia wa wnn mutumi snn ya fadi scores dinsu inda Lamid ta dara bestyn nata da maki biyu…tun kafin a gama fada midwives suka hau ihu suna tafi sbd sunyi winning…sake juyawa Aysha tayi tana kallon Sa’eed sake zaune gefenta tayi mishi gwalo…daria kawai ya saki yana daga shoulders dinshi…daga nan dai aka sallamesu suka fara fita yayinda wnn mutumi yace a tsayar masa da Aysha yanason mgn da ita…Bobby na zaune yana jinsu amma uffan baice ba as shima ta kanshi yakeyi yanxu…ba musu Nur yayi mata mgn ta tsaya shi kuma mutumin ya taso zuwa inda take yanata smilling yace”yammata sannu da qoqari”..dan murmushi ta saki batace komai ba..yace”saqonki yana nan zuwa gareki gobe inshaAllah..zan iya samun phone numberki?..”shiru tayi tana tunani kanta kasa sai kuma ta dago kan tana bude baki zatayi mgn idanunta suka fada cikin nashi da sukayi wani irin jaa yana kallonta dasu kaman zasu fadi kasa…sauke idonta tayi da sauri sbd jin wnn abun da bata qaunar ji duk suka hada ido dashi…turo bakinta tayi dan ko baa fada ba tasan har yanxun idanunshi na kanta…shi kuma mutumin jin batace komai ba sai ya zaro card dinshi ya bata yana cewa”make sure kin kirani dan Allah…I want to discuss something with u”…gyada mishi kai tayi tana murmushi tace”zan kira inshaAllah”…daga haka ya juya yana murmushi ya koma inda yake…itama juyawa tayi zata fita Bobby ya tashi da sauri kaman ana tunkudashi yabi bayanta a kan idon Nur dake monitoring dinshi tun daxu…sbd saurin da yakeyi kafin ta fita hall din ya cimmata sai ya danyi slowing down ba tareda ya kalli gefenda take ba yace”meet me now”…daga haka ya sake daga kafa yayi wucewarshi…ita kuma ta bishi da harara kaman idon zasu koma jikinshi…cikin immitating dinshi tace”wai meet me now..sai kace durkusawa yayi ya haifeni masifaffen banza inyamuri kawai”…kai tsaye office dinshi ta wuce daga nan tana rikeda wayarta a hannu…tana shiga Bobby daketa sintiri cikin office din ya juyo yana kallonta voice dinshi na fita da kyar sbd zazza6i da 6acin ran da yakeji yace mata”are u satisfied?..kinje kinyi presentation kuma kin samu abunda kikeso hope u are now satisfied?..”dan turo baki tayi tana kauda kanta tace”aini ba sbd kowa nayi ba sbd department dina ne”…tun kafin ta rufe baki a fusace yace”if u dare say another word saina kwada maki mari a wurin..am i ur mate?..”shiru ta sakeyi tana cigaba da turo bakinta..ita fa kome zaiyi yanxu bazai daga mata hankali ba tunda ta riga tayi abunda takeso kuma sunyi winning…shi kuma ganin yanda taketa faman hade rai tana turo baki cikeda wani haushin yace”dama it’s what you’ve always wanted to get Men’s attention and now sai ki zuba ruwa kasa kisha tunda kin samu abunda kikeso…you think duk biye biyen maza da kikeyi banida labari kou?..well i am aware of every single thing da kikeyi kawai zuba maki ido nayi inga iya gudun ruwanki kuma na gani…sbd haka bear it at the back of your mind today babu abunda zai hanani sanar da Dad dinki duk iskancin da kikeyi?..so get ready for it”…ya karasa mgn har yanxu yana huci kaman angry lion…Aysha kuwa tunda ya ambaci kalmar biye biyen maza taji gaba daya ranta ya 6aci…wato ma kallon da yake mata knn?..idan akace biye biyen maza fa ana nufin karuwanci knn?..so this is what he thinks of her shiyasa komai sai yace zai hadata da daddy?..lokaci daya wasu hawaye suka ciko idonta dan sosai taji ciwon mgnr daya fada…ta dago idanun ta zuba masa su cikin nashi hakan kuma ya bawa tawagar hawaye da suka cika idanun nata damar saukowa fuskanta…bata damu da goge su ba tana kallon tsakar idanunshi yau ko wnn tsoron da idanun ke bata bataji ba sbd tsabar 6acin rai…shima kallon nata cikin idon yake yanaso ta gane 6acin ran data haddasa masa sbd abunda tayi..shine shi data cuta baiyi kuka ba sai ita da baiyi wa laifin komai ba?…cikin tsananin 6acin rai da bai ta6a ganinta ciki ba tace”so this is what u think of me?..karuwa mai biye biyen maza right?..”kallonda take mishi ne yaji ya kasa jurewa abunda bai ta6a faruwa dashi ba all his life kawai sai ya dauke kan daga gareta yana sake jin sabon kunchi na rufeshi zuciyarshi kaman zaiyi bindiga sbd kumburan da yake…juyawa kawai tayi zata fita daga office din a fusace yace mata”come back here?..”ai ko sauraronshi batayi ba ta bude kofa ta fita da gudu bayan ta bugo mishi kofan da mugun karfi har saida ya runste ido sbd karan da yayi…zuciyarshi na sake tafarfasa ya dunkule hannunshi ya kaiwa table dinshi duka yana fadin”damn it”…wani jiri yaji ya fara daukanshi dan haka ya karasa kam sofa ya zauna da sauri yana dafe head dinshi da yaji ke barazanar rabewa gida biyu…bude kofa akayi secretary dinshi ta shigo tana cewa”Sir pro…”bai bari ta karasa ba ya daga mata hannu har yanxun yana dafe da head dinshi yace mata”get out”…sake bude baki tayi zatayi mgn a fusace yace”i said get the hell out of my office..are u maddd?..”juyawa tayi da sauri ta fita daga office din jikinta har ya dauki rawa sbd tsawar da yayi mata…after like 5 mins Nur ya shigo office yana fadin”wai Bobby what’s wrong with u ne these days?..what is the matter with you?..”a fusace shima ya dago yana kallonshi da eyes dinshi da suka koma kaman garwashi sbd ja ya nuna mishi kofa yace”malam get the hell out of my office..leave me alone”…daure fuska shima Nur yayi yace”ni kake kora office dinka Bobby?..”a fusace ya sake dagowa yace”to hell with u an koreka din me zakayi?..kaga malam leave my office before I loose my temper with you”..ya karasa mgn yanaji kaman ya kwada masa mari..kawai haushinshi yakeji that har ya wani dakatar da ita sbd tayi mgn da wani qaton sbd shi baisan ciwon kanshi ba…Nur da ranshi ya gama 6aci shima yace”well tunda haka kace am not going anywhere until u loose it with me..fight with me if that’s what u want”…dafe goshi Bobby yayi yana dan murzashi abhankali feeling extra hot inside…kawai bayason ya biyema haushin da yakeji yanxu dan ba karamin tashin hankali zasuyi ba idan ya biyema hakan…mikewa yayi a fusace zai bar mashi office din Nur ya wani irin jawoshi ya dawo dashi baya yana cewa”where are u going”…fizge hannunshi Bobby yayi yana nunashi da finger dinshi yace”Fuck you”…daga haka ya juya ba fita daga office a mugun fusace…kai tsaye inda driver yayi parking motarshi ya nufa saidai bai ha driver din ba..sake dafe kanshi yayi ya jingina jikin motan yana sauke numfashi a jere sbd tashin hankali…can ya hango drivern ya taho dan haka yana zuwa bai bari ya fara masa dogon jawabi ba yace”open the damn car”…da sauri yasa key ya bude motar Bobby ya bude back seat ya shiga shi kuma driver ya rufe mashi kofa snn shima ya shiga side dinshi ya tasheta suka tafi…saida suka hau kan titi yace”Sir where are we going to..”a takaice yace dashi”home”…driver bai sake mgn ba ya kama hanyan airport road…suna isa gida ya bude mota ya fita still yana dafe da kanshi ko wayoyinshi daya ajiye nan kusa dashi bai dauka ba…Mr Obi ya kwashi wayoyin da suit dinshi yabi bayanshi dasu…yana shiga kai tsaye ya kama hanyan part dinshi bai ko lura da Mummy dake zaune parlor ba…ganin yanda yake tafiya yana hada hanya kuka ga head dinshi dake rike har yanxun Mummy ta kira sunanshi”Bobby”…juyawa yayi yana kallonta still yana rike da head dinshi yace”Mummy”…nuna masa kusa da ita tayi tace”zo nan”..ba musu ya juya zuwa cikin parlon…ya zauna nan inda ta nuna mashi snn ya sauke hannunshi daga kanshi yana kokarin daidaita kanshi wai kar su fahimci yana cikin wani hali…Mummy da duk kokarinshi saida ta fahimci halinda yake ciki da igbo tace”what is wrong with u?..”kakalo murmushi yayi kafin yayi mgn tace”karka fara cemin you are fine nasan you are not..why kake rikeda head dinka haka?..”lumshe idonshi yayi tareda dora head dinshi kan shoulder dinta yana sauke numfashi…hannu takai tana shafa head din nashi tace”fadamin meya sameka Bobby?..”dago kan nashi yayi a hankali yana kallonta kawai sai yaji hawaye sun ciko mashi ido…baidai bari sun zubo ba amma idanun sai shinning sukeyi sbd hawayen dake cikinsu..ganinshi a gabanta sai yaji damuwan na sake mishi yawa zuciyarshi yayi wani irin rauni da sam baiyi irinshi ba daxu…hankalin Mummy ya tashi da ganin kwalla a idanunshi a rikice ta sake bude baki zatayi mgn ya kuma maida kanshi shoulder dinta murya can kasa yace” i just want to be alone Mummy..please!”batayi yunkurin hanashi ba ta dago kan nashi tana gyada kai tace”it’s ohk u can go..we’ll talk later”…bai sake cewa komai ba ya mike yana sake dafe head dinshi ya wuce flat dinshi yana takawa da kyar sbd nauyi da legs dinshi sukayi mashi…da kyar ya iya kai kanshi parlor ya fada kan three seater yana sauke numfashi…har yanxu wani irin ciwo heart dinshi yake mishi..wani irin zafi yakeji a cikinta kaman ana hura huta a ciki…shidai yasan da kyar idan Lamido batayi ajalinshi ba…baisan meyasa Allah zaiyi masa irin wnn jarrabawa a kanta ba…shi har yanxu ko kusa zuciyarshi bai ta6a bashi cewa there is a reason behind abunda yakeji ba kawai gani yake sbd amanarta da daddy ya bashi ne…da kyar ya iya mikewa ya kai kanshi ciki tareda fadawa bathroom ya sakar ma kanshi ruwa batareda ko kayan jikinshi ya cire ba…saida ya gama jikewa tsaf snn ya rage kayan yayi wanka ya fito daure da towel a waist dinshi…jallabiya kadai ya iya zurawa a jikinshi ya maida towel din bathroom snn ya dawo ya kwanta kan sofa yana sake jin yanda ciwon kanshi ke karuwa…baifi minti shidda da kwanciya ba bacci yayi gaba dashi…dama shi haka yake indai 6acin rai yakai 6acin rai kanshi zaiyita ciwo sai ya samu yayi baccin nan yake samun saukin ciwon.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128Next page

Leave a Reply

Back to top button