Dr. BOBBY COMPLETE HAUSA NOVEL

Dr. BOBBY COMPLETE HAUSA NOVEL

Ana kawo result din Bobby yayi saurin karba daga hannun messenger daya kawo har ya fara budewa sai kuma yayi saurin maidata yanda take tareda juyawa yana kallon Aysha da har yanxu ke zaune tana kallonsu..juyawa yayi suka hada ido da Nur sai kuma ya sake juyowa gareta ya sakar mata murmushi.. Lamido data kasa gane what they are up to kawai sai ta sauka daga gadon a hankali tana kallonshi ta nuna bathroom dinshi tace”zanyi alwala”..da sauri kmr jira yake yace”ok babe”..ta saki murmushi snn ta juya ta shiga bathroom din…tana shiga Bobby yayi saurin bude papern ya wara ido sosai yana karanta content din dake ciki idanunshi na sauka inda yaga an rubuta positive yayi saurin yar da papern tareda juyawa ya kankame Nur sosai kmr zai maidashi ciki..cikin so much excitement ya juya language zuwa Igbo yanda bazata fahimta ba yake cewa”Nur it’s positive.. it’s positive wlh.. Alhamdulillah Alhamdulillah Alhamdulillah”..ya karasa mgn still yana rungume dashi kaman shine mai cikin..shima Nur farin ciki sosai ya taya abokin nashi dan haka yayi hugging nashi back tareda daka tsalle yana wani iri ihu shima da Igbo yace”ekele bro..ekele”(congratulations bro.. congratulations)..shima Bobby tsallen yayi exactly irin yanda Nur din yayi kawai sai Hamdala yake yama rasa inda zaisa kanshi sbd excitement..haka suka rungume juna suna ta faman tsalle a dakin kmr kananun yara..Aysha dake la6e bakin kofa tana kallonsu batasan lokacinda ta fashe da daria ba..yanda suka rungumi juna suna tsalle tsalle sai suka koma mata kaman small kids..wato dai su biyun nan are so something else..dama tunda taga yanda suke kallon kallon tasan kilan space sukeso ta basu and gashi nan ta gani saidai Allah kadai yasan dalilinda yasa suka wnn farin cikin because ba gane language da suke speaking take ba..daria takeyi sosai wanda rabonta da irinshi tun kafin faruwar incident din jiya…Saida suka gama tsalle tsallensu Nur yayi saurin daukan paper da Bobby ya yarda a kasa shima ya karanta..nan take ya wara ido yana sake duban abokin nashi da wani killer smile ya danyi kasa da voice dinshi yanda bazata jiyoshi ba yace”oh my Goodness yanxun five weeks knn da aurenku and the pregnancy is four weeks..what a sharp shooter”..ya karasa mgn yana kashe mashi ido shidai Bobby bai iya cewa komai ba tsabar farin ciki kawai sai ya durkusa ya fara sujood shukur shi kuma Nur ya kama kugu da hannunshi daya..dayan hannun kuma ya dafe forehead dinshi dashi snn ya danyi bending kaman zaiyi ruku’u ya shiga juya waits dinshi yana taka rawa a hankali yana cewa”aga m abu nna..aga m abu nna”..(am going to be a father..am going to be a father)..cikin excitement sosai yake rawa yana waka Kai kace shine za’ayi ma haihuwan..Bobby daya gama sujood dinshi tun daxu dagowa yayi kawai yana kallonshi with a very wide smile..yanda yake rawan ba karamin daria ya bashi ba..da dadewa dama yasan Nur yafi karfin aboki a wurinshi saidai ya kirashi da brother so ko kusa baiyi mamakin wnn farin cikin da yake tayashi ba..shi din mai sonshi ne kuma tsakani da Allah..ya tabbata wnn excitement da yake ciki da za’a bincika zuciarshi za’a ga har cikin ranshi yake tayashi farin cikin..he is one in billion..samun aboki irinshi yana da wahala sosai and shiyasa yake godia wa Allah for having him..soyayyan da suke ma juna genuine ne ba fake ba…Lamido dake bathroom tana kallonsu tayi daria kaman cikinta zai kulle..dukda batasan me sukema wnn farin cikin ba ta tabbata it’s something huge don tunda take bata taba ganinsu cikin such excitement ba..Saida ta gama kallon snn tayi alwalan ta fito daga bathroom din kanta a kasa tana kokarin boye darian dake son sake kufce mata.. Nur daya dage yana dirkar rawa yana ganinta yayi saurin mazewa yana wani shafa kai shi a dole ba kamashi tayi ba…Bobby dake kokarin danne dariar dake cinshi juyawa yayi ya isa gareta kafin ta zauna kan bed ya janyota jikinshi kawai sai ya rungumeta so tight yana sauke numfashi..ta kwalo ido waje tana kokarin kwace kanta sbd presence na Nur amma sam yaki sassauta rikon da yayi mata balle ta samu daman kwacewa din..wani irin farin ciki ya tsinci kanshi a ciki.. right now gani yake dunia babu Wanda ya kaishi farin ciki kaman dai ba shine yake ganin babu wanda ya kaishi shiga kunchi da damuwa a while a go ba..wato Allah ba yanda bayayi da bayinshi a duk lokacin da yaso..idan yaso ya saukar Maka da farin ciki haka idan yaso ya saukar maka baqin ciki.. that’s how life is shiyasa masu iya mgn sukace ba kullum ake kwana a gado ba and it’s true..ba koda yaushe mutum ke dawwama cikin farin ciki ko akasin haka ba..dole watarana za’a jarrabaka da either happiness or sadness saidai Allah ya bamu ikon yadda da qaddara mai kyau da mara kyau…yayinda yake rungume da ita Nur sai ya zaro phone dinshi daga aljihu ya shiga camera ya fara musu video yanajin yanda shi kanshi suka burgeshi sai yaji inama shi da pretty ne haka..at this point sai yaji wani shaukin sonta ya kamashi..yaji inama a bashi ita ya aura koda bata gama secondary din ba amma yasan that can never be possible..Saida Bobby ya dauki lokaci mai tsaho yana rungume da ita yana kuma sake ma Allah godia cikin zuciarshi snn ya raba jikinshi da nata tareda hade goshinshi da nata ya lumshe ido yana sakejin wani extraordinary feeling yana sake bijiro mishi..he missed her like crazy sai kuma abun ya hadu da farin cikin samu karuwa tsakaninsu..he just can’t thank Allah enough for such a blessing..hannu ya sake mikawa ya zagayo waist dinta dashi pulling her more closer to himself snn ya lumshe ido ya manna mata peck a goshinta followed by cheeks da tip of her nose..yana bude ido yaci karo da Nur da har zagayowa yayi ta saitin da faces dinsu zaifi fitowa sosai yana cigaba da recording video din yana sakin murmushi hadda su gyada kai..suna hada Ido yayi saurin saving video din ya wani kashe mashi ido daya yana cewa”ahuru m ihunanya”..(I see love)..murmushi Bobby ya saki tareda gyara mata hijab dinta snn yayi mata side hug yana kallon beautiful face dinta yace”i think we should go home now”..batayi musu ba ta gyada mishi kai alamar ok shi kuma ya sake pecking forehead dinta snn ya kama hannunta suka bar office din Nur na binsu a baya..sallamar driver dinshi yayi yace ya wuce da motar gida su kuma suka shiga motar Nur suka nufi gidan a cikinta..duk yanda Aysha taso ya zauna front seat kin yadda yayi wai saidai ya zauna kusada ita gashi kuma ya kasa dauke ido a kanta daidai da one second..gani yake kaman idan ya rufe idanun za’a tasheshi daga bacci ace dreaming yake..ita dai mamakin wnn sudden change din nashi take don batasan meya sauko dashi daga dokin zuciar da ya hau all of a sudden ba..amma koma menene she’s happy tunda ta dalilinshi ya dena fushi da ita..sai satar kallonshi take tanajin yanda tayi missing dinshi itama..ba dan presence na Nur ba da babu abunda zai hanata mannewa a jikinshi kafin su karasa gida amma bazata iya ba sbd tanajin nauyinshi sosai..gashi kuma suna hada ido dashi sai yayi pecking forehead dinta dan haka tilas ta dena kallon nashi sbd batason wnn abubuwa da yake mata gaban provost wlh..idan shi yana ganin friend dinshi ita fa har yanxun tana mishi kallon gentle provost dinsu mai bala’in kirki da mutunta students dinshi.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128Next page

Leave a Reply

Back to top button