Dr. BOBBY COMPLETE HAUSA NOVEL

Dr. BOBBY COMPLETE HAUSA NOVEL

Da wuri suka fito daga Class din as a result of message data gani na Hammanta yana ce mata sun karaso…suna fitosa ta hango motanshi ai batasan sanda ta taka a guje zuwa wurin ba…Bilkisu ta shiga girgiza kai tana fadin”Allah nunamin randa zaki girma Lamido”…tun kafin ta karasa duk suka bude mota suka fito…Hamman nata ne da Yusra sai kuma Husna mai cewa ko zaizo bazata zo ba…kai tsaye tana isa ta wani d’ane jikinshi tana dariyan farin ciki…shi kuma ya rabata da jikin nashi yace”ke har yanxun bakisan kin girma ba koh?..”daria ta saki tareda dan kwa6e fuska tace”nidai ban wani girma ba”…murmushi kawai yayi ya girgiza kai yasan Maama will never change…ita kuma sai ta juya ta janyo Husna da Yusra ta rungumesu gaba daya kafin ta dago tana cewa Husna”kikace kuma bazaki zoba?..”murguda baki kawai Husna tayi batace komai ba…a daidai lokacin Billy ta karaso garesu aikam Husna na ganinta ta karasa gareta ta wani rungumeta kafin ta dago tace”nima ga yayata nan”…murmushi kawai Billy tayi tareda kama hannun Husna suka karasa ta fara gaida Hamma…bayan sun gama gaisawa tace ya kamata su karasa daga ciki…kaman jira suke kuwa duk suka shiga mota zuwa cikin Hostel…daidai inda ake parking yayi snn suka bude mota suka fito…yace su shiga ciki dasu Husna shi da akwai inda zaije ya dawo…su Aysha hadda wani marairaicewa akace”amma dai Hamma ba dadewa zakayi ba koh?..”ya saki murmushi ganin wnn shagwa6an nata da bai karewa yace”bazan dade ba Maamata…da wuri zan dawo muyi mgnr daya kawoni garin”..nan dai sukayi sallama dashi ya wuce su kuma suka shiga ciki…direct dakinsu Billy ta bude suka shiga Husna tayi wani irin tsalle ta dire akan gadon Billy tana fadin”nima dai ina candy FCNM din nan taku zance daddy ya kawoni…makarantan ba karamin burgeni take ba”…Aysha data kama Yusra suka zauna kan nata bed din tace”ba wani FCNM da zakiyi yarinya…ni kaina yanxu da za’a cireni so nakeyi dan bakisan yanda take ba shiyasa kike sonta”…tace”koma dai ya take Allah Adda ina sonta”…Billy ta fito daga kitchen dauke da lemuka da ruwa sai Cake dasu meatpie ta kawo musu..ta nemi wuri ta zauna kusada Husna tace”to me kukeso a dafa muku?..”Yusra tace”Hamma yace idan ya dawo zai kaimu eatery ko Adda?..”Aysha tace”yes Billy kawai mu bari ya dawo sai ya kaimu muyi lunch dinmu a waje”..Billy tace”to ku fara cin wnn din”..ba musu su hajia Husna aka sauko aka dauki lemo da cake za’a fara sha sai tace”wai ni ina bestynku ne kam?..tunda mukazo banji wata tayi mgnrshi ba”..dan ta6e baki Billy tayi tace”bestynta dai”…Husna na daria tace”aah Adda Billy hadda ke wlh”…tace”God Forbid”…Lamido dake sauraronsu tana daria itama tace”Husna karki damu anjima kadan zaki ganshi a nan indai besty ne…baima san zakuzo ba nasan da tun daxun yazo”…Husna data fara shan lemo da cake dinta tace”ya kamata yaxo mu gaisa dai gaskia…Yusee bazaki ci cake din ba koh?..”Aysha da kanta ta dauki lemo da cake din ta mika mata itama ta amsa ta fara ci.

Karfe daya da wajen rabi Hamman nasu ya dawo…nan ya kirasu a waya duk suka sake shiryawa snn suka fito ya kwashesu suka tafi…basu tsaya iya eatery kadai dan har shopping saida ya kaisu dukda suna ce mishi basu bukatan komai and sun kusa yin hutu Hamma Najeeb bai sauraresu ba saida ya kwasan musu duk wani abu da yasan students kamarsu suna bukata…su Husna kuwa kayan kwadayi sukaita kwasa itada Yusra kaman ba gobe…kan hanyansu na komawa Hostel Husna taga wani sabon cinema a kan zaria road tace”Hamma dama ka shiga damu cinema muyi kallo wlh..kasan inason kallo a cinemas”…shidai baice komai ba sai kai daya girgiza mata…bayan sun koma hostel suka samu wani wuri kaman garden suka zauna su Yusra nata cin kayan da suka siyo shi kuma ya dubi Aysha sosai yace”i hope kin hakura da batun komawa gida koh?..”ta wani rausayar da kai tace”ai nasan daddy bazai yadda ya cireni ba”..yace”good u understand that..yanxu inaso ki zama more careful kan komai da zakiyi..kinga ko a gida dama kinada wnn careless din sai ki jona abu a wuta kice zaki tafi wani wurin ki barshi ko kuma kice kin manta dashi..yanxun da yazo da tsautsayi wuta ya kama dakin fa kinga da gaba daya konewa zakuyi”…tana wani turo baki tace”na dena Hamma”…yace”Good…kema Bilkisu inaso ki kara kisa min ido a kanta sosai…duk kikaga ta jona abu zaka tafi ta barshi ki kira koni ko Ammi ki fada mana”…da sauri Billy tace”inshaAllah Hamma”…daga haka ya mike zuwa mota sai gashi ya dawo da wani da akayi wrapping kaman gift guda biyu…ya mikama Aysha daya itama Billy ya bata daya…Aysha ce ta fara bude nata taga wani hadadden mug fari mai daukeda logon Man United sai wani sbu kaman doll da akayi mishi siffar Pogba yana sanye da kayan ball sai kuma hannunshi rikeda ball din a can kasan abun aka rubuta Man of the Match sai kuma latest jessy dinsu red and black mai daukeda logon Man U itama bayanta kuma sunan Pogba ne da katon number 6 a jikin wandon ma haka…sbd tsabar farin ciki Aysha batasan sanda ta rungumeshi taba daria ba…wnn karon shima rungumeta back yayi yana ganin how happy she looks…dama yasan yanda take son Manchester da Pogba dole ma zataji dadin gift din shiyasa ya siyo mata…saida suka gama hug dinsu snn ya dagota yana kallonta yace”hope u like it”..da sauri tace”i like it mana sosai ma Hamma…kasan tsakanina da Pogba ai”…yace”na sani shiyasa na siyo miki”…tace”nagode sosai Hammana Allah ya saka maka da alkhairi ya baka mata ta gari”…ya dan ja cheeks dinta yana daria yace”Ameen Mamana”…Husna ta hade rai tace”ai dama Hamma munsan zaman da zamuyi dakai…nasan wlh kafi son Adda akanmu”…murmushi kawai yayi yace”Husna kenan”..ya juya ga Billy dake rikeda nata gift din tana kallonsu tana murmushi…yace”if you are done smiling kema saiki bude mana naki mu gani”…ba musu ta dakatar da murmushin da take ta shiga bude nata…komai na ciki iri dayane the only difference shine ita nata na PSG ne madadin Manchester doll din kuma na Mbappe instead of Pogba…sosai murmushin dake fuskanta ya fadada…sai taji itama kanta da d’an uwanta ne ba abunda zai hanata rungumarshi tsabar farin ciki…full of excitement tace”Nagode Hamma Allah ya saka da alkhairi”..yace”Ameen Hajia Bilkisu..yanxu bari muzo mu dauki hanyan kunsan tafiyanmu da nisa”…nan da nan Aysha ta kwa6e fuska tace”Hamma tun yanxu?..”yace”banaso muyo dare ne Maama kuma anjima kadan zakiga Ammi ta fara kira so gara mu tafi sbd mu sauka da wuri”…bata kuma cewa komai ba sai turo baki da tayi…gaba daya suka mike suka fita daga wajen…suna zuwa jikin motanshi kafin su shiga motan Sa’eed ya karaso wurin…yayi parking da sauri ya fito zuwa inda suke yace”Hamma badai tafiya zakuyi ba?..”yace”wlh tafiya zamuyi Sa’eed banaso muyi dare a hanya”..Sa’eed ya juya yana duban su Husna yace”yammata”..tana wani fari da ido tace”sunana Husna Lamido”…yace”to sannu Husna Lamido ya hanya?..”tace”Alhamdulillah Hamma bestie”…ya dan wara ido kafin yace”har yanxu Hamma bestyn nan dai?..”tace”eh mana ba bestie sunanka ba?..”yace”sunana Sa’eed”..ta wani makale kafada tace”oh oh nidai hamma bestie zance”…bai sake mgn ba sai murmushi da yayi…ya karasa wurin Yusra suka gaisa itama tana cewa hamma besty shi kuma yana bayaso…haka dai suka gama gaggaisawa daga nan suka shiga mota suka tafi…Lamido tabi motan nasu da kallo idonta na cikowa da hawaye…Billy ta kwashi gifts dinsu tayi ciki shi kuma Sa’eed ya jata suka zauna yana fadin”haba mana bestie..bakya gajiya da kuka ne?..”ta wani sake tale baki tace”bestie na gaji da makarantan nan wlh..infact am tired of the whole city i want to go home”…murmushi ya saki ganin yanda take mgn sai kace yarinya cikin ranshi yace”gaskia mijin bestie zaisha fama wlh”..a fili kuma sai ya shiga ban baki da bata hakuri har ya samu da kyar ta tsayar da kukan.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128Next page

Leave a Reply

Back to top button