Dr. BOBBY COMPLETE HAUSA NOVEL

Dr. BOBBY COMPLETE HAUSA NOVEL

The next day kasa fitama yayi da wuri sbd tunanin abunda zuwan nashi zai haifar…yadai san a yanda take da shegen rawar kai yanda tayi performing a komai na jiya yau din ma zaiyi wahala idan batayi performing ba..shi kuma baisan meyasa yakejin abunda yakeji ba and Allah ya sani bazai iya kiranta ya hanata ba sbd kar tayi tunanin wani abun daban…da yanada ikon hana kanshi jin abunda yakeji da ya aikata hakan wlh ko don ya samawa kanshi salama amma bayada damar hakan…wnn dalilin yasa bai samu fitowa ba har saida yaga Nur ya fara kiranshi a waya and yasannshi da shegen naci haka zaiyita jera mishi kira idan har ba fitan yayi ba.

Wani daki ne kusada auditorium dinsu inda daya wanda zasuyi performing suke ciki kowa yana karasa shiryawa…cultural dance suka shirya na Hausa,Fulani,igbo da kuma yoruba…and kowa daga cikinsu yana sanye cikin traditional attire na tribe da zaiyi representing…Lamido sarkin rawa zatay participating kusan gaba daya sbd ita koya musu rawar…da farko cewa tayi only Fulani da Yoruba zatayi sai hod na social department dinsu yace tayi participating gaba daya…Hausa Dance shine na farko dan haka koda mc ya kira iya wanda zasuyi hausa dance din ne suka fita daga dakin…as usual itace a gaba tana rikeda sign board kaman najiya saidai shi an rubuta day 2 cultural activities…wata kuma daga cikinsu ta rike wani da aka rubuta Hausa Dancers a jiki…waqa aka sakar musu ta hausa mai dadi yayinda suke shigowa cikin wurin…gaba dayansu suna sanye cikin normal dogon riga na atamparsu iri daya kowacce ta daura dankwalinta babu mai mayafai cikinsu…bayan sun karasa dance floor sun tsaya dj ya samo waqar hausa ta gargajiya yayi playing snn suka fara dancing…yau ma Bobby yana zaune mazauninshi na jiya and gaba daya tunda ya dora idonshi a kanta ya samu gagarumar matsala don komai nashi tsayawa yayi cak banda zafi ba abunda yakeji har cikin heart dinshi…lumshe idanunshi yayi yana salati dan abunda yake jin yaji jiya was nothing compared to what he is feeling right now…ji yake kaman yaje ya dauketa ya fita da ita daga wirin…haka nan yakejin ciwon kallon da mutanen wurin zasuyi mata tana rawa kamar batasan ciwon kanta ba.

Rano✨

Wnn littafin na kudi ne ban yadda wani ko wata ya fitarmin dashi ba…masu buqatan siya zasu tura 300 zuwa 2208991344 Aisha Ahmad Tijjani Zenith Bank…sai a tura evidence of payment via 07063800556.
22
Ranshi bai sake 6aci ba saida yaji yanda gaba daya wurin ya kaure da tafi da sowa ana hailing dinsu..nan take yaji wani abu yazo ya tokare masa wuya…abun bai tsaya haka ba har liki mutanen da akayi inviting suka fara tasowa suna musu…bayan sun gama aka kara tafa musu sosai snn suka fita mc yacigaba da zance kafin next dancers su fito…dakin da suka shirya suka koma nan kuma suka fara arranging next dancers da zasu fita wato Yoruba Dancers…Lamido ce kadai tayi changing dress dinta zuwa na yoruba snn ta shiga cikin sauran suka koma ciki…suma dai da tafi da sowa akayi welcoming dinsu…Dr.Bobby yana zaune sam baiyi mamakin ganinta ba dan yasan dama hakan zai faru saidai bai saniba ko zai iya cigaba da jure abunda yakeji har su gama…yau dai ya rantse kome zai faru sai yayi mata mgn saidai idan taga dama misquoting din nashi he no longer cares..kawai haushi yakeji that gaba daya festival din ma ya fita daga kanshi kuma ya rasa wnn masifa da akan yarinya guda daya yana neman rasa sukuni da nutsuwarshi…suna isa dance floor aka sa musu waqan yoruba suka fara dancing…tafi da sowa kam sun shashi kaman ba gobe ga kuma ruwan kudi da suka samu daga mazauna wajen…lokacin da suka fito zasuyi na igbo Bobby kasa dauke ido yayi a kanta sai yaga kaman duk kayan da ta saka ba wanda yayi mata kyau kamansu…baisan ko don shi ya kasance igbo din ba amma kayan sun amsheta kaman itama igbo din ce…sai yaga kaman idon kowa na wurin a kanta yake sbd kyawunda tayi…bata sake bashi mamaki ba saida suka fara rawar…sunyi kokari matuka kaman dama inyamuran ne su…har yanxu kuma wnn zafin da yakeji yana nan wanda shine yasa gaba daya baya enjoying zaman wurin…Fulani dance shine na karshe and lokacinda suka shigo Bobby baki da hanci ya saki yana kallonta…tunda yake bai ta6a tsaywa ya kalleta irin na yau ba…tayi mishi kyau fiyeda yanda bakinshi zai iya fada..shi baima ta6a ganin kyanta kaman na yau ba tunda ya santa…haka akasa musu waqar fulani sukayi rawa sosai yanda ya kamata…and again an watsa musu naira snn wani babban mutumi dake wurin yayi musu kyautar kudi masu yawa…wani kuma daga cikin baqin shima yace ya bawa Aysha kyautan sabuwan waya Smsung Galaxy…farin ciki sosai takeyi har hakan ya kasa 6oyuwa dan sai murmushi takeyi Bobby kuma kamar bala’i idanunshi suna kanta yana ganin yanda dimples dinta ke fitowa as a result of smile da take…kasa cigaba da zaman wurin yayi kawai ya mike kaman wanda yakeda mutanen 6oye ya fita daga hall din kusan gaba daya mutane suka bishi da kallon mamaki…Nur ne ya mike da sauri yabishi a baya yana dab da shiga office dinshi ya iskeshi yace”Bob are u alright?..lafia naga ka tashi ana taro ko wani abun ya faru ne?..”juyawa yayi a fusace yana kallon Nur din snn ya nunashi yatsa yace”Fuck you”..daga hakaya bude office dinshi ya shiga ciki tareda bugo kofar da karfi…Nur mutuwan tsaye yayi a wurin yana kallonshi da mamaki…to meya sameshi haka?..kodai wani saga ciki guests din yayi mishi abu?..duk kokarinshi na yaga yayi pointing finger kan dalilin tasowarshi daga wurin ya kasa…baiyi yunkurin binshi cikin office dinba kawai ya juya tareda komawa can wurin still yana tunanin abunda akai mishi.

Bobby na shiga office din ya zauna tareda dora kanshi kam table yana sauke numfashi da sauri kaman wanda yayi race…ko kusa baya son wnn sabon al’amari dake kokarin kunnowa cikin rayuwarshi..bayaso sam…baisan kan wane dalili zai dinga jin haka akan yarinyar da bai hada komai da itaba…shi tunda yake ma bai ta6a samun kanshi cikin yanayi irin wnn ba sai yanxu…gaba daya yarinyar nema take ta zame mishi tauraruwa mai wutsiya…ciwo yakeji sosai na raye rayen da taje tayi a bainan nasi..kuma sbd rashin sanin darajar kai ko dan mayafi bata yafa ba ballantana ayi mgnr hijab..gaba daya ya kasa gane wace irin yarinyace ita?..duk sai yaji kaman bai kyautawa babanta daya damka amanarta a hannunshi ba…kaman wanda akama allura ya mike da sauri ya fita daga office din…can inda audit din yake ya nufa yana shiga premises din wurin yaga Billy ta fito daga ciki tana waya tana ganinshi tayi saurin kashe wayan da takeyi tana kallonshi a tsorace…voice dinshi a cunkushe yace mata”where is ur friend?..”da sauri ta nuna auditorium din tana cewa”tana..ciki”…”go and call her”..ya fada hands dinshi zube cikin aljihu…ba musu Billy ta juya da sauri ta koma ciki…can tsakiyar dance floor ta hangota bayan sun gama performance dinsu aka sakar musu kida suka fara rawa gaba dayansu…haka Billy ta kutsa ta cikin mutane zuwa inda take kawai sai ji tayi ta kamo hannunta ta shiga janta…Lamido ta kwace hannunta tana turo baki tace”Billy rawa nakeyi dan Allah”…harara me kyau Billy ta watsa mata before tace”to kicigaba da rawa ai ga Proprietor can yana nemanki”..bata rufe baki ba Aysha ta zaro idanu tana fadin”dan girman Allah da gaske?..”kama hannunta Billy tayi suka fita daga wurin snn tace”Allah da gaske nake..yana can a waje fuskan nan kaman bai ta6a daria ba dan wlh har tsorata nayi dana kalleshi”…nan take hankalin Aysha ya fara tashi tace”na shiga uku meyasa yake nemana kuma?..”Billy tace”indai kinsan bakiyi laifin komai ba ki kwantar da hankalinki..kiyi addu’a kije ki sameshi in Allah ya yadda ba abunda zai miki”…girgiza kai kawai Aysha keyi tace”zo muje ki rakani dan Allah”…Billy ta kwalo idanu waje tana fadin”Ni?…rufamin asiri Lamido in mutu maza su kaini ba mata ba…haka nan inje yayita zazzaro idanun nan nashi yasani sakin fitsari a wando”…dukda tashin hankalin da take ciki saida mgnr Billy ya sata daria…sai kuma ta marairaice fuskanta tace”na shiga uku tsoron zuwa nakeyi wlh…nasan yanxu abu karami yake jira ya hadani da daddy”…Billy tace”ba fada miki inshaAllah ba komai kedai kawai kije kiji mezai fada idan ba so kike ki kara wani laifin ba”…jiki a sanyaye ta gyara mayafinta snn ta fita daga wajen…bata sameshi nan waje ba dan haka ta wuce office dinshi…tana shiga ya dago fuskanshi da yayi murtuk kaman na marasu imani kawai ya mika mata hannunshi murya a cushe yace”bani wayarki”…mika masa wayar tayi da sauri tareda sunkuyar da kanta kasa tana wasa da fingers dinta…shi kuma yana amsan wayan yasa digits dinshi snn yayi dialing…wayanshi dake ajiye kan table dinshi yayi ringing alaman kiran ya shigo snn yayi quitting call din tareda ajiye wayan a kusada nashi…Aysha dai har yanxun kanta na kasa tana kwararo mishi addu’a cikin zuciyarta…tsoronta Allah tsoronta kada ace wani laifin tayi ya kira daddy ya fada masa…shi kuwa kallonta yakeyi yanajin tamkar ya kwada mata mari don haushi..dubi dai yanda ta wani nustu a gabanshi kaman mutumiyar kirki amma dazu taje ta gama bayyanar da jikinta wa mutane suka kalla…ko rantsuwa yayi yasan da kyar babu wanda bata burgeba a cikin wadanda suke wajen…kawai ciwo yakeji that a gaban idonshi abun ya faru and he couldn’t do a thing…cikin muryan daya kusa sanyata fitsari yace”wato ke bakida hankali kou?..sbd bakisan ciwon kanki ba kikaje kina rawa gaban mutane kina musu tallan jikinki kou?..”dan dagowa tayi ta kalleshi kafin ta mayar da kan nata da sauri dan tsoro idanun ma suka bata…saida ta dan marairaice snn tace”tallan jikina kumah?..”a fusace yace”if u dare say another word a wurin saina kwada maki mari…tambayana ma kikeyi sbd bakida kunya kou?..”shiru tayi tana turo baki…yace”well let me call ur Father and tell him all you’ve been doing”..yana karasa mgnr ya dauki phone dinshi dake nan kan table ai batasan time din da ta kama hannun nashi ta rike gam ba sbd tsoro…cikeda tashin hankali tace”Sir dan Muhammadu rasulillahi kar ka kirashi..i beg of u please”..ta karasa mgnr hawaye ba zubowa kan cheeks dinta…Bobby dake kallon yanda ta rike mishi hannun yace”how dare you?..”sakin hannun nashi tayi da sauri tana cewa”am sorry…Sir dan girman Allah ka rufamin asiri karka fada wlh fada zaiyimin”…sake daukan wayan yayi yana searching contact din daddy yace”da kina tsoron fadan ai bazaki aikata abunda ba daidai ba”…wnn karon hannayenta ta hade waje daya in a pleading tone tace”Sir na rantse da Allah ban karawa kayi hakuri plss”…ajiye wayan yayi yana kallonta..dama baida intension din kira yayi haka ne kawai dan ya tsoratata tunda already yasan yanda take tsoron mahaifinta…idonshi a kanta yace”fadamin meyasa bakijin magana?..”tana cigaba da hawaye tace”am sorry”…yace”ba wnn na tambayeki ba..i said meyasa bakyajin mgn?..why kikeda fitina?..”shiru tayi tana goge hawayenta sai can kuma tace”nima ban saniba”…tsaki ya saki tareda daukan wayanta yana mika mata yace”leave my office immediately..and if u like gobema kizo kiyi abunda kikayi yau kiga idan ban sanar dashi ba”..kar6an wayan tayi tana turo baki ta juya ta ta fita daga office din..tana ganinta a waje ta sauke wani ajiyar zuciya a fili ta furta”kuma Allah ya isana wlh..inyamurin banza”…shi kuwa sai daga baya duk haushin kanshi yabi ya kamashi…wai ma ina ruwanshi da rayuwarta ne at the first place…mamakin kanshi yakeyi shi that ya tsani Fulani especially na Gombe amma wai shine har yake kokarin protecting yarinyar da yasan asalin ‘yar Gombe ce?..baisan ko don sbd mutuncin mahaifinta da yake gani bane…abu guda daya sani shine dukda kasancewar babanta bafulatani kuma na Gombe yana matukar ganin kima da darajarshi and shine mutum na farko daya faraji ya kwanta mishi a rai bayan sanin cewa shi din bafulatanin Gombe ne…kilan sbd kyawawan maganganun da yayi kan Dad dinshi ne amma maganan gaskia mutumin yayi mishi dari bisa dari…itama kuma ‘yar tashi yasan sbd mahaifinta yakejin abunda yakeji and nothing more.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128Next page

Leave a Reply

Back to top button