Dr. BOBBY COMPLETE HAUSA NOVEL

Dr. BOBBY COMPLETE HAUSA NOVEL

Washegari har wajen goma bata tashi ba sbd baccin da bata samu tayi sosai ba jiya..Bobby na nan zaune yana kallonta ko nan da can ya kasa matsawa sbd gudun kada ta tashi baya kusa..saida yaga rana ta farayi gashi kuma yau Friday snn ya samu yayi wanka ya shirya kanshi cikin farin shadda da akama dinkin kaftan..yasa hula white sai takalmin kafarshi shima white..bayan ya gama feshe jikinshi da turaruka ya dauki wayarshi ya fita sbd kiran da Nur keta mishi tun daxun..yana fita parlor yayi picking call din yana cewa”yane”..a daya bangaren Nur yace”normal..ya jikinta?..”a hankali yace”gata nan dai wlh..har yanxu tana kwance”.. Nur yace”subhanallah zazza6in dai?..”zaunawa Bobby yayi kan one of kujerun parlon before yace”shine fa..amma dai yanxu naji da sauki sosai..bata samu bacci bane jiya shine yanxun take ramawa”..Nur yace”ohk Allah ya kara sauki..gashi kuma kace yau zatayi baqi koh?..”Bobby na shafa kanshi yace”sun kusa zuwa ma yanxu haka..kana ina yanxu?..”Nur yace”ina shiryawa kafin sallahr jumu’a”.. Bobby yace”alright mu hadu a masallacin nima yanxu zan fito”..yace”alright sai ajima”..shima yace”sai anjima”..daga haka suka aiye waya..Bobby ya sake komawa dakin har lokacin bacci takeyi..ya taba forehead dinta yaji babu zafi sosai sai ya gyara mata kwanciya tareda pecking forehead dinta snn ya dau keys dinshi ya fita zuwa main house..bayan sun gaisa da Mummy yace mata zaije masallaci daga nan zai biya eatery ya siyo ma su Husna abinci tace he shouldn’t buy anything tasa ayi musu girki sbd tasan dama Ayshan ba lafia..godia yayi mata sosai snn ya mata sallama ya fita bayan yace Miemie ta dinga shiga tana duba mashi ita time to time idan ta tashi ta kira ta sanar dashi.

Around 2:17 su Billy suka shigo Kanon Dabo.. Husna ce ta kira Bobby ta sanar dashi karasowarsu yace su karasa gida shima yanxun zasu wuce..kusan a tare motocinsu suka yi parking a compound din gidan..nashi da na Nur sai kuma na Hamma Najeeb da sukazo a ciki..shi ya fara fita ya nufi inda suke sukayi musabiha da Najeeb snn yace su shigo su fara gaisawa da Mummy sai suje inda Aysha..Mummy ta tarbesu da farin ciki sosai suka gaisa tana tambayarsu ya Ammi da daddy suka amsa da suna lafia..bayan Miemie ta gama setting dinning tace suje su fara cin abinci kafin Aysha ta tashi daga bacci sai suje itama su gaisa.

Bayan sun kammala suka nufi gidan nasu gaba daya tareda Najeeb dake sauri ya wuce aikinda ya kawoshi…suna shiga compound Yusra tayi saurin kwace hannunta cikin na Billy ta shiga cikin gidan da gudu tana kiran”Addah..Addah”..da sauri Bobby yabi bayanta gudun kar ta tasheta a bacci..suna shiga parlor yace they should make themselves comfortable shi zaije ta fito musu da ita..Husna ta bishi da kallo tana kunshe daria tace”Allah sarki Uncle Bobby..da gani Adda ba karamin wahalar dashi takeyi ba”..Miemie dake kusa da ita ta dan matsar da kunnenta kusa da nata tace”ke batada lafia”..da sauri Husna ta juya tana kallonta tace”da gaske?..ko ciki ne da ita?..”gyada kai Miemie tayi tana sake yin kasa da murya tace”but don’t tell anybody oo.. Uncle Bobby might slaughter me”..hada ido sukayi suka tafa Billy dai kallonsu kawai take tana mamakin yaushe suka zama kawaye…Bobby na shiga dakin yaga kan gadon wayam dan haka ya bude bathroom da sauri ya shiga sai ya ganta tsaye jikin sink ta zubama mirror idanu tana hawaye..da sauri ya karasa tareda janyota jikinshi hankalinshi har ya fara tashi tace”what?..”goge tears dinta tayi tana girgiza masa kai..rikota yayi ya fito da ita snn ya zaunar da ita gefen bed shima ya zauna yana rikeda hannunta yace”baby menene plss?..akwai inda ke maki ciwo ne?..”girgiza kai ta sakeyi tana cewa”No”..hannu yakai ya karasa goge mata tears din snn yace”kinga su Husna sunzo dan Allah ki bar kukan nan indai baso kike suyi tunanin wani abu ke damunki ba”..kai ta sake gyada mishi without saying anything..shi kuma yayi pecking cheeks dinta snn ya mike yana cewa”let me get u something to wear sai muje parlor ku gaisa dasu”..kallonshi kawai tayi batace komai ba shi kuma ya fita da sauri zuwa bedroom dinta don dauko mata kayan da zatasa..tagumi tayi da both hands dinta tana tunanin abunda ya dameta..lissafi tayi yau kusan 2 weeks knn ya kamata period dinta yazo amma baizo ba sai kuma ga fever ta farayi da amai..dukda ba test tayi ba tanada tabbacin morning sickness take..tasan ciki ne da ita wlh.. musamman data tuna yanda suka rungumi juna suna farin ciki jiya a hospital sai ta sake tabbatar da zarginta..kawai gani takeyi baici ace ta samu ciki yanxu ba..Ina ma laifin tayi ko 6 months ne idan batayi 1 year ba amma wai ciki tun yanxu knn dai haihuwan 9 months din da bataso shi zatayi and Allah kadai yasan what will people say about her..kilan haka za’a zauna ayita gulmarta kaman yanda take zama tayi na mutane itama..ita bawai haihuwan ne bataso ba kawai bataso mutane suce daga yin bikinta ta samu ciki sai kace dama jira take..tayi nisa cikin tunani har batasan time din da ta fara hawaye ba..she knows for sure yasan da mgnr cikin yana sane ya boye mata..bayan few minutes ya dawo da kayan nata a hannunshi..ya taimaka mata tasa snn ya dan gyara mata fuska yanda bazasu gane tayi kuka ba ya kama hannunta suka fita zuwa parlon.

Rano✨

Wnn littafin na kudi ne ban yadda wani ko wata ya fitarmin dashi ba…masu buqatan siya zasu tura 300 zuwa 2208991344 Aisha Ahmad Tijjani Zenith Bank…sai a tura evidence of payment via 07063800556.
67
Hannunta na cikin nashi har suka shigo cikin parlon..tana hada ido dasu Husna batasan sanda ta kwace hannunta daga nashi tayi saurin karasawa inda suke kawai sai ta shiga kokarin daukan Yusra da itama tana ganin nata ta taso cikin farin ciki sosai take cewa”Habibty”..itama Yusra rungumeta tayi tana daria tana kuma jin yanda har yanxu take kokarin dagata amma ta kasa..ta dago tana kallonta tana daria tace”Addah bazaki iya daukana ba yanxu”..da sauri Bobby daya karaso ya zauna kusada Nur yace”tell her”..Aysha tayi pecking forehead dinta snn taja hannunta suka zauna tana cewa”I missed u guys sosai wlh”..itama Yusra zaunawa tayi kusada ita tace”muma munyi missing dinki Addah”..daga haka ta juya tana kallon Billy data wani kura mata ido tana kallonta tace”what?.”Billy tace”aah me kikaji nace?..”dan murmushi ta saki tareda matsawa tayi hugging dinta itama tana cewa”nayi missing dinki”..Husna da tun daxun bakinta ke kaikayi ganin hug din nasu bana kare bane tace”Adda kinga yanda kikayi kyau kuwa..kinyi wani fresh kin canxa”..juyawa Aysha tayi tana kallonta sai kuma ta dungure mata kai tana murmushi tace”idan bakiyi haka ba ai ba sunanki Asma’u Lamido ba”..Husna da har yanxu ke murmushi itama tayi hugging dinta tana cewa tayi missing dinta..Hamma dai na zaune yana kallon wariyar launin fata..saida ta gama da kowa snn ta dawo da kallonta gareshi tana wani murguda baki tace”ba ruwana ni dakai”..daria ya saki tareda juyawa yana kallon Bobby yace”inaga saika lamarin nan Dr..wnn matar taka rikicinta yawa ne dashi wlh”..dan murmushi Bobby ya saki yana kallonta yace”baby C’mon mana..ko me yayi ai yakamata ya wuce tunda har ya taso yazo inda kike”..da sauri Najeeb yace”exactly..kuma bayan zuwa ma har matata na kawo mata da qannena amma still take cewa ba ruwanta dani”..ya karasa mgn yana kashe ma Billy dake kallonshi idanu..tayi saurin kawar da kan nata tana daria..ita bazata iya wnn abun nashi ba..Lamido kuwa tasowa tayi daga inda take ta dawo nan kusa dashi ta zauna tana kallonshi da smile din nan nata dake sa both dimples dinta fitowa tace”to Hamma sannu da zuwa..Ina yini”..juyawa yayi yana kallonta da kyau shima yace”lafia lau my Maama..hope kina lafia”..tace”am fine..ya aiki”.. yace”Alhamdulillah”..juyawa tayi ta kalli Billy da wani dan iskan murmushi snn ta sake dawo kallonta gareshi tace”Ya Billy?..”kallon Billy shima yayi kafin ya dawo da dubanshi gareta yace”aminiyarki ce ai..so Kunfi kusa”..da sauri tace”aah wlh ni Kunfi kusa yanxu”..daria ya saki yana girgiza kanshi yace”yanxun dai tunda na kawo maki su i have to take my leave”..da sauri ta mike tana marairaicewa tace”ko ruwa fa baku sha ba..kuma ni banyi girki ba”..Najeeb yayi relaxing yana cigaba da kallonta yace”kuma gaskia yunwa mukeji”..sake marairaicewa tayi tana kallonshi sai kuma ta juya gasu Billy suma duk tana sunyi wani kalar tausayi Husna hadda cewa”yanxu Adda mu taso gari ya garara tun daga Gombe muzo gidanki amma ko abinci bakiy mana ba..gaskai saina fadawa Ammi”..hankalinta ya sake tashi jin tace zata hadata da Ammi tayi rau rau da ido kmr zatasa kuka tace”ai dai banida lafia”..daga haka ta juya zata nufi kitchen Bobby yayi saurin mikewa ya kamota yana fadin”baby wasa fa suke maki sunci abinci”..dagowa tayi tana kallonshi a hankali tace”da gaske?..”hannu yakai yana goge mata dan guntun hawayen daya gani a Idonta tace”da gaske nake mana..Mummy tasa anyi musu abinci”..rungumeshi tayi da karfi tana sakin murmushi tace”Allah ya sakama Mummy da aljannah”..ya dagota yana jan dogon hancinta yace”Ameen Ameen love”..daga haka ya dawo da ita parlon sai taga duk suna mata daria..samun wuri tayi ta zauna tanata daure dauren fuska shidai Najeeb ya mike yace zai wuce don ana can ana jiranshi..sukayi sallama da Bobby da Nur snn ya fita su kuma suka bishi a baya..har mota suka rakashi suka sakeyi sallama snn suka dawo ciki shi Kuma yaja motar yayi gaba…suna dawowa Nur da gaba daya hankalinshi ke gare Miemie yace”pretty yau ba zuwa gidan aunty knn?..”da sauri Miemie ta dubi Aysha tace”zamuje mana..ko aunty Aysha?..”Lamido da taga yanda Bobby ya wani tsareta da ido yanason yaji amsar da zata bada ta hade ranta itama tareda fadin”eh mana”..tana gama fadan haka ta jasu suka wuce bedroom dinta Bobby yabisu da Ido..suna shiga ciki Nur ya kwashe da wani daria yana cewa”tofa kai saidai kayi hakuri na yan kwanakin nan dan naga alama Lamido tunda ta samu mutanen nan mantawa zatayi dakai”..harara mai kyau Bobby ya watsa mashi yana cewa”do u know ur problem?..”Nur yace”nope”..Bobby yace”dan iska ne kai wlh..kuma a haka kake tunanin zan dauki ‘yata in baka..u better wake up dan idan ba canxa hali kayi ba tsakaninka da Miemie saidai kallo daga nesa”..ya karasa mgn yana wani daure fuska kai kace da gaske yake..shi kuma Nur nan take ya shiga hankalinshi sai ya hau bashi hakuri yana cewa”kaifa matsala na dakai bakasan wasa ba”..kallonshi Bobby yayi yana kokarin sakin dariar dake cinshi yace”inyamurin banza”..yana rufe baki shima Nur yace”Kai kuma bafulatanin banza ba”..gaba daya suka hada baki suka sheke da daria kaman wasu kananun yara..bayan sun gama Nur yayi saurin cewa”yauwa ya mgnr cikin?..did she knows?..”a hankali Bobby yace”anya kuwa?..i don’t think so..kawai nidai addu’a nake koda ta gane kar ta daga hankalinta da yawa”..dafashi Nur yayi ganin kmr abun na damunshi yace”don’t worry bazata damuba inshaAllah..mutum nawa ne ke neman haihuwan basu samu ba so ita da Allah ya bata am sure bazata kasa nuna farin ciki ba”..gyada kai kawai Bobby ya iyayi yana cewa”i hope so”.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128Next page

Leave a Reply

Back to top button