Dr. BOBBY COMPLETE HAUSA NOVEL

Dr. BOBBY COMPLETE HAUSA NOVEL

The next morning da wuri suka gama shiryawa kowa cikin well ironed uniform dinta da dan mini hijab dinsu as usual..kafin su fita daga room dinsu Lamido ta dauki wani pink veil dinta mai dan girma ta yafa akan uniform din nata don tasan idan ma bata sa ba saiya mata mgn..Billy sai daria take mata itama tana rama tsokanarta da taitayi jiya haka su fita daga dakin..kmr kllum yauma school bus dinsu ne ya kwashesu kowa za’ayi dropping nashi hospital da akai posting dinshi..Freedom suka fara zuwa and abun da ya basu mamaki bai wuce ganin su biyu kadai akai posting Freedom din ba dan gaba daya sauran dake cikin bus din ba wanda take a nan…suna fita suka nufi cikin asibitin kai tsaye…office din CNO suka nufa as usual don yayi masu posting sai yace suje office din Dr Bobby yace shi da kanshi zaiyi musu posting bashi ba..wani irin kallon juna sukai suka hada ido suna fita Billy ta sake rushewa da daria..Lamido bata kulata ba har suka isa office dinshi..kafin suyi knocking wani messenger dinshi dake zaune gefe da alaman su yake jira ya tashi ya bude musu office din yana cewa”doctor yace ace ku shiga ciki ku jirashi..sun shiga theater ne tun daxu”..basuyi masa musu ba suka shiga office din Lamido sai binshi takeyi da kallo tana tuna abubuwa a dama da suka faru cikin office din nan nashi..ta tuna ranar farko data fara shigowa office din lokacinda sukaje bikin Aneesa ta bar ward dinsu ba kowa har hakan yayi sanadin rasuwar wata mata..ranar ne ta fara shigowa office dinshi yayita sata aiki snn ya hanata zama for almost 5 hours..ta tuna lokacinda batada lafia ya kawota nan ya dubata sai kuma lokacinda Provost ya kawota sbd yayi fushi da ita..she remembers how he hugged her at that time..how he wrapped her with his hands..batasan lokacinda ta lumshe ido tareda zaunawa nan kujeran dake kusada ita ba..nan take komai daya taba faruwa a office din ya shiga dawo mata daga masu dadi har masaru dadin..ta tuna randa yake cewa bazaiyi posting nata inda takeso ba until she promised to stay far away from doctors da duk wani staff namiji and her reply was”bazan kulasu ba ai dama bana da interest kan doctors da health workers sbd son matansu yayi yawa”..sake lumshe ido tayi tana tuna yanda komai ya faru a office din…bit by bit ta shiga remembering duk wani moment da ta taba spending a office din har zuwa time dinda taji ciwo a kafa..how he treated her..da yanda ya daukota cak tun daga parking space zuwa cikin office din..tayi nisa sosai cikin tunani har batasan wayanta dake cikin bag dinta nata ringing ba saida Billy ta daddage ta kwada mata duka a cinya snn firgigit ta dawo hayyacinta..ta wani hade rai tana kallon Billy yace”wnn wane irin mugunta ne..kinji zafinda naji kuwa?..”murmushi Billy ta saki tana fadin”yi hakuri Ammi keta kiranki tun daxu fa kina can kina tunani”…daukan wayan tayi da sauri taga two missed calls from Ammi dan haka tayi dialing number dinta tana kara wayar a kunne…Ammi na dagawa tace”ina kika shigane naketa kira baki dauka?..”da sauri tace”Ammi ban ganiba wlh..ina kwana”..Ammi tace”lafia lau..ya makarantan”..tace”fine Ammi..yau mukayi reporting asibiti”..Ammi tace”to Allah ya taimaka..dama tuna maki zanyi karki yadda kiyi abunda bashi knn ba..ki nustu ki kama kanki yanxu kinga dai mgnr aure ne tsakaninki da mutumin nan idan kikaje kikayi abunda mutuncinki zai zube a wurinsa ke zakizo daga baya kinajin kunya sbd haka ki kula sosia”..gyada kai takeyi tace”insha Allah Ammi zan kula..i will be a goo girl”..Ammi tace”to Allah yayi albarka..ina Bilkisu?..”tace”gata”..snn ta mika mata wayar..Billy na amsa itama ta gaisheta kafin ta amsa da fadin”so nakd kisamun ido akanta sosai duk kikaga zatayi wani abu daba shknn ba ki kira ki fadamin”..da sauri Billy tace”zanyi haka inshaAllah Ammi”..daga haka sukayi sallama ta mikama ma Aysha wayarta..ta karba tana sake dinke fuska tace”sbd mugunta kika dakeni Billy..kinji zafin da nakeji kuwa”..kallonta Billy keyi tana kunshe daria tace”to Allah baki hakuri nidai”..ta daddage zata fara masifa aka turo kofar office din aka shigo nan take ta hadiye masifar da takeson saukewa tareda kasa da kanta kmr mara gaskia..kamshin perfume dinshi kawai taji ta gane shine don a jikinshi kadai tasan irin wnn kamshin…shigowa cikin office din yayi waya kare a kunnenshi idanuwanshi kuma kyam akanta har ya isa seat dinshi ya zauna..kallonta yacigaba dayi yana sauraron abunda ake fada mai ta wayar banda gyada kai ba abunda yake itadai Lamido tayi wani tsit ko numfashi ma a nutse take daukanshi sbd kada ace tayi ba daidai ba…muryanshi taji yace”abunda zai faru yanxu ki turota tazo ta sameni zuwa anjima sai ik duba maki ita inyaso duk yanda ake ciki i’ll let u know”..shiru ya sakeyi kafin kuma yace”alright sai anjima”..daga haka ya ajiye wayar yana kallon yanda ta dage wasa da fingers dinta kmr ‘yar yarinya..juyawa yayi yana kallon Billy da ido ya tambayeta”what happened to her”..Billy ta bude hannayenta alaman she have no idea..sake juyawa yayi gareta still kanta a kasa Billy ta gaisheshi ya amsa ba tareda ya dauke idon daga kanta ba..”Aysher”..ya kira sunanta a hankali..maimakon ta amsa sai cewa tayi”ina kwana”..komawa yayi yai relaxing kan kujera yana dan rotating dinshi yace”yau bazan amsa gaisuwan nan idan baki dago kin kalleni ba”..sake sunkuyar da kanta tayi tana turo baki..yace”bazaki kalleni ba?..”kin dagowa tayi shi kuma yacigaba da kallonta yana shafa gemu zuwa sajenshi yace”then yau zamu yini office din nan knn”..juyawa yayi ga Billy dake kallon love iya love yace mata”kice ta bude idonta idan baso take mu kwana office din nan ba”..ajiyar zucia Billy ta sauke before saying”Lamido open ur eyes mana”..banza itama tayi mata taki dago kan nata..ganin haka ya juya ga Billy ya sake cewa”ina kikeso ayi posting dinki tunda naga ita zaman office din nawa takeso”..da sauri ta dago idanunta tace”ni ba zaman nan nakeso ba”..yace”then look into my eyes”..shoulder ta makale mashi tace”ni banason kallonsu”..yace”why?..”tace”suna sani jin wani iri”..murmushi kawai ya saki tareda gyara zama yace”to ku fadi inda kukeso ayi posting naku”..da sauri Billy tace”sir ni theater nakeso”..tana rufe baki Lamido tace”nidai bazanjd theatr ba gaskia”..bai sake mgn ba yayi posting Billy theater ta tashi ta tafi..ita kuma yace ta fadi inda takeso yayi posting dinta tace maternity..baiyi musu ba yayi posting dinta can itama ta mike zata tafi yace”banda mgn da maza dan Allah”..kai kawai ta gyada mashi ta fita tana sakin ajiyar zucia..batasan meyasa these days duk take taredashi take jinta kaman a prison ba..hatta numfashinta ba daidai yake tafia ba ta kuma rasa dalilin wnn abu haka..mutuminda ba tun yau ta sanshi ba ta rasa meyasa sai yanxu takejin wnn bala’i a kanshi..shikam da kallo ya bita har ta fita snn ya janyo wasu files dake kan desk dinshi ya fara dubawa yanata zabga murmushi..saida ya gama going through the files snn ya ajiyesu ya fita daga office din zuwa maternity don yin ward round.

Kwanaki nata tafia yayinda Dr Bobby ke gwada mata tsantsar soyayya..gaban kowa nuna mata so yake babu ruwanshi saida ita ya barta dajin kunya..har mamakin yanda baida kunya take wlh..koda yake ba abun mamaki bane idan akayi duba da ya hada jini da inyamurai…kullum ta shigo asibiti sai ta fara zuwa office dinshi don idanma bata je ba shi zuwa yake har inda take ya bata kunya..haka zai ajiye duk wani abu da yakeyi ya tashi ya rakata har maternity tun abun na bata kunya har tazo ta denaji..daga karshe ma hanata bin school bus yayi yasa driver dinshi ke zuwa ya daukosu daga hostel snn ya maidasu idan sun tashi aiki..Lamido tun tana ignoring abunda takeji game dashi har ta fara saduda..soyayyan da yake gwada mai tsayawa a rai ne don kullum ta koma hostel tayita tunaninshi knn har wani lokacin ta tsinci kanta tana murmushi..tana jin dadin yanda yake kulada ita sosai da kuma yanda bai iya 6oye abunda yake feeling gameda ita..duk wanda yayi zama 10 mins dasu saiya fahimci ba dan karamin so yakeyi mata ba…abu daya da watarana yake bata haushi shine kishinshi da yayi yawa..gaba daya yabi ya takureta a asibitin ta yanda ko mgn yaga tanayi da namiji shknn ta shiga uku don saiya mata fada..har mamakin yanda yake daure face dinshi take sai kace bashine ke mata mahaukacin so ba amma kan kishi gaba daya idanunshi rufewa suke..snn ga dokar saka hijab daya kafa mata shima ba karamin takura bane a wurinta amma haka nan ta hakura take sakawa dan ko by mistake ya ganta ba tareda hijab din nan ba sai an samu matsala..a 6angaren Billy da Hammanta kuwa soyayya ce mai karfi suke yinta don yanda suke son juna abun har mamaki yake bata..wani lokaci idan Billy na waya dashi saidai tayi zaune tana kallonta a daidai lokacin sai itama soyayyan da sukayi da Prof ya shiga ya dawo mata..ta tuna itama fa da haka takeyi da saurayinta amma with Proprietor komai ya canxa mata..dukda zuwa yanxu ta rage jik kunyanshi amma har yanxun bata iya sakewa tayi mashi mgnr daya shafi love kmr yanda shi yake mata..bata sani ba ko har yanxu bata fara sonshi bane amma dai ta tabbata ya samar ma kanshi special place a cikin zuciyarta.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128Next page

Leave a Reply

Back to top button