Dr. BOBBY COMPLETE HAUSA NOVEL

Dr. BOBBY COMPLETE HAUSA NOVEL

Suna shiga daki Aysha da Billy suka baje kan gado suna hirar yaushe gamo yayinda su Miemie,Husna da Yusra suka bar musu dakin suka shiga dayan bedroom dinta suma suka dasa nasu labarin..yanda Husna da Miemie suka sake da juna zakayi tunanin tun tasowarsu dama suie qawance while ba haka bane..kawai hali ne yazo daya shiyasa qawancen nasu yayi daidai..har yamma yayi suna nan suna abu daya dan sallah kadai ya tada su shima suna idarwa suka sake dorawa daga inda suka tsaya..magrib na kawo kai jikinta ya fara rufewa da zazza6i wanda a daidai lokacin shima Bobby da suka fita da Nur tun daxun duk hankalinshi ya dawo gareta dan yasan daidai wnn lokacin zazza6in yake rufeta..sallama sukayi da Nur ya dawo gidan da sauri don yanaso yaga halinda take ciki..gashi yinin yau dama duk bataci wani abincin kirki ba..yana shiga ya iske Miemie da Husna sun wani baje a parlor suna labari suna kallo..suna ganinshi kowa ta shiga taitayinta har hada baki sukayi wajen fadin”Uncle Bobby sannu da zuwa”..yana dan murmushi yace”yauwa..Ina Bilkisu da Aysha?..”Husna tace”suna daki.. should i call them?..”yace”eh kice musu suzo”..da sauri ta mike zuwa bedroom din da suke ba’a dauk lokaci ba sai gashi sun dawo tareda su..tun daga nesa yake kallonta yana ganin yanda fuskan nan nata ke a daure yasan abunda ake gudu ya afku..suna karasowa ciki Billy na dan murmushi tace”Sir sannu da zuwa”..yace”yauwa Bilkisu..dama ce muku zanyi u should go get ready we are going out for dinner”..da sauri Miemie tace”Uncle Bobby Mummy tace an gama abinci fa”..kallonta yayi kmr bai gane me tace ba ita kuma ta sake cewa”tun daxu ta kirani tace zata aiko suwaiba ta kawo abincin nan..that ba sai Aunty Aysha tayi girki ba”..ajiyar zucia ya sauke yana gyada kai kafin yayi mgn Billy tace”Sir basai an kawo ba zamuje can muci”..tana rufe baki Husna ma tace”eh zamuje can Uncle Bobby”..kai kawai ya gyada tareda cewa”ohk”..yana kallon Lamido da har yanxu batasa baki cikin mgnr nasu ba..karasawa yayi inda take tsaye ya kama hannunta suka nufi flat dinshi..Husna tabisu da kallo tana murmushi Saida suka shige snn ta dawo da kallonta ga Miemie tana cewa”gaskia kuna ganin love a gidan nan..anya kuwa nima ba inyamurin zan samu in aura ba..naga kaman sunfi hausawa iya soyayya”..tana rufe baki Miemie ta sheke da daria tace”kamar a kunnen Uncle Bobby kika Fadi mgnr nan”..Husna ta wara ido da sauri tana cewa”ki rufamun asiri dan Allah in mutu maza su kaini ba yammata ba”..Billy dai daria ta saki tareda juyawa ta koma bedroom.

Suna shiga ya zauna nan parlor tareda zaunar da ita kusa dashi yana kallonta kmr zaisa mata kuka yace”zazza6in ne koh?..”Kai ta dora a shoulder dinshi tareda gyada mishi kai..a hankali yakai hannu yana shafa kanta yace”kiyi hakuri kinji..zai dena inshaAllah”..lumshe ido kawai tayi hawaye na cikowa cikinsu ta kira sunanshi”partner”..yace”na’am baby”..runtse idon ta sakeyi nan hawayen dake ciki suka silalo ka fuskanta tace”ciki ne dani koh?..”yayi shiru yana kallon spot daya kmr bazai ce komai ba sai can yace”who told u that?..”da sauri tace”i don’t have to wait sai wani ya fadamun..i noticed some changes a tareda ni and koda banyi test ba na tabbata am pregnant..morning sickness nakeyi”..ta karasa mgn tana rushewa da kuka..da sauri ya juya tareda rungume gaba daya a jikinshi yana patting bayanta yace”stop crying plss”..batace mishi komai ba saida ta gama kuka iya son ranta snn ta sake dagowa tana goge tears dinta tace”kasan ciki ne dani koh?..”yayi mata shiru kawai dan baisan me zaice ba..ta shiga gyada kai tana cewa”ko baka fada ba nasan u knew it all along..ai jiya Ina kallon yanda kuke murna kai da Provost bayan an kawo result”..kallonta yakeyi har yanxu ya kasa cewa komai..saida ya bari ta gama mitarta tsaf snn ya mikar da ita tsaye yana cewa”now u need to stop talking..muje kici abinci sai kisha magani before fevern naki yayi yawa”..batace mishi komai ba itama tabishi suka fita daga dakin..gaba daya suka fita tareda su Billy zuwa main house tunda sunce a can zasuyi dinner…Mummy na ganinsu ta tarbesu da fara’a snn tace su karasa dinning ga abincin can..duk suka isa suka zazzauna Miemie na kokarin serving Husna tace a barta tayi..ba musu kuwa suka barta duk tayi serving din nasu suka fara ci shidai Bobby na tsaye kusada Aysha yana kallon yanda take ta faman jujjuya abincin ta kasa kaiwa bakinta..kujera dake kusada ita ya janyo ya zauna yana kallonta kmr zaisa kuka yace”eat mana baby”..kallonshi tayi a hankali sai kuma ta girgiza kai tace”bashi nakeso ba”..matsawa yayi kusada ita sosai tareda kama hannunta yace”then me kikeso?..”ta juya ta kalli su Billy taga duk hankalinsu naga abincin da sukeci snn ta dawo da idanunta gareshi tana wani hade rai tace”Custard zansha”..ya dan marairaice mata yace”amma baby custard kadai bazai rikeki ba tunda duk yau bakici abinci sosai ba”..kallonshi ta danyi yanda taga duk ya tashi hankalinshi sai ya bata tausayi dan haka ta sake janyo plate din abincin tana jujjuyawa tace”to zan faracin wnn idan mun koma sai insha custard din”.. kanshi ya shiga gyada mata yana murmushi sosai yace mata”yauwa partner”..ta saki dan smile snn ta shiga cin abincin a hankali shi kuma yana aikin kallonta..ganin shi baida niyyar cin abincin ta juya tana dubanshi tace”kai bazaka ci ba?..”hannunta ya kama ya rike idanunshi a kanta yace”ni ke nakeso kici..banso kina zama da yunwa”..murmushi ta Kara saki snn ta maida plate din nan tsakiyarsu tasa mashi spoon tana cewa”to muci wnn din tare”..murmushin shima ya saki bayan yayi pecking hannunta snn ya dauki spoon ya shiga cin abincin shima..daurewa kawai take tana turawa amma ko kadan batajin dadinshi a bakinta..bayan sun kammala suka dawo parlor inda Mummy ke zaune tana jiransu suka dan taba hira bayan sunyi sallahn isha yace su mike su koma gida..Husna dai tace”Uncle Bobby nidai zan kwana a nan tareda Miemie”..Bobby na murmushi yace”to Mummy kinada baqi knn”..Mummy tace”aikam kin kyauta Asma’u dan da baki Fadi haka ba nasan ita kanta Miemien cewa zatayi a can zata kwana”..Aysha dai kunyarta takeji yasa ta kasa cewa komai..bayan sun mata sallama suka koma gidan tareda Billy da Yusra..duk yanda taso ya bari taje inda su Billy hanata yayi sbd fever dake sake sauko mata..dole tayi sallama dasu ta dawo dakinshi inda yake nan zaune yana jiranta…custard din da tace tanaso yaje ya dama ya kawo mata tasha sosai snn ya rage mata kayan jikinta suka kwanta..can dare ta tashi tana ta kwarara amai don kaf abincin da taci saida ta amayar dashi..duk hankalinshi ya tashi haka ya gyara wurin tsaf snn yayi mata wanka ya dawo da ita ya kwantar a kan gadon tanata faman kuka kmr karamar yarinya..hankalinshi yakai kololuwar tashi gaba daya ya rasa inda zaisa kanshi yaji dadi..da dadewa dama yasan zaisha fama da ita musamman daya fuskanci dan banzan raki ne da ita..dan ciwo karami da bai taka Kara ya karya bama langwai take mashi balle laulayi da kowa yasan yanda yake da cin rai musamman daya kasance shi ba wani specific magani yake dashi ba dole saidai mutum yayi hakuri har lokacin tafiarshi yayi..duk yanda yaso ko black tea ne tasha kasa Sha tayi wai idan tasha zatayi amai haka nan ya hakura ya kyaleta bayan ta gama kukan bacci yayi gaba da ita.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128Next page

Leave a Reply

Back to top button