Dr. BOBBY COMPLETE HAUSA NOVEL

Dr. BOBBY COMPLETE HAUSA NOVEL

Lamido’s Palace…

Da sauri ta fito daga dakinsu daga ita sai dan towel a jikinta ta shigo parlonsu da akayi decorating dinshi da flowers da baloons kmr dai wani shagali za’ayi a ciki…duba takai zuwa ga wasu set of baloons masu kyau da aka jerasu daga can saman wall din dakin an rubuta Happy Birthday Aysha a jikin baloons din batasan time din da ta saki murmushi tana karema decor din parlon kallo ba…abun ya karamin kayatar da ita yayi ba tun ma ba’a fara celebration din ba..rabonta da celebrating birthday tunda ta cika 15 sai yau kuma data cika 20 ta samu ta lalla6a Ammi da kyar ta amince mata tayi bayan ta gama kafa mata dokoki iri iri…Billy ce ta fito daga dakin nasu ta shiga duban Aysha daketa kallon decorations din parlon tana sakin murmushi tace”ikon Allah..yanxu Lamido bazaki zo ki shirya ba sai mutane sun cika gidan knn?..”juyawa tayi da sauri tana cigaba da murmushinta tace”Billy bazaki gane farin cikin da nake ciki bane..wai nice nake cika 20 years yau din nan..oh Allah Alhamdulillah”..tsaki Billy ta saki tana harararta tace”wlh da Ammi zan hadaki idan baki wuce kin fara shiryawa ba..yanzun mukayi waya da Sa’eed yace har sun kar6o cakes din suna hanyan dawowa fa”..juyawa tayi da sauri ta koma dakin tana cigaba da sakin murmushi kmr ta6a66iya…da kallo Billy ta bita itama tana murmushi cikin zuciyarta tace”Allah dai ya nunamin ranar da zaki girma Lamido”..daga haka itama ta koma dakin suka fara shiryawa.

Karfe hudu da rabi ta gama shirinta cikin straight gown na wani black material sai walwali yakeyi tasa red turban a kanta gashin nan da yasha uban gyara yana kwance luf luf kmr na balarabiya..light make up da tayi applying ba karamin sake fito da kyawunta yayi ba..su Billy da sauran cousins dinta kuwa straight gown suma sukayi na wani red material kowa tasa black turban akai…Husna ce ta shigo cikin irin kayansu itama tasha kyau kmr babu gobe tace”Addah dan Allah kuyi sauri ku fito mutane sun fara zuwa fa”..hannun Aysha dake tsaye gaban madubi sai kalkale takeyi Billy ta kama tana fadin”zo muje dan Allah keda bakya gajia da kallon madubi”..binsu tayi suka fita daga dakin tana kokarin kwace hannunta…parlon yana nan cikeda cousins dinta mata wanda yawanci mates dinta ne sai mates din Husna suma duk suna sanye cikin nasu kayan iri daya dasu Husna suna ganinta suka hada baki suna fadin”happy birthday to you Lamido”..karasowa tayi cikin parlon tana kallonsu da murmushi tama kasa cewa komai…kowa sai yaba irin kyau da tayi yake kafin a fara tace Husna taje ta shigo mata da besty ciki…ba musu kuwa ta juya ta fita kmr dama jira take..jikin motarshi ta sameshi yanata danna wayarshi ta dan daga murya yanda zai jiyota tace”Hamma besty Adda tace wai ka shigo ciki”..maida wayarshi yayi aljihu yana murmushi ya shiga takawa zuwa inda take yana cewa”bazaki dena Hamma bestyn nan ba koh Husna Lamido?..”dan murmushi ta saki tace”to yi hakuri na dena fada..Hamma Sa’eed”..wani murmushin ya kara saki kafin yace”yauwa yanxu kikayi mgn”..daga haka suka shiga cikin parlon..daidai lokacinda Hamma Najeeb shima ya gama shiryawarashi ya fito suka karasa ciki a tare..can dinning suka nufa suka zauna yanda zasuna ganin duk abunda sukeyi daga nan wurin…Billy da Lamido suka karasa kusada table da aka cikashi da manya manyan cakes dinta guda biyu da snacks da drinks kala kala suka tsaya..kafin ta yanka cake din ta dago tana duban su Sa’eed dake dinning ta wani turo baki abunka da an riga an saba tace”Hamma to ku karaso a yanka cake din mana”…ba musu suka taso zuwa wurinda take..Hamma ya tsaya right hand dinta dasu Husna gefenshi..Sa’eed kuma ya tsaya left hand dinta sai Billy gefenshi..gaba daya sukayi extending hands dinsu bayan anyi counting to three suka shiga yanka cake sauran occupants din wurin nata singing mata”happy birthday to u..happy birthday to u..happy birthday dear Aysha..happy birthday to u”..tana gama yanka cake din ta dauko ta sama Hamma a baki tareda Husna da Yusra snn ta sake daukan wani ta sama Billy da besty suma duk a bakinsu..masu daukan pictures da videos nata yi daga nan kuma duk akabi aka shashshafa ma kowa cake din a fuska bayan duk ta basu sunci sai kuma aka cigaba da hotuna…Sa’eed sai so yake ya samu ya fita amma ta hanashi..yana juyawa zatace”besty dan dawo a daukemu da wance”..haka nan ya hakura har aka gama pics din snn suka koma dinning shida Hamma suka zauna…Husna da Billy ne sukaje sukayi mgn da Ammi wai tazo suyi pictures..saida suka hadata da Allah annabi snn ta yadda ta fito akayi nusu pictures din Lamido sai wani rungumarta take Ammi ta danyi kasa da murya yanda ita kadai zataji abunda take fada tace”zakici ubanki ne wlh..kici gaba da rungumana kmr wata sa’ar wasanki”..batasan lokacinda ta kwashe da daria ba…Ammi ta sake cewa”zanyi maganinki”..haka dai sukaita rungumarta suna daukan hotuna har Sa’eed saida Lamido ta kira wai yazo ayi musu hoto da Ammi..ba musu ya taso akayi musu…ana gama pictures din Ammi tayi komawarta daki su kuma suka kunna home theater suka sa kida suka fara dancing abunsu..ko ban fada ba nasan kunsan mutumiyarku gwanar rawa ce dan haka ta gyagije tanata dirkar rawa sauran suna tayata…a takaice babu kalan waqar da basuyi rawanshi ba..anyi naija anyi na hausa musamman Ado Gwanja Fav din nata..basu tashi daga partyn ba sai wajen magrib…nan cousins dinta duk suka watse bayan sun cikata da gifts iri iri..ya rage daga ita sai su Husna sai Billy da besty sai kuma Hamma…sallah suka farayi snn suka zauna suna duba gifts din data samu..Hamma da Sa’eed da suka dawo daga masjid kowa yayi presenting nashi gift din ta karba tana godia…na Hamm ta fara budewa latest jessy ne manchester da baby doll na pogba..sbd tsabar farin ciki batasan lokacinda taje ta rungumeshi ba..bayan ta dawo ta bude na besty shi kuma taga wani hand band mai kyau red color am rubuta besty a jiki..sai locket mai shape din heart shima an rubuta besty a jiki sai kuma wani hadadden diary da pen a jikinshi shima yana daukeda sunan besty…farin cikinta kasa boyuwa yayi sai kallonshi kawai takeyi kaman wata sokuwa..motsi daya biyu zatace”besty nagode sosai”..shi har saida ya gaji da godiyan nata ma wlh…kafin suyi dinner Hamma yaje ya roki Ammi kan yanaso ya fita dasu suyi dinner a waje idan ta amince knn..tace ba damuwa suje amma kada su dade…yana zuwa yace musu duk suje su shirya they are going out for dinner yanxun…ba Lamido kadai ba hatta Billy dasu Husna murna sukeyi…nan da nan kuwa sukaje suka sake shiri kowa ta fito suka fita compound.. Lamido da Husna suka shiga motan besty Billy da yusra kuma suka shiga na Hamma..haka suka fita daga gidan kai tsaye Hamma ya wuce dasu Blue lounge and resto…kai tsaye vip section suka shiga aka kawo musu menu kowa yayi ordern abunda yakeso…bayan few minutes aka kawo musu abunda sukayi order nan kuma suka fara ci suna dan taba hira…Husna ce ke basu labarin wani classmate dinta da yake sonta wai kullum itada friends dinta sai sun sashi ya kawosu nan wurin sunci abinci ko kuma yazo ya musu takeaway sai daria suke suna jinjina wulakancin Husna…a daidai wnn lokacin kuma Bobby suka shigo wurin tareda wani cousin dinshi daya dage kan lallai sai ya rakoshi yaci abinci…wani irin 6acin rai da faduwar gaba yaji sun riskeshi at once sakamakon tozali da yayi da ita tana zaune a tsakiyar maza tana cin abinci kuma tana daria…ranshi ba karamin baci yayi ba..wai yarinyar nan wace iri ce ita?..karasawa yayi ya samu table daga nan bayansu ya zauna yayinda cousin dinshi da sukazo tare ya shiga ciki wurin wani friend dinshi…daga nan inda yake yana iya hango gashin kanta dake waje..runtse ido yayi ya rasa dalilinda yasa batada burinda ya wuce tayi kwalliya ta fito da gashi..sam baisan wace irin fitinanniya bace ita…kamar ance ta juyo yaga ta mike daga seat din da sauri tana rikeda wayarta tazo ta wuce ta inda yake zaune tana amsa waya…riga da skirt ne a jikinta wnn karon ta daura dankwali amma mayafin nata akai ta dorashi dukda cewa ba mai girma bane..kallon yanda each and every part of jikinta ke moving as a resulf saurin da take yayi…wani irin zafi yakeji na fitowa da tayi a haka..yanxu yasan kaf mazan dake wurin nan ba wanda bai kalleta ba haka suma wanda take tare dasu kilan har taba jikin nata ma sunyi…tunanin haka yasa kanshi yai wani mugun sarawa da bai shirya masa ba…juyawa yayi ya kallesu yaga hankalinsu ba kanta yake ba snn yasake dubawa da kyau yaga kowa harkan gabanshi yake dan haka ya mike daga inda yake a hankali ya karasa inda take kawai saiji tayi an fizge wayar dake hannunta an jata da wani irin karfi an fitar da ita daga wurin…daddagewa tayi zata kwada ihu yayi saurin toshe bakinta da hannunshi..da yaga tana neman 6ata mishi lokaci ya wani hade rai ya zuba mata idanunshi da yasan dole su ladabtar da ita..lokaci daya ta hadiye wani yawu kafin yacigaba da janya har zuwa inda motarshi..budewa yayi ya zurata ciki snn shima ya zagaya ya shiga tareda locking kofar daga ciki…cikin tsananin tashin hankali ta sake bude baki zata kurma ihu yayi azamar janyota ya matseta a jikinshi yana kallon cikin idanunta…wara idon tayi sosai tana kallonshi tana mamakin me ya kawoshi Gombe kuma..kodai aljani tayi gamo dashi ne?..nan hankalinta ya sake tashi ta shiga zubda hawaye tana”wa innahu sulaimanu wa innahu…”kasa karasawa tayi saboda kallon da ya tsareta dashi…tabbas shine ba aljani bane don duk dunia babu wanda idan ya kalleta takejin irin haka sai shi..amma meya kawoshi Gombe?..bude baki tayi zatai mgn ya dora finger dinshi akan bakin tareda hade fuskanshi da nata cikin wata irin dacin murya yace”ke har yanxu bakida hankali bakisan ciwon kanki ba koh?..”lamgabewa tayi tana kallonshi a hankali tace”sir ms nayi?..”harara ya watsa mata mai kyau kafin ya nuna jikinta yace”take a look at yourself..ke ko kunya bakiji ba kika fito haka kuma tareda maza”..girgiza mishi kai tayi kafin tace”sir it’s my birthday today shine amma ya fito damu muyi dinner amma ni ba haka nake fitowa ba”..kallonta yayi ya danyi yayi shiru jin tace its her birthday..wato tsanar da tayi mishi har yakai da zatayi birthday bata fada mashi ba..kawai sai yaji ranshi ya sake 6aci..nan take ya kuma daure fuska ya bude mata kofa murya cunkushe yace”fita”..kallonshi tayi da mamaki jik abunda ya fada..ta dan rausayar da kai tace”nifa..”bai bari ta karasa ba ya sake nuna mata kofar da har yanxun ke bude yace mata”ki fitamun a mota nace”..kin gita tayi kawai ta tsaya tana kallonshi..kallon nata shima yayi for like 2 mins kafin ya dauke idonshi..ta sauke numfashi kafin a hankali tace”am sorry”..juyowa yayi yana dubanta yace”for?..”tace”for everything..am sorry for everything plss”..kai ya gayada mata kafin ya sske pointing mata kofa yace”naji..now kije..ki tafi kawai bana son ganinki anymore”..idanu ta wara taa kallonshi da mamaki shi kuma ya sake hade rai ya juyar da kanshi gefe..ba yanda ta iya haka ta bude motar ta fita duk sai bataji dadin yanda yayi treating dinta ba..does this mean ya dena sonta?..aikam indai yanda yake nuna yana sonta da gaske bai isa yace ya dena sonta yanxun ba..dole ma tasan yana sonta walakancin ne kawai ya motsa mashi..kallonshi tayi ya lumshe ido tareda jingina kanshi da kujera..yanda ya rufe ido sai lashes dinshi suka kwanta kasan idon nashi kmr na mace…lips dinshi dake nan very thick ta kalla sai kuma idanunshi dake sata nutsuwa ko bata shirya ba…kyau na musamman taga yayi mata dama kuma tasan shi din mai kyau ne amma yau sai taga kaman karo mishi kyawun akayi…runtse idonta tayi da sauri cikin raunin murya ta kuma tace”sir am sorry plss”..bude idanunshi yayi a hankali jin yanda voice dinta ke cracking har yanxun face dinshi daure yace”i said babu laifin da kikamin..ko bakida kunne ne?..”a razane take kallonshi cikin tsananin mamaki..gaba daya sai taga ya birkice ya dawo mata asalin proprietor data sani mara mutunchi..ba shiri ta sauka daga motar tana cigaba da mamakin wnn masifa da yayi mata..duk yau sai bataji dadin sudden change din nashi ba..knn dai tafiso yayita chasing dinta tana walakantashi idan ba haka ba why zataji ba dadi sbd yayi mata abunda dama ba yanxun ya fara ba..masifa dai tun daya fara ganinta yake zazzaga mata shi don haka zuwa yanxu ya kamata ta saba amma sai taga wani daban tunda ta mance when last ya mata wnn bala’in nashi..haka tana tafe tana tunani har ta koma inda ta baro.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128Next page

Leave a Reply

Back to top button