Dr. BOBBY COMPLETE HAUSA NOVEL

Wata qanwar daddy ce tazo har gidan da suke ta shiga da ita bathroom bayan ta hada mata ruwan wanka full of turaruka tace tayi maza tayi wanka ta fito…tana kuka sosai ta shiga tayo wankan ta fito daidai lokacin kuma Aunty Fiddausi ta kawo mata kayan da zata saka suma bayan an gama turarasu..har zuwa lokacin bata bar kuka ba haka suka hada kai suka gama shiryawa tsaf qanwar daddy mai suna Aunty Amina ta nada mata farin laffaya daya amshi jikinta sosai..daga nan kuma suka kama hannunta suka fita tareda some of friends da cousins dinta da za’a tafi kai amaryan dasu…gidansu aka fara kaita daddy da Ammi sukayi mata nasiha sosai tareda yi mata fatan samun dawwamammen farin ciki a gidan aurenta..daga haka daddy yace su kaita wajen Lamido..Aysha dake kuka wiwi zuwa tayi ta rungume Ammi tana Kara sakin wani kukan kmr dai mutuwa zatayi ta barsu..duk karfin hali irin na Ammi saida ta zubda hawaye itama..ko Allah yasan ba karamin kewar ‘yarta zatayi ba amma ya zasuyi?..haka gadonmu yake domin kowacce mace saita dandani wnn zafin na rabuwa da iyaye yayin da zata tafi dakin miji..har su Husna da Yusra kuka suke sosai Billy na tayasu..abun sai ya zama kmr a gidan mutuwa ba gidan biki ba..Saida daddy yayi da gaske snn suka iya 6an6areta daga jikin Ammi sukayi gidan Lamido da ita..ko cikin mota bata dena kuka ba har suka isa gidan Lamido..nan ma cike yake da uncles dinta haka suka dangana da ita har kusa da Lamido snn suma suka zauna..nasiha ya shiga mata shima sosai duk kan zaman aure da rayuwar gidan miji..bayan ya gama wasu daga cikin uncles dinta suma sukayi nasu daga nan kuma aka sake daukanta zuwa wajen wadanda sukazo daukanta suke..tana kuka sosai aka bude back seat ta shiga ciki tareda aunty Fiddausi da Aunty Amina da suka sanyata a tsakiya Billy kuma na front seat driver ya tada motar suka tafi..da akwai wasu motocin guda biyu daya na cousins dinta da wasu daga friends dinta dayan kuma duk yan uwan daddy da Ammi ne zasuje sbd event din da za’ayi a can Kano.
Gidan Waziri aka fara kaita nan ma Waziri ya hadasu tareda Bobbyn yayi musu nasiha sosai daga nan kuma kai tsaye suka wuce Kano don su Mummy already sun dauki hanya tun daxun..shima Bobby daga nan gidan suka shiga motocinsu suka tafi tareda zugar abokai da coworkers dinshi..ko a hanya duk tunaninshi ya koma kanta ne..yanda yaga take kuka daxun abun ba karamin daga hankalinshi yayi ba..wai shi wnn kukan dole ne sai anyishi ko kuwa nata ne dai ya wuce gona da iri?..duk hankalinshi yaji ya koma gareta so yake kawai yaji dalilin wnn uban kukan da take.
Karfe biyar da wasu minutes suka shigo garin Kano..har zuwa yanxun amarya Aysha bata dena kuka ba..face dinta har ya kumbura eyes dinta sunyi jajir sbd kukan da taci…direct gidan su Bobby aka wuce da ita inda su Mummy da suka rigasu sauka sun shirya tsaf domin welcoming amarya..ana shigo da ita wasu sisters din Mummy guda biyu suka mike tareda kama hannunta har zuwa parlon Mummy..nan ma yana cike da mutane wanda yawancinsu duk yan uwan Mummy ne da qawayenta..bedroom suka wuce da ita tareda sauran mutanen da sukazo tare…nan da nan sai bedroom din ta cika taf da mutane masu son ganin amarya..saida suka gama turereniyarsu snn aunty sumy ta kwashi su Aunty Fiddausi da sauran wanda sukazo tareda zuwa flat dinta da akayi musu masauki a can..ita kuma amarya sai aka barta tareda Billy da Walida a flat din Mummy..suna fita Billy ta matsa kusada ita tareda bude fuskanta dake rufe da lafayan jikinta..fuskan taga ya kumbura suntum likewise eyes dinta sbd tsabar kuka..dan langabewa tayi tana kallonta tace”yanxu Lamido bazaki dena wnn kukan ba?..haka kikeso kije wurin event din fuska a kumbure?..”banza Aysha tayi da ita tanajin kmr ta Kara sakin wani kukan..bazasu gane ba ita kadai tasan what she’s going through right now..ji take kmr tace itadai ta fasa a maidata gaban iyayenta amma akace it’s too late to cry when the head is cut off…matsowa walida tayi kusa dasu tace”ki rabu da ita Billy kilan so take mijin nata idan ya ganta yace batayi mishi kyau ba da kumburarren fuska”..wani harara ta maka mata kmr ba itace ke kuka a while ago ba nan take Billy da Walida suka hada ido tareda kwashewa da daria..ringing din wayar Billy ne ya dawo dasu hayyacinsu..tana ganin wanda ke kira tayi daurin dauka tana sakin wani murmushi tace”ango ango ango”..murmushi Bobby ya saki on the other side yana shafa gashin kanshi yace”pls are u together with her?..i have been calling her bata answering kuma i really want to know how she’s doing..is she still crying?..”murmushi Billy ta Kara saki tana kallon Lamido data wani lafe kan gado tana sauke ajiyar zucia tace”Sir taki dena kukan nan har yanxu wlh..tun daga Gombe take abu daya gashi har munzo Kano bata dena ba..bakaga yanda face da eyes dinta suka kumbura ba”..lumshe Ido Bobby yayi yana sauraron abunda take cewa before yace”u mean har yanxu kuka takeyi?..”Billy tace”kuka takeyi wlh..gashi anjima kadan za’ayi wani event din kaga ai bai kamata aga face din amarya kumbure ba”..yace”ohk ki bata wayan idan kuna tare”..ba musu Billy ta mika mata wayan tana cewa”mijinki”..amsan wayan tayi ta Kara a kunnenta ba tareda tace komai ba..Bobby da yaji saukar breathe dinta cikin wayan yasan ta kar6a mgn ne kawai baza tayi mishi ba..murya can kasa yace mata”so kin dena kaunata right?..”girgiza kanta tayi tana wani turo baki tace”No”..yace”then why are u still crying?..bakiso hankalina ya kwanta ne?..”nan ma kai ta sake girgiza mishi hawayen na sake ciko idanunta tace”kawai am missing home..Ina missing Ammi da kowa da kowa”..a hankali ya sake cewa”I know baby..nasan da ciwo amma try not to cry again please!..for me”gyada kai ta shiga yi kmr yana ganinta tace”na dena”..ya dan saki murmushi before saying”to nagode love..i can’t wait to…”bata bari ya karasa ba Kitt ta kashe wayar tareda mikawa Billy tana wani turo baki..tun kafin ya karasa dama tasan me zai fada so bazata tsaya ta saurareshi ba..shi baisan halinda take ciki bane da zai dinga damunta da irin wnn maganganun.
Suna idar da sallahn isha’i aka shiryata cikin traditional Igbo attire daya matukar amsanta..shima Bobby shiryawa yayi cikin igbo attire sak irin nata..kyawunshi sai ya Kara fitowa sosai cikin kayan Aysha daketa kallonshi ta kasan idonta sai taga kaman bashi ba..ya koma mata inyamurin Proprietor dinsu sak masifaffen nan mai shegen takura mata…shima a nashi 6angaren yana dora idanunshi a kanta yaji komai nashi ya kwance..he was like Tabarakallah MashaAllah Alhamdulillah..gani yake duk dunia ba namijin daya kaishi dacewa da auran mace kyakykyawa kamarta..she is the real definition of beauty..yanxun kuma daya ganta cikin wnn dress sai yaji kaman yaje ya dauketa yayita juyi da ita sbd farin ciki..she looks so cute..so takeaway kmr yanda itama take ganin yama fita yin kyau…a nan compound din gidansu za’ayi dakeda haske sosai za’ayi event din don yanda wurin yakeda haske tamkar ba dare ba…anyi decorating wurin komai irin na inyamurai haka kuma duk jama’a dake wurin sanye suke cikin igbo wrapper da akayi ma dinkin boubou da zani kowa ta daura zanin kan riga bayan an dageshi can sama kmr dai yanda inyamuran na asali sukeyi..su Mummy Kalan nasu daban itada sauran manyan wajen dasu aunty sumy yayinda su kuma su Billy,Miemie,Husna,Yusra,Ilham,walida da duk sauran Yara da yammatan dake wurin suma nasu iri daya ne..a takaice duk wanda yazo Sai an bashi irin wnn dress yasaka snn zai shigo wurin..suma su Nur suna sanye da nasu kayan duk na inyamurai sun sanya ango a tsakiya…wata cousin din Mummy ce tazo ta kama hannun ango zuwa inda aka tsayar da Aysha don a tare akeso su shigo filin…tana zuwa ta kama hannunta ta saka cikin nashi snn tayi mishi rada a kunne taja baya tana kallonsu…zame hannunshi yayi daga cikin nata a hankali tareda zagayawa da hannun zuwa wait dinta ya tallafota a jikinshi sosai snn suka shiga takawa a hankali zuwa cikin filin…kida sosai aka sakar musu yayinda occupants din wurin keta tafa musu don abun ya burgesu ne sosai…Aysha da takejinta uncomfortable sbd kama waist dinta da yayi a hankali takai hannu zata cire hannun nashi daga jikinta shi kuma ya sake matse waist din nata yanda ba yanda zatayi ta zame hannun ba tareda mutane sun lura ba..dan bata rai tayi kanta a kasa tace mishi”partner let go mana.. people are watching”..murmushi ya saki mai kyau tareda Dan matsar da bakinshi saitin ears dinta yanda zata jishi sbd tsayi daya fita sosai yace”let the people watch mana ai it’s not haraam..besides haka al’adan event din yake..dolene groom yayi holding bride dinshi to himself idan ba haka ba za’a ce he’s not romantic ni kuma nasan am super romantic so bazan yadda mutane suyimin kallon am not romantic ba”..dan daga kai tayi ta kalleshi tana mishi puppy eyes shi kuma ya lumshe Ido tareda pecking eyes din nata aikuwa mutane suka kaure da ihu da tafi abun ya burgesu..su aunty Fiddausi da sauran yan uwan Aysha dai abun har kunya ma ya basu while yan uwan Ammi inyamurai abun ya kayatar dasu sosai..su a wurin su wnn ba wani abu bane groom yayi pecking bride dinshi ranar traditional event..infact ko kissing dinta zaiyi su bazasu ga wani abu ba tunda kusan al’ada ne hakan shiyasa duk musulman cikinsu basu cikayin traditional event din ba sai bayan daurin aure…bayan sun isa inda aka tanadar musu sun zauna ko hutawa basuy ba aka bukaci ganinsu a fili wai zasu taka rawa..haka nan suka sake fitowa suka tsaya a floor din yayinda aka saka musu traditional song shidai yana rike da hannayenta yana dan moving legs dinshi a hankali don bai wani iya rawa ba shikam..Mummy ce ta fara fitowa tazo tana musu watsin kudi daga nan kuma duk sauran yan uwanta suka fara tasowa suma..bayan sun gama Yan uwan amarya suma suka fito daga nan kuma sai abokai da kawaye..Bobby daga nan inda yake yana hango yanda Nur yaje yasa Miemie a kwana sai zuba mata rawar kai yake…murmushi kawai yayi yana girgiza kai cikin zuciarshi fadi yake”Allahumma yahdika Nur”.