Dr. BOBBY COMPLETE HAUSA NOVEL

A takaice taro yayi kyau kuma ya bada ma’ana matuka..amarya tasha gaisuwa da runguma a wajen sisters din Mummy dashi kanshi angon nata don ba ko kunya yake rungumeta gaban uban jama’ar dake wajen…karfe goma da kusan rabi suka tashi masu tafia gida suka tafi Wanda zasu kwana a gidan kuma kowa ya nemi makwanci…amarya tana flat din Mummy tareda su Billy yayinda su Aunty Fiddausi da sauran wanda suka rakota suke flat din aunty sumy zuwa da safe wasu zasu fara yin gaba saura kuma zasu bari har yamma su mika amarya dakinta snn su wuce…Bobby a ranar shima sai barin gidan yayi sbd yanda yake cike da jama’a Kai tsaye gidansu Nur suka wuce daga shi sai Nur din don sauran abokanshi duk a Kano suke so ana tashi kowa ya kama gabansa..suna hanya Nur time to time yake juyawa yana kallon yanda yayi relaxing jikin kujera ya wani lumshe ido yayi tsit kmr yana tunani…murmushin iskanci ya saki daidai lokacin da suka karaso cikin gidansu yace”gaskia su Mummy basu kyauta ba..taya zasu bar fresh ango kamarka ya kwana dakin tuzuru kaman ba yau aka daura maka aure ba”..banza Bobby yayi dashi dan a yanxu ba lokacin rigima ne dashi ba…sake murmusawa Nur yayi bayan ya gama parking motar yace”shawaran da zan baka kawai kayi sneaking kaje har inda take ka sameta don Allah ya gani ba abun farin ciki bane ango kamarka yayi spending first night dinshi ba tareda amarya ba”..wani kallo da Bobby ya watsa mashi baisan lokacinda ya kwashe da daria ba hadda dukan starring…Saida yayi me isarshi snn ya dan tsagaita yana cigaba da binshi da kallon da kana gani zakasan na tsokana ne yace”C’mon Bob wnn hararan fa?..am only trying to be of help don nidai Allah ya sani bazan iya kwana randa aka dauramin aure ba tareda amarya ba..hauka ma akeyi knn”..ya karasa mgn yana shafa kai gami da sakin murmushi…murmushi shima Bobbyn ya saki tareda dagowa yana kallonshi da kyau yace”don’t worry badai ni kakema wnn iskancin ba?..bari muga wanda zai shige maka gaba a neman auren Miemie..wlh idan kayi wasa da kaina zan cema babanta kar ya kuskura ya baka aurenta tunda dan iska ne Kai”..ai tun bai rufe baki ba Nur ya koma kalar tausayi yana cewa”gaba Bob wnn ai mugunta ne..nidai kayi hakuri wasa nake maka wlh..idan ma so kake inje in dauko maka Lamido i can do that amma kar kace zakasa a hanani aurenta pls..inasonta sosai wlh”..daria shima Bobbyn ya kwashe da ita tareda bude motar ya fita..Nur ya bi bayanshi da sauri yana cewa”Bob please mana..plss I love her”.
Washegari tun safe su Aunty Fiddausi suka shiga gidan amarya dake nan kusada gidan nasu suka gyara mata shi tsaf..suka kumayi duk wani necessary abu da gidan ke bukata daga nan kuma da yawa daga cikin Wanda suka rakota suka wuce Gombe aka bar iyaka Aunty Fiddausi da Aunty Amina sai walida da Billy.
Karfe hudu aka gama shiryata tsaf aka sake nadeta da wani lafayan snn aka kaita wajen su Mummy sukayi mata nasiha daga nan kuma aka bude kofar shiga gidan nata dake nan cikin gidan suka nufi can da ita…abun mamakin shine har yanxu Hajia indo bata bar kuka ba kmr dai yauma daga Gomben aka daukota aka sake zuwa Kano da ita…suna rike da hannunta har kofar gidan Aunty Amina tace tayi Bismillah snn ta shiga da kafar dama..ba musu tayi hakan snn suka shiga zuwa ciki.. compound din yanada girma sosai dukda baikai na asalim gidansu girma ba shima yanada girma ba laifi…a hankali suje tafia har sukazo entrance nan ma aka sake cewa tayi Bismillah da shiga da kafar dama snn suka shiga cikin parlor..basu ajiyeta ko ina ba sai one of bedrooms dinta dasu Billy ke ciki suka zaunar da ita kan gadon bayan sun sake mata nasiha sosai suka bar gidan sbd gudun kar ango yazo ya riskesu a dakin amaryarshi…daga ita sai Billy da Walida aka bari..Billy ta matsa kusada ita tareda bude face dinta tana kallonta with murmushi tace”har yanxu dai kukan kike Lamido?..”banza tayi mata tareda mikewa ta ware lafayan dake jikinta ta nufi wani kofa datake zargin bathroom ne..bayan few minutes ta fito sai kuma ta tsaya daga nan kofar bathroom din ta kama kugu ta shiga karema dakin kallo…walida da Billy suka hada ido kafin walida tace”zo muje kiga gidan naki da kyau”..girgiza Kai tayi still tana rikeda kugunta tace”mutane zasu iya shigowa”..da sauri Billy tace”aah ba wanda zai shigo wlh ai tun daxu sukazo suka gama ganin gidan..shi kuma angon ki nasan sai after magrib zai shigo so let’s use this opportunity ki karema gidanki kallo sosai”…dan murmushi ta saki jin abunda Billy ta fada sai Kuma ta daga kafada tareda fadin”ohk”..daga haka suka fita daga bedroom din..sauran bedrooms dinta guda biyu suka fara shiga ta gama gani snn suka dawo parlor daga nan Kuma sukayi kitchen…sbd tsabar mamaki ma kasa cewa wani abu tayi don gidan yayi mata kyau ne fiyeda yanda take zato..hakika daddy da Ammi sunyi kokari sosai wajen zuba mata abun arziki a gidanta kaman yanda shima mijin nata yayi kokari matuka wajen tamfatsa mata gida mai kyau da tsaruwa kmr wnn..she just fell in love with the house har batasan lokacinda dan guntun damuwan da take ciki yayi disappearing ba..zagaya gidan sukayi sosai ko wane lungu da saqo Saida suka shiga ta kalli abunta snn suka wuce flat dinshi..walida ta kama handle din kofa zata bude Aysha tayi saurin tareta tana cewa”babu Wanda zai shigan min 6angaren miji”..wara ido Billy tayi tana dubanta tace”to mun rigaki ganin 6angaren mijin naki ma”..tace”eh ai lokacin bana nan amma yanxu da nake nan ba wanda zai sake bari ya shigar mata 6angarenshi..haka nan kowa ya gane mana sirrinmu”..daria Billy ta saki kafin tace”kinada gaskia Kam..wnn sirrin ai tsakaninki dashi ne and nan da anjima kadan sirrin zai fara aiki so bai kamata mu shiga ba”..daria ta Kara saki walida na tayata…ita Kuma Aysha sai jikinta yayi wani sanyi qalau tunawa da gagarumi aikin dake gabanta da tayi…yanxu fa mgnr Billy gaskia ne Koh..yanxu babu kunya sai mutumin nn yazo yace zaiyi mata wani abu Koh..kai amma ai da kunya..to ta Ina ma za’a fara ne Kam?..duk jikinta a sanyaye ta bar jikin kofar tareda komawa parlor ta zauna ta zuba uban tagumi kmr marainiya..ya zatayi da al’amarin nan ne wai?.
Karfe takwas daidai motan Nur ya shigo gidan tareda Bobby daya kasa dena daria tun daxu..he is just smiling kmr mara hankali..gani yake no man is as happy as he is right now..he is super duper happy..he just can’t believe yau shine zai kwana gida daya..daki daya kuma gado daya da love of his life..oh Allah what a blessing!..what a happy moment!..it’s like a dream come true..the long awaited day has come.
Yeeepeee????????????????????????????????????
Rano✨
Wnn littafin na kudi ne ban yadda wani ko wata ya fitarmin dashi ba…masu buqatan siya zasu tura 300 zuwa 2208991344 Aisha Ahmad Tijjani Zenith Bank…sai a tura evidence of payment via 07063800556.
57
Da sallama suka shiga parlon daya cika da qamshi sbd turaren wuta dasu Billy suka saka..suna nan zaune cikin parlon Aysha da face dinta ke lullu6e da lafaya tana zaune tsakiyarsu..saida gabanta yayi wani irin faduwa sakamakon qamshin perfume dinshi da taji..dukda bataji voice dinshi ba don Nur kadai ne yayi sallama amma tasan tare suke sbd wnn qamshin nashi daya cika wurin…a nuste suka karasa ciki suka zauna Nur yana kallonta da fara’a sosai yace”amarya bakya laifi”..sunne kanta ta sakeyi ba bakin mgn..Billy dake kallonsu da murmushi itama tace”sannunku da zuwa sir..ina yini”..yace”lafia Lau..ya hidiman biki”..tace”Alhamdulillah”..walida ma ta gaisheshi ya amsa Bobby dai yana zaune sai kallonsu yakeyi kmr mutum mutumi..da zasu gane da barin wnn gaishe gaishen nasu sukayi suka fara gamawa dashi don Allah ya sani so yake su tafi su barshi da matarshi…Nur dake ankare dashi sarai yasan abunda yake saqawa cikin ranshi shiyasa duk ya sallami abokansu wai ba sai sun rakashi wajen amarya ba..shima Nur din dan ba yanda zaiyi dashi ne amma da shi kadanshi zai taho wlh…gyaran murya yayi tareda Bismillah kaman wani malami snn ya shiga musu nasiha kmr yanda aka saba idan an raka ango gidanshi ba’a tashi sai an dan yi musu nasiha ko yayane…kallonshi kawai Bobby yake yanda ya dage shi bai yadda ba fada yake musu abun sai ya bashi daria ma wlh..wai Nur ne yau da wa’azi kmr mutumin kwarai…Saida ya gama surutu da zolayarshi snn ya mike yana yima Bobby wani kallon kasan Ido yace”to ango mu zamu wuce..Allah ya baku zaman lafia da zuri’a na gari”..kai kawai Bobby ya gyada mishi yana murmushi..su Billy suma mikewa sukayi walida ta koma bedroom ta dauko musu bags dinsu Nur ya kama hanya zai fita Bobby na bayanshi..su Billy ma sun juya zasu tafi Lamido ta riko hannunta da sauri tana sakin kuka..da sauri Bobby ya dawo cikin parlon yana kallon yanda ta kwakwume hannun Billy yace”partner ki saketa mana..ai ba Bauchi zata wuce yanxu ba”..banza tayi mishi tacigaba da kukanta..Nur dake kallonsu ya fashe da daria yana cewa”wlh dole kiji tsoro Lamido..ni kaina zuwa yanxu tsoron mijin nan naki nake balle ke”..harara Bobby ya watsa mashi tareda karasawa inda take ya janye hannunta a hankali Billy dake daria tayi saurin kama hannun walida suka fita daga parlon suna daria..Nur dai na tsaye yana wani kallonsu yana murmushi Bobby yazo ya jashi shima suka fita kofar parlon yana binshi da wani kallo yace”oya go saida safe”..murmushi Nur ya Kara saki yace”dole kace saida safe mana.. anyways Allah ya baku zaman lafia mai dorewa..Allah kuma yasa kayi mata ciki a yau din nan”..tun kafin ya karasa Bobby ya tunkudashi tareda komawa cikin gidan ya rufe kofarshi..Nur ba karamin dan iska bane wlh..wai Allah yasa yayi mata ciki..yana dawowa parlon ya sameta zaune nan inda ya barta har yanxun kuma bata dena kuka ba..da sauri ya karasa ciki ya zauna kusada ita baice mata kala ba kawai sai ji tayi ya dauketa cak ya dora akan cinyarshi tareda rungumeta ga jikinshi sosai..tureshi ta farayi tana turo baki tace”ni ka saukeni banaso”..hannu yakai ya bude fuskanta da yake lullu6e ya tusrama face din nata ido yana kallo kmr ba gobe..wani irin nutsuwa da kwanciyar hankali suka saukar mashi..a hankali ya hade fuskanshi da nata tareda cupping fuskar nata da hannayenshi yana kallon eyeballs dinta yace”welcome..to your house..Mrs Bobby”..lumshe idanunta tayi tana sake turo baki ga gabanta sai faduwa yake..murmushi ya saki mai kyau tareda sunkuyawa a hankali yayi brushing lips dinshi akan nata for like 3 secs snn ya janye yana sake rungumeta sosai a jikinshi…Aysha dai tsuru tayi tana rarraba ido don Allah ya gani ba karamin tsorta tayi da yanayinshi ba..yanxu ya zatayi ta fitar da kanta daga wnn cakwakiyar ne?..wani tunani ne yazo mata kuma tayi na’am dashi dan haka bata sake yunkurin kwace kanta daga jikinshi saima Kara lafewa da tayi tana lumshe Ido..lokaci mai tsaho suka dauka a haka shima idanunshi na lumshe banda Hamdala da godia wa ubangiji ba abunda yakeyi a cikin zuciyarshi..a hankali yayi breaking hug din bayan yayi pecking forehead dinta ya sake daukanta cak zuwa flat dinshi..ita da idanunta na kulle ne har suka shigo parlonshi…dan bude idon tayi a sace ta shiga karema parlon nashi kallo shima yayi mata kyau sosai daga nan Kuma ya wuce bedroom dinshi..yana shiga ya direta a kasa tareda kama lafayan dake jikinta ya warwareshi ya ajiye akan gado sai kuma ya shiga karema jikinta kallo riga da skirt din jikinta sunyi mata kyau ne sosai kuma sun amshi jikin nata..sake karasawa yayi yayi hugging dinta yana dan rocking dinsu a hankali ya sake ce mata”Mrs Bobby”..nan ma dai shiru ta sakeyi ba bakin mgn shi kuma ya sake matseta jikinshi yakai bakinshi daidai kunnenta kafin yace”matar Bobby talk to me mana..what happened to ur mouth?..”makale shoulder dinta tayi alaman she won’t say a thing shima bai sake takura mata ba ya ajiyeta nan gefen bed dinshi snn ya shiga bathroom..alwala yayi ya fito snn itama yace ta shiga tayi alwala zasuyi sallah..ba musu ta shiga bathroom din itama tayi alwala ta fito..ya dauko lafayanta daya ajiye kan bed ya yafa matashi kmr hijab snn ya shimfida musu praying carpet suka tada sallah…raka’ah biyu sukayi tareda addu’o’i sosai na samun zaman lafia da kwanciyar hankali mai dorewa da kuma zuri’a mai albarka..sun dauki almost ten minutes Bobby nata kwararo addu’a kafin ya idar..yana mikewa itama ta mike tana dan kallonshi kasa kasa tace”zan..je..dakina”..murmushi ya sakar mata bayan ya mayar da praying carpets din inda suke ya kama hannunta suka fita daga dakin..main parlor suka dawo ya dauki ledan da suka shigo dashi suka karasa zuwa dinning..da kanshi yaja mata seat ta zauna shima ya zauna kusada ita snn ya bude ledan..kaza ne a ciki da yaji kayan lambu sai qamshi yake sai Kuma fresh milk mai sanyi..mikewa yayi zuwa kitchen ya dauko plate da cup snn ya sake dawowa ya zauna yayi serving dinsu..itadai tana zaune tana kallonshi batada bakin mgn…bayan ya gama da kanshi ya shiga feeding dinta tana tun nokewa ita bazata ci ba har dai ta hakura ta danci Wanda zataci don tasan ba saurara mata zaiyi ba idan ba cin tayi ba..ya dauki fresh milk din shima ya bata a baki tasha dan kadan tace ya isheta snn ya daidaita saitin inda tasa bakinta shima yasa nashi bakin a wurin ya karasa shanye Wanda ta rage..suna hada ido ta wani dauke kai tana turo baki shi kuma ya kashe mata ido daya yana murmushi…Kazan yaci dan kadan shima snn yasa sauran a fridge ya maida plate da cup din kitchen snn ya sake kama hannunta suka bar dinning din..ganin hanyar bedrooms dinta suka nufa har wani ajiyar zucia ta sauke shidai baice mata komai ba har suka shiga dakinda aka ajiyeta daxu..direct closet dinta ya bude ya shiga yana duba kayan da zai dauka mata na bacci bai gani ba dan haka ya fito zuwa inda aka jere boxes din lefenta ya shiga budesu har yaci karo da wanda ke cike da undies da sleeping dress ya dauki box din gaba daya snn ya sake kama hannunta suka koma flat dinshi..ajiye box din yayi a kasa snn ya zauna zai fara bude box din yaga yanda tayi wani tsaye a gabanshi tana turo baki sai ya mike yana sakin smile ya karasa inda take..hannu yakai ya zame dankwalin dake kanta nan take black long hair dinta ya bayyana..lumshe ido yayi tareda kai hannu yana shafa gashin nata yana sauke numfashi..he just every single thing about this girl..he loves everything she have..saida ya gama shafa gashin nata to his satisfaction snn ya jata ya zaunar da ita gefen gado yana ce mata”sit right here”..murguda baki tayi kmr zatasa kuka tace mishi”kaina a bude fa”..dungure mata kai yayi yana dan hararanta yace”see you..sai kace ba kece mai son fitoda gashin naki waje ba”..daure fuska tayi tana sake turo baki shi kuma ya saki murmushi gamida girgiza yace”continue pouting those lips na kusa nayi maganinsu ai”..da sauri ta maida bakin nata tana sake daure fuska..shi Kuma bai sake bi ta kanta ba ya bude box din ya shiga neman mata kayan da zatasa..duk wanda ya dauko tana gani har wani dagashi yake yana kare musu kallo snn ya ajiye..saida ya daga almost ten duk baiga Wanda yayi mashi ba ita kuma tana zaune tana kallon ikon Allah..wani taga ya dauko red din riga mai hannun vest da bombshort mai net a jiki..wani murmushi ya saki yana sake jujjuya kayan ya kare musu kallo snn ya mika mata tun ma kafin yace wani abu cikin daure fuska tace”na rantse da girman Allah bazan sa wnn ba”..kallonta kawai ya tsaya yi kmr ta kwashe da daria amma ya dake..irin wnn shiga masallaci haka..wnn rantsuwa da wuri tunma kafin yace tasa din..baiyi mata musu ba ya maidasu ciki snn ya dauko wata purple din riga batada tsayi sosai itama kuma hannun vest ne da ita amma jikinta is very cotton unlike wancan da yake net..sake Mika mata rigan yayi shima bai jira tayi mgn ba yace”na rantse da girman Allah sai kin sa wnn rigan”..kallonshi kawai takeyi fuskan nan a kwabe da gani kiris take jira ta sakar masa kuka amma batayi ba..karban rigan tayi ta ajiye tana wani kawar da kai gefe shidai baice mata komai ba ya tattara sauran kayan ya maidasu cikin box din snn rufe ya daukeshi ya ajiye a gefe..tana ganin ya fara rage kayan jikinshi ta wani runtse ido wai bazata gani ba..murmushi kawai yake mata har ya gama cire kayanshi ya fada bathroom..brush kadai yayi ya fito don already yayi wanka kafin ya taho..yana fitowa itama yace taje tayi brush ta sako rigan nata ta fito..batayi musu ba ta mike ta fada bathroom shi kuma ya dauko wani three quarter fari yasa tareda singlet shima white snn ya hau gado ya kwanta yana jiran fitowarta yau ko pyjamas bazai sanya ba shi Kam..a hakanshi zai kwana yanda zaifi jin dadin baccin sosai…Aysha kuwa tunda ta gama brush din ta sanya rigar taga gaba daya tsayinta ko guiwarta bai kai ba sai ta nemi wuri ta zauna tana tunanin yanda za’ayi ta bari ya ganta da wnn rigan..idan ba iskanci ba dama taya zai wani bata wnn dan iskan rigan yace tasaka kuma a gabanshi..sai yanxu take sake tabbatar da mgnr da ake cewa gaba daya maza basuda kunya..Saida ta kwashi kusan minti goma a na ciki kmr daga sama kawai taga mutumi a gabanta ya dauketa cak ya fita bathroom din da ita..runtse Ido tayi tana karanta innalillahi a cikin ranta har taji ya kwantar da ita akan gado shima ya kwanta tareda switching off bedside lamp dakin yayi duhu don already ya kashe sauran bulbs din..hannunshi yakai tareda janyota ya hada da jikinshi tanajin yanda yake sauke ajiyar zucia a jere a jere itadai tayi mukus kmr mara lafia..cikin wata irin murya da bata sanshi dashi ba taji yana cewa”ki tayani addu’a rabbi ya bani ikon kulawa dake gwargwadon iyawata..Allah ya bani hakuri da juriar zama tare dake ba tareda cutarwa ba..Allah yasa na iya rike amanarki da iyayenki suka bani snn kada Allah ya kawo ranar da ni Attahiru zan juya maki baya ko in dena sonki ko inyi maki wani abu dazai sosa zuciarki..kada Allah ya nunamin wnn ranar har karshen rayuwata”..gaba daya shiru sukayi na dan lokaci kafin yacigaba da cewa”Ina sonki sosai Aysher kuma har dunia ya tashi nasan bazan ta6a son wata kmr yanda nake sonki ba..I love u so much and Ina godia wa Allah daya bani ke a matsayin mata..inshaAllah bazakiyi regretting aurena ba har abada”..hawaye taji sun wanke mata fuska har batasan lokacinda ta rungumeshi ba itama kawai sai sheshshekar kuka take tama kasa bude baki tayi mgn..son da yake mata da dadewa tasan mai girma ne and wnn maganganun da yayi sai taji tausayinshi ya kamata sosai..taji bazata iya aikata abunda ta shirya zata aikata don hanashi kasancewa da ita ba instead zata hakura ta kuma jure duk wani abu da zaizo mata dashi..she’s going to be strong for him ko don sbd yanda yake azabtuwa da soyayyarta…lokaci mai tsaho ta dauka tana kuka a jikinshi Wanda har hakan ya fara ta6a zuciarshi..a hankali ya dago fuskanta yana kallo kafin daga bisani ya lumshe ido tareda hade bakinshi da nata..aikuwa diff ta hadiye kukan ta shiga rarraba idanu kmr shege a rabon gado…lokaci mai tsayi suka dauka a haka kafin ya zame bakinshi a hankali tareda sake hadeta da jikinshi yana shafa gashin kanta muryanshi can kasa yace mata”sleep”..da sauri da kulle idanuwanta tana sake lafewa a jikin nashi gabanta yana cigaba da faduwa har wani zazza6i taji yana neman kamata..addu’a kawai take Allah ya bata karfin halin da zata iya juran duk abunda zaizo mata dashi don sosai take a tsorace musamman da Billy ta sake tsoratar da ita daxu…shi kuma gani yayi bai kamata ya aikata wani abu a yau din ba sbd yasan gobe gidan zai cika taf da mutane sai kuma body temperature dinta da yaji yayi rising kmr fever zai rufeta..a hankali yaja duvet ya lullu6esu dashi snn yayi addu’a ya shafa mata shima ya shafa a jikinshi daga haka ya gyara mata kwanciya ya dora kanta a chest dinshi snn ya lumshe ido yanason bacci yazo yayi awon gaba dashi har baizo ba..har ita ta samu baccin shi nashi idanun a kekashe suke tamkar ba dare ne ba..kawai farin ciki kasancewa tareda ita ma kadai ta isa yasa bacci yayi kaura daga idanunshi..ganin da gaske ba baccin zaiyi ba sai ya kwantar da ita kan pillow a hankali ya sauka daga gadon ya shiga bathroom ya dauro alwala snn yazo ya tada sallah don ya sake nuna godia wa Allah daya cika mashi burinshi na samunta a matsayin mata.