Dr. BOBBY COMPLETE HAUSA NOVEL

Washegari Alhamdulillah ta tashi da sauqi sosai don babu fever a jikinta snn duk wani wuri dake mata ciwo jiya yau bata tashi da ciwon ba saidai tunda ta tashi da shagwa6a ta tashi don banda kuka ba abunda take mishi wai ya tsaneta shi kuma ya rikice sai aikin rarrashi yake..ko wanka saida yayi da gaske snn ya samu tayi daga nan ya bata tea da magani tasha maimakon tayi bacci sai ta dora daga inda ta tsaya..kuma duk tana sane take wnn iskancin wai acewarta wahalar daya bata jiya ne take fanshewa sbd shima yaji a jikinshi kmr yanda taji..dama a dunia ba abunda take so kmr tayita zuba ta6ara ana biye mata yau kuma sai abun nema ya samu wai matar driver ta haifi mota..sosai ta rikitashi da wnn iskance iskancen ko breakfast bai samu yayi ba har yanxu don hanashi motsawa tayi ko na da can yana tashi zata fara kuka tana bubbuga kafa wai zaije ya barta..haka nan bawan Allah zai dawo yayi zaune yana rikeda ita yana bata baki amma duk a banza..kallonta kawai yake yanda take shagwaban yana lallashi sa abun ya burgesu matuka..bai taba sanin akwai ranar da zaiji irin wadan nan abubuwan na burgeshi ba saida ya hadu da ita..wato dai ita koma me zatayi yanaso kuma abun sha’awa ne a wurinshi..saida tayi bacci snn ya samu ya shiga bathroom don yin wanka..ita kuma yana shiga ta bude ido tana kyalkyala daria cikin duvet sbd kar yajiyota..draman nasu ba karamin kayatar da ita yake ba..ai wlh saita fanshe duk walakancin da yayi mata jiya shima sai yaji idan da dadi kasa mutum a gaba kayi masa abunda bayaso..tanajin fitowarshi tayi saurin maida idonta ta kulle shi Kuma ya karaso ciki dakin daure da towel a waist dinshi sai wani karami a hannunshi yana gashin kanshi..stool din gaban mirror ya janyo ya zauna snn ya shiga shafa cream ita kuma ta bude ido tana kallonshi daga kwncen da take yanda bazai gane tana kallonshi ba..broad shoulders dinshi ta tsaya kallo yanda suke nan fari tas don jikinshi har yaso yafi face dinshi haske..ga skin dinshi har wani glowing yakeyi sbd tsabar gyara kmr skin din mace..yana gama shafa cream ya shiga shafa mayukan gashinshi tana combin kanshi daga nan kuma ya dawo kan sajenshi da duk fuskanshi babu abunda take qauna kamarshi..tana kallon yanda ya shafeshi da mayuka masu kyau snn yayi using brush comb ya taje tun daga sajen har zuwa gemunshi..kallonshi kawai Lamido keyi tana murmushi ashe dai haka mijinta yake dan gayu bata sani ba..haba no wonder kullum wnn sajen nashi ke kara laushi da sheqi ashe kudi yake kashe mashi haka..yana gamawa da sajen ya shiga shafa turarukanshi masu masifar qamshi..tun tana kallonshi a kwance har batasan lokacinda ta mike zaune tareda tallabo cheeks dinta da hannayenta ta wani tsura mishi ido tana murmushi ba..duk yanda takai da son tayi fushi da mutumin nan bazata taba iyawa ba..she loves him to the extent that kome zai mata bazata iya dogon fushi dashi ba..yanxu dai gashi duk wahalan da tasha jiya a dalilinshi kallonshi kadai yasa ta manta da duk wahalan data sha sai more kallonshi takeyi kmr yau ta fara ganinshi..Bobby kuwa tunda ya fito bathroom dama yasan idonta biyu don ya lura da yawan motsin da take nuna mata ne kawai baiyi ba yayi pretending kmr baisan tana idon nata biyu..and koda ma baiyi noticing motsinta ba ya tabbata daga lokacinda ta kafa mashi wadan nan idanun nata dole zai fahimci kallonshi takeyi sbd tasirin da idanun nata ke dashi a tareda shi..kai tsaye suke piercing har cikin zuciyarshi so babu yanda za’ayi ta dauki tsahon minti guda tana kallonshi dasu ba tareda yaji a jikinshi cewa kallonshi takeyi ba..abun kuma ba karamin qayatar dashi yayi ba..gashi dai ita take kallonshi amma yasan ko ita bazata kaishi enjoying kallon nashi da take ba don kallo ne mai cikeda so da kauna ba ordinary kallo bane da ake iya samunshi wurin kowa da kowa..special kallo ne da sai mutumin da ake mutuwar so za’ayi ma irinshi and he’s glad she does that don hakan ya sake tabbatar mashi da cewa matarshi Aisha na tsananin kaunarshi kmr yanda shima yake tsananin kaunarta dukda yasan nata son bai kama kafar wanda yakeyi mata ba..murmushi ya saki bayan ya kammala duk abunda zaiyi ya juya ya nufi closet dinshi bayan ya kashe mata ido daya..daria ta saki itama tana binshi da kallo sai kuma ta sauka daga gadon daga ita sai yar rigarta da baifi iya guiwarta ba ta nufi closet din nashi itama..ciki ta shiga ta ganshi yana neman kayan da zai sa..a hankali ta karasa ta tsaya a bayanshi tareda fadawa jikinshi tayi mashi kyakykywan hug ta baya..saida ya lumshe don dadi har baisan time din da rigar dake hannunshi ya zame ya fadi kasa ba..yana jinta a jikinshi yaji kmr komai nashi aka dakatar sbd tsabar shaukin da ta shiga..shi har yanxu mamakin wnn emotions din da kullum sake sabunta kansu suke..a tunaninshi tunda sunyi aure kuma har sun zama daya zai samu saukin wnn emotions din amma it’s like abun ba haka yake ba sam..sai yakega ma kmr abun karuwa yakeyi akan na baya..lumshe Ido yayi yanajin yanda duk wani ga6a na jikinshi ke amsan sakonnin da take tura mashi in a breaking voice ya kira sunanta”Ay..sher”..kasa amsawa tayi ta kwantar da kanta a bayanshi tanata faman murmushi..a hankali ya juyo da ita suna facin juna yayi cupping fuskanta da hannayenshi full of excitement yace”I love u so so very much baby..duk dunia nasan idan aka dauke daddy da Ammi baza’a samu Wanda ke sonki kmr yanda nakeyi ba..i love u sosai”..ya karasa mgnr yana hada face dinshi da nata..Lamido da farin cikin dunian nan ya isheta sbd wnn kalaman nashi sai kace yau ta fara jinsu daga bakinshi kasa dena washe baki tayi kmr gonar audugu..dan dagen kafa tayi ta dafa shoulders dinshi da both hands dinta sbd yafita tsaho sosai ta samu ta manna mashi peck a tip of hancinshi don tsayinta kasa kaiwa forehead dinshi yayi sbd tsayinshi..tana gamawa Bobby ya rungumeta da kyau yana blowing mata kisses ta ko ina yana murmushi..wlh bai ta6a sanin haka aure yake ba..tabbas da yasan haka zama aure yake kilan da tun lokacinda ya fara sonta zaiyi duk yanda zaiyi yaga ya aureta tun kafin a kawo wnn lokacin..baisan ko nashi auren ne yazo a haka ba sbd sonda yake mata oho..bakinta yakai saitin kunnenta ya sake mata whispering”i love u”..murmushi take sosai ta dago tana kallon idanunshi tace”nima ina sonka sosai..i can’t imagine my life without u..i love u so much”..pecking forehead da cheeks dinta yayi yana cigaba da smiling..a hankali ta janye daga jikinshi ta sunkuya ta dauko mashi rigan daya yar a kasa..Mika mashi tayi tana murmushi instead of ya kar6a sai ya makale mata shoulder dinshi yanayi mata nuni da finger dinshi wai tasa mashi da kanta..batayi musu ba ta balle botles din rigan shi kuma ya rage tsayinshi daidai yanda zata iya sa mashi ta zura mashi rigan snn ya mike yana gyara collarn rigan..ita tayi mashi buttoning rigan ta saka mashi links snn ya Miko mata trouser wai shima ta saka aikuwa ta fice daga wurin da gudu tana mishi daria..shima darian ya saki yana ayyana lallai ta wareke tunda har take iya gudu har haka..Sharp sharp ya karasa sa kayan ya sake gyara gashinshi jikin mirror dake nan ciki snn ya fita..bai sameta nan dakin ba harta gama gyara gado ta fita dan haka ya fice shima zuwa bedroom da yasan dole nan zai sameta..bai sameta a nan ba saida ya bude another one ya ganta a ciki tana kokarin saka skirt dinta..tayi wanka dama tun daxu so tana shigowa kaya ta dauka ta fara sawa don yau kome zaiyi sai taje gaida Mummy wlh..yana karasowa ciki ta gama veiling dinta dan haka ta shiga dubanshi tana dan daure fuska tace”nifa yau zuwa zanyi in gaida Mummy”..kallonta ya danyi kafin ya saki murmushi gamida girgiza kanshi yace”ba sai kinje ba tace da kanta zata shigo dubaki anjima”..ai tun bai rufe baki ba ta sake dinke fuska tana binshi da wani kallo tace”nidai wlh sai naje..ai ba daidai bane ace har sai itane zatazo inda nake ni banje na gaisheta ba”..murmushi yake cigaba dayi cikin ranshi yace”abubuwan sun motsa knn?..”a zahiri kuma matsawa yayi kusa da ita ya kama hannunta yace”to meye abun 6ata rai kuma baby..shknn kisa hijab dinki muje”.. kallonshi da wani expression a fuskanta tace”ban gane hijab ba..daga nan zuwa gidan naku zakace insa hijab?..”hannu yakai zai sake kamo dayan hannunta tayi sauri kaucewa tana hararanshi..bai sake cewa komai ba ya karasa ya kama hannun nata suka fita daga dakin..wanda aka fara ajiyeta a ciki suka shiga ya saki hannun nata a nan shi kuma ya shiga closet ya dauko mata katoton hijab ya dawo ko mgn baiyi mata ba ya janyota ya zura mata shi ba tareda ko veiling dinta ya cire ba..ya kalleta from sama zuwa kasa then from kasa zuwa sama yaga komai na jikinta a rufe yake dan haka ya saki murmushi yana shafa gemunshi yace”perfect..now we are good to go”..banza tayi dashi ta dauke kai tana turo baki..shi kuma ya kama hannunta a haka suka fita daga gidan..bayan sun fito compound ya saki hannunta yayi locking kofa snn ya sake kama hannun nata suka nufi kofan da ake koma cikin gidan nasu ta nan..sai yanxu Lamido ta samu damar karema compound din gidan nata kallo don tunda aka kawota bata sake fitowa ba balle ta kalleshi da kyau..yanada girma sosai da akwai motocinshi guda biyu daga can gefe sai kofan da suka nufa shima yana daga gefe don ba kowa ma zai fahimci akwai kofa a wurin ba..tayi mamaki da taga ashe gidanta da main house din nasu kusa da kusa suke saidai kowanne gate dinshi daban sai dan kofa da akayi wanda zasu iya shiga main house din ba tareda sunbi ta gate ba..sosai yanayin tsarin wurin ya burgeta..suna karasawa Bobby ya bude kofar nan suka fada gidansu Mummy.