Dr. BOBBY COMPLETE HAUSA NOVEL

Dr. BOBBY COMPLETE HAUSA NOVEL

Rano✨

Wnn littafin na kudi ne ban yadda wani ko wata ya fitarmin dashi ba…masu buqatan siya zasu tura 300 zuwa 2208991344 Aisha Ahmad Tijjani Zenith Bank…sai a tura evidence of payment via 07063800556.
61
Suna shiga aunty data fito daga kitchen ta rike baki baki tana kallonsu da mamaki sosai tace”yanxu Bobby mara lafiyan ka dauko ka fito da ita sbd rashin hankali?..”tana gama fadin haka kuma ta karasa inda suke tareda kama hannun Aysha ta rike cikin nata tana kallon with concern tace”kema kika yadda ya fito dake bakida lafia Aysha?..”sunne kai tayi tana murmushi tace”ai naji sauki aunty”..cikin ranta kuwa haushi taji da yazo ya tona mata asiri a wurinsu..yanxu shknn tasan da kyar idan basu san menene ma yayi coursing zazza6in nata ba..amma dai ya cuceta wlh..kamata aunty sumy tayi suka karasa parlor yayinda shi kuma yabisu da kallo yana murmushi..wnn son da suke nuna mata ba karamin faranta mishi rai yake ba..yana son yanda suke tayashi sonta sosai ba kadan ba..karasawa yayi ciki shima ya zauna yana kallon aunty sumy yace”ita fa da kanta tace sai na kawota shine zaki wani tsaremu da mgn ko welcoming dinmu bakiyi ba”..harara ta juya ta sakar mashi tana nuna Aysha tace”ita dai ya kamata inyi welcoming amma ba kai ba..dan rainin hankali kawai”..daria sosai yasa hadda girgiza kai yace”siriki ne dai dake kuma har yanxu baki dena wadan nn abubuwan ba”..shiru aunty sumy tayi tana kallonshi don dama ranar daya fada mata haka Saida taga alamun da gaske yake..ta bude baki zatayi mgn Mummy ta fito daga flat dinta tace”hayaniyar me nakeji ne haka?..”da sauri Bobby ya mike ya karasa gareta yana kokarin fadawa jikinta cikin igbo yace”Mummy nah”..Mummy dake murmushi tayi saurin kaucewa tana daria tace”let me welcome my daughter first”..daga haka ta wuce cikin parlon tana cigaba da mishi daria shi kuma ya wani tale baki kmr zaisa mata kuka yace”Mummy ni Koh..ni kikaima haka Koh..shknn nagode”..batace mishi komai ba tana isa inda Aysha take ta dagota tareda rungumeta a jikinta tana cewa”welcome to your Family daughter”..wani irin kunya ne ya kama Aysha tama rasa inda zata 6oye kanta sbd ita..gashi Mummy ta rungumeta har yanxun taki rabata da jikinta..aunty sumy na kallonsu with a very wide smile tace”Mummy bakiga kyan da kukayi a haka ba wlh..let me call Sab yazo da camera yayi muku hoto a haka a gaskia..kunyi kyau fa sosai kaman a daukeku a gudu”..Murmushi Mummy tayi tareda janye Aysha daga jikinta tana kallonta da fara’a tace”ya jikin naki?..hope bashi ya takura maki zuwa bayan bakida lafia ba”..girgiza kai Aysha tayi tana sunne kai duk kunya yabi ya isheta wlh..Bobby dake tsaye inda Mummy ta baroshi yana binsu da kallo tun daxu sai yanxu ya samu damar karasowa cikin parlon shima ya samu wuri ya zauna nan inda suke zaune yana fadada murmushin fuskanshi sbd farin cikin yanda suka tarban mishi ita..durkusawa tayi har kasa tana gaishesu yayinda Mummy ta dawo da ita zaune tana ce mata ta dena wnn durkuson ita dai ta yafe mata..aunty sumy da kanta ta shiga kitchen ta kawo mata lemo da ruwa dasu cupcakes tace ta fara ci kafin a karasa abinci..sai nan nan sukeyi da ita kmr zasu maidata ciki sbd soyayya ita sai kunya suke bata wlh..Mummy sai ce mata take duk Bobby yayi mata abunda ba daidai ba tazo direct ta fada mata ita kuma zatayi mata maganinshi itadai har yanxu babu bakin mgn sai na murmushi..mutanen nan ba karamin burgeta suke ba..dama tun ba yau ba tasan yanda suke gudanar da rayuwarsu cikin so da kaunar juna tasan Kuma inshaAllah bazata samu matsala dasu ba..ganin bata ta6a komai da aka kawo mata ba Bobby da kanshi ya zuba mata lemo a cup ya hada da cup cake din yana mika mata ita kuma tayi kmr bata gani ba don kunya yake bata..aunty sumy na hada Ido dashi ta sakar mashi harara shi kuma ya kashe mata ido daya yana cewa”to ko abinci bataci ba matsa saina kawota wurinku..yanxu kuma an kawo naga kunya ya hanata ci shine zan bata da kaina”..ba aunty sumy kawai ba har Mummy Saida tayi darian wnn rashin kunyan nashi.. Bobby da Aysha dama ai tasan zaiyi rashin kunya tunda tasan soyayyar da yake mata ba ordinary so bane..fatanta dai Allah ya dawwamar da wnn farin cikin da suke ciki har karshen rayuwarsu.. Allah kuma ya basu zuri’a masu albarka…suna nan zaune sunata janta da labari tun tana jin kunya har daga baya ta ware suka cigaba da labarin da ita..Kiran Nur ne ya shigo wayanshi ya dauka nan yake ce mashi photo albums dinsu ne na biki aka kawo mashi so yana kofar gida ya fito a amsa..Bobby yace ya shigo main house kawai don suna nan tareda Ayshan..babu wasting of time Nur ya shigo cikin gidan yana cin karo da aunty sumy sai yaji kunya ya lull6eshi musamman daya ga irin kallon da Bobby ke jifanshi dashi yana murmushi.. Allah dai yasa ba zuwa yayi ya tona mashi asiri yace musu yace yana sonta ba..yasan halin kayanshi tsaf zai iya aikata hakan amma dai daya gama dashi..har ya karaso cikin parlor ya zauna bai yadda ya hada ido da itaba yana zaunawa ya shiga gaida Mummy ita kuma ta amsa mashi with smile tana tambayanshi ya gajiyar biki yace gajia yabi lafia..a nutse ya juya yana gaida aunty sumy da hankalinta gaba ke ga albums data gani a hannunshi..bayan ta amsa gaisuwan nashi tace”wnn albums din biki ne a hannunka?..”kai a kasa Nur ya mika mata allbums din yana cewa”eh”..aunty sumy ta amsa ta fara dubawa yayinda shi kuma Nur suka shiga gaisawa da Aysha..sai tsokanarta yake wai har ta fara kumatu itadai sai murmushi don ba saba irin wnn wasan tayi dashi ba..har yanxu daukanshi take matsayin College Provost dinsu so bata iya sakewa tayi wasa dashi kmr yanda yake mata..aunty sumy dake kallon pictures din biki sai zuzuta kyan da sukayi take tana nunama Bobby dake zaune kusada ita wani picture da sukayi gaba dayansu tace”dan Allah wnn baiyi kyau ba Bobby..kallemu fa kmr wasu larabawa”.. Bobby dai daria kawai yake yana kallon Nur da yake satar kallonshi yana Maka mashi harara..for the first time yau yakejinshi wani irin cikin familyn Bobby..wani sabon kunya ne ya shigo tsakaninsu sakamakon son nan da yakewa Miemie amma da shi ba haka yakeji idan yana cikinsu ba wlh..sakewa yake yayi abunda yaga dama don daukansu yakeyi daya da family dinshi amma yanxu wnn is gone sai jin kunya da sunkuyar da kai kawai..Saida ta gama kalle hotuna tsaf tana zuzutasu snn ta mikama Aysha tana ce mata”ungo wnn ki fara gani Aysha kafin Mummy ta gama da sauran”.. Mummy tace”aah kuyi kallonku ni zan gani a nutse ba lallai sai yanxu ba”..Aysha batayi musu ba amsa album din tana kallon yanda cover dinshi yayi bala’in kyau tasan cikin ma dole yayi kyau shiyasa aunty sumy tayita exergerating..page din farko ta bude nan taci karo da wani beautiful picture dinsu ita dashi ya wani rike mata hannu yana kallonta itama tana kallonshi tana murmushi..a can saman page din kuma in italics aka rubuta The Waziri’s Meets The Lamido’s sai daga can kasa kuma aka rubuta Attahir Waziri Weds Aysha Lamido..sbd tsabar farin ciki batasan sanda ta lumshe ido takai hannu tana shafa ilahirin page din ba..yayi mata kyau ne nesa ba kusa ba..ya kuma kayatar da ita kwarai..a nuste tacigaba dabin pictures din tana kallonsu daya bayan daya tana murmushi daidai lokacin kuma Miemie da Sab suka shigo parlon..tun safe suka fita ya rakata tayi registration na jamb shine sai yanxun suke dawowa..Bobby najin sallamarsu ya juya da sauri yana kallon Nur sai kuma ya fashe da daria har yana tafa hannu..Mummy tace”kai bakada hankali ne?..wnn wane irin daria ne?.”tsayar da dariar yayi yana kallon Nur yanxu yace”Mummy karki damu abokina nake yiwa”..juyawa Mummy tayi ga Nur tace”is he alright?..”da sauri Nur yace”wlh he is not Mummy..amma ki barni dashi nasan yanda zanyi maganinshi”..girgiza kai kawai Mummy tayi tana jinjina wnn iskancin na Bobby..daga yin aure kuma sai ka zama shashasha?..to Allah ya shirya..su Miemie na karasowa da taji sunyi komai normal ta mike zuwa flat dinta don bazata iyama wnn iya shegen na Bobby ba..cikin ranta kuwa farin ciki take sosai na ganin yanda walwalarshi ya dawo haka..bata ta6a tsammanin zuwan lokaci irin wnn da Bobby zai dawo rayuwa normal kmr kowa da kowa ba..ko a haka saidai tace Alhamdulillah don ubangiji yayi mata komai sai kuma fatan gamawa da dunia lafia..Nur da tun daxun kanshi ke kasa sai yanxu ya samu damar dagowa yana kallon Miemie don har yanxu aunty sumy bata gama kallon pictures ba..daidai lokacin itama ta kalli inda yake aikam suka hada ido Nur har cikin ranshi yaji wani abu amma ya danne ya shiga kallonta yana murmushi..murmushin itama ta saki tareda karasawa ta zauna kusa dashi tana kallonshi tace”uncle Nur ina yini”..da sauri yace”la..lafia..lau..ina kukaje..haka?..”Miemie tace”registration din jamb naje nayi kasan mun kusa graduation”..gyada kai ya shigayi yana dubanta da murmushi yace”MashaAllah ashe pretty ta kusa graduation..to Allah yasa albarka”..tana murmushi tace”Ameen..saura baifi 2 months ba mu fara waec”..yace”Allah ya bada sa’a”..tace”Ameen Uncle Nur”..daga haka kuma sai ta bar inda yake ta koma wurin Aysha ta wani rungumeta tana murmushi tace”aunty Aysha sannu da zuwa”..kafin Aysha tayi mgn Bobby yayi saurin janyeta daga jikinta yana mata wani kallo yace”are u mad?..”dan turo baki tayi tace”naji dadin ganinta ne fa”..Bobby ya matsar da ita daga wurin yace”oya San inda dare yayi maki kuma kar na sake ganin kinyi mata irin wnn abun dan ranki saiya 6aci”..zaunawa tayi kusada mamanta tace”to kayi hakuri”..Nur dake gaisawa da Sab duk yana sauraron wnn iskancin na Bobby yasan kuma da gayya yakeyi haka sbd ya kular dashi and he succeed..sbd presence na aunty sumy a wurin yasa bazai kulashi ba amma dole ma yayi maganinshi wlh don ya fuskanci walakancinshi karuwa yayi bayan auren nan nashi..bayan sun gama kallon albums din an gama lunch don haka duk sukaci abincin tare daga nan kuma Bobby yabi Nur suka fita zuwa hospital bayan yayi sallama da matarshi yace ta zauna nan tare dasu Miemie idan ya dawo sai ya biyo ta nan ya dauketa.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128Next page

Leave a Reply

Back to top button