Dr. BOBBY COMPLETE HAUSA NOVEL

Bayan sati biyu…
Rayuwa suka gudanar mai cikeda soyayya cikin sati biyun nan..duk wanda ya zauna dasu yaga yanda suke concentrating akan junansu abun zaiyi matukar burgeshi don sai kayi tunanin a cikin gidansu aka halicci soyayya..they are the perfect couple da basa gajia da nunama juna love and affection..duk au biyun are meant for each other and each one of them can die for the other..hatta su Mummy da sauran yan gidan sun auren nasu aure ne irin na soyayya wanda ba ko ina ake samun irinshi ba..kusan kullum suna tare a gida don hutun one month ya dauka na zuwa aiki dan haka bai fita sai idan akwai emergency case da babu wanda zai iya handling sai shi..kullum yana nan tareda ita sai kuma main house da yake shiga gaida su Mummy amma ita ba kullum yake barinta zuwa ba..a halin yanxu batada problem din komai domin ko kewar su Ammi da takeyi yanxu ya ragu sosai sbd tsabar kulawan da yake bata wani lokaci har mantawa ma takeyi da kowa na dunia????..saidai kusan kullum zatayi waya dasu dan ko bata kira ba Ammi na kiranta ko su Husna sbd haka rayuwa is full of happiness a garesu baki daya sai dan abunda baza’a rasa ba na bahaushe da yake cewa zo mu zauna zo mu sa6a..masu aiki har biyu Mummy tasa aka kawo mata amma tace guda daya ma ta isa dan haka aka sallami dayar ita kuma daya ta zauna tana dan tayata su shara da mopping da sauran aiyukan gida..girki dai da kanta take abunta saidai ta dan taimaka mata haka gyaran 6angaren mijinta da bedrooms dinta shima da kanta takeyi ita mai aiki iyakarta gyaran parlor,dinning dasu kitchen sai kuma ta kama mata wasu abubuwan..dakinda take kwana yana daga can gefe so tana kammala aiyukanta dama can take komawa dan haka babu takura a tsakaninsu..abu daya dake dan damunta shine rashin fita da baya barinta..shi koda yaushe yafiso suyita zaune a gida kmr a nan aka halicce su musamman ita da ko compound bai cika son tana zuwa ba wai ko baki zata raka ta tsaya iya kofar parlor shi bai yadda ta fita compound masu gadi na kallonta ba..wnn shine kadai damuwarta sai kuma asibiti da takeso ya barta ta fara zuwa sbd mates dinta gaba daya suna asibiti waiting results amma banda ita hakan kuma ba karamin damunta yake ba..gani take kmr idan ta dauki lokaci mai tsaho bata aiki skills dinta na iya guduwa su barta and ko Allah yasan batason haka ita da takeson wucewa Cyprus ta cigaba da karatu ai bazata so tayi loosing skills dinta sbd rashin practicing ba dan haka ta kuduri niyyar sanar dashi ya barta ta fara zuwa ko Freedom ne don tasan ko rasuwa zatayi bazai bari taje wani asibiti apart from nashi ba..ita sai yanxu wnn kishin nashi ke damunta wlh..ta lura ba karamin kulle hakan zai haifar mata ba and Allah ya sani ita bazata juri kullum tayita zaune a gida kmr wata mara abunyi ba..yanxu ko aiki ta samu batasan da yaya zai barta tayi ba da wnn shegen kullen da yake mata..kullum kuma tana cikin hijabi kmr matar malam..ko Nur ne zaizo gidan haka zai zunduma mata jibgegen hijabi a jiki tayita fama dashi wani lokaci ma sai taji kmr tasa kuka..tun jiya take tunanin yanda zata fada mishi tana son komawa asbiti amma batasan ta yaya ba kawai addu’a take Allah yasa kai tsaye yace mata ya amince taje aiko da batasan farin cikin da zata tsinci kanta a ciki ba.
Tun daxun da ya kirata yace gasu nan zuwa tareda Nur tayi saurin karasa girkin da take tareda taimakon mai aikinta mai suna saude suka jera komai kan dinning snn ta wuce dakinta don yin wanka ita kuma saude ta karasa gyara kitchen snn ta dauki abincinta ta wuce dakinta kmr yanda ta saba…Aysha na fitowa daga wanka ta dauko wani riga da skirt na atampa ta saka ta kafa daurin dankwalinta da yayi das a kan nata snn ta kawo veil daya shiga da atampar jikin nata ta yafa tunda dai tasan ko rasuwa zatayi bazai barta ta fita ba tareda wani abu a jikinta ba..mayafin ma tasan da kyar idan ba cewa zaiyi ta cire ba amma addu’a take Allah dai yasa ya barta dashi yau daya dai itama ta saka abunda takeso..bayan ta gama gyara fuskarta ta dauki turare daga kan madubi zata shiga fesawa a jikinta kawai taji an rike hannunta kmr daga sama ya kwace turaren daga hannun nata ya ajiyeshi nan inda yake snn ya juyo ta yana kallon fuskanta yace”wai bana hanaki sa turare idan Muna tareda baki ba?..”marairaicewa tayi tana kallonshi bata dai ce komai ba..shi kuma ya saki smile yana sake matsawa jikinta yaja cheeks dinta da hannayenshi yace”kinyi kyau sosai”..murmushi kawai ta saki tana gyada kai har yanxu bata ce komai ba shi kuma yace”tareda Nur muke dauko hijab dinki muje”..sake marairaicewa tayi tana dubanshi da puppy eyes tace”partner dan Allah inje a haka..kaga veil din dana yafa fa mai girma ne”..girgiza mata kai Bobby ya shigayi tun ma kafin ta rufe baki yace”bazan iya ba wlh..there is no way da zan bari ki fita bayan duk wnn kyan da kikayi”..kallonshi kawai take kmr tasa kuka..a fusace ta bar wurin ta koma kan gado ta zauna ta rungume hannaye tace”to kaje ka sallameshi da kanka ba sai nazo ba”..karasawa yayi shima ya zauna yana yin kasa da murya yace”yanxu baby sbd…”bai karasa ba ta mike ta bar mishi dakin duk rai a 6ace..da sauri shima ya mike yabi bayanta nan yaga ta bude kofa zata shiga daya bedroom dinta yayi saurin kamota yana cewa”ki tsaya muyi mgn plss..ya kamata ki fahimceni love..inada kishi sosai akan duk wani abu da nakeso..yanxu kina ganin..”still bai karasa ba ta katseshi da fadin”shine nace kaje ka sallami bakonka kai kadai ba tareda ni ba”..ganin juyawa tayi zata shiga dakin yasan kuma tana shiga kulle kofa zatayi yayi saurin rungumeta ta baya ya lumshe ido yace”to..kiyi hakuri..yanxu kije da veil din amma next time bazan yadda ba”..banza tayi dashi ta wani tureshi ta wuce parlon tana murguda masa baki shima yabi bayanta yana jijjiga kai..ita dai har abada bazata dena wnn rikicin nata ba..kan a very minor abu zata daga mashi hankali kuma idan baiyi yanda takeso basu ba zaman lafia..ya fuskanci ita din hukuma ce saida lallashi..zaune ya sameta a parlor suna gaisawa da Nur daga nan kuma tayi mishi introducing abinci dake dinning ba musu suka karasa dinning don dama tareda yunwar su suke..saida ta gama serving dinsu komai snn ta bar dinning din tanajin yanda Nur da har ya fara cin nashi abincin keta santi yana cewa abokinshi yayi sa’ar mata data iya sarrafa abinci..itadai murmushi tayi tareda komawa parlor..saita tuna a gida yanda sam bata son girki..shiyasa kusan kullum suke rigima da Ammi kan aiki ita kanta bata ta6a zaton akwai time da zaizo wai taji bazata iya bari wata tama mijinta bincin da zaici ba..duk kiyayyanta da shara dasu wankin toilet yanxu da kanta take na flat dinshi kuma ko kadan hakan baya damunta saima faranta mata da yakeyi..at least bata bama wata mace kofar da zata shigo rayuwar mijinta ba..hakan da takeyi kuma na burgeta..yanxu ta dauki full responsibility dinta na house wife duk wani aiki daya kama na mijinta ne da kanta take yinshi..tana nan zaune har suna gama cin abincin suka dawo parlor Nur har yanxu bai bar santin girkinta yana cewa ta ita abinci ba..ita kuma kallonshi tayi tana murmushi tace”Sir kar ka damu da kaina zan koyawa Miemie yanda nake girki sbd idan ta iya ta dinga yi maka a gidanka”..wani irin zare Ido Nur yayi yana mamakin abunda take..jmya juya yana kallon Bobby dake danne daria yace”amma kaci amanata..yanxu zuwa kayi duk ka fada musu nace ina sonta?..”da sauri Bobby yace”ni ba wanda na fadawa sai ita kuma itama believe me bani na fara fada mata ba da kanta ta gano sbd shegen rawar kanka dan haka stop blaming me..wnn rawar kan naka yasa ta gane ni kuma data tambayeni nace mata its the truth”..dafe goshi Nur yayi yana murmushi kmr bazai sake mgn ba can yace”amma dai baku bari ta sani ba koh?..”harara Bobby ya watsa mashi yace”kasan ko aikena kayi bazanyi such mgn da itaba balle baka aikeni ba..da bakinka zaka fara fada mata inshallah”..ajiyar zucia ya sauke yana murmushi ita kuma Aysha ta koma dinning din ta gayar inda suka bata snn ta koma daki don bata cika son zama if yana tareda baki ba musamman Nur da har yanxu ta kasa sakewa dashi as abokin mijinta.