Dr. BOBBY COMPLETE HAUSA NOVEL

Dr. BOBBY COMPLETE HAUSA NOVEL

Kai tsaye yana fita parking space ya nufa…driver na ganinshi ya mike da sauri yazo ya gaisheshi tareda tambayanshi motan da zasu fita…Bobby bai iya cewa komai ba sai juyawa da yayi yana kallon motocin..idonshi ya sauka kan wata Benz dinshi daya dade bai hau ba dan haka yace a fito da ita kawai..cikin hanzari Mr.Obi yayi clearing motan dukda dama ba wani datti ke gareta ba cox ana yawan wankesu snn ya fito da ita..ya bude back seat da kanshi ya shiga snn driver yaja motar bayan ya gama warming dinta suka fita daga gidan..kai tsaye yace ya fara kaishi Hospital.

Bai baro asibitin ba sai after 11 kai tsaye kuma suka wuce College…suna hanya ya kira Nur yace gashi nan zuwa shima yace dama already yana cikin college din shi yake jira…da yake akwai dan nisa tsakanin Hospital da College din basu suka isaba sai 12…bai fito daga mota ba ya kira Nur sai gashi ya fito daga office hihi ma ya da cikin motan nasu suka shiga Hostel din…as always sukayi parking daidai second gate snn suka fito zuwa ciki…daya daga cikin Matrons dake kula dasu tayi musu jagora har cikin apartment da abun ya faru..wutar apartment din ya dauke gaba daya..Nuru yace”amma daga wane room abun ya fara?..”ba musu Matron ta kaisu har cikin dakin..babu kowa ciki kasancewar an riga an sanar dasu cewa Provost zai shigo dan basu san har proprietor zaa zo ba…karema dakin kallo suka hau yi idanun Bobby ya sauka kan gadon Lamido da har yanxun ke shimfide da bedsheets na Man Utd..ya kalli gadon da kyau sai kuma ya ta6e baki cikin ranshi yana mamakin wai mace da football…duk iya dubansu basuga wani alama na wani abu ba har sun juya zasu fita ta fito daga kitchen hannunta rike da plate din indomie tana cewa”Billy you need to taste this…”magananta ya makale sakamakon mutanen data gani a dakin…yau ma dai kaman ko yaushe jessy ne a jikinta fara na Manchester sai wandon jessyn daya tsaya mata iya guiwa…gaba daya tsayawa sukai suna kallonta…ita kanta mutuwar tsaye tayo a wurin don kwata kwata batasan suna cikin dakin ba…juyawa tayi da sauri tana zazzare idanu kaman wanda tayi ma sarki karya…idanunshi ya sauka bayan rigan nata da aka rubuta POGBA da capital letters sai a kasa kuma aka zana katoton number 6…wani haushi yaji ya sake turnukeshi…ita kuma kaman wanda aka tsikara ta bude wardrobe da sauri ta rarumo hijab din Billy ta zura a jikinta…sai a yanxu Nur ya samu baki mgn”Lamifo is this your room?..”tana kokarin kakalo smile tace”yes sir..good afternoon “..yace” afternoon amma garin ya wuta yayi spark a nan?..”tayi kasa da kanta ganin irin kallon da Bobby ke mata tace”muma bamu saniba sir..kawai muna zaune sai mukaji wani kara”..bata rufe baki ba Bobby ya juya ga Matron data rakosu yace”waye dayan wanda suke tare a dakin?..”da sauri matar tace”bari a kirata Bilkisu ce”..daga haka ta fita sai gasu sun dawo tareda Billy da tayi kasa da idanu sbd idanun Dr.Bobby da ko kusa bata kaunar ya zuba mata su…sumi sumi ta karaso cikin dakin tareda tsayawa kusada Lamido da itama nata tun dazun yake kasa…shi kuma ya shiga binsu da kallon da suka tsana ya ganeta sarai itace ta rakata Clinic ranan da ya mata allura..baisan meyasa jikinshi ke bashi akwai dalilin yin spark din ba..kuma as far s Lamido is concern yasan abunda yafi haka ma zata iya aikatawa cox a dan ganin da yayi mata yaga alaman ba karamar fitinanniya bace..cikin voice din daya sake tsoratar dasu yace”now tell me..waye ya kusa haddasa min gobara a building?..”sukayi shiru ba mai kwarin guiwar yin mgn cikinsu…ya daka musu wani tsawa yace”are the two of you deaf?..”jiki na rawa Billy tace”Sir itace ta jona iron ta barshi a jiki”..tana rufe baki itama Aysha tace”Sir karya ne itace ta jona iron din ta tafi tayi bacc..”ragowar mgnr nata ya makale sakamakon idanu data hada dashi…wani irin kulululu taji cikinta nayi kaman zataje toilet..Allah ya zubama idanun nan nashi wani kwarjini na musamman dake sa mutum ya shiga taitayinshi da zaran ya hada ido dashi…shi kuwa Bobby da gayya yayi hakan don yasan duk iskancinta ta kalli cikin idonshi saita saduda…lokaci guda wasu hawaye suka ciko idanun nata gashi har yanxu ya kafeta dasu ko blinking bayayi…hatta Bilkisu da nata idanun ke kasa ji take kaman ana wura mata wuta a cikinta tsabar tashin hankali…maimakon ya dauke idanun nashi sai ya shiga takawa a hankali har zuwa inda take…ya tsaya dab da ita hannayenshi zube cikin pockets dinshi cikin wani stern masculine voice dinshi yace”Now speak”..idanunta ta lumshe hawayen dake ciki suka cigaba da gangarowa cikin ranta ko duk addu’an da yazo bakinta yi take dan yanda taji kaman an daureta da sarqoqi ne an kuma jefata a cikin kurkuku tsabar rudanin data shiga…ganin halin data shiga Nur yayi saurin matsowa inda suke saidai kafin yayi magana Bobby ya daga mishi alaman he shouldn’t say a thing..ba yanda ya iya haka ya koma baya tareda rungume hannu yana binsu da kallo.

Masu bukatan siya zasu tura 300 zuwa 2208991344 Aisha Ahmad Tijjani Zenith Bank..sai a tura evidence of payment ta 07063800556.

Rano✨

????Dr.BOBBY????

By Aysha Rano✨

Wattpad@aysharano22

07

Saida ya sake dinke fuskanshi tsaf snn yace”i said speak”..a hankali tayi kasa da kanta tana fidgeting fingers dinta kuma har yanxu gayyar hawaye basu dena sukuwa kan fuskanta ba tace”Sir bacci ne ya daukeni”..ba tareda ya dauke idonshi daga kanta ba yace”da kika jona iron din sai bacci ya daukeki right?..”a hankali ta gyada mishi kai…a fusace yace”how dare you do that?..qona min building kikeso kiyi?..”tayi shiru kanta a kasa..yace”i said qona min building kikesonyi?..”ba tareda ta dago ba ta girgiza kai alaman aah..shi kuma cikin wani additional 6acin rai da yaji yana saukan mishi yace”Billahi if you dare repeat this again you will see the devil side of me..are you mad da zaki jona abu a wuta snn kije kina bacci?..”ya karasa mgn yana wani huci..shi kanshi baisan daga ina wnn 6acin ran ke saukan mishi ba…Nuru ya karaso tareda kama hannunshi yace”zo mu tafi dan Allah what’s done is done saidai a kiyaye gaba kuma”..baiyi masa musu ba ya bishi suka fita daga dakin matron ta bi bayansu…suna fita ya daddage ya fizge hannunshi dake cikin na Nuru snn ya karasa inda motarshi yake ya bude ya shiga…shima Nur karasawa yayi ya shiga snn ya dauko wayanshi ya kira mai gyara musu wuta yace azo a gyara a yau din nan…bayan ya kammala ya juya yana kallon Bobby daketa faman cika yana batsewa yace” Bobby are sure you are alright?.. wnn 6acin ran duk na meye?..”ko kallon inda yake baiyi ba balle yasa ran samun amsa…shima baiyi expecting amsan nashi dan haka yaci gaba da mgnrshi”you shouldn’t have acted like that sai kace secondary school?..besides kudi fa suka biya”..tun kafin ya rufe baki ya juyo yana kallonshi da wani irin karaji yace”seriously bayansu kake bi?..yanxu da sun konamin building zaka iya biyana ne?..kuma da suka biya kudi ai ba kudin building dina suka biya ba kudin zama cikin Hostel suka biya so dole inyi mgn idan naga zaayi min 6arna”…shiru kawai Nuru yayi yana kallonshi deep down yasan da akwai abunda ke damunshi…ya tabbata wnn fushin ba iya na an kusa kona masa building bane dole da akwai wani abun a kasa…har suka koma cikin makaranta ba wanda ya sake cewa komai a cikinsu…kafin su fita Nuru yace zai sauka dan bai gama aiyukan da yakeyi ba..babu wasting of time driver yayi parking shi kuma ya bude motar ya sauka snn suka cigaba da tafiya…bayan fitarshi Bobby ya sauke wani numfashi da yake rike dashi tun dazu tareda jingina jin seat din da yake hadi da lumshe idanu…baisan wane irin bala’i bane ya hau kanshi yau din nan…shi kanshi haushin kanshi yaji yanaji bai kuma san dalili ba…har ga Allah maganan da Nuru ya fada yasan its not that far from the truth..bai kamata yayi acting kaman yanda yayi ba amma ko Allah ya san shi kanshi baisan abun da ya hau kanshi ba a lokacin..bai kuma san daga ina duk wnn masifan yayita tahowa gareshi ba…kawai shidai ya tsinci kanshi cikin tsananin 6acin rai which he couldn’t control..ya lunshe ido yana sake budewa har yanxun idanunshi basu dena hasko mishi ita sanye da kayan ‘yan ball ba…ya saki wani tsaki kuma wai sbd tsabar iskanci shine ta juya musu baya wato tunda sun gama ganin gaba su kalli bayan ma knn…yau ya sake tabbatar da cewa ita din sangartacciya ce..idan ba haka ba why yarinya mace kamarta zaa barata tana supporting wani football club kuma har a gidansu a biye mata ana wani siya mata jessy da gajeren wando tana sawa..wai har bedsheet na Manchester sai kace wata namiji…runste idon yayi yana wani girgiza kai duk a kokarinshi na ya dena ganin pictures din nata saidai to no avail…gaba daya yaji yayi dana sanin zuwa Hostel din ma at the first place..daya sani da Nur ya kirashi kawai yace mishi bazai samu daman zuwa ba da shknn babu shi babu ganin wnn masifa…wnn yarinyar ya rasa wace iri ce ita da take kokarin yi masa kutse cikin rayuwarshi…ya tabbata masifan daya rufeta dashi hadda tsanar da yayi ma ‘yan garinsu yasa shi haka…kilan da bai san ‘yar Gombe bace bai zama lallai ya aikata abunda yayi ba…jingina ya sakeyi yana kara sakin wani tsakin duk ranshi yabi ya jagule…a daya 6angaren kuma ga wancan mara kunyan da yake kokarin sake kustowa cikin rayuwar ‘yar uwarshi again..baisan me yake takama dashi ba har da zai dauki waya ya kirata sbd bashida kunya…sai kuma wnn kaddararren lecture da Mummy tace sai yaje yayima yaran can..shi sam wnn abun bi gamsheshi ba…baima san taya zai fara shiga class ya rike marker yace zaiyi musu lectures ba..baisan ta ina zai fara ba…a takaice har suka kai gida bai dena wadan nan tunane tunanen ba..gaba daya kanshi ya dauki wani zafi kaman wanda ke amfani da wutar lantarki.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128Next page

Leave a Reply

Back to top button