Dr. BOBBY COMPLETE HAUSA NOVEL

Da dare suka shiga main house sakamakon kiranshi da Mummy tayi tace yazo tareda Aysha tanason magana dasu.
Rano✨
Wnn littafin na kudi ne ban yadda wani ko wata ya fitarmin dashi ba…masu buqatan siya zasu tura 300 zuwa 2208991344 Aisha Ahmad Tijjani Zenith Bank…sai a tura evidence of payment via 07063800556.
62
Tun daga compound da yaga bakuwar mota yasan lallai sunada baqi a gidan maybe ma shine dalilin kiran nasu da Mummy tayi saidai suna shiga parlor yaci karo da akasin haka..baban su Miemie ne zaune cikin parlon sai aunty sumy da yaran nasu gaba daya..duk yanda yaso kar ya tuna abun da suka faru a baya kasawa yayi dan yana ganinshi yaji komai ya shigo dawo mishi kmr yanxu abun ke faruwa..yana ganinsu ya taso da sauri yazo inda suke yana mika mai hannu da murmushi..Mika nashi hannun shima yayi yana kokarin ganin ya danne abunda yaji cikin ranshi suka shiga gaisawa a haka..bayan sun gama ya kalli Aysha itama suka gaisa duk yayi congratulating dinsu on their marriage..du Miemie ma suka gaidasu snn ya kama hannun matarshi suka nufi flat din Mummy..tana zaune parlor ita kadai suka shigo ciki..tana ganinsu ta saki murmushi har suka karaso ta kama hannun Aysha dake kokarin durkusawa a kasa ta zaunar da ita nan kusa da ita tace”har yanxu bazaki dena wnn ba koh”..murmushi kadai tayi kanta kasa..batasan meyasa har yanxu ta kasa sakewa da itaba..kunyarta takeji sosai ba kadan ba..bayan sun gaisa Mummy na dubanshi tace”Kun hadu da Isma’il a parlor?..”yace”na ganshi Mummy”tace”Waziri ne ya kira wai yazo su sake daidaitawa tunda auren bai yiwu tareda naku ba idan sun daidaita sai a maidashi nan da sati biyu”..gyada kai kawai yayi yace”to Allah tabbatar da alkhairi”.. Mummy tace”Ameen ko har yanxu bakason mgnr ne?..”da sauri yace”aah indai taga zata koma ai inaga hakan zaifi ko dan sbd yaran ma”.. Mummy tace”ko daxu da yazo bakaga murnan da yaran sukayi ba ni har tausayi suka bani wlh”..gyada kai Bobby yayi yace”to Allah ya za6a mafi alkhairi..dama shiyasa kikace muzo?..”tace”aah mgnr zuwa Enugu ne bikin Tauhid”..Bobby ya dan wara ido yana kallonta yace”wai bikin har yazo?..”tace”yazo mana jibi nakeso mu wuce shiyasa nace kuzo tare in fada muku don kuje ku fara shiri”..dan marairaicewa yayi yana kallonta yace”yanxu Mummy sati biyu..”ai bata bari ya karasa ba tace”nace kuje ku shirya Bobby banason mgn..itama Sumayya dasu Miemie duk tare zamu wuce shi Sab dai tunda yana makaranta banda shi”..kallonta kawai yake bai sake cewa komai ba sai kai daya daga mata..Mummy kuma ta juya tana kallon Aysha tace”ai kinason zuwa ko Aysha?..”da sauri ta gyada kai tana murmushi tace”sosai ma Mummy..i love travelling”..da fara’a Mummy tace”MashaAllah”..Bobby da yaji haushin reply din nata ya dungure mata kai yana dan hararanta yace”sarkin yawo kawai”..bai ajiye hannu ba shima Mummy ta dungure nashi kan tace”kai kuma sarkin kulle ba”..da sauri ya dafa kan yana kallonta kmr zaisa kuka..a tare Mummy da Aysha suka tuntsire mishi da daria..he look funny ne yanda yayi squeezing face dinshi..shima dan murmushi ya saki yana relaxing kan kujera shi bason tafian nan yakeyi ba wlh..yasan yanxu idan sukaje sai suyi sati a can shikuma takura zaiyi ya sani..dan ba yanda zaiyi da Mummy ne amma da bazai je ba wlh..yasan idan taso abu irin haka dole ne yayi hakuri yayi yanda takeso musamman idan abu ya shafi zumunchi don shi gani yakeyi duk dunia babu mace mai son yan uwan da zumunchi kmr ita..sun dan ta6a hira kadan har su aunty sumy suka shigo bayan baban su Miemie ya tafi suma aka cigaba da hiran dasu..farin ciki kawai suke na tafia Enugu amma banda Bobby da ba haka aka so ba wai qanin miji yafi miji kyau.
Koda suka koma gida haka yayita kumbure kumbure wai shi bayaso ita kuma tana mishi daria..da kanta ta hada musu kayan tafia kowa akwatinshi daban amma yana gani ya fito da kayan ya hadesu cikin guda daya wai yanda ba wanda zai rabasu tunda kayansu na hade dole a bar masa matarsa..itadai daria yake bata dan tasan duk sbd me yake wnn abubuwan…washegari ma haka tayita shirye shirye tana bude jaka ta fito da wani kayan ko ta saka wani aikin knn tunda ta tashi daga bacci kmr wadda bata ta6a zuwa wani gari ba..murna kawai take ta samu saken fita don tun da akayi biki idan aka dauke gidan Mummy babu inda take zuwa.. she’s always at home kmr matar malam..suna gama lunch ya dauketa zuwa daki wai zaiyi maganin dariar da take mashi aikam nan da nan ta shiga hankalinta ta fara bashi hakuri kmr zatayi kuka..shi kuma bai saurara mata ba saida yayi maganin bakin da take dariar dashi..bayan sunyi wanka ya sake janta suka koma gado wai duk yau ta jama kanta a haka zasu yini tunda take mishi daria itadai batace komai ba don tasan ko zata shekara cewa ya kyaleta ba kyaletan zaiyi ba shiyasa tayi shiru da bakinta..ganin kmr he is in a good mood tace bari tayi using wnn opportunity tayi mashi zancen komawa hospital..tana kwance a jikinshi tana wasa da gemunshi tace”partner”..hannu yakai ya sake matseta jikinshi yafin ya amsa da”yes partner”..murya can kasa tace”So nake in koma asibiti”..da sauri ya dago yana kallonta yace”are u sick?..”tace”No inaso in koma aiki ne..kaga duk yan class dinmu fa suna waiting results amma ni banda ni”..ta karasa mgn tana kwabe fuska kmr zatasa kuka..Jan cheeks dinta yayi yana murmushi yace”kema zaki koma ai amma ba yanxu ba”..da sauri tace”when”..yace”when the right time comes”..kallonshi ta tsaya yi kmr zatasa kuka..sai kuma tale baki ta shiga bubbuga legs dinta akan gadon tace”nidai inaso in koma plss..so kake skills dina ya gudu”..daria yakeyi sosai bayan yayi pecking lips dinta yace”ba wani skills dinki da zai gudu.. believe me very soon zaki koma”..banza tayi dashi tana cigaba da diddirza kafafunta..baiyi yunkurin hanata ba sai matsar da bakinshi da yayi saitin kunnenta yace”naga alama u want some more and believe me idan kika cigaba da abun nan kome ya biyo baya ke kika siya”..tun bai rufe baki ta shiga hankalinta don tasan kadan daga aikinshi yayi yanda yace wlh..ita wani lokaci har mamaki yake bata..shidai kullum ayita abu daya ko gajia bayayi.
The next morning kmr yanda Mummy tace suka tafi Enugu gaba dayansu…basu sauka a can ba sai around 3 don haka bayan sun huta gajia Mummy da kanta ta kaisu gidan wani uncle dinta suka gaisheshi daga nan kuma sukaje bikin da ya kawosu.. traditional Igbo day sukayi suma exactly irin wanda akayi na bikinsu saidai Lamido gani take kmr wnn din yafi nasu batasan ko sbd su din gaba daya inyamuran bane amma abun ya burgeta matuka haka ta dinga daukan pictures da videos tana turama su Ammi da Billy wai su kalli bikin inyamurai..ranan basu dawo masaukinsu ba sai dare sosai..gida ne guda na Mummy da sauran ‘yan uwanta suka sauka a ciki..daki daya aka basu da Miemie,aunty sumy da Ilham Mummy kuma ita kadai sai Bobby tareda wani cousin dinshi..yaji haushi sosai da aka rabashi da matarshi amma ba yanda ya iya da Mummy dan yanxu yana mgn ne zatace ya zama mara kunya snn ita kanta Ayshan ya fuskanci murna ma takeyi da hakan..bayan sun dawo duk sukayi shirin bacci kowa ya kwanta saidai tana kwanciya kiranshi ya shigo wayarta dan haka ta mike zaune bayan ta daga kiran tace”partner bakayi bacci ba”..tana rufe baki yace”how do u want me to sleep without u?..plss kizo parlor ina nan ina jiranki mu tafi..i can’t sleep without u”..dan murmushi ta saki tana girgiza kai tace”yanxun partner kawai sai Mummy taga nazo dakinka?..no can’t do that plss..besides naga ba kai kadai zaka kwana a dakin ba”..tun bata rufe baki ba yace”we’re not sleeping here hotel zamuje..plss baby kiyi sauri kizo am waiting for u here”..dan langabewa tayi kmr yana ganinta tace”partner kayi hakuri i can’t come out now..kaga Mummy fa bazata ji dadi ba idan na b…”tun bata karasa ba yace”then bari inzo in daukoki tunda cewa kikayi u can’t come out now”..zare idanu tayi hadda su rufe baki jin abunda ya fada..ita fa bazai sata jin kunya ba wlh..sanin zai iya aikata abunda ya fada ta mike da sauri ta sama kofar key tareda dawowa cikin dakin ta zauna tanaji ya kashe kiran tasan nan din ya taho..yana zuwa kuwa ya murda kofa yaji a rufe ya kira bata dauka ba dan haka ya koma daki cikin ranshi yace yasan yanda zaiyi maganinta.