Dr. BOBBY COMPLETE HAUSA NOVEL

Washegari bayan sunyi sallama da kowa suka dawo Kanon Dabo..around 2 something suka isa gida dan haka kowa matsuguninshi ya wuce don huta gajia.
Kwanakin da suka biyo baya kuma shirye shiryen daurin auren aunty sumy suke da za’ayi this coming Saturday..dukda ba wani biki zatayi sosai ba sudai sunata shirinsu wai a cewarsu yanda ta dade batayi aure ba ya kamata tayi biki sosai ita Kuma tace baza tayi ba..maza ne kadai zasuje Gombe daurin aure mata kuma suyi yininsu a nan gidan nasu zuwa dare kuma akai amarya don Waziri yace bai yadda da a daura aure kuma amarya tacigaba da zama a gida ba gwara a hada komai ayishi lokaci daya a wuce wajen…tunda Aysha taji mgnr zuwa Gombe duk ta daga hankalinta wai dan Allah yaje da ita amma yace sam ba inda zataje tunda bada mata za’ayi tafiyar ba..haka ta karaci fushinta ta gama daga karshe ya lalla6o ya lalla6a kayarsa suka shirya kmr dai yanda aka saba.
Ranar Saturday kmr yanda aka tsara su Bobby sukaje har Gombe inda Waziri ya sake maida aurenta da Isma’il akan sadaki mafi kankanta…Kai tsaye daga wajen daurin aure wurin reception suka wuce inda Bobby keta tsokanar Nur wai ‘yar yara zai aura tunda gashi bikin uwa da ubanta yazo kuma wai hadda reception..daria yakeyi sosai ya dauka aunty sumy ce kadai mai dabi’un yara ashe shima mijin nata haka yake idan ba haka ba meye wani reception kmr auren fari..gashi kuma sai wani farin ciki yake yana gaisawa da mutane yanda kasan bai ta6a aure ba shidai Nur sauraron iskancinshi kawai yakeyi babu bakin mgn don shi kanshi dai yaji abun wani banbarakwai wai namiji da suna hajara..gaba daya sirikar tashi baya tunanin ta bashi sama da four years amma ya zaiyi tunda yana son ‘yarta?..shi kanshi dai zuwa yanxu ya tabbatar da ‘yar yara din zai aura kaman yanda Bobby yace amma who cares?..shidai fatanshi bai wuce ya auri Miemie ba kuma yasan da yardan Allah zai samu so bashida wani matsala da yarintar iyayenta…kafin a tashi daga reception suka bar wurin zuwa Lamido’s Palace don zuwa ya gaida daddy da kuma Lamido kmr yanda Waziri yace lallai kada ya bar Gombe ba tareda yaje ya gaishesu ba..suna daukan hanya shima Nur ya fara nashi iskancin shidai yanajinshi baice komai ba don tareda driver suke..gidan Lamido suka fara zuwa suka gaisheshi daga nan kuma suka karasa gidansu dama daddy da bai dade da shigowa gari ba..a parlonshi suka sauka bayan sun gaisa ya tambayesu aiki da sauransu suka amsa da lafia..daddy ya dora da tambayan ko Aysha tanayi mashi wani abun don a cewarta yasan har yanxu wauta bai saketa ba..shidai Bobby ya amsa da ba komai don harga Allah idan yace yarinyar nan tayi mashi wani abu daga aurensu zuwa yanxu to tabbas ya zalunceta..Ammi tasa Husna ta kawo musu abinci dasu ruwa duk suka kasa sakewa suci wai akan hanya suke..ko suna nan cikin parlon Aysha ta kirashi kusan say uku bai dauka ba sbd daddy and yasan duk Kiran bazai wuce akan yaushe zasu dawo ba?..Ammi ma tazo suka gaisa itama ta tambayi ko tana mishi wani abu da ha daidai ba yace shidai ba abunda take mishi lafia Lau suke zaune hakan kuma ya mara dadi matuka tace ashe dai ‘yar tata ta fara hankali yanxu..nan dai sukayi sallama dasu suka wuce kai tsaye daga nan kuma suka dauki hanyan Kano..tun a hanya Bobby ya kira aunty sumy yana tsokanarta wai an daura itadai tayi mashi banza daga karshe ma kashe wayarta tayi tana ayyana kalar walakancin da zatayi mashi duk ya shigo hannunta…karfe biyar da wani abu suka sauka Kano inda kai tsaye gidan Bobby suka sauka don main house dai sunsan bazai shigu yanxu ba sbd jama’a don haka suka fara branching a nan kafin mutane su ragu…bayan sallahn magrib few mutane da Mummy tayi selecting suka raka amarya aunty sumy gidanta.
Wnn knn
Bayan sati biyu…
Tsahon 5 weeks knn da bikin Bobby da Lamido..cikin 5 weeks din nn Aysha ta sake tabbatar da ba wata mace a zuciar mijinta sama da ita..ta kuma tabbata tafi duk wata mace sa’a da kuma dacewa da samun miji kmr nata..he is such a loving and caring hubby..he is super romantic..he is handsome and rich..he is so so down to earth infact he is all in a man and she is so very lucky to have found him..yanda yake nuna mata tsantsan so da caring abun har mamaki yake bata..kawai sai takega kaman duk dunia ba namijin dake nunawa matarshi so haka..kullum bai gajiya da nuna mata how much he loves and care for her..wnn dalilin yasa itama ta sake kware mishi..zuwa yanxu duk wani abu da yakeso ta sani ta kumayi registering dinshi cikin brain dinta tana mishi baja kolin irin nata caring din..tasan a daidai lokacin da yake da bukatan wani abu a wurinta likewise she knows exactly how to handle him..ita kanta yanxu har mamakin kanta take yanda ta dawo fitsararriya sbd shi..sam ta dena wnn kunyan don gani tayi idan fa ta tsaya kallon ruwa tsaf kwado zaizo ya mata kafa shiyasa ta tattara dan ragowan kunyan ta ajiye a gefe ta kuma shiga nunawa mijinta shi kadai ne namijin da zataso har karshen rayuwarta..rayuwarsu is so full of soyayya,farin ciki da kuma girmama juna kmr ba Lamido da Bobby da basa ta6a jituwa a baya ba..bayan four weeks da biki Bobby yayi resuming office ranan har kuka saida tayi masa wai bazaije ya barta ita kadai ba batasan shima idan na son ranshi ne bazaije ya barta ba amma it’s his work dole ba yanda ya iya haka zai koma tunda bazai taba dawwama zaune a gida ba..ranan yini tayi kuka saida ya dawo ya fara aikin lallashi ta hanyar da yasan iya taurin kanta sai ta saduda kuma hakan ne ya faru don tuni ta mance da wani kuka ta bada kai bori ya hau.
Yau Thursday karfe hudu da 35 mins ya dawo daga office..ya shigo ciki rikeda briefcase dinshi as usual ya kama hanyar flat dinshi sai Kuma yajiyo kmr motsinta a kitchen dan haka ya ajiye briefcase din nashi a nan parlor ya nufi kitchen din..tsaye ya ganta jikin gas tana kokarin juye ruwan zafin data tafasa a wani bowl daga ita dai jean da Jessy dinta na Man u red..kallonta ya tsayi from head to toe yanda shape dinta ya fito sosai a cikin kayan..ya hanata da Jessy din nan amma har yanxu taki denawa wai ita tafi sabawa dasu dole haka nan ya bari take sawa a gida bada son ranshi ba
..a hankali yana karasawa ciki ya dagata sama ya shiga juyi da ita cikin kitchen din yana kissing duk inda yaci karo dashi a jikinta full of excitement yake cewa”baby am back..i missed u so much..muahh”ya karasa yana sake manna mata peck a forehead dinta ita kuma ta zagaya hands dinta a wuyanshi tana kallonshi da murmushi tace”welcome back love”..makale mata shoulder yayi tareda nuna mata lips dinshi da hannu daya yana wani kashe ido yace”here”..makale nata shoulder itama tayi tana dungure kanshi tace”No”..fuska ya kwabe kmr zaisa kuka ya shiga bubbuga legs dinshi a kasa still Kuma yana daukeda ita a hannunshi kmr ba abu mai nauyi ya dauka ba yace”Allah sai kinyi”..daria ta saki tareda matsar da head dinta tayi pecking forehead dinshi snn ta dago tana murmushi tace”now saukeni”..shoulder ya sake makale mata alamar he won’t..kallonshi tayi for some secs sai kuma ta lumshe ido ta dora finger dinta akan lips din nashi kafin ta bude idon tace”promise it won’t pass that”..da sauri yace”i promise..only kiss”..lumshe Ido tayi bayan tace”ohk”..snn ta sake matsawa a hankali ta hade bakinshi da nata shima yayi grabbing da sauri kmr abunda yake jira knn..after like 5 minutes ta samu ta kwace bakinta da kyar tana kokarin sauka kasa tace”wnn shine promise din?..”ajiyeta yayi tareda sake janyota ya hadata da jikinshi yana sauke numfashi yace”sorry i couldn’t stop myself”murmushi ta saki bayan ta janye hands dinshi daga jikinta ta shiga nuna mishi kofa tace”oya muje kayi wanka sai kazo kaci abinci”..shoulder ya sake makalewa yana kallonta kasa kasa yace”No..me kikeyi a kitchen?..”kama hannunshi tayi suka fita daga kitchen din tace”custard zan dama”..da sauri yace”nima ina shan custard din plss”..girgiza kai tayi tana murmushi tace”naji..amma muje ka farayin wanka first”..bai sake yi mata musu ba yabita har zuwa flat dinshi..suna shiga bedroom ta saki hannunshi snn ta zaunar dashi gefen bed ta shiga unbottoning shirt din jikinshi..kallonta kawai yakeyi yanda ta cire shirt din nashi ta ajiyeshi gefe ta zare singlet shima ta ajiye gefe sai kuma ta mikar dashi tsaye ta zame trouser leaving only shorts a jikinshi snn ta sake jan hannunshi har cikin bathroom shi kuma sai binta yake kaman wani rakumi da akala..tana gama hada mishi komai ta fita da sauri don tasan tsaf zai iya riketa ya hanata fitowa ita kuma bata shiryama wnn fitinan nashi ba shiyasa tayi saurin fitowa tun kafin ya rutsa ta…closet dinshi ta shiga ta fiddo mai kayan da zai saka snn ta fita don karasa dama custard dinta tunda already tayi setting dinning tun kafin ya dawo..saida ta sake kunna gas ruwan ya tafasa snn ta dama custard din ta fito dashi a hannu tana juyawa da spoon..a dinning taja kujera ta zauna tana cigaba da juyashi don so take ya danyi sanyi kafin tasha..tana sane taki komawa dakin sbd gudun kada ma ya ganta ya hanata fitowa..komawa tayi kitchen ta zuba milk da sugar cikin custard din nata snn ta sake dawowa dinning din ta zauna ta fara shan abunta hankali kwance..Bobby ko yana fitowa daga bathroom sharp sharp ya shirya cikin kayan da ta fito mashi dasu snn ya fita don cin abinci..yana hangota zaune tana shan custard dinta yace”baby rowa koh?..”dan dagowa tayi tana kallonshi daidai lokacinda ya karaso dinning din ya ja kujera ya zauna kusada ita ta mika mashi bowl din tace”to Bismillah”..makale shoulder dinshi yayi yana hararanta yace”banaso ai saida na roka kika bani”..da sauri tace”to zan dama maka wani”..tabe baki yayi yana girgiza kai yace”No”..nan da nan ta tale baki ta shiga mishi kukan karya tana bubbuga legs dinta kasa tace”Allah nidai sai kasha”..murmushi yayi sosai gamida dan matsawa saitin kunnenta yana shafa gemunshi yace”baby da kiyi saving wnn strength din for later..naga kaman zaifi maki amfani a can”..da sauri ta hadiye kukan nata tana hararanshi tace”ni saloon zaka kaini ai”..plate ya dauka ya fara serving kanshi tayi saurin mikewa ta karba tacigaba dayi shi kuma ya relaxing ya rungume hannu yana kallonta da murmushi yace”saloon da yamman nan baby?..”da sauri tace”eh ai Kaine kace yau zamuje kuma nidai bazan sake kwana kaina ba kitso ba”..kama hannunta yayi bayan ta gama serving dinshi yace”baby da ki bari sai gobe”..tun bai rufe baki ba tace”ni yau nakeson zuwa”..bai sake cewa komai ba ya shiga cin abincinshi itama tacigaba da Shan custard dinta..yana cin abinci yana santi dan da gaske tana maida hankali tayi mashi girki yanda ya kamata shiyasa a kullum yakejin abincin nata so delicious kaman abunda ta karanta knn a school..tana gama Shan custard din ta mike zuwa flat dinshi ta dauko car keys dinshi tun ma kafin ya gama yace mata ba yanxu ba snn ta wuce bedroom dinta ta zumbula zumbulelen hijab dinta ta fito rikeda phone dinta a hannu alamar she’s ready to go..yana gama cin abincin yayi clearing dinning din da kanshi snn ya koma parlor yana sipping drink..kokarin kunna tv yake kawai sai ganinta yayi tsaye a gabanshi tana mika mashi key din mota..daria ya saki yana kallon yanda ta wani hade rai yace”yanxu baby ko hutawa bazanyi ba?..”kai tsaye tace mishi”idan mun dawo sai ka huta..nasan da hutawa wlh cewa zakayi sai gobe ni kuma am tired of zama da gashina a haka so kawai ka tashi muje ko kuma wlh in kira Mummy”..ajiyar zucia ya sauke tareda mikewa ya amsa key din suka fita daga gidan..tunda tasama ranta sai taje yasan idan ma baije ba ba barinshi zatayi ya sarara ba and tana hadashi da Mummy yasan nashi ya kare.