Dr. BOBBY COMPLETE HAUSA NOVEL

Dr. BOBBY COMPLETE HAUSA NOVEL

Suna isa gida dama direct main house Nur ya shiga yayi parking snn ya bude kofa ya fita..shima Bobby fitowa yayi snn ya zagaya ya fito da ita sai wani hadata da jikinshi yake ita kuma tana kaucewa amma still bai bari bar har suka shiga gidan..Nur dai a baya yake binsu yana murmushi har yanxu kasa dena smiling sbd excitement..he is so happy for the both of them..suna zuwa daidai entrance Lamido ta dakata tareda zare hands din Bobby daga jikinta tana kallonshi da dan marairaicewa tace”partner just stop it mana..Mummy fa tana ciki”..murmushi ya saki tareda bending ya danyi pecking lips dinta snn ya kama hannunta ya rike yana kallon eyeballs dinta yace”is this ohk?..”girgiza mishi kai tayi da sauri tana kwabe fuska tace”Noo”..sai kuma ta shiga bubbuga kafa zata fara mishi kukan karya yayi saurin sakin hannun nata yana cewa”No no don’t do that plss..gashi na saki hannun naki is that ok?..”kai ta gyada mashi tana sakin murmushi sai kuma ta shige cikin parlon..da kallo ya bita har ta 6ace ma ganinshi snn ya sauke wani ajiyar zucia mai karfi daidai lokacinda Nur ya karaso inda yake dan haka suka shiga ciki a tare..Lamido na shiga Miemie dake zaune dinning tana karatu tayi saurin mikewa tazo gareta tana wara idanu cikeda mamaki tace”Goodness!..aunty Aysha me yayi maki haka naga kin samu sauki?..”Bobby da yaji duk abunda ta fada ya dan watsa mata harara yana cewa”gidanku nayi mata”..da sauri ta kama bakinta tana yin kasa da kanta tace”ohh yi hakuri Uncle Bobby”..bai sake ce mata komai ba ya wuce flat din Mummy shi kuma Nur ya karaso nan cikin parlon ya zauna yana kallon Miemie da yakejin kmr ya maidata ciki yace mata”hey pretty”..kama hannun Aysha tayi suma suka karasa ciki suka zauna snn ta dawo da kallonta gareshi tana murmushi tace”Uncle Nur ina yini”..yace”fine pretty..ya exams?..”tace”Monday zamu fara”..yace”MaashaAllah..Allah bada sa’a..yasu aunty da Ilham?..”..tace”Ameen Ameen Uncle Nur nagode..su Aunty suna gidansu muma gobe zamuje ko aunty Aysha?..”ta karasa mgn referring to Lamido dake zaune tana sauraran conversation dinsu tana daria kasa kasa..da sauri tace”yeah indai naji sauki sosai gobe zamuje inshaAllah”..sai kuma ta mike tunawa da batayi sallah ba tace ma Miemie”rakani daki inyi sallah plss”..ba musu Miemie ta mike suka nufi dakinta dake nan cikin parlon don ta baro flat din aunty sumy tun baya barinta gidan..suna shiga Aysha tace mata ta koma kar su bar Nur shi kadai a parlor dan haka Miemie ta koma parlor yayinda ita kuma ta tayar da sallahrta..har yanxu kuma ba wani karfi takeji a jikin nata sosai ba.

Rano✨

Wnn littafin na kudi ne ban yadda wani ko wata ya fitarmin dashi ba…masu buqatan siya zasu tura 300 zuwa 2208991344 Aisha Ahmad Tijjani Zenith Bank…sai a tura evidence of payment via 07063800556.
66
Bobby na shiga ya iske Mummy a parlor suna waya da aunty sumy..bai damu ko ta gama wayan ko bata gama ba kawai yana zuwa ya zauna kusada ita tareda mata side hug ya kwantar da kanshi a shoulder dinta cikin so much farin ciki yace”nwunye m di ime Mummy”..(my wife is pregnant Mummy)..da sauri Mummy ta dago kanshi tana kallonshi cikin tsananin farin ciki tace”are u for real?..”da sauri yace”yes i am Mummy..she is four weeks pregnant”..wani irin zare idanu Mummy tayi cikin so much excitement kafin tace wani abu aunty sumy data gama sauraran duk abunda ya fada sbd call dinsu is still connected ta saki wani irin guda tana cewa”My Bobby is becoming a Father.. Alhamdulillah”..da sauri Bobby ya dauki wayan daga jikin Mummy ya manna ta kunnenshi yace”yes aunty am becoming a father..am becoming a father”..wani murmushi ta karasa saki before tace”congratulations qanina..Allah kawo mana babyn nan lafia and extend my regards to Aysha kace mata nace she should take care of our baby sosai”..ajiyar zucia ya sauke yana cewa”aunty ai har yanxu bata sani ba..i didn’t tell her”..da sauri aunty sumy tace”why?..”yace”rigima zataimun ne..i have to wait for the right time..yanxun allow me to talk to my Mummy plss..my regards to Ilham..kice mata her Uncle Bobby yayi missing dinta da yawa”..yana gama fadin haka bai jira jin me zata ce ba yayi disconnecting call din don yasan aunty sumy da zance sake dauko wani dogon surutun zatayi..yana ajiye wayar Mummy dake kallonshi full of surprise tace”meyasa baka fada mata ba Bobby?.. what’s the meaning of this?..”kama hannunta yayi yana dan marairaicewa yace”Mummy nasan halinta rigima zataimun wlh..kullum cewa take ita batason ta samu ciki da wuri and tunda Allah baisa ta gane ba we shouldn’t tell her plss”..a hankali Mummy tace”amma kasan zata iya ganewa ko ba’a fada ba Bobby..she is a health worker too..zata iya noticing some changes a jikinta da zaisa ta fahimci ciki ne da ita”..yace”na sani Mummy amma we shouldn’t tell her now..gwara mu bari har zuwa lokacinda zata fahimci tana dashi din da kanta maybe by then bazata dagamun hankali ba”..ajiyar zucia Mummy ta sauke sai Kuma ta rungumeshi cikin so much happiness tace”am so happy for u son..Allah ya basu lafia ita da abunda ke cikinta snn Allah ya sauketa lafia”..rungumeta back shima yayi yana wani lumshe ido sbd dadi yace”Ameen Ameen Mummyna..i can’t love u less”.

Da dare bayan sun dawo gida ya tilasta mata taci abinci snn ya bata paracetamol sbd fevern da yaji kaman zai dawo mata..suna zaune parlor suna kallo tanata faman cin apple daya yanyanka mata a plate daga ita sai dan sweet pants dinta blue da crop top baby pink..kanta da akayima kitso a bude sai daukan ido yake sbd kyan da yayi..yayinda ta maida hankali wajen cin apple dinta Bobby kuma yana zaune yana kallonta kmr yau ya fara ganinta..she looks do adorable right now..so looks cute that har baison ya dauke idanunshi daga kanta..kallonta kawai yake yana imagining yanxun da akwai da ko ‘yarshi inside her tummy..banda smile ba abunda yake saki yana shafa saje zuwa gemunshi cikin so much happiness..kawai he’s eager to see tummy dinta ya zama qato..he can’t wait for the baby to come..he wants to hold the baby’s hands snn yayi kissing forehead dinshi yace he loves him or her..he just can’t wait for the baby’s arrival..he’s so desperate..yayi nisa sosai cikin tunaninshi sai sakin smile yake kuma har yanxun yana shafa beard dinshi kmr wani sabon kamu..kamar daga sama yaga ta mike da sauri ta kama hanyar bedroom dinta har tana hadawa da gudu sbd ringing din wayanta data jiyo..nan da nan ya dawo hayyacinshi tareda mikewa shima yabita da sauri yanajin wnn gudun da take har cikin zuciarshi wlh..yayi zaton wani gagarumin abun zatayi a dakin but to his biggest surprise yana shiga yaga ta dauki wayanta da bai dena ringing ba tayi saurin picking call din ganin Hammanta ke kira ta zauna gefen gado tareda Kara wayan a kunnenta tana wani cunno baki tace”ba ruwan ni dakai”..daga daya bangaren Hamman nata ya saki daria yana cewa”C’mon mana Maama..ba’a jin tsakanina dake fa?..”sake turo bakin tayi tace”ba wani Maama ni ka dena kirana Maama tunda baka damu dani ba”..jingina Bobby yayi jikin kofar dakin tareda rungume hannu yana kallon ikon Allah..yanxun Najeeb din takema wnn shagwaban sai kace muharraminta?..Najeeb dake dariar wnn rikicin nata yace”ohk wait kiji abunda zan fada maki..gobe zamuzo Kano”..batasan lokacin da ta saki wani irin ihu ba sbd farin ciki tace”dan Allah da gaske Hamma?..”yace”of course mana..tareda su Husna da Bilkisu”..nan take ta Kara sakin wani ihun tana cewa”Hamma amma dai kwana zakuyi koh?..”da sauri yace”Ammi tace banda kwana so a goben zamu dawo”..dan marairaicewa tayi kmr yana ganinta tace”haba mana plss..ya kamata ku kwana ai”..yace”idan kinaso su kwana saidai ki kira Ammi da kanki”..yana gama fadin haka tace”alright let me call her yanxu”..daga haka ta kashe kiran sai kuma ta shiga neman number Ammi zatayi dialing..a hankali Bobby ya karasa inda take ya wani daure fuska ya fizge wayar daga hannunta yace”are u mad?..bakida hankali zakizo kina gudu haka?..and waya fada maki ana yima cousin irin wnn shagwaban?..”murmushi ta saki tana kallon yanda ya hade girar sama dana kasa..batace dashi komai ba sai mikewa da tayi tareda matsawa inda yake ta shige jikinshi..a tare suka saki ajiyar zucia Bobby ya zagayeta da hands dinshi murya can kasa yace”how many times do i have to tell u this?..na fada maki cewa duk wani cousin dinki ba muharraminki bane amma bakiji..ko so kike na fara kishi dashi?..”a hankali ta girgiza mashi kai alamar no..yace”then meyasa kike mashi abubuwan da ni kadai ya kamata kiyima a matsayina na mijinki?..kina tunanin bana jin haushi ne?..”a hankali ta dago kanta tana kallonshi shi kuma yayi cupping fuskanta yana cigaba da kallonta yace”if u think bana jin haushi u are very mistaken baby..kishi nakeji sosai duk naga kina mishi wnn shagwaban..banaso”..hannunta ta mika itama tayi cupping nashi fuskan tareda dan dage ta manna mishi peck a forehead snn tace”to na dena partner..am sorry”.. pecking nata back shima yayi yana cewa”na hakura love..yanxun yaushe ne zasuzo?..”da sauri ya dago taga jikinshi tana cewa”gobe..inaso in kira Ammi ince ta barsu su kwana yace saidai inyi mgn da ita”..ba musu ya kama hannunta suka zauna snn ya mika mata wayarta dake hannunshi yace”ohk call her”..da sauri ta karba tayi dialing number din Ammi..tana dagawa Aysha ta wani marairaice tana langabar da wuya kmr Ammin na ganinta tace”Ammi banida lafia”..daga daya bangaren Ammi tace”Amin wa’alaiki salaam”..da sauri ta gyara mgnrta da cewa”sorry salamu alaykum Ammi”..Ammi tace”wa alaiki salaam..ya gidan”..tace”lafia lau amma banida lafia”..ta karasa mgn kmr zatasa mata kuka ta wayar..Ammi tace”rashin lafiar kikema wnn abun sbd har yanxu bakida hankali”..turo baki tayi tace”Ammi zazza6i nakeyi sosai fa..kuma hadda amai”..Ammi tace”to Allah ya sawake..laifin Bobbyn ne da bai danqara maki allura ba”..daria sosai mgnr Ammi ya bata aikam ta shiga yinta kmr ba gobe..Saida tayi me isarta snn tace”Ammi wai su Husna zasuzo gobe?..”Ammi tace”eh zasuzo inshaAllah..tareda Bilkisu da Najeeb”..Aysha tace”Ammi dan Allah dan annabi su kwana”..Ammi tace”aah Aysha su da zasuzo da yawa banason suzo su takurama mijinki ne gwara suzo a goben su dawo ai yafi babu”..da sauri tace”Ammi dan girman Allah su kwana shida bama a dakina yake kwana b..”bata karasa ba Ammi tace”zakici ubanki wlh..wa kikaji ya tambayi inda yake kwana..wato har yanxu wnn shashancin yana nan kanki koh?..”shiru tayi tana danne dariarta tace”to Ammi kiyi hakuri..amma dan Allah su kwana ai munada dakuna da yawa”..Ammi tace”shknn sai suyi kwana biyu..dama shi Najeeb yace akwai aikin da zaiyi a garin na kwana biyu so idan ya gama sai su dawo tare”..cikeda farin ciki tace”yauwa Ammi nagode sosai Allah ya kara girma..Ammi kema dai ya kamata kizo wlh”..Ammi tace”zanzo amma ba yanxu ba..saiki daure ki dinga shan magani ba sai ama tilastaki ba..Allah ya baki lafia ya maku albarka gaba daya”..cikin tsananin jin dadin addu’an na Ammi tace”Ameen Ameen Ammina..nagode”..Ammi tace”shknn sai anjima..ki gaida Bobbyn dasu mamanshi”..da sauri tace”zasuji inshaAllah..sai da safe”..daga haka sukayi sallama..Bobby kmr jira yakeyi ta ajiye wayar ya shiga kyalkyala mata daira sosai..dama da dadewa ya fuskanci there is a little drama between the mother and the daughter..hakan kuma its the sign of love they have for each other..yanda ta dauko zancen ba’a dakinta yake kwana ba ita kuma Ammin ta katseta was so very funny to him..kallonshi tayi yanda yake mata daria tana dukan chest dinshi tace”what?..”ya kama hannunta ya rike yana kokarin dakatar da darian nashi yace”nothing baby..kawai dai am happy gobe su Husna zasuzo”..lokaci daya ta washe bakinta itama tace”nima am happy sosai sbd nayi missing dinsu..i can’t wait to see them”..tana rufe baki ya dauketa suka fita daga dakin yana cewa”yanxun muje ki karasa cinye apple dinki sai muje mu kwanta sbd mu tashi da wuri koh?..”kai ta gyada tana sake lafewa a jikinshi..daga haka suka fita daga dakin..parlor ya koma ya dauki sauran apples dinta snn ya wuce flat dinshi..zaunar da ita yayi kan sofa tareda dora mata plate din apples din akan laps dinta yace he’s coming..parlor ya koma ya kashe su tv da bulbs snn ya rufe gidan da key ya koma flat din nashi..kwanciya yaga tayi bayan ta ture apple din nata gefe..ya karasa da sauri ya dagota yana cewa”baby what?..why baki cigaba da cin apple dinki ba?..”hannunshi ta kama ta dora a forehead dinta idonta har ya ciko da hawaye tace”kaji fevern nefa zai dawo”..da sauri ya zauna tareda dorata a jikinshi yana girgiza mata kanshi yace”no don’t cry plss..bazai dawo ba inshaAllah”..kuka ta fara mishi sosai tace”Allah zai dawo..yanxu haka su Husna zasuzo gobe ni banida lafia”..rungumeta yayi sosai yana shafa bayanta cikin sanyin murya yace”baby dan Allah stop crying..idan kina kuka zakiyi ciwon kai fa”..shiru tayi mishi tana cigaba da hawayenta as Allah kadai abunda takeji..nan take hankalinshi ya tashi ya shiga aikin rarrashi..gani yake kmr wnn kukan zaiyi affecting babyn cikinta..yasan yanda baason pregnant woman da damuwa shiyasa yake tsoron wnn halin nata.. yanxu idan wani abu ya samu babynshi ya zaiyi?..lalla6ata ya dingayi sosai har tayi bacci a jikinshi ya samu ya kwantar da ita..har zuwa lokacin kuma jikinta akwai zafi sosai dan zafin ma yafi wanda yaji a jikin nata daxun..lumshe ido kawai yayi yana tunanin taimakon daya kamata ya bata..yasan babu treatment din da zai dauke mata wnn zazza6in indai ba lokacin daukewan shi ne yayi ba..gashi kuma yanxu tunda yasan tanada ciki dole bazai dinga bata drugs anyhow tana sha ba tunda yafi kowa sanin illar hakan..addu’a kawai yake kada Allah ya dora mata laulayi mai wahala dan baisan yanda zaiyi da ranshi ba..shi kanshi yasan daga mashi hankali zata dingayi da wnn koke koken nata shiyasa yake fatan Allah ya bata mai sauki yanda bazasu sha wahala sosai ba..ya dade nan zaune yana kallonta saida dare yayi nisa snn ya samu ya gabatar da sallah shima ya kwanta nan kusada ita tareda sanyata a jikinshi.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128Next page

Leave a Reply

Back to top button