Dr. BOBBY COMPLETE HAUSA NOVEL

Dr. BOBBY COMPLETE HAUSA NOVEL

Washegari bayan ta idar da sallahr asuba ta dade sosai zaune inda tayi sallahr tana ta addu’o’i bayan ta kammala azkhar dinta..Bobby kuma na masjid bai dawo ba..sosai take addu’a tana rokon Allah ya sauketa lafia ya kuma raya mata abunda zata haifa cikin tafarki madaidaici..saida gari ya fara haske snn ta shafa addu’an snn ta shiga kokarin mikewa amma sai me?..kugunta taji ya rike gam ta kasa ko kwakwkwaran motsi a wurin..ta kai hannayenta biyu ta dafe waist din dasu snn ta sake yunkurawa zata tashi sai kuma taji bayanta shima ya rike da sauri ta sake komawa ta zauna ta rintse ido tana maimaita innalillahi a cikin ranta..Saida taji ciwon ya dan lafa snn ta sake kokarin mikewa a karo na uku still taji bazata iyaba dan haka ta koma tacigaba da zama tana salatin annabi..Bobby daya dawo daga masjid direct kitchen ya shiga ya hado mata tea da shanshi ya zama mata constant duk ya dawo daga sallahn asubah dama saiya fara hada mata yake shiga daki..yana shiga ya ganta zaune nan inda tayi sallah ya ajiye mug din hannunshi kan table da sauri ya nufi inda take yana dagota yace”baby are u alright?..”a hankali ta dago ido tana kallonshi yaga eyes din are so red nan take hankalinshi ya tashi baisan sanda ya durkusa nan kusada ita ya kamo hannnuwanta yana tambayanta what’s wrong ba..dan murmushi ta saki ganin har hankalinshi ya tashi tace”ba komai fa partner..kawai tashi zanyi naji bayana ya rike amma believe me yanxu banajin komai”..kamata yayi ya mikar da ita tsaye snn ya shiga kare mata kallo wai ko zaiga wani canji tattare da ita still yaga ba komai dan haka ya rike hannunta ya zaunar da ita kan sofa bayan ya zare hijabin dake jikinta..tea dinta ya dauka ya mika mata yace”to ga tea dinki Kisha”..murmushi tayi ta karba shi Kuma ya dauke carpet da tayi sallah dashi ya ajiyeshi inda ya dace snn ya sake dawowa ya zauna nan kusada ita yana kallonta tana shan tea din…bayan ta gama ya sake kamata suka kwanta kan gado ya rufesu da duvet cikin lokaci kankani kuma bacci yayi gaba da ita shi kuma ya kasa baccin sbd har yanxu bai gama yadda she’s alright ba..gani yake kmr idan ya rufe ido ya fara baccin wani abu na iya faruwa da ita har saida ya ga baccinta yayi nisa snn shima ya lumshe ido baccin yayi awon gaba dashi…can cikin bacci Lamido taji kaman ana yi mata suka a maranta nan take ta bude ido baccin ma gaba daya yayi kaura daga idonta..dan motsawa tayi da nufin ta gyara kwanciya sai kawai taji wani irin ciwon mara ya sake kamata har batasan lokacinda ta wani irin salati cikin tsananin tashin hankali ba..da sauri Bobby ya bude ido jin kmr kuka take aikam yana ganinta ya mike zaune da sauri yana janyota jikinshi yace”baby what’s wrong”..hannayenta na rike da mararta tace”ba..ya..na..mara..ta..way..yo”..sauka yayi daga gadon da sauri ya dora t shirt akan singlet da three dake jikinshi snn ya dauketa cak ya fita daga dakin da ita..sbd tsabar bala’i ko kuka ta kasayi sai faman salati take dan da gaske tayi zaton karshenta ne yazo..Bobby ma duk a gigice ya fita daga gidan kai tsaye mota ya bude ya sakata ciki snn ya shiga ya tayar da ita suka fita daga gidan..direct hanyar clinic dinshi ya nufa ita kuma tana baya sai faman murkususu take tana maimaita innalillahi..har wani zufa ke keto mata despite air condition dake aiki cikin motar..Bobby gaba daya gigicewa yayi ko driving din yaji kaman bazai iya ba amma dole yacigaba dayi dan kafin ma yace ya kira driver dinshi yazo wani bata lokaci ne haihuwa Kuma ba zaman jiransu zaiyi ba ya sani.. addu’arshi dai bai wuce Allah ya sauketa lafia ba..yana shiga hospital ko parking space bai karasa ba yayi parking daga nan bakin gate tareda bude motar ya fita itama ya fito da ita da sauri yayi cikin asibitin..da yake safiya ne babu mutane sosai asibitin sai few daga cikin staff da masu jinya da suka kwana a nan..labour room ya nufa da ita kai tsaye yaci sa’a kuma ya tarar da matron salamatu on duty dan haka yayi saurin shigar da ita ciki yace tazo ta duba mishi ita..babu wasting of time matron tayi mata ve nan kuma taga cervix dinta is 4 cm dilated koda ta sanar dashi hankalinshi sake tashi yayi don yasan zaiyi taking nata so many hours before ya gama fully dilation tunda primi ce..ga kuma ciwo da take fama dashi tun yanxun dan yanda takejin maranta kamar zai rabe gida biyu ne dan azaba..waya ya zaro daga aljihunshi ya kira aunty sumy yace ta samesu asibiti that bazai iya fadama Mummy ba don tashin hankalinta zatayi sosai so gwara ya bari idan ta haihu sai a fada mata..suna gama waya da ita ya kira Nur shima ya sanar dashi suna asibiti daga nan kuma ya ajiye wayar tashi ya shiga taimaka mata da kanshi..hannunshi ta rike gam cikin azabar da takejin kmr shi zaiyi ajalinta tace”par..tner..zan..mutu..mutuwa..zanyi”.. girgiza mata kanshi yakeyi duk a rikice yace”bazaki mutu ba inshaAllah baby..lafia zaki haihu”..girgiza kai kawai Lamido take tana karanta innalillahi wainna ilaihi rajiun..har yanxun bata dena zufa ba ga kuma ciwon yakici yaki cinyewa..tun tana ganin abun kmr wasa har tazo ta fara gaskata tunaninta da gaske mutuwarta ne yazo..sosai take shan wahala amma wai ace har yanxu 4 cm take?..anya kuwa zata iya haifan babyn nan da kanta?..Bobby dai na tareda ita duk ya rikice dan kmr ma bazai iya cigaba da aikin ba amma da taimakon matron ya samu yayi gripping kanshi snn yacigaba da bata duk wani taimako da yasan tana bukata at this stage of labour..bayan lokaci kada n aunty sumy ta karaso asibitin nan Kuma yace taje gida ta taho musu da kayan haihuwa Dan shi bai samu ya dauko komai ba sbd rudu daya shiga..ba musu kuwa ta koma gidan ta dauko kayan da taimakon su Husna da suke gidan ta kuma ce kar su bari Mummy taji labari har sai idan ta haihu..lokacinda ta dawo asibtin suka hadu da Nur a kofar shiga labour room din yanata kiran Bobby amma baya dauka..a karo na farko da taji wani irin nauyin Nur ya kamata kasancewar yanxu tasan shine yake son Miemie..gaba daya sai tajita wani uncomfortable dashi unlike before da har wasa da daria sukeyi a tsakaninsu..shima kanshi Nur din rasa abunda zai ce mata yayi sai yayi kasa da kanshi kawai yana gaisheta cikeda respect kmr yanda ya saba..aunty sumy ta amsa snn tayi excusing kanta ta shiga ciki ward din ta bada kayan aka Mika masu..waiting room aka bude mata ta shiga yayinda shi kuma yaketa sintiri yana kai kawo a wurin yanda kasan matarshi ce nan ciki zata haihu.

After a long suffering Allah ya taimaketa da kuma taimakon perfect hubby dinta ta haifi santalelen yaronta namiji..yana zuwa dunia dama daya tsala wani irin kuka hatta Nur dake waje saida ya jiyo sautin kukan..sosai Bobby ke farin ciki da kanshi yayi mata komai ya gyarata matron kuma ta gyara baby snn sukayi moving nata to postnatal matron na rikeda jaririn dake lullube da shawl..har lokacin Bobby bai amsa yaron ba duk kuwa da yanda yakejin kmr ya ajiye duk wani abu da yakeyi yaje ya karbeshi amma baiyi hakan ba saida suka kaita postnatal snn matron ta mika mashi babyn ya karba da Bismillah yana kallon cute face din babyn da at once yaji wani iri so da kaunarshi na sake mamaye ko wane lungu da saqo na heart dinshi..lumshe Ido yayi tareda matsar da bakinshi ya Karanta addu’a sosai ya shafama babyn sai kuma yayi kissing forehead dinshi tareda mannashi da chest dinshi a fili ya shiga furta”Alhamdulillah! Alhamdulillah! Alhamdulillah..Allah ya rayaka cikin tafarkin islam”..ya jima sosai rungume da yaron kafin ya kwantar dashi a cradle tareda karasawa kusada ita ya zauna ya kama hannunta ya rike bayan yayi pecking forehead dinta cikin tsananin happiness yace”Rabbi ya saka maki da aljannah..i love u so much”..itadai bata ma San yanayi as tunda ta samu ta haihu wani baccin wahala yayi gaba da ita..sai a lokacin ya tunada su aunty sumy dake waje nan yace matron ta turosu ciki shi kuma yayi saurin daukan wayanshi ya dannawa Mummy kira…tana dagawa cikin excitement yace”Mummy guess what?..”Mummy tace”just go straight to the point which one is guess what?..”murmushi ya karasa saki yana sake godema ubangiji cikin zuciarshi yace”Mummy Aysher ta haihu..u need to see my son Mummy he is so so very cute..he is more than handsome Mummy ina sonshi sosai wlh”..shiru Mummy tayi kmr bata fahimci me yace ba har saida ya sake kiran sunanta snn tace”u mean Aysha ta haihu?..”yace”yes Mummy tun asuba muke asibti and bata dade da haihuwa ba”..wani Hamdala yaji Mummy ta saki kawai sai yaji tayi disconnecting call din ya maida wayarshi aljihu dan yasan yanxun nan za’a ganta ta iso asibtin..aunty sumy na shigowa ta rungumeshi cikij farin ciki take cewa”Oh Allah mungode Maka..Alhamdulillah”..shima rungumeta back yayi har yanxu ya kasa dena murmushi yace”am now a father aunty Sumayya..i can’t believe this”..rabashi da jikinta tayi cikin tsananin murna ta karasa inda babyn ke kwance ta daukoshi tana kallonshi with so much love tace”Allah ya Maka albarka”..daga haka ta ajiyeshi tareda komawa inda Aysha ke bacci itama ta rike hannunta tana kallonta with smile tace”sannu da kokari Aysha..Allah maki albarka kema ya baki lafiar breastfeeding”..Bobby dake tsaye yana kallonsu yace”Ameen Ameen”..daidai lokacin Nur ya shigo Bobby na ganinshi yayi saurin isa inda yake yayi hugging dinshi so tight yana ce mishi”u have become a father man.. congratulations to u”..rungumeshi back Nur yayi cikin so much excitement yace”Congratulations to u too bro..am so happy for u..Allah ya raya mana boy”..da sauri Bobby yace”Ameen..Ameen Ameen”..har yanxun sai suna rungume da juna sun kasa rabuwa musamman Nur da yakejin kaman ya taka rawa dan farin ciki amma ba halin yin haka sbd aunty sumy dake cikin dakin..duk sai yaji kaman baby expressing farin cikinshi yanda ya kamata ba..a hankali ya zame jikinshi shima ya nufi cradle din yaron..ya dagoshi yana washe baki kmr gonar auduga yace”Allahumma barikh ya Habibi..barakhallahu lakha”..ya karasa tareda yima yaron addu’a ya shafa mashi shima snn yayi saurin ajiyeshi ya fita daga dakin yana cewa”i will be back soon”..daga haka ya fita waje shi Kuma Bobby ya karasa inda babyn yake yanata kallonshi yanajin kmr zai maidashi ciki sbd son da yake mashi..ko 30 mins baiyi da zuwa dunia ba amma jin sonshi yake ta ko ina a cikin zuciyarshi wnn baisan ya zaiji ba idan yaron yafi haka girma Kuma.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128Next page

Leave a Reply

Back to top button