Dr. BOBBY COMPLETE HAUSA NOVEL

Dr. BOBBY COMPLETE HAUSA NOVEL

Finally dai yau an haifi dan soyayya???? welcome to parenthood Uncle Bobby and Aunty Lamido❤️????

Rano✨

Wnn littafin na kudi ne ban yadda wani ko wata ya fitarmin dashi ba…masu buqatan siya zasu tura 300 zuwa 2208991344 Aisha Ahmad Tijjani Zenith Bank…sai a tura evidence of payment via 07063800556.
70
Nur ne ya dawo dakin dauke da zamzam da dabino kai tsaye inda babyn ke kwance ya nufa ya daukoshi snn ya mikama Bobby ruwan zamzam din yace”come and give it to him”..ba musu Bobby daya kasa dena smiling ya matso yana bude zamzam din shi kuma Nur yana rikeda babyn haka sukayi bashi zamzam din yasha tareda dabinon da Bobby ya danyi chewing snn ya matsa mashi ruwan a bakinshi..aunty sumy dai na zaune tana kallonsu tana smiling..wnn friendship nasu ba karamin burgeta yakeyi ba tuntuni..they treat each other like brothers..Saida ta bari sun gama bashi snn tana dan murmushi tace”so doctors basa ma kids dinsu exclusive breastfeeding knn?..”kallonta sukayi gaba dayansu ba dai Wanda yace mata wani abun ita kuma ta sake cewa”naga dai kune kullum kuke counselling mutane kan su dinga ma yaransu ebf amma ku gaku nan Medical doctors daku kunzo Kuna bama yaronku ruwa ko one hour baiyi a dunia ba”..Nur dai kanshi na kasa ya kasa cewa uffan sai Bobby ne yace”aunty wnn ai ba normal water bane..zamzam ne fa”..daria kawai tayi bata sake cewa komai ba.

Mummy na shigowa dakin direct dama inda ta hango cradle ta nufa Bobby yayi saurin mikewa zakiyi hugging dinta tayi saurin kaucewa tana cewa”abeg let me pass..ana ta sabon jini wa yake ta kai”..daga haka ta karasa inda cradle din yake ta dauko babyn ta shiga kare mashi kallo..Bobby ya wani kwabe fuska yace”Mummy amma nine danki fa bashi ba”..harara ta sakar mashi tace”to daga yanxun shine yarona not u”..sake kwabe fuska yayi yana kallonta sai ta bude mashi hannu tana daria sosai tace”come here my son..the latest dad”..da sauri ya karasa ya shige jikinta Mummy ta hadasu shi da yaron mashi tayi hugging nasu so tight tana yima Allah godia cikin ranta..saida suka gama expressing farin cikinsu snn ya janye jikinshi Mummy kuma ta maida babyn cradle snn ta nufi inda Aysha..kallonta tayi yanda take bacci peacefully ta sauke ajiyar zucia tareda furta”Alhamdulillah Alhamdulillah..Allah shine abun godia”.

Karfe 12 saura driver ya kawo Husna da Miemie tareda abinci da Mummy tace suzo dashi..zuwa lokacin Aysha ta tashi daga baccin har ma ta dan ware tana responding to mgnr da Aunty sumy ke mata har yanxun ko babyn bata dauka ba wai kunyar mummy takeji..ganin da gaske ba daukan nashi zatayi ba gashi ya fara rigima dole ta tashi suka bar dakin itada aunty sumy da Miemie ya rage daga ita sai Husna..cikeda farin ciki Husna ta karasa ta dauko mata babyn ta kawo mata shi tana cewa”take a look at him Addah..he is more than cute..har na kira Ammi na fada mata”..kallon nashi Lamido tayi tanajin wani irin sanyi na ratsa zuciarta..soyayya mai girma taji tanayima yaron just by looking at him..nan take taji she’s so attached to him kaman dai ba yau yazo dunia ba..tana dan murmushi ta dagoshi ta mannashi da chest dinta snn ta sauke wani ajiyar cuzia tana godema Allah cikin zuciarta Husna Kuma na zauna tana kallonsu with adoration..shigowar Bobby yasa ta mikewa ta fita daga dakin bayan ta gaisheshi..a nutse ya karaso cikin dakin ya zauna nan kusada ita tareda yi mata side hug yana lumshe eyes dinshi yace”na gode sosai partner..May Allah reward u abundantly”..dan murmushi ta saki tana Kara rike babyn a jikinta shi kuma ya dagota daga jikinshi tareda durkusawa nan kasa ya kama hannunta yana kallon eyeballs dinta yace”i don’t have enough words to thank u baby..i just want u to know that ina sonki and zan cigaba da sonki till my very last breathe..thank u for making a father today..Allah ya raya mana shi yayi mashi albarka”..kai kawai Lamido take gyada mishi tama kasa cewa komai.. shi kuma sosai ya rikice mata yanata faman godia hade da expressing mata how much he loves her..banda blushing ba abunda takeyi sbd dadi..itama tana sonsu fiyeda komai nata.

A ranar akayi discharging dinta suka koma gida bayan an tabbatar da itada babyn suna cikin koshin lafia..suna komawa gida ta samu kira daga daddy da Ammi duk sai murna suke sun samu grandson ita har ta kasa tantance wanda yafi wani murna da haihuwar nata..a ranar wata Goggonta tazo daga Gombe sbd ta zauna da ita ta kuma kula da ita da babyn gaba daya..Billy ma dake can tana ta faman shirin biki without her best friend tana samun labarin haihuwar ta kirata vid call tanata ihun murna wai a nuna mata danta ta gani..sosai suka bata lokaci suna video call Billy sai santin babyn take wai kmr tayi tsuntsu tazo Kano.

Bayan kwana hudu…

Cikin kwanakin nan Lamido taga asalin so da kauna daga wajen family da friends..ba family dinta ba ba kuma familyn Bobby ba..sosai suke samun kula itada baby abun har mamaki yake bata..mutanen Gombe zai zuwa suke ganin baby wasu kuma suna nan bazasu tafi ba sai bayan suna ciki hadda aunty Fiddausi..Besty ma yana samun labarin haihuwar a bakin Husna ya kirata ya mata barka tareda alqawarin zaizo ganin baby..haka zalika yan school dinsu ma da yawa sunzo abun dai ba’a cewa komai..Bobby kuwa bai cika zama ba yanxun as yanata shirye shiryen raka Waziri India ganin doctor dan Waziri da kanshi yace lallai saidai suje tare dashi..shima da kanshi yazo ganin baby har Kano tareda uncles din Bobby da kuma some of their family members..family din Mummy ma sunzo sosai kasancewar ita din mace ce mai zumunchi so kusan kowa yana kokarin yazo duk wani sha’ani daya shafeta…ahalin Lamido ma sunzo sosai tun daga kan uncles dinta da aunties dinta dama sauran family da friends..wasu sun wuce a ranar wasu kuma sunan nan sai anyi suna.

Yau ma kmr kullum tun safe suke fama da baki yan barka gashi babyn sai kuka yake an rasa abunda ke damunshi..har kuka itama saida tayi wai batasan me yakeso tayi mashi ba kuma..da kyar ta samu yayi bacci da taimakon Goggonta dake tareda ita..tana zaune gefen gado tana kallon yanda yake bacci peacefully sai taga ya koma mata kmr babanshi..he looks exactly like Bobby dan ko abu guda nata bai dakko ba..haskenshi eyes dinshi nose dinshi bakinshi and even fingers dinshi irin na Bobby ne sak..komai da komai irin nashi ga kuma dan banzan rigima da yake dashi shima ta tabbata na baban nashi ya dauko..hannu takai tana shafa soft hair dinshi tana cigaba da kallonshi tana murmushi Goggonta ta shigo dakin da ruwan zafi a flask tace”au yanxu Aisha har yanxu kina nan zaune kina kallon danki sbd rashin kunya so kike ruwan wankan ya gama wucewa ne kome?..”dan daure fuska tayi tana duban Goggon nata tace”yanxu dan Allah Goggo baza’a hakura da wankan yamman nan ba..shima fa da kanshi yace a denamun wanka sau biyu nidai dan Allah kiyi hakuri tunda anyi da safe sai a bari gobe Kuma”..wani tsaki Goggo ta saki tareda shiga bathroom ta juye ruwan flask din cikin wanda ta sirka tun daxun snn ta dawo dakin ta kama hannunta suka shiga bathroom din tare..duk yanda batason wankan dai saida Goggonta tayi mata wai shine zaiyi saurin dafa mata jikinta tunda yanxun ya dawo danye sbd haihuwan da tayi..suna gamawa ta dawo dakin tanata wani bace bacen rai itada Goggo bata kulata ba tayi wucewarta as tun daxun ta riga tayima babyn wanka..shiryawa tayi cikin dogon riga bayan ta gama shafa cream da perfume dinta snn ta koma kan gadon ta zauna tana cigaba kallon yaronta..a haka Bobby ya shigo dakin ya sameta..har ya karasa ya zauna kusada ita bataki shigowarshi ba Saida yayi mata side hug snn ta dawo hayyacinta sai kuma itama ta zagaya hands dinta around waist dinshi tana pecking shoulder dinshi tace”so u are back?.”yace”yes baby how is my baby and u”..tace”as u can see we are all fine..just missing u”..juyoda ita yayi hugging dinta sosai snn yayi breaking hug din yana rikeda hands dinta yace”believe me i missed u more”..murmushi kawai ta saki tana cigaba da kallonshi..a hankali ya saki hands dinta tareda dauko baby dake bacci abunshi shima yayi pecking goshinshi yana kallon yanda he looks just like him ya dan bata face dinshi”i told him to look like u but he didn’t”..daria Aysha ta saki tana kallon babyn itama tace”and i told him to look like u so mgn na yaji ba naka ba”.. murmushi shima yakeyi yace”don’t worry nasan next ones bazasuyi kama dani ba..inshaAllah next baby girl dake zatayi kama ba dani ba..now do u have any name in mind da kikeson asa mashi?..”girgiza kai tayi tana dora kanta a shoulder dinshi tace”No..duk sunan daka sa mashi is ok by me”.. pecking forehead dinta yayi yana cewa”that’s why i love my baby so much..u are one in zillion”..daria kawai ta saki jin wai ya ambaci zillion.. hankalinshi ya maida kan babyn yana tuna conversation dinsu da Mummy a while ago..he asked if da akwai name da takeso a saka mashi and her reply was duk sunan daka saka mashi daidai ne Bobby.. already dama yanada sunan da yakeson sa mashi amma sbd ya basu right dinsu yasa ya tambaya and he’s glad sun bar mashi zabi..a hankali ya daga babyn yayi mashi huduba cikin ears dinshi snn ya maidashi kan shoulder dinshi yana patting bayanshi murya can kasa yace”he’s named Noor.. Nuruddeen”..wara ido Aysha tayi out so much excitement tace”sunan provost right?..”a hankali Bobby ya daga mata kanshi yana cigaba da patting bayan babyn yace”yes..he’s more than a friend to me u know..we became brothers”..tayi hugging dinshi tana cigaba da smiling tace”i knew that already..Allah ya raya little Noor Allah kuma yasa ya dauko halin mai sunanshi”..dan tabe baki Bobby yayi yace”ba kowanne ba gaskia..bakisan yanda Nur yakeda sa ido bane and i don’t want my baby to be like him”..daria ta saki shima yana dariar ya hadasu yayi hugging da ita da babyn yana sake jin kaunarsu har can cikin zuciarshi.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128Next page

Leave a Reply

Back to top button