Dr. BOBBY COMPLETE HAUSA NOVEL

Dr. BOBBY COMPLETE HAUSA NOVEL

Biki ya rage saura 2 months Bobby da Aysha suka tafi aikin Hajj hade da honeymoon dinsu wanda Mummy tace itakam bazata je ba sbd shirye shiryen bikin Miemie..wnn dalilin yasa suka tafi su biyu tareda little Nur da yayi girma ya Kara wayo sosai kuma kamanninshi da babanshi na sake fitowa…Malaysia suka fara zuwa for their honeymoon aikam anyi kara’in honeymoon sosa dan ba wanda zai gansu yace ba latest couple bane saidai idan little Noor aka gani..sosai suke enjoying honeymoon dinsu Aysha mai cewa zata koma karatu duk ta mance da wnn tana enjoying life dinta to the fullest..satinsu hudu suka wuce Saudi inda daga nan kuma zasu dawo gida dan immediately bayan sallah za’a fara bikin Miemie..sun gabatar ibadar su yanda ya kamata sun kumayi addu’a sosai na neman zaman lafia mai dorewa da zuri’a masu albarka da kuma fatan gamawa da dunia lafia..nan ma 4 weeks sukayi kafin su dawo daidai lokacin kuma an fara shagalin bikin Miemie so basu samu zama ba dan suna dawowa suka shiga harkan biki kuma.

Kusan sati guda akayi ana shagulgulan biki dan events sukayi sosai kmr dai bazasu kare ba inji Bobby yace shi har ya gaji da attending events din ma..yan uwan Aysha da yawa sunzo bikin daga Gombe ciki harda Ammi da bata zuwa gidanta ba sai Yusra da Husna da kuma Aunty Fiddausi da Billy dake dauke da katon cikinta itama da alama dai bakin Aysha ne ya kamata don da kyar idan ba haihuwar 9 months din zatayi ba..a lokacin ne Aysha ta samu labarin wai ashe soyayya ne tsakanin Husna da Bestynta abun kuma ba karamin dadi yayi mata ba dan tafi kowa sanin waye Sa’eed haka zalika tasan Husna ba karamin dacewa tayi da damunshi a matsayin miji ba..ranar da aka kai amarya gidanta su Aysha sune gaba gaba itada Billy da sauran familyn Mummy sai kuma yan uwan babanta..su Hajia Husna kuma sune qawayen amarya..sosai su Aysha sukayi mata nasiha sosai kafin su bar gidan ita kuma banda kuka ba abunda take wai tama fasa auren su maida wajen Mummy haka dai suka samu suka lalla6ata suka bar gidan.

Bobby da kanshi ya rako Nur har compound din gidanshi amma kememe yace shi bazai shiga ciki ba tunda amaryar tashi matsayin ‘ya take a wurinshi that shi bazai iya wnn rashin kunyan ba..haka Nur yanaji yana gani Bobby yaki rakashi ga kuma wani iskanci da yake ta mashi tunda aka fara bikin wai yabi mashi yarinyarshi a hankali if not da kanshi zaizo ya dauketa if yaga yana neman hallakata..Nur bai samu bakin cewa komai as haushinshi yakeji for not rakashi cikin gidan amma ba yanda zaiyi dashi haka yana gani ya tada motarshi ya bar gidan ya gama masa iskanci iri iri daga karshe dai shi kadai ya shiga wajen amaryarshi as dama idan aka cire Bobbyn ba wasu abokai yake dashi ba.
Allah sarki Miemie Saida ta bani tausayi dan da gaske Nur bai saurara mata sbd tsabar azaba gari na wayewa ta dokowa Aysha kira wai dan Allah dan annabi tace ma uncle Bobby azo a dauketa daga gidan that bazata iya zama ba wai kasheta zakiyi..hakuri sosai Aysha ta bata tareda tura mata Billy gidan taje tayi mata duk abunda ya kamata don hanashi zuwa inda yake tayi balle ya taimaka mata..Bobby Kam yana samun labarin ya dinga 6a66aka daria kmr mahaukaci sabon kamu dan takanas yaje har inda Nur din yake yayita mashi daria yana tsokanarshi wai tsabar shi novice ne shine yaje yayima yarinya fata fata har take cewa bazata iya zama dashi ba..Nur dai baice dashi komai as yasan duk wnn abun ramuwa ne yakeyi tunda shima ba kalan tsokanar da bai masa ba lokacin nashi bikin.

Haka rayuwa yacigaba da tafia musu cikin zaman lafia da kwanciyar hankali..ga kuma uwa uba tsantsar soyayya da kulawa da juna..lokacinda ta mashi zancen komawa asibti yace ta bari idan Nur ya bude asibtinshi sai ta fara aiki a can that idan asibti daya suke bazasu maida hankali suyi aiki ba..hakan kuwa akayi don ana fara aiki asibitin na Nur mai suna Annur specialist hospital ta fara aiki a can as a staff midwife..little Noor da yayi wayo ya zama Kato dashi take barinshi wajen Mummy da ko kusa yanxu bata kaunar rabuwa dashi dan ganinshi takeyi kmr Bobbynta…yanada wata 10 a dunia Aysha ta sake samun wani cikin aikuwa zo Kuga tashin hankali a wajenta kmr wanda tayi cikin shege..wai a matsayina na midwife bai kamata ace tayi haihuwa irin wnn ba ya kamata ace saita yaye Little Noor kafin ta samu wani cikin..Bobby dai baida bakin cewa komai sai na bata hakuri gashi laulayi takeyi sosai kusan fiye ma da wanda tayi a cikin small Noor hakan yasa har aikin ma ajiyeshi tayi tacigaba da rainon cikin a gida..shi kuma small Noor kusan koda yaushe yana wajen Mummy gashi ya hanata yayeshi wai sai yakai 17 months…haka dai ta hakura take fama da ciki da kuma shayar dashi don dai ba yanda zatayi ne amma da tuni ta yayeshi ta huta.

Cikinta nada 5 months Billy ta haifi yarta mace aikam sunje Gombe sunsha suna yarinya taci sunan Maman Hamma Aysha suke kiranta da Maama..Saida sukayi sati biyu itada small Noor daya kara girma da wayo kuma yana yawonshi ko ina snn suka dawo Kano..nan kuma tacigaba da zaman jiran nata haihuwan itama.
Kamar yanda yace yana shiga 17 months ta yayeshi ya koma wajen Mummy gaba daya..cikinta na shiga wata tara ta haifi twins dinta mata masu kama da ita sak kmr an tsaga Kara an karya gasu kuma kamarsu daya da juna dan ko Bobby Saida yayi da gaske snn ya iya ganesu…farin ciki a wajen wnn ahalin ba’a mgn dan duk wani Maison Aysha da Bobby Saida yayi musu farin cikin samun wnn karuwar..Yara masu mugun kyau da shiga rai kuma identical twins..ranar suna Yara sukaci sunan Mummy da Ammi wato Maimunatu da Nadia anci ansha anyi shagali sosai wajen sunan kmr sunan fari.

Bayan wata daya Miemie itama ta haifi baby boy dinta mai sunan Bobby..fadan farin cikin da sukayi is a watse of time amma sunyi murna sosai musamman daya kasance anyima Bobby takwara dan hatta nickname din iri daya ne..Attahir ne sunanshi na gaskia amma za’a dinga kiranshi da Bobby…rana suna shima Bobby ya taka rawa gani sosai fiyeda tunanin mai tunani..haka Mummy da aunty sumy sunyi farin ciki sosai da wnn takwara na Bobby kuma takwara daddy tunda sunan daddy shima yaci.

Twins din Aysha nada one and half year akayi bikin Husna da Sa’eed..su amara Lamido sati biyu taje tayi a Gombe dan har aka gama biki aka Mika Husna gidanta dake Kaduna bata dawo ba saida ta sake komawa Gombe..kowa ya kalleta ita da yaranta sai sun burgeshi dan yanda suke kyawawa dasu kuma masu wayo da shiga ran mutane..kwana hudu suka karayi suka dawo gida Kanon Dabo inda Kuma suka dora daga inda suka tsaya..tuni dama tacigaba da zuwa aikinta so no more zaman banza a gida..daga little Noor har twins din wajen Mummy take barinsu da nanny dinsu taje aikinta ta dawo.

Yau ma kmr kullum tana zaune dakin yaran nata da sukayi bacci ta sanyasu a tsakiya sai addu’a take musu tana bin dukkaninsu tana shafa musu a jikinsu..Bobby dake tsaye bakin kofa yana kallonta a hankali ya karaso ciki yana kallonta da murmushi hannayenshi rungume a chest dinshi yace”this is not fair baby”..kallonshi tayi itama tana murmushin tace”me Kuma nayi again partner?..”yace”kaga daya hankalinki yanxu ya koma kan twins dinki mana..tunda kika samesu ni da aboki kika dena kulawa damu Kuma”..murmushin dai take cigaba dayi snn ta mike daga inda take ta tsaya nan kusa dashi tareda mishi side hug ta dora kan akan shoulder dinshi tana kallon yaran nata dake baccinsu peacefully tace”ni ban wani dena kulawa daku ba partner..kishi kawai kukeyi dasu”..hannu yakai shima ya zagaye waist dinta dashi yana kallon kids din nashi yace”no kinfi damuwa dasu a kaina”..daria ta saki before tace”oh yanxu ka dawo kai kadai banda little Noor knn?..”yace”yes mana duk kinfi basu time dinki akaina..kuma dai kinsan ni nafisu bukatarki a kusa dani”..har yanxu bata dena murmushi ta danyi dagen kafa ta manna mashi kiss a right cheek dinshi snn tace”yi hakuri ai from now zuwa safiya duk time dinka ne and babu yaron da zai cinye Maka shi believe me”..murmushi ya saki yana kallon kids din kafin ya dawo da kallon nashi gareta yana cewa”bazan taba gajiya da godia wa Allah daya mallaki mun such a lovely family kaman ku ba..u guys are my everything and i love u so much”..sake rungumeshi tayi itama tana kallonshi eyeballs dinshi tace”we also love u so much papa..u mean the entire world to us..we are so proud of u”..rungume juna sukayi suna kallon yaransu cikeda so da kauna.. little Noor na kan gadonshi yana bacci likewise twins suma suna kan nasu bed din suna bacci rungume da juna..matsawa yai yayi kissing yaran duk snn ya rufesu da duvet snn ya jata suka fita dakin bayan sun kashe masu haske yana rungume da ita yake cewa”ina sonki kwatankwacin son da Umar Faruk ke yiwa Amal(INA ZAN GANTA)..snn ina kishinki kaman yanda Dr.Taheer ke kishin Layla(Dr.TAHEER)”..murmushi sosai takeyi ta kasa dena blushing sbd words din nan nashi means the entire world to her..Saida suka shiga bedroom dinshi ta hade goshinshi da nata snn tace”nima inasonka sosai partner..u are my hubby,my love,my soul partner,my darling..my very own husband and the father to my beautiful kids..i love u unconditionally”..lumshe Ido Bobby yayi ya hade bakinshi da nata itama tayi grabbing nashi da sauri nan kuma wasan ya sauya tsakaninsu.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128Next page

Leave a Reply

Back to top button