Dr. BOBBY COMPLETE HAUSA NOVEL

Dr. BOBBY COMPLETE HAUSA NOVEL

Bobby bai samu dawowa gida ba sai yamma likis…su Miemie ya samu a parlor suna kallo..gaba daya suka mishi sannu da zuwa ya amsa idonshi kan Sab da hankalinshi gaba daya ke ga phone dinshi yace”kai yaushe zakuyi resuming school ne?..”Sab yace”next week ne but dan Allah inaso in kara ko one week ne plss”..bai rufe baki ba Bobby yace”C’mon keep quiet..waye zai bari ka kara one week din?..you are deceiving yourself”…daga haka ya kama hanyan parlon Mummy…ga mamakinshi bai sameta a parlon ba sai ya nufi bedroom dinta yana mamakin meye sa bedroom da wuri haka…Allah yasa dai lafiyanta qalau…yana tura kofan ya shiga sai sallaman da yake kokarin yi ya makale a bakinshi sakamakon abunda ya gani…Mummy ce zaune gefen gado tana hawaye Anty Sumy na zaune kusada ita tana hawayen itama…baisan lokacinda ya saki suit dinshi dake a hannunshi ba ya karasa cikin dakin da sauri…gefen Mummy ya zauna ya kamo hannayenta hankali tashe sosai yace”Mummy what is happening here?..why are you two crying?..”damke hannunshi Mummy tayi ta juya tana kallonshi tace”your grandfather Bobby..Waziri..idan bawan Allahn nan ya mutu baisan inda kuke ba bazan ta6a yafema kaina ba Bobby..you need to see his condition..he is seriously..”bai bari ta karasa ba ya rungumeta a jikinshi…itama saitayi lakwas a jikin nashi tana cigaba da hawaye…suka hada ido da Anty Sumy dake kallonsu tana hawaye itama..da ido ya tambayeta me yake faruwa ta buda mishi hannu alaman he has no idea…saida yaji kukan nata ya dan tsagaita snn ya sake dagota still yana rikeda hannayenta yace”Mummy kukan ya isa haka please kar bp dinki yayi rising..besides waya fada maki condition da wazirin ke ciki?..how did you know?..”tace”a news na gani wai ciwon nashi yayi worst har sun daukeshi daga Egypt zasu maidashi india..Bobby he is seriously sick inaso kuje ku dubashi idan ya dawo”..cikin 6acin rai tuno abubuwan da suka faru a baya yace”but Mummy why?..why zamuje dubashi bayan bai damu damu ba..bai damu ko muna raye ko mun mutu ba?..”yana rufe baki tace”because he is your grandfather Bobby..komai girman laifin da yayi he is still the father to your Dad and nobody can change that”..ta kamo hannunshi snn tacigaba”do you think if your Dad was alive zaiji dadin yanda kake treating mahaifinshi?..do you think he would be happy if we choose to hide ourselves from them komai girman abunda suka aikata?..”a hankali ya zame hannunshi daga nata lokaci daya idonshi sukayi jajir sbd 6acin rai yace”but Mummy we didn’t hide ourselves from them sune basuga daman su nemi inda muke ba..for five long years Mummy idan suna sonmu meyasa basu nememu ba?..”yana rufe baki tace”because he is sick Bobby..sanin kanka ne tun ranan da mahaifinku ya fadi ya mutu bai sake samun lafia ba”…cikin anger daya fara kasa controlling yace”dukda bashida lafia if he really love us..if he really want to see us he could’ve at least ask one of his selfish and wicked sons to look for us but he didn’t and do you known why?..because he hates us..he despise…”bai kai ga karasawa ba yaji saukan kyakyawan mari a cheeks dinshi…ya dafe cheek din da sauri yana duban Mummy dake kallonshi rai a 6ace itama…Anty Sumy ta taso da sauri ta kama hannun Mummy hawaye na wanke fuskanta tace”Mummy take it easy please..kinsan condition dinki Mummy kar wnn abun yasa bpnki yayi rising please”..ta karasa mgnr tana kuka sosai…Bobby da yayi suman wucin gadi sai yanxu ya dawo hayyacinshi…tun da yake zai iya counting sau nawa Mummy ta dakeshi but now she slapped him sbd azzaluman mutanen can..wasu hawaye yaji suna cikowa idanunshi amma ya dake bai bari sun zubo ba ya dora kanshi a shoulder dinta murya can kasa yace”am sorry for hurting you Mummy amma kinsan gaskia nake fada fa..mutanen nan basu ta6a kaunarmu ba Mummy..kema basa sonki amma meyasa kikeso mu sake kai kanmu inda suke bayan duk laifukan da sukayi?..”dago kanshi tayi tareda cupping fuskanshi tace”because they are your relatives Bobby..they are your Family and Family will always be considerd as Family nor matter what..so try to understand me please”…shiru kawai yayi yana yanajin yanda maganganunta suke neman kashe mishi jiki…Anty Sumayya dai na zaune tana kallonsu..itama Mummy ganin tasirin da maganganunta sukayi ta sake yin kasa da murya tace”try and understand Bobby please..ko bamu nemesu yanxu ba dole watarana dalili zai sa mu nemesu shiyasa nakeso mu daidaita dasu tun kafin zuwan wnn lokacin..”shiru ya sakeyi idanunshi lumshe yana sauraronta…ita kuma Mummy ta dan saki murmushin cin nasara snn tacigaba”kaga watarana Aurenku ne zai taso kuma nasan kasan duk dunia babu inda mutum zaije neman aure a bashi ba tareda dangin mahaifi ba..and gaba daya ku ukun babu wanda keda aure gara Sumayya ta ta6ayi hadda yara amma kai da Sabeer baku ta6ayi ba Bobby..dole kuma watarana lokaci zaizo da zamu bukaci suzo su nema muku aure”…sake daure fuska yayi jin ta fara zancen aure yace”indai wnn mutanen ne zasu nemamin aure Mummy wlh na gwammace har in mutu banyi aure..Anty Sumy da Sab kuma duk wanda bazai kar6i aurensu a wurina ba saidai ya hakura”..ta bude baki zatayi mgn ya dora finger dinshi kan bakinta yace”enough talking about them please..yanxu ki samu ki kwanta kina bukatan hutu sbd bp dinki..maganan zuwa dubiyan Waziri kuma Allah ya dawo dashi lafia sai muje”…lokaci daya murmushi ya mamaye fuskanta tace”da gaske zakuje Bobby?..tasan indai ta samu ta shawo kanshi ragowar basuda matsala dama Bobbyn shine mai taurin kain…yace”anything for you Mummy..yanxu dai ki samu ki huta sosai”..da sauri ta shiga gyada mishi kai tace”Allah ya muku albarka”..yace”Ameen Mummy”..Anty Sumy ce ta taimaka mara ta kwanta shi kuma ya juya a hankali ya fice daga dakin zuwa nashi…a gurguje yayi wanka tareda alwala ya fito ya tayar da sallah tubda an idar a masallaci…ya dade zaune yana addu’a kan Allah ya mantar da Mummy mgnr zuwa dubiyan nan dan fa shi har yanxu baiji zai iya daukan kanshi ya kai Gombe ba..har abada gani yake bazai ta6a iya mace kalan rashin imani da suka gwada musu ba har shi wazirin daya kasance kakansu…da kyar ya samu ya mike daga wurin da yayyi sallahn ya fada kan gado ya kwanta…ya runtse idonshi da karfi yana jin duk wani abu daya faru na daow mishi kaman yanxu yake faruwa…bayason yana wnn tunanin amma ya kasa dakatar da kanshi.

ASALIN LABARI…

Our free pages sun kusa karewa fa..keep on subscribing before kuji diff kaman an dauke wuta????

Masu bukatan siya zasu tura 300 zuwa 2208991344 Aisha Ahmad Tijjani Zenith Bank…sai a tura evidence of payment ta 07063800556.

Rano✨

????Dr.BOBBY????

By Aysha Rano✨

Wattpad@aysharano22

10

ASALIN LABARI…

Lokacinda Attahir wato mahaifin Bobby yakai ma mahaifinshi Wazirin Gombe mgnr yanason Auren Nadia daya hadu da ita a kano kai tsaye yace bai amince ba sbd kasancewarta ba bahaushiya ba…hankalinshi ya tashi sosai ganin da gaske waziri naso ya rabashi da matar da yafi kauna a dunia..ya jema mahaifiyarshi da mgnr itama ta nuna batada taimakon da zata iyayi masa har tunda mahaifinshi yace ya hakura da ita kawai ya hakura…bai hakuran ba yacigaba da lalla6a waziri yana nusar dashi illar nunama wanda ba yarenku daya ba banbanci…ya kuma nusar dashi cewa har tunda ta kasance musulma kuma yar Nigeria yana ganin ko addini bai haramta mishi aurenta ba…ran waiziri ya 6aci sosai ya kuma ce matukar shi ya haifeshi bazai ta6a amince mishi ya auri inyamura ba…wnn mgn ba karamin daga hankalin Attahir yayi ba…step brothers dinshi da suke ganin waziri ya fifitashi a kansu nan suka samu damar shiga suna cigaba da ingizashi kan kar ya yadda ya amince ya hada jini da inyamurai wnn zuga kuma yayi tasiri a wurinshi sosai…Attahir da yaga bashida wani mafita kuma bazai iya hakura da Nadia ba kai tsaye yaje ya samu kakarshi mahaifiyar waziri knn yayi mata bayanin duk abunda ke faruwa nan kuma ta goyi bayan lallai sai an aura mishi matar da yakeso…hakan ba karamin 6ata ran waziri yayi ba amma ya hakura ba don yanaso ba ya tura aka nemo masa auren yarinyar har Enugu state bisa umarnin da mahaifiyarshi ta bashi kan lallai lallai ya aurama Attahir matar da yakeso idan baiyi haka ba kuma itama zata tsine masa kmr yanda yayi ikirarin zai tsinewa nashi dan.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128Next page

Leave a Reply

Back to top button