Dr. BOBBY COMPLETE HAUSA NOVEL

Lokacinda Anaesthesia ya saketa ta tashi daga bacci sai yaga hawaye a idonta…hankalinshi yakai kololuwar tashi ya kuma ce dole ta sanr dashi damuwarta…itama din ba yanda ta iya duk yanda take kokarin 6oye mishi abubuwan da suka faru kasawa tayi saida ta fada mishi…6acin ran da ta gani a fuskanshi bata ta6a ganin irinshi a tattare dashi ba..yanxu kiyayyan da suke masa har yakai ga suyi abandoning matarshi tana labour wanda ba dob taimakon neighbor dinsu ba da kilan yanxu ya rasa matarshi da kuma babyn data haifa..zai iya yafe komai amma banda wnn cin kashin da sukayi masa..wnn dalilin yasa ya yanke shawaran da zaran ta warke zai daukesu su bar Gombe gaba daya tunda baiga amfanin zaman nasu ba.
Haka yake jinyar matarshi shi kadai sai neighbors dinta dake yawan xuwa kullum wasu har suyi girku su kawo…mahaifiyarshi ma bata taba zuwa ba sbd waziri daya hana amma munubiya zuwanta biyu shima duk wazirin bai sani ba take zuwa…saida ta samu sauki sosai yace ta fadi sunan da takeso a sa ma babyn nan take kuma tace sunanshi takeso yasa sbd tana ganin duk dunia yanxu batada wanda ya kaishi sai ‘ya’yanta…baiyi mata musu ba yayi mishi hudu ba da sunan Attahir tace zasu ringa kiranshi Bobby.
Daga asibiti ko gidansu basu koma ba suka wuce kano…bayan kwana biyu suka bi flight zuwa delta state inda a nan suka cigaba da rayuwa tareda yaransu.
Bayan shekara biyu suka koma Lagos sakamakon transfer da akayi mishi ya koma Lagos din da aiki…lokacin Sumy nada 6 years Bobby kuma nada 2…tsahon wadan nan shekarun kuma basu sake zuwa Gombe ba saidai yaje shi kadai ya dawo…ana haka Allah yayiwa mahaifiyarshi rasuwa…wnn karon kam gaba daya suka tafi kuma basu dawo ba sai bayan kwana bakwai…har zuwa lokacin kuma daga waziri har sauran siblings dinshi babu wanda ke kaunar matarshi da yaranshi…haka akwa kwashi tsahon shekaru babu jituwa tsakaninsu wanda hatta yaran dukda ba wasu shekaru sukeda ba sunsan akwai matsala tsakanin iyayensu da familyn babansu especially Bobby da yafi ‘yar uwarshi riko da kuma zafin zuciya.
Sbd wnn matsalan yasa ko auren qanwarshi da zaayi bai samu labari ba sai gab da bikin…yaji ciwon hakan sosai sbd ganin cewa yarinyar nan batada kowa yanxun daga wazirin sai shi da suke ciki daya da ita tunda mahaifiyarsu ta rasu…haka sukaje Gombe suka dawo bayan kammala bikin.
Bayan shekara goma Nadia da yaranta ke kira Mummy ta sake haifan namiji wnn karon yaron yaci sunan waziri Adam suke mishi laqabi da Sabeer.
Zaman Lagos na musu dadi sosai don basuda damuwan komai kuma babu wanda ke kyamansu unlike Gombe da ko zuwa basu sonyi sbd yanda ‘yan uwan Dad dinsu suke treating dinsu.
Bobby nada 17 years ya gama secndary school Sumayya kuma already ta fara karatu a University of Lagos shi kuma Sab yana primary school…zuwa wnn lokacin mahaifinsu yayi kudi sosai dan yana matakin deputy controller General na Nigerian Custom…kai tsaye ya tura Bobby America dan yacigaba da karatunshi a can.
Sumayya na kammala karatu aka aura mata isma’il da suka fara soyayya tun a university aka mikata gidanta dake Kanon dabo…unluckily itama mother inlow dinta bata sonta…dama Isma’il kadai ne danta namiji sauran duk mata ne suma kuma ba son nata suke ba…bayan shekara daya da biki ta haifi Miemie da aka sama sunan grandma dinta ta wajen uba wato Maryam ake kiranta Miemie…har zuwa wnn lokacin basa jituwa da sisters din mijinta dama mamansu gaba daya..kullum cikin nuna mata kiyayya suke kawai sbd ba ita sukeso ya auraba snn kuma da kasancewar Mum dinta igbo…wai Isma’il ya gur6ata musu family tunda ya hada musu jininsu dana inyamurai…haka aka cigaba da tafiya har ta sake haifan Ilham…ita kuma sunan Mummy aka sa mata Nadia ake ce mata ilham…wnn maida suna ba karamin tada rigima yayi tsakinshi da familynshi ba..wai don me zai sama yarinya sunan inyamurai…Sumayya da bata ta6a tanka duk abunda suke mata ba wnn karon kasa hakura tayi saida ta wanke su tatas ta kuma ce duk wanda ya sake izgili ga sunan mahaifiyarta sai sun kwashi ‘yan kallo dashi…labari na zuwa ga Isma’il mahaifiyarshi ta sanyashi gaba da kuka wai matukar yana sonta sai ya saki Sumayya tunda batasan darajanta ba tayi mara rashin kunya…da sukaga bazai saketa ba sai sukasa ya sake auran ‘yar sister din mamanshi sbd a kuntatawa Sumayyan…sunyi nasara kuma domin duk son da mijinta ke mata saida ta fara ganin canji tattare dashi…ya fara mata abubuwa wanda da ba haka yakeyi mata ba…gaba daya ma sai rayuwarshi ta koma 6angaren amaryarshi ita kuma ko oho don ko inda take bai cika zuwa ba…wnn abu yayi matukar daga hankalinta sosai tana ganin ko don yaranshi ai bai cancanci yayi abandoning dinta haka ba…daga karshe datayi kokarin nuna masa rashin dacewar abunda yakeyi sai yace taje ya saketa saki daya…bata sake wasting time ba kuwa ta hada kayanta ta wuce Abuja sbd a lokacin Daddynsu na matakin Controller General na Nigerian Custom so sun koma Abuja da zama…lokacin Ilham tana da shekara uku…haka suka cigaba da zama tareda iyayenta da kuma yaranta basu da matsalan komai…after a year Bobby ya kammala karatunshi a America lokacin shekaranshi kusan 9 a can…gaba dayansu suka shirya suka tafi America sukayi witnessing convocation dinsu snn suka dawo tareda shi Bobbyn da yakeda 27 years a lokacin…Sab kuma yanada 17 years kuma shima ya kammala secondary school.
Bayan kaman sati biyu da dawowanshi suka tafi kano wani taro da akayi inviting Daddy sai yace suje gaba daya…suka sauka nan gidanshi dake garin shi kuma ya wuce inda zasuyi taronsu…duk tsahon wnn shekarun daga Bobby har siblings dinshi babu wanda ke marmarin zuwa Gombe sbd cikinsu ba wanda baisan kalan hatred da sukeyi ma Mummynsu da su kansu ba…Bobby kuwa a lokacin ko mgnrsu ma baisonji…wani lokaci sai Daddy ya kira waziri ya waya ya hadasu su gaisa amma kowa zai kar6a shi kuma sai ya kirkiri wani abun ya tashi ya bar inda suke…Mummy duk tana lura dashi ta kuma san baya kaunarsu ne sam amma ko kusa batajin dadin hakan…tanaso ace ya samu kyakykyawan mu’ala da dangin mahaifinshi ko don sbd nan gaba ba wanda yasan me zai faru sai Allah.
A ranan bayan sun tashi daga taron shima ya wuce gida tareda zugan securities dinshi…misalin karfe 4:16 na yamma kiran wani brother dinshi ya shigo wayanshi…bayan ya dauka yake sanar dashi cewa waziri ne ba lafia kuma tun jiya yake cewa a kirashi yazo yanason mgn dashi…hankalinshi tashe sosai yace gashi nan zuwa Gomben yanxun…ba yanda Mummy batayi dashi kan ya bari da safe ba tunda yamma yayi amma yace sam bazai iya kwana while mahaifinshi nacan babu lafia kuma yana son ganinshi ba…babu yanda ta iya haka tabishi da addu’a…before ya fita ya shigo cikin gidan ya samu Miemie da Sab sai Sumayya a parlor nan yace musu zaije Gombe ya dawo suma suka mishi addu’an sauka lafia…yana shirin fita Bobby ya shigo parlorn rungume da Ilham da tayi bacci a hannunshi…shi kanshi yana ganinshi all dressed up yasan da akwai inda zaije…bayan ya fada mishi Gombe zaije ga mamakin dukkaninsu da shi kanshi Bobbyn yace zai rakashi…Daddy yayi mamaki sosai don sarai yasan duk yaran ma babu wanda yafi tsanan Gombe kamanshi amma yau shi da bakinshi yake cewa zai rakashi…bai yadda ya bishi ba yace zai tafi da driver shi kuma yanada bukatan ya zauna ko don ya kula da Mummy da sauran yaran…haka nan ya hakura amma har cikin ranshi baiso haka ba…shi kanshi baisan dalilinda yasa yau yaji yanason bin mahaifin nashi zuwa Gombe ba…duk abunda ke faruwa Mummy na zaune tana kallonsu itama bason tafiyan nashi takeba especially da yace dagashi sai driver zasu tafi bazai tafi da securities dinshi ba…a takaice bai samu ya bar gidan ba sai around 5…kaman yanda ya fada dagashi sai driver din nashi sukashiga mota suka kama hanyan Gombe…suna dab da shiga garin dan sun wuce Azare kawai sai ganin babban mota suka from no where tayo kansu gadan gadan…a kokarin driver na ya kaucewa motan sai kan motan ya kwace daya hannunshi gaba daya…daga nan kuma basu sake sanin inda suke ba sai ganinsu sukayi a Hospital…yana bude idanunshi yaci karo da waziri dake rikeda hannunshi idonshi yayi jajawur sbd tsabar rudun da yake ciki…ga kuma wasu daga brothers dinshi suma zaune a wurin…cikin tsananin ciwon kan dake addabarshi yayi kokari ya rike hannun mahaifinshi dake rikeda nashi…idonshi na zubda hawaye yake neman mahaifin nashi da ya yafe mishi…shima kanshi wazirin kaman zaisa kukan yace ya yafe mishi dunia da lahira..shima kuma yana rokon yafiyanshi kan duk abubuwan da ya aikata wa iyalinshi…shi kanshi yasan bai kyautawa abunda yake amma sam ya kasa denawa…yanxun kuma daya ganshi kwancs cikin jini sai duk wnn tsanar da aka sa yake mishi ya 6ace 6att sai tarin kaunar da yake mishi tun can baya suka shiga dawo mishi…lokacinda su Mummy suka karaso gaba daya ba wanda ke cikin hayyacinshi…kuka kawai suke har suka karaso inda yake…idanunshi ya shiga zagayawa akansu yanajin kaman kallon karshe yake musu…ya kalli Mummy da idanunta sukayi suntum sbd kuka sai Sumayya da har yanxu bata dena kukan ba…can gefe kuma Sab ne da Miemie suma rungume da juna suna nasu kukan sai kuma Bobby dake rikeda hannun ilham idanunshi a kasa sbd bayason suga yanda idanunshi suka sauya sbd kuka…hannu kawai ya mika mashi alaman yazo gareshi…cikin karfin hali ya saki hannun ilham tareda karasawa kusa dashi ya zauna ya kama dayan hannunshi da yake free…murmushi sosai yaga yanayi dan haka shima sai shiga kakalo murmushin yana kallonshi…cikin muryanshi da ko fita baiyi sosai ya nuna su Mummy dake jere suna faman kuka yace”na bar maka su amana…inaso ka kulamin dasu fiyeda yanda nakeyi…inaso ka zama gatansu…ko kusa kar ka bari suyi kukan rashina Bobby…they are now your responsibility”…kukane sosai ya kwace ma Bobby ya kasa cewa komai sai kai kawai da yake girgiza mishi…shi kuma ya sake kallon Mummy cikeda wani irin rauni yace”Your Mom…batada kowa Bobby…banaso tayi kukan rashina make sure ka kulada ita yanda ya kamata”…wnn karon ba Bobby kadai ke kuka ba gaba daya sauran ma kukan suke wiwi…suka hada ido da Sabeer shima ya mika mashi hannu yazo nan suka hada kai da Bobby sunata kuka abunsu…waziri dake zaune yana kallonsu bai ta6a jin ya tsani kanshi ba kaman yanda yaji a yanxu…kallonsu kawai yakeyi tunda suka shigo yanda ba wanda yabi ta kanshi a cikinsu…ya fuskanci akwai soyayya sosai tsakin yaran snn kuma yayi mamakin ganin yanda sukayi girma gaba dayansu…sai yakejin wani ciwo na rashin sakewa jikokin nashi da har Sumayya tayi ‘ya’ya biyu bai taba ganinsu ba…ya kasa dauke idonshi daga kan Bobby sbd tsantsan kaman da yakeyi da Attahir dinshi…gaba dayansu ma sai yaji wani soyayyansu na daban na shiganshi…yaji gaba daya suna wani burgeshi gasu gaba dayansu tubarkallah dasu akwai kyau…hakika ya aikata kuskurenda shi kanshi baya tunanin zai iya yafema kanshi…bayan like an hour doctor yazo yace su barshi ya samu hutu…haka suka fita daga dakin sukayi cirko cirko a waje…Waziri dake waiting room yana hangosu sai ya fita daga dakin yace ace musu su shiga daka ciki su zauna…basuyi mishi musu ba suka shiga cikin dakin shi kuma ya kowa wani tareda yaranshi guda biyu da sukayi mishi rakiya…suna nan zaune akazo aka sanar dasu rasuwar drivern da suke tare dashi…hankalin kowa ya sake tashi masu kuka suka cigaba da gashi.