Dr. BOBBY COMPLETE HAUSA NOVEL

In summary dai shima Daddyn cikin dare Allah yayi mishi cikawa…fadan tashin hankalin da suka shiga 6ata baki ne…Mummy kuwa dama ana fada mata ta fadi wurin a sume…har wahegari bata farfadoba ga kuma bp dinta da yayi rising sosai dole aka bata alluran bacci.
Daga nan direct Gombe suka wuce dashi…lokaci daya mutuwan nashi ya watsu a gari kusan ko ina…karfe goma na safe akayi jana’izarshi aka kaishi gidanshi na gaskia(ubangiji kasa muyi kyakkyawan karshe)…shina waziri tun a wnn lokacin ya fadi dan ko jana’iza ba’ayi dashi ba…mutuwan ya dakesu ne sosai ba kadan ba…su Mummy kuwa gidanshi dake nan Gombe aka bude suka shiga itada yan uwanta da abokan arziki.
Ranan da akayi kwana bakwai rigima ya 6arke tsakaninsu brothers din Daddy suka dage kan lallai bazasu fita daga Gombe ba tareda anyi rabon gado an fiddama mahaifinsu kasonshi ba…a cewarsu tunda mahaifinsu nada gado suma suna dashi wai idan suka yadda suka bari Gombe ba’a raba ba suna iya yin sama da fadi da wasu abubuwan…kasancewar Waziri na kwance tunda akayi rasuwar sai baisan abunda yake faruwa ba…tareda Bobby sukaita yawo duk inda kadarorinshi suke ya kaisu suka gani snn aka shiga kotu akayi rabo aka fitarma waziri da rabonshi kaman yanda yake a addinance…a ranan da aka gama a ranan ya tattara su gaba daya suka bar garin ba tareda ko waziri sunje sun duba ba…duk yanda Mummy tayi dashi kan suje suga jikinshi snn suyi mish sallama kin yadda yayi dan shi gani yakeyi ma kaman da wazirin aka hada baki aka kashe musu mahaifi tunda kira akai aka ce shine bashida lafia amma da sukazo sai sukaga akasin haka.
Abuja suka koma direct sukayi parking abunda zasuyi parking…ya sai musu sabon gida a kano kuma bai yadda wani cikin ‘yan uwan Daddy sun saniba snn ya sake daukosu suka dawo…gaba daya saida yabi ya canxa musu sim card dukda dama ba wani communicating sukeyi da yan uwan daddyn ba amma still saida ya canxa musu dan kwata kwata baison sake ganin kowa a cikinsu…su barsu suji da ciwon kashe musu mahaifi ma da sukayi…ko Sab da ba wani contact dinsu yakeda ba saida Bobby ya amsa layinshi ya bashi new one…Mummy dai bada son ranta yake abubuwan nan ba amma ko yaya tayi mgn sai taga ranshi ya 6aci fiyeda tunani…da farko ma cewa yayi sai yayi bincike if ya samu da akwai sa hannun one of them a accident din Daddy then bazai ta6a hakura ba saiya mgnr court…da kyar da sidin goshi Mummy ta samu ta taushe shi ya hakura da zancen…itadai har zuciyarta bata zargin akwai sa hannun wani a cikinsu…kawai tanaga ai duk kiyayyan da suke mishi bazasu iya aikata wnn danyen aiki especially akan dan uwansu…a lokacin abokan mahaifinshi da yawa suna kokarin taimaka mishi ya samu aiki amma yace shi sam bazaiyi aikin force ba infact bazai ma iya aiki under government ba…da taimakon wani uncle din Mummy wanda ya kasance likita ya bude katon Hospital dinshi mai suna Freedom Specialist Hospital…ya dauki ma’aikata sosai kuma most of them yare ne as gaba daya yanxu ya tsani hausa fulani because yana ganin kaman duk halinsu daya da ‘yan uwan daddy…snn kuma ya tsani Gombe ya tsani duk wani abu daya fito daga garin…bayan shekara daya Allah yasa mishi albarka sosai dan ya kusan ninka abunda ya kashe a iya wnn shekaran…daga nan sai yayi tunanin ya bude Nursing and Midwifery College snn ya bude primary da secondary school duk a nan cikin kano…da yake kudi ne suke aikin in no time ya samu fili ya siya aka fara mishi aiki…a shekara na biyu ya bude Freedom College of Nursing and Midwifery Kano da kuma Freedom Science Academy Kano…nan ma yayi employing staff sosai suma kuma daga igbo sai yoruba sai kuma sauran tribes amma bai dauki bahaushe ko daya ba…a lokacin ya damqa Freedom Science Academy a hannun Aunty Sumy cox 6angaren data karanta knn shi kuma College din ya damqashi hannun abokinshi Dr.Nur…da shawarwarin Mummy dana sauran mutane abubuwa suke tafiya yanda ya kamata…cikin shekaru kalilan ya samu kudi fiyeda tunanin mai karatu…ya cire Miemie da ilham daga school da suke zuwa ya maidasu freedom shi kuma Sab ya nema mishi admission a Nigerian Police Academy Wudil as yana matukar son ya zama Police sbd it was his Dad’s ambition.
In summary cikin shekara biyar Bobby ya zama hamshakin mai kudi a kano state…tuni ya gina musu very big mansion a can airport road inda babu mutane sosai…gaba daya rayuwarshi yanxub bai cika son mu’amala da mutane ba especially hausawa cox yana ga kaman suma zasuyi treating nasu some how sbd kasancewar Mummy inyamura…gidane mai kyau da girman gaske inda babu wanda zai takurama wani a cikinsu…a takaice dai yana kulawa dasu sosai sosai kaman yanda yayima Daddy alkawari…cikin shekarun nan kuma ya sake bude another College of Nursing and midwifery a Lagos sai kuma Freedom College of Health Sciences and Technology shima a Lagos…da yake a can ya girma har yayi primary da secondary school so yanada mutane a can sosai da suke handling mishi Colleges din as bai cika samun time yana zuwa sosai ba saidai yana providing musu duk wani abu da suke bukata…bayan nan kuma ya bude Freedom Medical College Gwagwalada Abuja…itama ba karamin kawo mishi kudi takeyi ba and a wata baifi yaje sau daya ba wani lokaci ma sai yayi two months baije ba sbd aiyuka da suke mishi yawa…haka rayuwansu yacigaba da tafiya har zuwa yanxub da Mummy ke son dawo mishi da duk pain da agony da suka fuskanta a baya.
Inaga gobe zaku jini shiru sbd zan danyi tafia…sai zuwa jibi in Allah ya kaimu????????
Masu bukatan siya zasu tura 300 zuwa 2208991344 Aisha Ahmad Tijjani Zenith Bank…sai a tura evidencs of payment ta 07063800556.
Rano✨
????Dr.BOBBY????
By Aysha Rano✨
Wattpad@aysharano22
11
Bayan sati hudu…
Yau tuesday Aysha na zaune cikin dakinsu kan study table ta dora macbook dinta akan table din tana kallon wasan Manchester United da Liverpool live…sai ihu takeyi tana nishadi duk ta cika dakin nasu da ihu sbd best player dinta Pogba gana performing well…yana ta6a ball zata hau ihu yanxu ma daddagewa tayi ta kwalla wani uban kara tana fadin”Goaal..yes yes..go on senior Man..go ahead”…Billy data fita karatu tun daxun sbd exams da suka fara jiya ta shigo dakin rungumeda katon text book dinta a kirji…ta karasa ta ajiye text book din kan shelve snn ta shiga rage kayan jikinta tana hararan Aysha tace”duk kinbi kin cikama mutane daki da ihu sai kace a kanki aka fara kallon ball”…Aysha da gaba daya hankalinta ke ga abinda take kallo ta saki wani smile tace”bazaki gane bane Billy wani hadadden ci Ronaldo yayi yanxun nan…and kinsan waye yayi assist?..”sake ta6e baki Billy tayi tana daura towel a jikinta tace”ya wuce Martial ko Rashford…ko kuma wnn gantalallen Lingard din”…tace”to duk basu bane Pogba ne..kuma gaskia kika sake cewa Lingard dinmu gantalalle za’aji kanmu dake a hostel din nan”…sake ta6e baki Billy tayi tareda shiga bathroom…har ta fito daga wanka hajia indo na nan inda take tana kallon ball dinta…ihu kuma ba fasa yinshi tayi ba saidai Pogba bai ta6a ball amma sai tayishi…Billy tayi banza da ita ta gama shiryawa abunta snn ta shiga kitchen ta hado corn flakes ta fito…tana zaune tana sha wayanta yayi kara…ta dauka ganin one of colleagues dinsu dake cikin hostel ne…tambayanta yarinyan keyi yaushe zasu fita karatu dan duk aka fara exams suna haduwa suyi karatu gaba saya su ‘yan class dinsu dake cikin hostel din su 15…Billy ta amsa da bata sani ba su tambayo Lamido…tana tsaka da kallonta mutum biyu suka shigo dakin…daya daga cikinsu tace”Lamido ya mgnr karatun mu na yau ne?..kowa yana Common Room fa ku biyu kawai ake jira”…san juyowa tayi tayi musu kallo daya duk hankalinta naga kallon da take sam bataso a wuceta tace”safiyya dan Allah kuje ku fara da Billy ana gama wasan nan zan zo”..tana rufe baki Billy tace”babu wani farawan da zamuyi kawai idan bazaki koyawa mutane ba ki fada musu ba sai kima hanya hanya ba”…ta fada tana wani basarwa tasan tunda ta fadi bazata iya cigaba da kallon ba dan a dunia ta tsani mutum yace tayi mishi wulakanchi taki koya mishi wani abu…harara sosai ta sakarwa Billy kafin ta juya tana dubansu tace”ku bani 5 minutes plss ana tafiya half time zanzo”…Billy ta juyar da kai tana kunshe daria dama tasan maganinta knn…kaman yanda ta fada ana tafiya half time din ta mike ta fita hajia Bilkisu tabi bayanta…gaba daya sauran sun taru a Common Room din su biyu kadai ake jira…dakin yanada girma sosai snn da akwai expensive set of kujeru masu kyau a ciki hadda su tv da fridge da standard ac inshort dai babu abunda babu ciki har su curtains da center table like normal parlor dai sosai…each apartment sunada Common Room dinsu da bama wani zama ciki sukeyi ba sai idan abu ya kama irin haka…bayan sun zauna Billy tace”to yanxu da wanne ya kamata mu fara”…da sauri wata tace”mu fara complicated midwifery dan Allah…daxun dana daukoshi zan fara karatu har wani hazo hazo naga ina gani sbd tsabar bana fahimta”…gaba daya sunyi na’am da haka dan haka suka fara da shi din…course outline dinsu suke dauka sunabi one by one suna explaining snn duk wanda yakeda tambaya ya fada a amsa mashi…suna gamawa dashi sukayi other course din da shima zasuyi exam dinshi gobe snn suka watse.