Dr. BOBBY COMPLETE HAUSA NOVEL

Dr. BOBBY COMPLETE HAUSA NOVEL

10:30 sharp suka fito daga meeting…direct Bobby office dinshi ya koma har yanxun ranshi bai dena baci kan abunda Nuru yayi mishi ba…yana shiga ya wuce ya hadama kanshi coffee snn ya zauna kan one of luxury sofas dake cikin office din yana sipping coffee din a hankali yana sauke numfashi…dama duk yake cikin bacin rai baida abun sha daya wuce coffee shiyasa ko a gida yanada coffee machine a flat dinshi duk yaji yana son sha hadawa kawai zaiyi…saida ya shanye coffeen yana kokarin komawa seat dinshi wayanshi dake aljihunshi ya fara ringing… yana daukowa yaga My Mummy rubuce kan screen with all sort of heart emojis…murmushi kyakykyawa ya saki kafin yayi picking call din wanda har hakan ya bani mamaki sbd yanda naga lokaci daya duk wann sadness dake kan face dinshi ya bace…hakan alama ne na tsanstan kaunar dake tsakaninshi da Mom dinshi…yana dauka cikin igbo yace mata”Mummy nah”…itama da igbo din tace”Bobby nah”…yana sake sakin smile yace”Mummy how are you?..”tace”ina lafia Bobby..yanxun wani employee dinka yazo ya sameni”…shiru yayi yana tunanin waye?..lokaci daya kuma zuciyarshi tace mishi Dr Bukar ne…jin baiyi mgn Mummy tace”are you there?..”yace”yes am listening Mummy”…tacigaba da fadin”he said his name is Dr Bukar…he told me all that happened between you two kuma ya fadamin yayi nadama dan haka ina ganin you should get him back to his job inshaAllah bazai sake faruwa ba”…Bobby yayi shiru yana sauraronta kmr ruwa ya cinyeshi…yasan wnn duk plan din Nur ne…shine nan zai tura Dr Bukar wurin Mummy sbd yasan bazai taba iya tsallake umarninta ba…wani bacin rai yaji yazo mishi amma bazai iya nunawa Mummy ba kmr yanda bazai iya tsallake umarninta ba…tunda yake Mummy bata taba sashi yin abu yakiyi ba and bazai so ya fara yanxun ba especially not because of that bastard dan haka yayi lowering voice dinshi sosai yanda bazata gane he’s angry ba yace mata”it’s ohk Mummy inshaAllah zan maidoshi…i will talk to Nur sai ya kirashi ya fada mishi”…yana iya jiyo farin cikin da Mummy ta shiga kafin tace”nagode sosai Bobby Allah ya maka albarka…Allah kuma ya baka kids da zasu maka biyayya kmr yanda kakemin”…murmushi kawai yayi without saying anything… itama bata damu da cewarshi ba don tasan dama bazaice din ba tunda duk tayi mishi zancen aure ko yara haka yake behaving…kwata kwata ta kasa gane kan Bobby akan wnn alamari…tace”you send Obi by 1 yazo ya daukan muka abinci”…saida ya wani marairaice muryanshi yace”Mummy yau ba sai an kawo ba pls…am not hungry”..tun kafin ya karasa Mummy tace”No i insist..yanxun zan barka kacigaba da aikinka and make sure you take care of yourself”…yana wani lumshe eyes dinshi yace”i will Mummy..bye”…itama tace mishi”bye”..snn sukayi sallama…mikewa yayi a fusace ya fice daga office din zuwa office din provost wato Nur…secretary dinshi na ganinshi ta mike sauri tana wani sandarewa kaman taga soldier tace”good day sir”…ko kulata baiyi ba ya banka cikin office din…Nur na zaune da wata lecturer a gabanshi tana mishi bayanin wasu abubuwa kawai sukaga mutumi a gabansu…baidai ce komai ba sai huci da yake like an angry lion…Nur na ganin haka yasan sunyi mgn da Mummy dan haka ya mikama malamar file dinta yace”am sorry miss Fatima kije zuwa gobe ki dawo mu karasa”…ba musu ta mike da sauri ta fita daga office din dan Allah ya gani tsoron Bobby takeji…bama ita kadai ba almost all of his staff tsoronshi sukeji sbd yanda face dinshi kullum a daure kuma mistake karami sai yaceya kori mutum…saida yaga ta fita snn ya juyo yana kallon Nuru da angry eyes dinshi yace”why did you do that?..”Nuru ya koma seat dinshi ya zauna yana daga shoulders dinshi yace”because i have no choice”…a fusace Bobby ya sake fadin”but how dare you…who gave you that right…haka nan sai ka ringa tura kowane jick and jerk yana mgn da mahaifiyata…are you sick or something?..”dagowa Nur yayi ganin yanda yake ihu kawai sai yasa daria…Bobby ya sake kulewa dashi yaji kaman ya watsa mashi mari…”so i have become a mad person right?..”da sauri yace”No..kawai wnn hakilon da kake yake bani daria…kan dan karamin abu kaman wnn kake bacin rai haka…haba mana…you need to stop this pls”..wani malolo Bobby ya sakeji yazo ya tokareshi…bai sake yunkurin cewa komai ba kawai ya juya ya fita daga office din…kai tsaye nashi office din ya koma yana cizon dan yatsa…agogon office din ne ya buga 11 dan haka ya sake ficewa zuwa inda motarshi yake…Mr.Obi na ganinshi yazo ya bude mishi motar ya shiga snn shima ya shiga suka nufi hanyar hostel…ta mirror ya hango motar Nur na binsu a baya don tare dashi zasu shiga hostel din…shi kanshi hostel din tafiya ce mai dan nisa tsakaninshi da inda classes dinsu suke…a fisrt gate suka fara tsayawa inda Male Hostel yake suka shiga suka duba aiyukan snn suka wuce next gate inda anan Female Hostel yake…basuyi wasting time ba nan ma suna gamawa kowa ya shiga office dinshi suka koma cikin school…har yanzun Bobby bai denajin haushin abunda Nur yayi mishi ba domin baiyi niyyar dawoda Dr Bukar ba sam dukda dama can sbd Nur din ya daukeshi aiki amma da bazai dauki bahaushe ya ajiye clinic dinshi ba…kowa office dinshi ya wuce..
Basu sake fitowa ba sai lokacin sallah…da yake staff masjid daban yake dan haka Nuru baiyi wahalar hango abokin nashi ba…yana kokarin zuwa ya sameshi kawai yaga ya mike ya fita shi kuma sai ya saki daria yana girgiza kai…yasan halin kayanshi tsaf duk wnn fushin babu inda zaije dole haka zaiyi hakuri ya barshi ko bayaso…shi kuwa Bobby ko office bai komaba ya nufi Clinic dake ta bayan office dinshi…Clinical instructor na ganisnhi ya mike tareda gaisheshi..
Bobby ya amsa a takaice snn ya bukaci sanin if there is any complicated case ko kuma emergency da yake bukatan doctor’s attention… da sauri Mutumin da ya dauko wani file guda daya ya fara mishi bayanin patient din da yanayin ciwon nashi kawai sukaji wani hadadden kara daga cikin Clinic din…Bobby ya kalli mutumin yana kokarin yin mgn ya sakejin wani karan this time around hadda magana amma bai gane me ake cewa ba…ranshi ne yaji ya sake baci ya kalli mutumin tareda ware masa idanuwansa yace”what the hell is happening here?..where is this sound coming from?..”da sauri mutumin yace”pls sorry sir…i think its..”Bobby bai bari ya karasa ba ya juya ya kama hanyan ciki inda yake jiyo sound din da sauri mutumin ya bishi a baya…so yake ya mishi bayanin ba wani serious abu bane amma he won’t dare sbd yanda yaga ranshi ke baci ba abunda bazai iya aikatawa ba…suna kara kusantowa karan da sukeji na kara karfi…saida sukazo daidai injection room snn ya tsaya…yana tura kofan daidai lokacin ta sake sakin wani karan tana fadin”aunty Meena dan Allah Nooo…wlh idan kika bani magani zansha amma banason injection pls pls plssss”…wani kullutun bakin ciki yaji ya sake tokare mai makoshi…yanxu dama duk wnn ihun akan common allura akeyinshi?..a fusace ya tura kofa ya shiga ciki aikuwa gaba daya mutanen dake ciki suka juyo suna kallonshi…shima kallonsu yakeyi daya bayan daya fuskanshi daure yanda kasan bai taba daria ba…Nurse Meena ce tsaye rikeda injection da swab a hannunta sai kuma wata student sanye da uniform dinta farare sol da ratsin pink a hannun riga alaman midwifery take karanta knn…dayar kuma tana tsaye ta kankame wadda ke sanyeda uniform din jikinta har shivering yakeyi sbd tsabar tsoro…dogon hijab ne a jikinta daya haura guiwarta da kadan sai skinny trouser dake jikinta red…almost rabin gashin kanta is out sbd batasa dankwali ba kuma hijab dinta ya dan zame kadan…gaba dayansu ba wanda hantar cikinshi bai duri ruwaba sbd wanda suka gani tsaye a wurin…da sauri Meena ta risina tana fadin”good afternoon sir”…ba tareda ya saki face dinshi ba yace”afternoon… what’s going on here?..”da sauri Meena tayi pointing yarinyar dake sanye da hijab tace”Sir batada lafia ne shine doctor yace a bata wnn injection din to ita kuma batason injection shine take kuka”…wani haushi Bobby ya sakeji ya juya yana kallon yarinyar da idanunta ke runtse sai sauke ajiyar zuciya take…murya a kausashe ya kalli wadda take rikeda ita yace”let go of her right now”…da sauri ta matsa daka jikinta tana sunkuyar da kai gabanta nata aikin faduwa…itadai ko Allah yasan bakaramin tsoron Proprietor dinsu takeba…shi kuma ya tsayar da idonshi kan yarinyar da har yanxu bata bude idanu ba dukda cewa tasan shine a wurin kuma jikinta bai bar shaking ba sbd tsabar tsorata da tayi..duk iskancinta tana tsoronshi sbd tasan bashida mutunci ko kadan…saida ya sake daure face dinshi snn yace”C’mon open those eyes before i slap you”..da sauri ta bude idanun nata ta dora a kanshi..sai kuma tayi kasa dasu da sauri sakamakon kadawar da hantar cikinta yayi…ya mikama Nurse hannu ba musu ta mika mashi injection din snn ta sake dauko another swab da hand glove shima ta mika mashi…yana karba ya ware idanunshi masu ladabtar da fitinannu a kanta murya cunkushe yace”come over here”…tana dago kanta taga injection a hannunshi sai ta fara yarfa hannu tana fadin”dan girman Allah Sir…”bata samu courage din karasawa ba sbd idanunshi da suka ladabtar da ita…ta juya tana kallon friend dinta data rakota clinic din wai ko zata taimaka mata amma sai taga kanta a kasa…ta kalli nurse da clinical instructor suma duk taga alaman a tsorace suke sai ta shafama kanta salama ta shiga takawa a hankali sbd ciwo da kafanta ke mata har zuwa inda yake…hawayen dake zuba a idonta kuwa ko pump albarka…Bobby na tsaye da injection a hannu yasa glove a both hands dinshi har saida ta karaso snn ya sake murtukewa yace”turn your back”..batayi musu ba ta juya bayanta jikinta nata rawa…kallo daya yayiwa Meena ta gane me yake nufi dan haka ta karaso inda suke tareda kama hijab din jikinta ta daga bayan tayi covering dinsu da screen…ta sauke wandon jikinta a hankali nan take fair bombom dinta ya bayyana iya daidai inda zaayi injection din…Bobby ya dauke kanshi gefe tareda dan risinawa ya zura injection din a jikinta aikuwa ta saki wani irin ihu tana kokarin kwace kanta Meena tayi mata kyakyawan rikon da bazata iya kwacewa ba…saida ya gama injection din snn yayi disposing syringe a safety box ya cire glove dake hannunshi itama yayi disposing snn ya juya ya fita daga injection room din clinical instructor ya bi bayanshi…ita kuwa wadda akaiwa injection sai yanxun ta samu daman saki kukanta…tana kokarin dukushewa a wurin friend dinta tai saurin kamata suka zauna kan bed tanata kokarin mulmula mata wurin amma sai kaucewa take wai bataso a taba…zaunawa tayi kusada ita saida ta gama gursheken kukanta snn ta kamata suka fito daga dakin tana takawa da kyar sbd rikewan da kafan nata ya sakeyi…every month haka take fama duk zatayi period sai yasa mata ciwon kafa ko ciwon baya haka za’ayita tata6urza da ita kan allura sai kace small baby…har sukazo wucewa ta bayan office din Bobby bata dena kuka ba…saida suka fita ta samu daya daga cemet shairs dake wajen admin block ta zaunar da ita akai snn tayi dialing number da tayi saving da Lamido’s Bestie a wayarta…tana fara ringing ya dauka yana fadin”are you done?..”a hankali tace”yes muna ta wajen admin and kayi sauri kazo dan ta isheni da kuka”bata jira ko zaice wani abu ba ta kashe wayarta…ba bata lokaci kuwa sai gashi yazo inda suke…saurayi ne da akalla zaikai 25 years..baqi ne dogo kuma kyakyawa dashi yana sanye cikin uniform dinshi complete white yayi tuck in shirt dinshi…da sauri ya zauna kusa dasu yana duban mai sanyeda uniform yace”Billy kin tabbata ta samu sauki kuwa?..duba fa yanda take kuka?..”harara me kyau Billy ta watsa mishi tace”kajika da wani magana sai kace bakasan halin bestyn naka ba…allura fa akayi mata shine take wnn abun kamar an yankata”…bata rufe baki ba wadda akama alluran ta dago tana dubanta fuska shabe shabe da hawaye tace”ni wlh gara a yankani akan dai ayimin allura…sbd tsabar mugunta inata ce miki kizo mu gudu amma kika ki har saida wnn azzalumin yazo”..rai a bace Billy ta mike tana kokarin barin wurin tace”ba laifinki bane Lamido laifina ne da nake damun kaina a kanki…next time dama kina fara rashin lafiyarki saidai bestyn naki yazo ya kawoki Clinic amma bani Bilkisu ba…kuma wlh saina kira Ammi na bata labarin duk iskancin da kikayi”…tana gama fadin haka tayi wucewarta ta barsu a wurin…Lamido ta sake fashewa da matsanancin kuka shi kuma bestyn nata ya danyi kasa da murya yace”besty dont mind Billy kinji..yanxu ki daure ki tashi in maidaki hostel sai ki samu ki huta sosai”…yana rufe baki ta hau girgiza tana hawaye tace”i dont think i can walk besty..gaba daya leges dina sun sake rikewa”..ya sake fadin”daurewa zakiyi besty just try it zaki iya”…ba musu ta dafa kujeran da take zaune tareda mikewa da kyar…shima mikewan yayi ya nufi inda motarshi yake ya bude snn ya dawo ya taimaka mata suka karasa wurin..tana shiga shima ya zaga ya shiga snn tayar da ita suka nufi gate din hostel.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128Next page

Leave a Reply

Back to top button