Dr. BOBBY COMPLETE HAUSA NOVEL

Washegari bayan sun fito daga exam Aysha ta shiga kiran Sa’eed da tun safe bata ganshi ba…yana dauka tace”bestie where are you?..”yace”ina downstairs…kun fito daga exams?..”tace”eh..bari muzo downstairs din”…tana kashe wayan ta dubi Billy tace”muje yana kasa”…Billy ta wani hade rai tace”wai me zaiyi miki ne da kiketa nemanshi tun daxu?..”Aysha bata ce mata komai ba taja hannunta suka sauka kasa…can wajen wasu flowers masu kyau suka hangoshi yana zaune da wata class mate dinshi da alama yana koya mata abu ne…karasawa wurin sukayi suka zauna shi kuma ya sallami yarinyan da suke tare snn ya shiga kallonsu with a smile yace”so how was the exams?..Aysha tace”exam Alhamdulillah besty ya naka?..”yace”it was fine”…kallon Billy dake duba littafin hannunta yayi yace”so Bilkisu ya exams?..”tace”lafia lau”…ya kalli Aysha suka hada ido snn ya sske cewa”sai wani hade rai kikeyi sbd kin ganni…ki kwantar da hankalinki munayin counsil bazaki sake ganina ba”…ya karasa mgnr kaman wani abun tausayi…lokaci daya sai Billy ta dago tana kallonshi…idan akwai abunda ta tsana bai wuce yayi mentioning counsil exam ba duk sai taji jikinta yayi wani sanyi…ganin yanda ta kura mashi ido suka sake hada ido da bestyn shi sukasa daria…bayan sun gama yace” my Mom will be coming tomorrow.. hope zakuje ku gaisheta?..”da sauri Aysha tace”of course zamuje mana bestie..Allah ya kawota lafia…and yauwa bestie zaka kaimu lalle ranan Thursday idan mun fito daga exams…kasan cikin week din nan zaa fara bikin Adda Ruky”…yace”na sani besty amma baki ganin zaku samu matsala idan aka ganku da lalle?..nasan kinsan cikin ethics dinmu hadda kin applying wadan nan abubuwan”…tace”i know besty amma bansan ya zanyi bane…tun Thursday fa zaa fara bikin kuma ni bazan samu zuwa ba sai friday kaga banida time din yin lalle da sai na bari idan mun koma muyi…besides nafi son lallen kanawa yanxu..yafi namu kyau”…bai sake cewa komai ba kawai ya girgiza kai dan yasan tunda tasama ranta sai tayi lallen nan duk abunda zai fada ma ba changing mind dinta zatayi ba.
The following day kaman yanda suka tsara bayan sun fito daga exams suka koma hostel sukayi changing kaya snn ya kwashesu zuwa Tarauni gidan kakarshi…suka samu Mom dinshi zaune a parlor da Hajia sai dan autansu Mahmud…suka karasa ciki suka zauna snn suka gaisheta…ta amsa musu da fara’a tana tambayan su ya karatu…suka amsa da fine…tace”ga bestie ga Bilkisu koh?..”Sa’eed dake sauraronsu yace”Mom ashe baki manta ba”..tace”ya za’ayi na manta tunda kullum cikin zancensu kake”…Hajia tace”nima nan haka yake damuna da zancensu..magana daya biyu zaice besty tayi kaza ko kuma Billy tace kaza”…daria sukayi gaba daya jin yanda Hajia ke immitating mgnrshi…yana dan hararanta ta gefen ido yace”yanxu Hajia haka nake mgn?..”tace”oho kai ka sani”…sister dinshi ce ta fito daga daki waya kare a kunneta…tana ganinsu tayi hanging call din ta wani karasa cikin parlon da gudu ta fada jikinsu…Sa’eed yac”Lubna meye haka?..karya min su kikeso kiyi ne?..”ta daga jikin nasu tace”sorry yaya..nayi farin cikin ganin kawayena ne…kawayena da basu damu dani ba”..ta karasa mgn kaman zatai kuka…Mom tace”to sai ku shiga daki ku karasa mgn dan naga kaman they are not comfortable here”..Lubna ta mike tsaye rikeda hannayensu tace”yanxu kuwa Mommy”..daga haka
ta jasu zuwa dakinda ta fito Sa’eed ya bisu da kallo har suka shige…Hajia dake ankare dashi tun dazu tace”mutum dai yayita yaudaran kanshi da sunan kawance..watarana kana zaune wani zaizo ya dauke ya barka da cizon yatsa”…juyawa yayi yana kallonta yace” me kike nufi?..”tace”me kuwa nake nufi daya wuce kana son mace kana yaudaran kanka wani wai kuna kawance..idan bakayi da gaske ba kana zaune zata auri wani ta barka wlh”…yace”to ke waya fada miki inason wata a cikinsu?..we are just friends “..tace” shine nace kacigaba da yaudaran kanka Sa’eedu”…bai sake mgn ba ya juya yana kallon Mom dinshi sai yaga daria take musu..zaiyi mgn tace”babu ruwana tsakaninku ne wnn”..
Suna shiga daki suka zauna suna sake gaisawa…Lubna tace”da gaske mutanen nan baku damu dani ba..ko nemana fa ba wanda yakeyi a cikinku”…Billy tace”wlh abubuwan ne sai a hankali Lubna amma inshaAllah daga yanxu zumunchi sai kince ya isheki koba hakaba Lamido?..”da sauri tace”sosai ma kuwa..daga yanxu mun kulla knn har sai mun isheki”..tace”nikam ba wani dadin baki da zakuyi min dan bazan taba yadda ba sai naga kunzo har kd bikina snn zan yadda daku”..Billy tace”u mean an kusa bikinki?..”tace”in the next three months inshaAllah”..Aysha tace”Allah ya kaimu ya sanya alkhairi…amma besty bai ta6a fada mana ba wlh”..Billy tace”shine nima nake mamaki ai..koda yake kadan knn daga aikin Sa’eed”…nan kuma hiran nasu gaba daya ya koma kan bikin Lubna da irin shirye shiryen da zasuyi…if u see yanda suka sake da juna suna labari zakayi zaton tasowa sukai tare tun kuruciya nan kuwa basu dade da sani juna ba shima ta dalilin Sa’eed wani lokaci da tazo ta dade a kano ya kaita hostel dinsu shknn suka kulla kawance…basu fito daga dakin ba saida yazo da kanshi yace su fito ya maidasu snn suka fito…sukayi sallama da Mom da Hajia da har yanxu suke parlor…Mom ta basu dambun nama da tayoma Sa’eed da Hajiyarta cikeda wani flask aikam sukaita godia snn suka tafi har Lubna data dage zatayi musu rakiya…kaman yanda ya saba duk ya fita dasu sai ya siya musu kayan kwalama yake maidasu yauma haka ya tsaya a grand square ya sai musu su chocolates da sweets snn yayi dropping nasu a hostel su kuma suka koma tareda Lubna.
Washegari Thursday suna zaune a premesis kafin time din shiga exam dinsu yayi motan Proprietor ya shigo makarantan…Ayshata wani hade rai dan tana gani ta gane motanshi ne…ko gama parking motan baiyi ba securities da some of staff da sukaga shigowanshi sukayi inda motan yake kaman yanda suka saba…tana daga zaune tana ganin yanda suka bude mishi kofa ya fito sunata wani washe mashi baki hadda masu risinawa suna gaisheshi kaman wani ubansu…Billy ce ta fara lurada ita sai tace”are you okay?..”ta saki wani tsaki tana fadin”mutanen can ne suke bani haushi wlh…dubi yanda sukema inyamurin mutumin can kaman zasuyi mishi sujada…kawai dan mutum nada kudi sai kuyita kaskantar da kanku a wurinshi da yawa daga cikinsu mafa sun girmeshi”..girgiza kai Billy tayi tace”to ke ina ruwanki…kuma an fada maki ba inyamuri bane har yanxu kin ki yadda koh?..”ta maka mata wani harara tace”wai wnn mutumin zaki kalla kice ba inyamuri bane haba Billy..”Sa’eed daketa sauraronsu yace”da gaske ba igbo bane shi besty..ance dai Mom dinshi igbo ce amma babanshi bafulatani ne fa”…da sauri Billy tace”tell her…bafulatanin ma kuma dan garinku”…da sauri ta daga kai tana kallonta tace”what do u mean?.”Billy tace”ina nufin dan Gombe ne shi mana”…tun kafin ta rufe vaki tayi spitting tana binta da wani disgusting look tace”God forbid…how could such a heartless person come from Gombe?..gaskia i doubt that kilan dai bakuji daidai ba…and wether u accept it or not mutumin can inyamuri ne kuma na tabbata yana daga cikin masu assasa yakin Biafra sbd tsabar mugun halinshi”…daria suka sa mata gaba dayansu aikuwa ta cika tayi fam har ta mike zata bar wurin Billy ta janyota da sauri tace”to shikenan Sa’ees tell her mun yadda inyamuri ne shi”..da sauri yace”eh mana kuma a cikin inyamuran ma yana daya daga cikin masu assasa yakin Biafra so are we good now?..”murguda musu baki tayi tana hararansu…ganin time din exam ya gabato duk suka mike zuwa classes dinsu.