Dr. BOBBY COMPLETE HAUSA NOVEL

Taci sa’a tana zuwa aka fara raba question papers ta karasa seat dinta da sauri ta zauna…Billy daketa baza ido taga shigowanta tun daxu ta saki ajiyar zuciya dan sam hankalinta bai jikinta ganin har za’a fara bata shigo ba.
11 daidai suka fito daga exam hall…already Hamma Najeeb na zaune cikin mota yana jiransu dan haka suna fitowa suka nufi inda suka hango motanshi…shima yana hangosu ya bude motan ya fito…suna karasowa ta wani kwa6e fuska kaman zatasa kuka snn ta kama hannunshi ta rike idonta na cikowa da hawaye…hankali a dan tashe yace”what happened again?..”ganin taki mgn ya juya yana duban Billy yace”me akai mata?..”Billy ta buda hannu alaman bata saniba…shi kuma ya kama hannunta suka kan wasu cement chairs dake gefe still hannunta cikin nashi yace”Maama plss talk mana..waya ta6amin Mamana?..”tana turo baki tace”Hamma i don’t want to come back to this college kayi mgn da daddy plss”..yace”but Maama why?..did something happen again?..”tace”Proprietor ne…Hamma wlh ya tsaneni..kawai daxu yayita min wulakanci hadda cewa bazanyi exam ba sbd nayi lalle..nidai i don’t want to come back plss”…kamo dayan hannunta yayi yana dubanta da kyau yace”Maama kinsan daddy bazai ta6a yadda ba tunda ke kika dage sai an kawoki nan…but i think i have to talk to Proprietor din naku ya bar takura maki kawai”…tana goge hawayenta tace”there is no need..idan kaje ma wulakanci zai maka na sani…Hamma inyamuri ne fa..ko cikakken hausa bai iyaba”…yace”to indai bakiso inje in sameshi ki bar kukan nan haka..yanxun ku debo kayanku mu wuce amarya nata kirana wai inyi sauri in kaiku da wuri”..da sauri ta karasa goge hawayen nan da nan kuma saiga murmushi a fuskanta tace”laaa Hamma kasan har na manta wlh…Billy taso mu tafi nasan yanxu ana can ana shirye shiryen kamu”…girgiza kai kawai Billy tayi tana mamakin halin Lamido da shegen son biki..yanxun nan fa take kuka sha6e sha6e amma daga jin mgnr biki ta wartsake…kayansu kawai suka dakko daga wani class don dama basu fito da shirin komawa hostel ba..suka zuba su cikin booth snn suma suka shiga motan Hamma yaja suka tafi…basu samu yin sallama da Sa’eed ba as har time din yana exam hall bai fito ba..dama ba lokaci daya suka shiga ba so sun rigashi fitowa.
Saida suka fara tsayawa Bauchi suka ajiye Billy snn suka wuce Gombe bayan tayima Lamido alqawarin zata zo gobe ayi bikin da ita yau dai tanaso ta huta gajiya…suna shiga cikin Gombe murnanta ya kasa 6oyuwa dan ba karamin missing gida tayi ba…kai tsaye GRA suka nufa inda a nan Estate dinsu yake…Estate ne babba inda ciki duk wani wanda ke amsa sunan Lamido yake.. a nan ciki gidansu yake tun daga kan ‘ya’ya da jikokin Lamido maza baya bari suyi nesa dashi mata ne kadai suke fita shiyasa ake yima Estate din laqabi da LAMIDO’S PALACE…horn yayi jikin tangamemen gate din shiga Estate din wanda daga can samanshi aka rubuta THE LAMIDO’S in capital letters..masu gadi sukazo suka bude mishi yasa kan motar ciki…tsayawa fadan haduwan ciki ma bata baki ne kawai dai is one of the biggest and beautiful Estate i have ever seen…ya tsaru ne iya tsaruwa snn yana daukeda gidajen da ni kaina bazance ga adadinsu ba don sunada yawa sosai…layi na uku ya shiga by his right side snn yayi parking motan a daidai kofan gidan daya kasance shine na uku layin…tun kafin ya kashe motar ta bude kofa ta fita da gudunta ta fada cikin gidan…bata ga kowa a parlor ba dan haka ta wuce zuwa dakin Ammi…a gaban madubi ta isketa zaune tana daura dankwali ta karasa da saurinta tayo hugging nata ta baya tana fadin”Ammi nayi missing diki wlh”…a hankali ta juyo ta zame hannunta daga jikinta snn ta daure fuska tana kallonta tace”bakida hankali kou?..wnn shine sallaman?..”rungume hannu tayi tana turo baki tace”Ammi nayi kewarki nefa sosai shiyasa amma kiyi hakuri”…juyawa Ammi tayi tacigaba da daurinta tace”zakici ubaki ne”…sake turo baki tayi tace”yanxu Ammi ko gaisawa fa bamuyi ba”…Ammi data gama daura dankwali tana kokarin sa wayanta cikin hand bag dake hannunta tace”ni kike jira in gaisheki ai tunda ke kika haifeni”…kaman bata son mgn tace”Ammi ina yini..ya gida”…tace”lafia lau ki wuce kije kiyi wanka ana gama ma su Husna make up kema ayi miki ku taho..tun daxun ake tafiya sbd ke nace su jira ku wuce tare”…tace”to bari inje Ammi..amma Aunty Fiddausi bata zo bane?..”tace”bazata samu zuwa ba Mufid ne ba lafia wai…yanxun mu fara zuwa ku gaisa da daddy sai kije kiyi wankan”…tare suka fita daga dakin bayan Ammi ta yafa mayafinta…tayi kyau sosai cikin coffee lace daya amshi skin clour dinta sosai snn kallo daya zaka mata kaga tsananin kamar da Lamido takeyi da ita…a zahiri kuma bazaka ta6a cewa ta haifeta ba dan yanda suka jero sai sukayi kaman kawaye…a palor suka samu daddy zaune yana yin waya…suka karasa ciki Ammi ta zauna kusa dashi ita kuma malama A’ee ta zauna a kasa tana wani irn nutsuwa kaman mutumiyar kirki…bayan ya gama wayar ya dubi Ammi da tayi mishi kyau kwarai yace”har kin gama?..”tace”na gama daddy zuwa zanyi Najeeb ya ajiyeni a hall din kafin ya fita..su kuma idan sun kammala sai Idris ya kawosu”..gyada kai yayi yana fadin”ohk”..snn ya maida kallonshi ga Aysha da take zaune tsumu a kasa kaman ba ita ba..cikin sabuwar nutsuwar data aro ta yafawa kanta tace”daddy barka da yamma”..yace”yauwa Aysha an dawo?..”tace”mun dawo daddy”…yace”Maa sha Allah ya exams?..”tace”daddy Alhamdulillah”…yace”to Alhamdulillah ya ban ganku tareda Bilkisu ba?..”tace”sai gobe zatazo daddy”..ya gyada kai yace”Allah ya kaimu..sai kije ki fara shiryawa kar suzo suna jiranki”..a hankali ta amsa da”toh..”snn ta mike ta bar parlon…itama Ammi mikewa tayi da bag dinta a hannu tace”nima bari in wuce daddy lokaci na kara tafiya”..kama hannunta yayi ya zaunar da ita yace”ki bari in kaiki da kaina mana…irin kyau da kikayi ya kamata ace sai na gama gani zaki tafi”..murmushi ta saki tana girgiza kai tace”daddy bakada dama wlh…inaga sai kaga mun aurar da Aysha snn zaka gane girma ya fara zuwan mana”…yaja dogon hancinta yace”ke girma ya fara zuwan ma bani ba..kuma ko mun aurar da Aysha ni babu abinda zai canxaki cikin zuciyata”..daria ta saki tana jin kaunar mijinta ta ko ina a jikinta snn ta sake mikewa tace”to nidai ayimin uzuri in wuce ba don ni ba..nasan yanxu ana can ana menana wlh”…bai sake yunkurin hanata ba yace”sai kin dawo Allah ya kiyaye”..ta amsa da”Ameen”..with a smile snn ta fita daga parlon…a main parlor ta samu Najeeb na jiranta dan haka yana ganinta ya mike suka fita tare..dukda cewa hall din da suke bikin cikin Estate din yake yanada nisa sosai da baza’a iya zuwa a kafa ba.
Aysha kuwa tana shiga dakinsu ta iske Husna zaune ana mata make up din Yusra kuma na kwance kan gado…saida suka gama rungume rungumesu itada Yusra as usual Husna nata faman ta6e baki tana binsu da harara snn ta fada bathroom tayo wanka sharp sharp ta fito…lokacin am gamawa Husna an farama Yusra…ita kuma ta tayar da sallah bayan ta idar ta dauki kayanta da yake iri daya dasu Husna har dinki ta saka snn ta zauna zaman jira.
Karfe biyar da wani abu suka shigo cikin hall din…dukkaninsu suna sanye cikin atampan ankonsu dark blue da adon sky blue a jikinta…kaman yanda na fada dazu hatta dinkinsu iri daya ne haka daurin dankwali da akai musu shima iri daya ne..takalmi da jakansu ne ya bambamta amma duk color daya ne…hall din ya cika makil da mutane banda sautin waka ba abunda ke tashi a ciki…amarya na zaune high table tareda angonta…Aysha na hangota ta fara zuwa inda take kawai suka rungume juna cikin rada tace”adda ruky kinga kyan da kikayi kuwa?..”amarya data kasance cousin dinta domin diyar yayan daddy ce tace”duk kyauna ban kaiki ba Lamido”..ta matsa daga jikinta tana dan turo baki tace”kema Lamidon zakice?..”itama amarya komawa tayi ta zauna snn tace”yes koba sunanki bane?..”tace”sunana ne kaman yanda kema yake sunanki..so daga yanxu duk kika kirani da Lamido kema da Lamidon zan kiraki”..murmushi kawai tayi mata ita kuma ta juya ta tafi..can inda ta hango da yawa daga cousins dinta ta nufa wanda duk yawancinsu age mates dinta ne suma duk suna sanye da anko…nan suka hau rungume rungume suna farin cikin ganinta.