Dr. BOBBY COMPLETE HAUSA NOVEL

Rano✨
Wnn littafin na kudi ne ban yadda wani ko wata ya fitarmin dashi ba…masu buqatan siya zasu tura 300 zuwa 2208991344 sai a tura evidence of payment via 07063800556.
14
Miemie ta amsa kayan ilham din ta hadashi da nata cikin bag din data dauko snn ta samu wuri ta zauna…Hafsa ta mike tana duban Mummy tace”Mummy to bari muje in Allah ya kaimu gobe da kaina zan dawo dasu..nagode sosai da sasai Allah ya saka da alkhairi ya kara girma”…Mummy tace”ba komai Hafsa Allah ya bata lafia”..ta amsa da Ameen snn ta rike hannun Ilham zasu fita Mummy tace”Ilham ba sallama?..”juyowa tayi tana murmushi tace”ba bye Mummy mun tafi yawo”…murmushi na daria tace”to a dawo lafia”..daga haka suka fita Aunty Sumy da Miemie sukabi bayansu…kafin su karaso har ta bude mota sun shiga..suna zuwa Miemie ma ta bude ta shiga ita kuma Aunty Sumy tace”to shknn Hafsa sai goben koh?..”Hafsa tace”eh inshaAllah…ina godia fa Maman Miemie Allah ya bar zumunci”..Aunty Sumy tace”Ameen”..snn ta dagama ilham hannu alama bye itama ta daga mata…Miemie dai na zaune back seat duk rai a 6ace..sam batason zuwan inda matar nan wlh..dukda ba wani girma gareta ba time din she can still remember yanda sukayi treating nasu kaman ba family dinsu ba…bayan sun gama sallama Hafsa taja mota ta tafi ita kuma Aunty Sumy ta koma gida.
Basu zarce ko ina ba sai gidan kakarsu dake Kabuga…tana gama parking ta bude motar ta fita tareda kama hannunsu gaba daya su biyun suka shiga cikin gidan a haka…kakarsu na kwance parlor tana jiran karasowarsu…tana ganinsu ta mike zaune da kyar ta kama hannayensu kawai sai ta rushe da kuka..ba ita kadai ba hatta Hafsa saida ta tayata kukan…ko baa fada ba tasan tanajin ciwon raba Sumayya da Isma’il tunda gashi nan tun bayan rabuwarsu ta kasa gane kan danta…matar data aura mishi ma bai dade da rabuwa da Sumayyan ba ya saketa shi kuma ya tattara ya koma London da zama sbd baqin cikin rashin Sumy…kuka takeyi sosai tana cewa su taimaka su yafe mata snn su roki mamansu ma ta yafe mata…Ilham dai tayi tsuru as kwata kwata bata san inda zancen ya dosa ba…Miemie kuwa sarai ta fahimci me take nufi amma tayi gum da bakinta dan bataji zata iya yafewa ba itadai…ta dauki tsohon lokaci tana kuka tana su yafe mata ganin kamar numfashinta zai dauke suka rabata da hannuwan yaran da kyar snn suka dauketa suka maidata daki itada autarsu mai suna Safiyya…Hafsa na fitowa daga dakin ta dannama dan uwanta video call don yace tana daukosu ta kirashi vid call yanaso ya gansu…yana ganin kiran nata ya dauka tana murmushi tace mishi”to Yaya ga ‘ya’yanka dai yau na kawosu wajen Umma”…yace”kin kyauta sosai Hafsa..dan banisu mu gaisa plss”…ba musu ta mika musu wayan tace”speak to ur Dad”..Miemie ta wani hade rai snn ta karbi wayan…kallonsu ya shigayi sosai idonshi na cikowa da hawaye…it’s been six long years rabonshi da ganinsu..yanxun kuma daya gansu sai yakejin wani irin kewa da sonsu na sake shiganshi…murya can kasa yace”Mamana”…Miemie ta dan tsuke baki kafin tace”na’am ina yini”…yace”lafia mamana ya school?..”a takaice tace dashi”fine..”kallonshi ya maida ga Ilham da tayi tsit tana kallonshi dan ba saninshi tayi ba…shima saida yaji wani kuka ya taho mishi da yaga kallon da take masa…ko ba’a faa ba yasan kallon rashin sani ne wnn..wai ace yana matsayin mahaifinta amma ta tashi bata sanshi ba…shi kam ina zaikai zunubin yaran nan dana uwarsu?..itama murya a sarke yace mata”Maman Aunty”…ta sake yin zuru tana kallonshi dan bata gane me yake nufi ba..Miemie dai ta gane don bazata manta ba lokacin tana jaririya haka yake kiranta Maman Aunty ita kuma Miemien ya kirata da Mamana..itama Aunty tacema Miemie Maman daddy snn tacema Ilham Mamana…yayi kokari ya maida hawayen dake idonshi yace”baki sanni ba right?..”da sauri ta daga mishi kai…yace”i am ur father”..yarinyar ta wara ido sosai hadda su rufe baki tace”Uncle Bobby ne babanmu ai”…yace”yea he is ur dad but ni na haifeku”…idon ta sake budewa cikeda mamakin abunda ya fada tace” dama maza suna haihuwa ne?..”diff yayi kamar ruwa ya cinyeshi..sai can kuma yace”sunayi mana kinga ni din nan nine babanku..shi kuma Uncle Bobby uncle dinku ne shiyasa kuke kiranshi da uncle”…kafin Ilham ta sake mgn Miemie tace”sai anjima”…tana kokarin kashe kiran yace”don’t hang up plss..i missed u guys alot ko ganinku bazaki bari nayi ba?..”tayi shiru ba mgn shi kuma yace”ya Mamanku?..”ta sake cewa”she is fine..”shima ya danyi shiru na tsahon lokaci kafin yace”i know u are upset with me Miemie but believe me wlh nayi regretting komai dana aikata dan haka please inaso ki yafemin snn ki tayani rokon mamanki ma ta yafemin”…kallonshi Miemie tayi for like two minutes snn tace”toh..”daga haka bata jira me zaice ba ta kashe kiran..sam ta gaji da jin wnn maganganun nashi…ita har taso ta manta kamanninshi ma wlh..ilham kuwa dama bata sanshi ba so bata dauki abunda ya fada serious ba…haka suka kwana gidan duk basu wani sakewa dasu duk kuwa da yanda yan gidan suke kokarin jansu a jiki kin sakewa sukayi.
A can gida kuwa Bobby baisan tare dasu Hafsa ta tafi ba saida ya dawo daga Hospital around 9 na dare ya tambayesu Aunty Sumy tace sun tafi da Hafsa…wani hadadden kunchi yaji yana sauko mashi..yanxu knn Mummy saida ta tura yaran nan suka tafi?..bayan duk abubuwan da suka aikata a baya still take kokarin patching things up dasu?..ranshi gaba daya yaji ya 6aci..kawai ya wuce Flat dinshi…karfe goma da wani abu Mummy ta zuba abinci ta dauka da kanta ta nufi Flat din nashi…yana kwancen can kuryar gado ya juyama kofa baya..ta karasa ta ajiye abincin hannunta kan table snn ta isa gefen gadon nashi ta zauna…a hankali takai hannu ta zare hannunshi daya rufe fuskanshi dashi…ha dago yana kallonta snn ya mike zaune da kyar kaman mara lafia…sake kama hannun nashi tayi ta rike tana kallonshi da igbo tace mishi”so u are upset with me right?..”a hankali ya girgiza kai alaman aah…tace”you are lying nasan fushi kakeyi…kana jin haushi sbd na bari Hafsa ta tafi dasu koh?.”kasa yayi da kanshi baice komai ba…Mummy tace”Bobby you won’t understand..bansan ya zanyi maka bayani ba..kawai dai banaso ka nesantasu da yan uwan mahaifinsu kaman yanda ka nesanta mu da gaba daya yan uwan mahaifinku..ni kadai nasan how am feeling duk na tuna cewa grandfather dinku na nan da rai amma baisan inda kukeba tsawon shekara biyar…inaji a jikina bamu kyauta ba sam kuma nasan Allah bazai yafe mana…”bata karasa ba ya rufe bakinta tareda matsowa sosai ya rike hannayenta…idan ya bari tacigaba da magan nn tsaf zata kashe mishi jiki tasa ya farajin kaman shima bai kyauta din ba…ga kuma jininta da zai iya hawa idan bata bar wnn damuwan ba…yana kallon cikin idonta yace”Mummy ba laifi bane…ba laifinmu bane…laifinsu ne da basu ta6a yunkurin nemanmu ba…su kuma su Ilham nasan ke da kanki kinsan meyasa banso suje inda mutanen nan sbd ba sonsu sukeyi ba”…hawaye suka shiga sauka fuskanta tace”duk abunda in the past bai kamata mu bari yayi affecting future dinmu ba…we are all Humans Bobby and we all make mistakes…nasan abunda da sukayi is uncalled for amma ya zamuyi?..dole haka zamuyi hakuri dasu tunda sunyi nadama…zumunchi ba karamin abu bane Bobby banaso Allah ya kamamu da laifin yanke zumunta a ranar gobe kiyama”…tana karasawa wasu tawagar hawaye suka sake biyo fuskanta Bobby baisan sanda ya matsa tareda rungumota jikinshi ba…kuka takeyi sosai da alama dama ta jima tana neman inda zatayi kukan…bai hanata ba saida ta dakata dan kanta snn yace”Mummy to kukan ya isa haka plss and we shouldn’t talk about them again..am not angry anymore”…ta saki dan murmushi tana share hawayenta tace”then tashi muje kaci abinci”…baiyi musu ya mike ya koma kan sofa ya zauna snn ya janyo table data ajiye abincin akai ya fara cin kayanshi…itama mikewan tayi ta dawo kusa dashi ta zauna snn tace”and mgnr zuwa duba Waziri”…a takaice yace”yana nan Mummy..idan ya dawo zamuje gaba daya mu dubashi..are you happy now?..”sake gyada mishi kai tayi tana murmushi…shi kuma yacigaba da cin abincinshi amma deep down yasan abunda ya fada karya yake…ko kusa baijin zuciyarshi zai iya mance tarin munanan abubuwanda Waziri da iyalanshi suka aikata musu har yaje inda suke..sam hakan ba mai yiwuwa bane ya fada mata ne kawai dan ta dena damuwa amma baida intension din zuwa ko ina..shi a yanda yakeji mafa ko rasuwa waziri yayi saidai suje za’aziyya kawai su dawo amma ba wani zaman makoki da zasuyi tunda bai ta6a daukansu a matsayin Family ba.