Dr. BOBBY COMPLETE HAUSA NOVEL

Dr. BOBBY COMPLETE HAUSA NOVEL

Rano✨

Wnn littafin na kudi ne ban yadda wani ko wata ya fitarmin dashi ba…masu buqatan siya zasu tura 300 zuwa 2208991344 Aisha Ahmad Tijjani Zenith Bank…sai a tura evidence of payment via 07063800556.
15
Yau Sunday tun around ten Hamma ya tafi maidasu bisa umarnin daddy ya maidasu da wuri shima ya samu ya dawo gida da wuri kafin dare…karfe daya a cikin Hostel yayi musu…Hamma bai tafi ba saida ya tabbatar ba abunda suke bukata snn ya musu sallama ya wuce su kuma suka shiga area classes don duba Posting dinsu…gida biyu akayi dividing class dinsu first 19 aka turasu Freedom sauran 19 din kuma aka turasu Kinana…gaba daya ran Aysha taji ya 6aci itadai Allah ya sani ba son Freedom din nan takeyi ba…tasan ko baa fada ba Dr.Bobby mugun takurawa mutane zaiyi sbd yana ganin Hospital dinshi ne…ita kuma harga Allah yanxu batason abunda zai sake shiga tsakaninta dashi yazo yana mata rashin mutunci tunda ta fuskanci dabi’arshi ne…kallon Billy tayi tace”Billy zo muje muyi mgn da provost ko zaisa baki a canxa mana posting din nan…na tsani zuwa Freedom wlh”…Billy tace”but why?..asibitin yanada kyau fa Lamido..besides ko kinje wajen provost ma i don’t think zasu canxa maki cox ba’a ta6ayima mutum posting kuma daga baya a sake mishi ba..kawai ki hakura dashi nasan muna fara zuwa zakiji kina enjoying”…girgiza kai ta shigayi bayan Billy ta gama mgn tace”nidai dan Allah ko rakani ne kiyi plss…Allah bazan iya zuwa Hospital din nan ba haka nan da kayi small mistake Proprietor yace zaiyi maka rashin mutunchi”…daga kafada Billy tana cewa”Fine tunda bakiji shawara na ba…nima kuma babu inda zan rakaki sai kije ki dawo ina jiranki a nan”…hararanta tayi ganin itama zata mata wulakanci kawai ta juya ta tafi ita kadai…kafin ta shiga office din secretary dinshi tace baya nan amma yace idan anzo nemanshi ta kira ta sanar dashi dan haka tayi dialing number dinshi yana dagawa tace”Sir Lamido tazo nemanka”…daga other side din yace”kice ta sameni office din Dr.Bobby”..tana kashe wayan tace mata”yace kije office din Dr.Bobby yana can”…Aysha ta wani zaro ido jin ta ambaci Dr.Bobby tace”tsaya..waye Dr.Bobby?..”dan murmushi Secretary din tayi kafin tace”Proprietor mana”…wani irin diff tayi kaman wuta ya dauke mata…tabbas da tasan inda yake knn da bata bari an kirashi bama in the first place bare har yace taje can ta sameshi…itafa ta tsani abunda zai hadata da inyamurin nan ko kadan..sam batason hada sabga dashi sbd ta lura ba karamin mara mutunchi bane…gashi kuma Secretary ta ambaci sunanta da wlh bazata jeba sai tayi wucewarta ta dawo daga baya amma yanxun tunda yaji sunanta tasan zuwa ya zama mata dole ko don posting da takeso a sake mata tunda gobe zasuyi reporting…ganin tana 6ata lokaci a banza ta juya ta fita daga wurin tayi hanyar office dinshi tana sake sake cikin ranta sai kuma taji haushin kanta for tsoron wnn inyamurin…kawai ma gara taje inyaso ta dake ta fadi abunda ya kawota tasan duk tsiya dai bai isa yasa hannu a jikinta ba…da wnn sabon courage ta isa zuwa office din…bayan an bata permission din shigowa ta tura kofar a hankali ta shiga kai a kasa…yana zaune kan kujera yayinda Dr.Bobby shima ke zaune kan office chair dinshi…ta karasa ciki ta tsaya snn tacema Nur”good afternoon sir”…yace”Afternoon Lamido ya holidays” …ta dan kakalo murmushi tace”Alhamdulillah”..yace”to bismillah zauna inji meke tafe dake?..”tace”thank u ba saina zauna ba Sir…akan mgnr posting ne dama”…yace”Posting?..meya faru?..”saida ta hadiyi saliva trying very hard not to look at Bobby da zata iya rantsewa taji wann shegun eyes din nashi a kanta tace”Sir…banason inda akayi posting dina shine nace in maka mgn ko zakasa a canxa min?..”Nur dake kallonta yace”No problem ina akayi posting dinki?..”ta sake hadiye wani yawun snn tayi qundunbala tace”Freedom”…da mamaki sosai Nur yake kallonta yace”amma why bakison Freedom din?..naga students da yawa har so sukeyi ayi posting dinsu can”…kai tsaye tace”Sir kawai nidai banaso”…saida ya danyi shiru na wani lokaci kafin yace”shknn kije zanyi mgn da Isaac sai muga yanda za’ayi”..nan da nan ta saki smile tana fadin”thank u so much Sir..nagode”..wani mamakin ya sake kamashi ganin how happy she is kawai sbd xaa canxa mata posting…lallai bata son Freedom din kuwa kaman yanda ta fada…Dr.Bobby yayi shiru yana kallonsu saida suka gama yace”ba wanda za’a canxama posting”…a tare Nur da ita suka juya suna kallonshi…ganin kallon da suke mishi ya sake tamke fuska yana cewa”don me za’a canxa mata posting bayan ba haka akeyi ba…who did she think she is?..”Nur yace”amma…”bai bari ya karasa ba ya katseshi da fadin”if she can’t stay..she leaves”…mamaki sosai ya kama Nur kawai yayi sakato yana kallonshi…ita kuwa Aysha right now ji take kaman ta kwada masa mari…dan rainin hankali har ita zai wani ce she leaves?..wlh da daddynta zai amince da daga office din nan ko Hostel bazata koma ba zatayi gida saidai Bilkisu ta taho mata da kayanta amma she won’t sbd tafi kowa sanin halin mahaifinta…rai a matukar 6ace ta juya zata fita yace”dawo..”tsayawa tayi cak da tafiyar ita bata juyo ba kuma bata cigaba da tafiya ba…shi kuma ganin ta wani yi tsaye ta juya musu baya saiya tuna ranar da sukaje Hostel dinsu ma haka tayi musu…a kausashe yace”i said come back here…are you deaf?..”juyawa tayi ta koma gaban table din fuska a tamke…Dr.Nur dai relaxing yayi yana kallon wnn rigima nasu…ya shiga binta da wnn kallon da bata kauna snn ya nuna hannunta da fingers dinshi yace”remove those things”…a rikice ta dago tana kallonshi sai kuma ta dauke kan da sauri jin wnn abun da batasonji duk ya kalleta..hannun nata ta kalla zobuna ne na gold guda biyu ajiki kwata kwata mantawa tayi bata ciresu kafin ga bar gida ba…ta dan rage murya tace”Sir…”kasa karasawa tayi sbd wnn idanun dai daya zuba mata…bata sake yunkurin mgn ba takai hannu ta zarosu daga fingers dinta snn ta ajiye kan table din ta juya a fusace ta fita daga office din..shi kuma ya daukosu daga inda ta ajiye ya bude wani drawer dake kusa dashi ya watsasu ciki ya rufe…duk abunda yake idanun Nur na kafe a kanshi yana kallon latest behavior dinshi…mamakin ta yanda har ya lura da akwai zobe hannunta yake dan koshi da suke mgn da ita bai lura akwaisu a hannunta ba saida ya fada…wani murmushi ya saki yana shafa beard dinshi yace”Dr.Bobby tell me plss..do u love this girl?..”wani kallo Bobby ya bishi dashi kafin yace”what the hell…are you insane?..”Nur ya daga shoulders dinshi yace”no am not..kawai dai inaso in san ta yanda akayi ka lura da akwai rings a hannunta bayan koni da nake mgn da ita ban lurada hakan ba”…tsabar haushi kasa mgn yayi sai ido kawai daya zuba mishi yana mishi kallon da shi kanshi yasan zaiji ajikinshi…ilai kuwa Nur din ya dan yatsine fuska yace”C’mon stopping looking at me that way plss?..sbd kasan tasirin idanunka shiyasa kakeso kayita tsatstsare mutane dasu don kasa sunajin somehow..nidai stop looking at me plss tunda mgnr ne bakaso an barshi”…murmushin cin nasara ya saki tareda komawa yayi relaxing kan kujeranshi…Nur yace”dole kayi smiling mana tunda ka cuceni”…baice mishi komai ba sai shoulder dinshi daya daga.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128Next page

Leave a Reply

Back to top button