Dr. BOBBY COMPLETE HAUSA NOVEL

Washegari Monday kowa zaije yayi reporting a Hospital da aka kaishi…kaman kullum karfe 8 school bus dinsu ya kwashesu zuwa Freedom Specialist Hospital…daidai lokacinda suka isa Hospital din shima Dr.Bobby yazo..bayan bus dinsu yayi parking duk suka fito shi kuma bai fitoba sbd waya da aka kirashi…daga nan inda yake ya hangota suna mgn da Billy baidai san me suke cewa ba yaga sun nufi wurin wata mota…suna fitowa Aysha da tun shigowarsu taga motar babynta a parking space tace ma Billy”wlh Billy shine ba gizo yakemin ba..dama yace yau ko office bazai iya zuwa idan baizo ya ganni ba”…Billy da zuwa yanxun ta dan fara sakewa dashi tace”ikon Allah..kinga har ya rigamu zuwa”..Aysha daketa blushing tace”ai Allah kadai yasan tun yaushe yake a nan…zo muje kar ya gaji da jira”..ba musu Billy ta bita zuwa inda yake…tun kafin su karaso ya bude mota ya fito idanunshi kan Aysha yanajin kaman ya rungumeta ga jikinshi tsabar kewarta da yayi…suna karasowa Billy ta gaisheshi ya amsa da tambayan ya baby girl dinshi tace”wnn baby girl din taka fa sai kai…bazan iya da fitinanta ba”…yayi daria yace”anya kuwa zan yadda dake Billy?..”itama tayi dariyan tace”ai dama bazaka yadda ba na sani…nidai bari na shiga ciki sai anjima”..yace”to shknn Bilkisu ina godia sosai”..bata sake cewa komai ba ta bar wurin..shi kuma ya bude front seat yana kallonta yanajin kaman ya maidasmta cikinshi…ba musu ta shiga ya rufe kofa snn ya zagaya shima ya shiga…kallon juna kawai sukeyi kowa yanajin soyayyan dan uwanshi na karuwa cikin zuciyarshi…a dan zamansu dashi Aysha ta fuskanci zurfin da yayi a karatun boko baisa ya zubar da addininshi ba…yanada addini sosai dan tunda suke bai ta6a yi mata anything dirty ba..ko dirty talk bai ta6ayi mata haka kuma bai ta6a kama koda hannunta ba…wnn dalilin yasa sonshi ke karuwa cikin ranta..tasan matukar ta aureshi tayi dace da salihi kuma muminin namiji…shi kam ganin time na tafiya and baiso ta makara ya dan saki smile yana cewa”i missed you”..ita kuma shagwa6e fuska tayi kaman wata baby tace”i missed you more baby”..yayi murmushi tareda dauke kanshi dab yanda tayi da face dinta yasa yaji kaman yayi hugging dinta…yanason yarinyar nan to the moon…hira suka dan ta6a kadan snn yace mata zai wuce amma su shirya itada Billy da yamma zaizo ya kaisu shopping…ta wani lankwasa murya tace”baby u shouldn’t bother munada komai wlh”…hade rai yayi yace”banason musu baby..idan kuma ban isa ku amsa abun hannuna bane fine”…da sauri tace”to kayi hakuri na dena…zan fada mata inshaAllah”…yace”yauwamy little baby girl…yanxun ki shiga ciki kar suga kin dade baki shigo ba”..ba musu ta bude mota ta fita ta sunkuyo ta window suka sake yin sallama snn ya tada motar ya tafi ita kuma ta shige ciki…duk wnn abun da suke kan idanun Bobby daya gama wayan da yake tun daxu amma ya kasa fitowa daga motar…tunda yaga ya bude mata mota ta shiga da kuma yanda yake hango murmushinda take daga nan inda yake yasan confirm wnn boyfriend dinta ne…haka nan yaji wani irin haushinta ya kamashi cikin ranshi yace”she isn’t only a spoiled brat she’s also a flirt”…har saida yaga ta fito daga motan snn shima ya bude nashi ya fito…driver dinshi da tunda sukazo ya fito waje ya mika mashi briefcase dinshi ya amsa snn yasa kai cikin building din.
Tana zuwa ta samu colleagues dinta office din Chief Nursing Officer inda daga nan akayi posting dinsu various wards…Billy tana Antenal Clinic Aysha kuma tana cikin Labour Room…ranta duk ya 6aci an rabata da qawarta snn kuma an kaita maternity da bata kauna…sam batason aikin labour room sbd azabar wahala…aikine sosai suke yinshi kmr ba gobe shiyasa duk dunia ba ward da take son aiki kaman ANC ko Family Planning Unit…su aikinsu nada sauki and ba’a shifting amma yanxu tasa a labour room da kyar idan ba’a sata shifting ba…tanata 6ace 6acen rai suka fita daga office din..Billy ta wuce ANC tareda sauran da akayi posting dinsu tare itama Aysha suka wuce Maternity.
Karfe goma daidai Dr.Bobby ya shiga Maternity don yin ward round…wata Midwife dake zaune Nurses Station tana cike Register tazo da sauri ta gaisheshi snn ta koma ta fara harhada files din patents…ta dorasu gaba daya kan trolley snn ta turama Aysha data fito daga labour room yanxu tace”Aysha dan je kuyi ward round da Dr in samu in karasa cike Register nan”…ba yanda ta iya haka ta tura trolley din tayi gaba…yana tsaye kusada bed din wata patient da sukayima cs last two days yana mata tambayoyi Aysha ta karaso wurin…ta daure fuskanta sosai tana sunkuyar da kai kasa dan ko Allah yasan batason hada idanu dashi…tunda tazo wurin yaji zuwan nata amma yanda yayi zaka rantse babu wata hallitta a kusa dashi…hankalinshi gaba daya yana kan patient da yakema tambaya ko kallon bayanshi da yasan tana tsaye baiyi ba…tana fada mishi sunanta Aysha ta shiga nemo file dinta cikin tulin files dake kan trolley kawai sai ya kai hannu ya janyo trolleyn zuwa gabanshi ya dauki file din nata snn yacigaba da aikinshi…wani sabon takaici taji ya lullu6eta…meyasa mutumin nan keyi mata haka ne wai?..meyasa bashida kirki ko kadan?..ganin ya tura trolleyn da kanshi zuwa next bed itama ta ta6e baki cikin ranta tace”ka wutar dani nima”..ta juya ta koma ciki…midwife din da taga ta dawo tace”ya kika dawo kuma?..”kai tsaye tace”shi yace in dawo”…mikewa tayi daga inda take zaune ta fita zuwa inda yake..ita kuma Aysha ta zauna inda ta tashi tacigaba da cike nata register…bayan ya gama ward round har zai fita tace mishi akwai wadda ya kamata ya duba cikin labour room dan haka ya juya zuwa labour room din…Aysha na zaune tana aikin gabanta ko kallon inda suke batayi ba…sun shiga ciki suka samu matar dake ciki tanata fama har kan baby ya fara fitowa sukayi kanta da sauri…ganin harta jigata ranshi ya 6aci sosai…ita waccan zaman uban me takeyi da har patient ra kusa haihuwa bata sani ba…midwife da suke tare tana kokarin taimakawa matar ya dakatar da ita…tace”Sir babyn zaisha ruw…”bata karasa ba yace”call that useless da take zaune ta kyaleta ita kadai”…da sauri ta fita ta kira Aysha…yana ganinta ya sake dinke fuska yace”are u mad?..bakida hankali zaki wuce ki bar patient ita kadai cikin wnn situation din?..are u sick or something?..”dan turo baki tayi tace”ai ni bansan ta kusa haihuwa ba…kuma Register nake cikewa”…sbd tsabar takaici kasa ce mata komai yayi…yana nuna patient din yace”go and attend to her and make sure u did not make any mistake cox you’ll regret knowing me”…cikin zuciyarta tace”ai ko a yanxu i regret knowing u wlh…me za’ayi da sanin masifaffen mutum irinka”..karasawa tayi inda matar ta shiga taimaka mata…yana tsaye rungume da hannu yana kallonta kaman bai ta6a ganin yanda ake kar6an haihuwa ba…so yake yaga tayi mistake komai kankantarshi yaci mata mutunchi amma baiga tayi mistake din komai ba…wato dai ba brain kadai takeda ba har skills tana dashi…sam baiji ta wani burgeshi ba duk abunda take…ta kar6i haihuwan successfully ta gama ta kuma yi duk wani necessary abu daya kamata tayima matar da babyn sai a lokacin ya juya ya fita..ita kuma ta bishi da harara kaman idonta zasu fado tace”duk wani baqin hali dai a gun inyamurai ya kare…har abada basu son a zauna lafia”.