Dr. BOBBY COMPLETE HAUSA NOVEL

Dr. BOBBY COMPLETE HAUSA NOVEL

Around 5:30 suka gama shiri suka fito dan zuwa shopping da Prof kaman yanda suka tsara…bakin gate dinsu sukayi ido hudu da Sa’eed dake jingind jikin motanshi yana kokarin kiran one of them a waya…Aysha ta wara idanu tana kallonshi smilingly tace”my bestyyy”…dagowa yayi yana kallonta sai kuma ya daure fuska yana hararanta…ta karasa kusa dashi da sauri tana cewa”haba my besty…hope ba fushi kakeyi dani ba”…hararan nata ya sakeyi kafin yace”ba wani your besty…ni da aka manta dani”…da sauri tace”oh C’mon besty kaima dai kasan ba wanda ya isa ya mantaka..jiya fa na kira wayanka ban samu ba Allah”..kafada ya daga yace”baki damu ki ganni ba ai..ni da na damu ai gashi nazo har inda kuke”…kaman zatasa kuka tace”besty wai meye haka plss?..kanaso Billy tayi mana daria koh?..”juyawa yayi ya kalli Billy dake tsaye tana kallonsu ya wani kwa6e fuska irin yanda bestyn tashi keyi idan abubuwan suka motsa yace”Billy hadda ke ma koh?..kikaje kika biyewa besty kuka manta dani..is that fair?..”murmushin da bata shiryaba ta saki ganin yanda yayi da face dinshi…ta buda hannaye tace”ni babu ruwana da tsakaninku…kawai inzo in shiga anjima ku bani kunya”…murmushi shima ya saki yana kallonsu with smile yace”nayi missing dinku da gaske…sai nakeji kaman nayi tsuntsu naje Bauchi da Gombe”…murmushin suma suka kara saki Aysha tace”da gaske munyi missing dinka muma…yasu Mom da Lubna”..yace”they are all fine..amma ina zakuje ne haka?..”Aysha ta saki wani qayataccen murmushi kafin tace”wlh Baby ne yazo wai zai kaimu shopping.. muje kayi dropping namu bakin gate nasan yana can yana jiranmu”…kallonta Sa’eed yayi cikeda mamaki kafin ya juya yana kallon Billy yana neman karin bayani..ta daga kafada tana dan smiling dan ta gane me yake nufi tace”ai soyayya ya dade dayin nisa…bakaji har baby ma ake cemishi ba?..”Yace”shine nima nake mamaki ai..but when did this happened banida labari?..”tace”gaka ga bestynka ai”…juyawa yayi ya kalleta kafin yayi mgn tace”besty mu shiga mota idan mun tafi zanyi maka bayani”…baiyi mata musu ba ya bude motar suka shiga..yana gama warming dinta yayi reverse suka dauki hanyan fita hostel din…basuyi nisa ba yace mata”umhum ina sauraronki”…a nuste ta bashi labarin duk yanda sukayi dashi…saida ta gama yace”amma kina ganin ba matsala besty?..i mean kin tabbata mutumin kirki ne shi?..”da sauri tace”sosai mutumim kirki ne wlh besty…ask Billy ta fada maka tunda muke dashi bai ta6a min wani abu da bai kamata ba..he really is a gentle man”..gyada kai Sa’eed yayi yace”to Allah yasa..but still ya kamata muyi bincike a kanshi..i don’t want you dating a wrong guy kar azo a samu matsala”..murmushin jin dadi ta saki kafin tace”i trust you completely my besty…kayi duk binciken da kaga ya kamata”…dan juyawa yayi ya kalleta sai ya saki murmushi yace”za’ayi min dadin baki a cuceni”…tana daria tace”ba wani dadin fa..it’s the truth”..sake gyada kai yayi baice komai ba…Billy dama tana back seat tana chatting dinta so ko sauraronsu batayi…suna fitowa main gate suka hango motarshi parke daga gefe..saida ya karasa har kusada motan nashi snn yayi parking…suka bude mota suka fita shima ya fito daga cikin nashi motan…Sa’eed ya karasa ya bashi hannu suka gaisa kafin yace”Hope dai za’a bani aronsu for just an hour?..”yana murmushi yace”of course..Allah ya kiyaye hanya”..Prof ya amsa da”Ameen”snn sukayi sallama Sa’eed ya shiga motanshi ya wuce suma suka shiga na Prof suka wuce.

Rano✨

Wnn littafin na kudi ne…masu buqatan siya zasu tura 300 zuwa 2208991344 Aisha Ahmad Tijjani Zenith Bank…sai a tura evidence of payment via 07063800556.
16
Shopping sosai Prof ya shiga yi musu Aysha tun tana cewa ya kyaleshi haka har ta hakura kawai ta zuba mishi ido…ta lura ba karamin money spender bane shi..baijin kashe kudi sam..yanda yake musu siyayya ko shekara guda zasuyi a school sai haka…Billy dama batayi mgn ba kallonshi kawai take…saida ya dauki duk wani abu da students kamar su suke bukata snn ya wuce counter…bayan yayi payment akai musu packaging wani messenger ya dauki kayan yabisu dashi mota…ya zubasu nan cikin booth suma suka shiga suka wuce…a hankali Aysha ta juya tana kallonshi tace”Babyy..”ya dora hannu kan lips dinshi yace”shushsh ba sai kince komai ba pls”…shirun tayi bata sake mgn ba kaman yanda ya bukata…saida ya tsaya Pizza Hut yayi musu takeaway snn suka wuce Hostel…a bakin gate dinsu yayi parking Billy ta bude mota ta fita bayan ta mishi godia…Aysha kuma sake juyawa tayi tana kallonshi da cutest eyes dinta cikin shagwa6an da yake mutuwar so tace”Baby u shouldn’t have done this…i told u munada komai da komai fa”…kallonta yayi for like 5 mins kafin ya dauke kanshi yana sakin murmushi…this girl is damn cute..bai ta6a ganin wanda shagwa6a yakema kyau kaman ita ba..she is just different..sake turo baki tayi hadda bubbuga legs dinta a kasa tace”Baby manaa”…daria ya saki sosai har jikinshi na dan jijjigawa yana daga hannu yace”ohk am sorry…amma ke din ce bakiji baby girl…idan har am important to u zakiyi accepting kayan nan and azaki sake kokarin hanani siyan maki wani abu ba”…turo baki tayi tana kallonshi kaman zatasa kuka…kallonta kawai yake yanajin kamar yakai hannu yaja dan bakin da take turo mishi…tace”shikenan nima daga yanxu duk abunda na gani na siyan maka sai kayi accepting ka yadda?..”gyada kanshi yayi yace”na yadda”..nan da nan ta saki murmushi har dimples dinta suka lotsa…sun dan ta6a hira kadan kafin yayi mata sallama ya wuce ita kuma ta kwashi kayan da suka siyo ta shiga ciki…bata samu Billy a dakinsu ba dan haka tana ajiye kayan ta fita zuwa room 2b da ta jiyo hayaniyarsu a can…tana shiga wata daga cikinsu mai suna Rahma tace”yauwa ga Lamidon nan ma tazo”…karasawa tayi ciki ta zauna tana kallonsu tace”meya faru ake neman Lamido?..”Rahma ta sakw cewa”mgnr bikin Aneesa ne wlh…kinsan munyi mata alqawarin zamuyi selecting music mai dankaren dadi muyi training sbd muyi performing ranar dinner dinta?..”gyada kai Aysha ta shigayi tace”inaga shine dalilin da yasa take nemana…ko daxu naga missed calls dinta ina tareda Baby”…Rahma tace”yauwa to shine mukeso ki za6o mana latest music mai dadi snn ki koya mana rawan da zamuyi tunda dai kaf Hostel din nan ba wanda ta iya wani rawan kirki idan bake ba”…dan murmushi Aysha ta saki kafin tace”to ku da kuketa wnn lissafin Aneesan tace muku ‘yan class dinsu baza suyi bane?..kunsan fa ‘yan Nursing din nan da shegen iyayi”…wnn karon Billy ce tace”yo Lamido kamar bakisan ‘yan class din nasu bane?..babu abinda zasu iya wlh shiyasa itama Aneesan ta nememu kuma bai kamata mu watsa mata qasa a ido ba…dukda ba department dinmu daya ba year dinmu daya and tanada kyakyawan relationship damu sbd haka ba wanda ya kamata ya fitar da ita kunya idan ba mu din ba..koya kukace Midwives?..”da sauri suka hada baki suna fadin”Zancenki dutse hajia Bilisu”..sauke ajiyar zuciya Aysha tayi tace”shikenan sai mu fara this weekend…amma wane time kuke ganin zamuyi selecting evening ko night”…Rahma tace”kam night ai sai yafi sugar Lamido..yanda zamusha sha’aninmu babu wani takura”…gaba daya sukayi na’am da wnn shawara dan haka suka tsaida mgn kan zasu ringa dance training dinsu every Saturday and sunday around karfe 8 na dare.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128Next page

Leave a Reply

Back to top button