Dr. BOBBY COMPLETE HAUSA NOVEL

Dr. BOBBY COMPLETE HAUSA NOVEL

Tun daga wnn rana suka fara training dinsu kaman yanda suka tsara…every weekend suke taruwa suyi abunsu ba wanda ya sani…a haka suka cinye satin farko na clinical posting dinsu suka cinye na biyu…a cikin sati na uku ne za’ayi bikin and sun gama training dinsu tsaf daidai da anko duk cikinsu ba wadda batayi ba…duk tsawon wnn lokacin Aysha bata sake haduwa da Dr.Bobby ba a Hospital kuma yana shiga ward dinsu Allah ne kawai baisa sun sake haduwa ba shiyasa take cewa Allah ya amsa addu’anta dan koshi yasan yanda ta tsani ganinshi shiyasa suke samun sa6ani dashi.

Yau Saturday za’ayi dinner Aneesa gashi evening duty take kuma ta rasa wadda zata kar6an mata aikin zuwa gobe…jiyama Allah ne ya taimaketa wata daga cikin staff din dakin ta kar6i evening din tayi mata ita kuma tayi mata morning sbd event din jiya kamu ne so tana tashi daga Hospital din ta koma Hostel suka shirya suka tafi…event din yau kuma na dare ne gashi bata san wanda zai rike mata aikin ba…tun daxun take zaune gefen gadonta tana daure da towel sai tufka da warwara takeyi…tsoro takeji kar ta tafi biki wani matsala ya faru ayi blaming dinta…sai wata zuciyar tace mata tayi tafiyarta kawai ai bai zama lallai ita kadai take evening ba so dayar zata rike dakin…da wnn shawara na zuciyarta ta yanke hukuncin zuwa bikinta kawai dan Allah ya gani bazata iya hakura da zuwa dinner nan ba…yanda sukayi training idan bataje ta baje kolin rawan nan ba matsala za’a samu ta sani…Billy data fito daga wanka ta kalleta ganin tayi nisa cikin tunani tace”to ya muke ciki ne Lamido?..kin samu mai rike miki aikin?..”sauke ajiyar zuciya tayi a hankali tace”ashe bani kadai zanyi evening din bama..da akwai wata staff kuma nasan bazaki zuwa ba”…Billy da har ta fara shiryawa tace”har naji dadi wlh dan Allah ya sani idan bakije bikin nan ba bazamu ji dadinshi ba muma…yanxu ki karasa shiryawa kisa kayanki nasan wnn dan rainin wayon bestyn naki ya kusa zuwa…kuma dai kinsan make up da zuwa da wuri mukayi ba bazamu samu mai kyau ba”…wani murmushi Aysha ta saki tareda mikewa zuwa wardrobe dinta tace”tsakanin keda bestyn za’aga waye dan rainin wayo a cikinku…ke kice mishi dan rainin wayo shima ya kiraki da haka..duk zaku gaji da munafurcinku ne ma ku dawo kan hanya”…cak Billy ta tsaya da kokarin saka skirt da takeyi tace”what are u insinuating?..”Aysha ta fashe da daria itama ta fara zura kayanta tace”nothing ooo…am just talking to myself “…tsaki kawai Billy ta saki taci gaba da shiryawanta…ko ten minutes basu kara ba suka gama shiryawa kowa ta dauki abinda take bukata suka fita inda Sa’eed ke jiransu…yana daukansu direct sukayi Zoo road inda za’ayi musu make up.

Mummy ce ta Aunty sumy suka fito compound din gidansu kowacce sanye cikin lace dinta na alfarma sunyi kyau sosai da gani kasan gidan biki zasuje…sai Ilham da Miemie dake sanye cikin nasu lace din suma iri daya da yayi matukar amsarsu Sab kuma ya dade da komawa makaranta…aunty sumy har ta bude motarta da zasuje bikin da ita Mummy tace” sake kira min Bobby Sumayya…wlh idan baije bikin nan ba sai naci mutunchinshi”…aunty sumy murmushi tayi kafin ta sake dialing number Bobby ta mika mata wayan…saida ya kusan katsewa yayi picking Mummy ko jira yayi mgn batayi ba cikin igbo tace”wato ka rantse dai bazaje bikin nan ba ko Bobby?..haka daxu kiri kiri kaki zuwa daurin aure shine yanxu dinner ma kace bakazo ba?..”saida ta bari ta kai aya snn yayi kasa da murya yace”Mummy ina Hospital fa..wlh aiyuka ne a gaba na idan baki yadda ba ga Nur ki tambayeshi”…a takaice tace”bawa Nur din waya”…ba musu ya mika mishi wayan…shima yana amsa before yayi mgn Mummy tace”kana jina Nuru?..”yace”inaji Mummy”…tace”tell him duk ya sake muka bar wurin dinner nan baije sai yaga 6acin raina wlh…kan wane dalili zaiki zuwa bayan yasan yanda nake da uwar yaron nan…snn shima abokinshi ne amma sbd iskanci ya mishi yawa ya wani cemin yana aiki a gabanshi”…Nur yayi kasa da murya sosai yace”kiyi hakuri Mummy zamuzo tare inshaAllah…Allah ya huci zuciyarki”…bata sake cewa komai ba ta kashe wayar…suka shiga motar aunty sumy gaba dayansu suka fita daga gidan…shi kuwa Bobby dafe goshinshi yayi yana dan murzawa a hankali…duk yaji maganganun da Mummy ta fada and baiji dadin musun da yayi mata ba sam…ya mance when last Mummy tayi mishi mgn cikin fushi haka…kuma shi kanshi yasan bai kyauta ba…angon abokinshi ne sosai dan lokacin suna lagos shine babban abokinshi…Mom dinshi kuma aminiyar Mummy ce itama tun a Lagos suke zumunchi har zuwa yanxu basu dena ba shiyasa ma take kokarin hadashi aure da qanwar angon Rayhan shi kuma baya sonta sam…kafin Nur yayi mgn ya dauki car keys dinshi tareda mikewa yace”muje ka rakani wajen bikin nan plss..nasan yau idan banje ba mai rabani da Mummy sai Allah”…Nur daria ya dan saki shima ya mike tsaye suka fita daga office din snn yace”nima dai banga dalilinka na kin zuwa ba…angon nan fa abokinka ne kuma yayan matar da zaka aur…”Bobby bai tsaya jin karshe ba ya kara gudun tafiyarshi ya barshi a baya dan bayason ji sam…baisan meyasa ya tsani a hadashi da wnn Rayhan din ba wlh…he hates her with passion…saida suka tsaya nan gidansu Bobby sukayi wanka kowa ya sake shiri snn suka tafi wurin dinner a motan Nur…lokacin har anyi sallahn isha dan haka sukavfara tsayawa masallaci auka gabatar da nasu snn suka wuce…suna isa hall din amarya da ango na isowa…basu bi takan brides maida da sukaga anata faman jerasu ba wai da sunan zasu shiga da amarya kai tsaye suka shiga hall din…duk iya wulla idonsu basu hangi Mummy ko su antu sumy ba coz hall din nada girma sosai dan haka kawai suka karasa wani table suka zauna Bobby sai faman cika yake yana batsewa dan ko Allah yasan shi ba maison zuwa biki bane…sam bayason hayaniya shiyasa duk wani abu indai ya hada da taron jama’a shiga bai sonshi sbd tsabar rashin son mutane irin nashi…a can waje kuwa saida su Aysha suka shirya kansu tsaf snn mc yace ma dj ya sakar musu waqan shigowa da amarya…dj kuwa yasa waqan da sukace sunaso snn suka fara shigowa a hankali suna dan bin waqan hade da rawan da yayi matching song din sosai…Aysha ce a sahun farko sai Rahma a gefen ta su Billy kuma suna bayansu wasu kuma suna bayan amarya da ango ma’ana sun sanya su a tsakiya knn…tunda suka shigo hall din gaba daya kallo ya koma kansu gaba daya lace sukayi anko sea green har head dinsu ma sea green sai dinki kawai daya bambamta…su Aysha ansha make up sosai dam idan ka kalleta zaiyi wuya ka ganeta sbd tsabar kyau da tayi…Nur ne ya fara ganeta aikuwa ya wara ido sosai yana kallonta sai yaga almost gaba dayansu ma students dinsu ne…to me ya kawosu nan kuma?..bai samu amsar tambayan shi ba saida ya ga amaryar itama yaga student dinsu nan take ya saki murmushi yana fadin”No wonder…Bobby kasan yaran can gaba daya students dinmu ne…amaryar ma ai Nursing takeyi na ganeta a year two take”…Bobby da gaba daya hankalinshi ke kan wayanshi dan dagowa yayi a hankali yana kallonsu and idanunshi basu fada ko ina ba sai kan Lamido dake tikan rawanta hankali kwance tana smiling da gani tana enjoying abunta…wani irin haushi yaji ya turnukeshi…baisan meyasa these days yake yawan haduwa da ita ba…ya tsani ganinta wlh sbd duk ya sauke idonshi akanta yana sashi tunowa da abubuwanda ya faru dasu a baya…abun takaicin kuma duk yanda yaso dauke idonshi kansu kasawa yayi har suka raka bride and groom suka zaune snn sukayi dividing kansu into two wasu suka tsaya side din amarya wasu side din ango suna cigaba da rawansu…gaba daya hankalin kowa na hall din na wurinsu dan ba karamin burgewa sukayi ba…daya bayan daya sukw fitowa kowacce ta taka mutane suka fara zuwa suna musu liki abun dai dai wanda ya gani…Dr.Bobby kuwa haushi ne cikeda zuciyarshi yana mamakin yanda iyayen yaran nan suka bari suka fito biki haka gansansan dasu ko mayafi babu…saida suka gama rawarsu snn suka zauna nan kuma mc ya fara kodasu yana yabon irin rawar da sukayi…har zuwa yanxu basu hangi su Mummy ba bayan amarya da ango sun fito fili aka kira Maman ango snn ya gansu sun fito suna ma bride da groom ruwan kudi har su Miemie da suke kanana…suna hada ido da Mummy tayi musu alaman suzo da hannunta…ba musu suka mike zuwa inda suke shidai Bobby fuskan nan a daure kaman wanda aka aikoma sakon mutuwa…suna zuwa Mummy ta zaro bundle na 500 daga jakanta ta mika musu wai suyi liki dashi…Bobby ya dan dauke kanshi tareda zaro wanda ya fito dasu daga aljihunshi ya shiga likama amarya da angon…shima Nur ya zaro nashi ya fara likin…bayan sun gama ango ya mika musu hannu suka gaisa tareda congratulating dinshi suka bar wurin amarya dai kanta na kasa tana mamakin a ina mijinta yasan provost da proprietor dinsu…su Aysha kuwa suna zaune inda aka tanadar musu dan haka ba wanda ya lura dasu a cikinsu…biki yayi biki yayinda wayanta dake cikin bag dinta keta vibrating alaman ana kira ita kuma da gayya daki dauka dan tasan Prof ke kira ita kuma fushi takeyi dashi…saida taga ba dena kira zaiyi ba ta koma can bayan hall din inda ba hayaniya sosai ta samu seat ta zauna snn ta zaro wayan daga bag dinta tareda sliding takai kunne…ta wani cuno baki taki cewa komai kaman yana ganinta…a hankali taji yace”baby girl fushi kikeyi koh?..”saida ta murguda masa baki snn tace”nidai na dena kulaka”…yace”subhanallahi baby idan kika dena kulani ya zanyi?..kinaso kiyi kisan kai koh?..”sake murguda bakin tayi tace”to ba kaine ba…cewa fa kayi bazakazo in ganka ba”…yace”wlh ni kaina ina son ganinki baby girl amma baa wurin biki ba…haka nan sai in kama biyoki wurin biki niba karamin yaro ba”…ta wani tale baki kaman zatasa kuka tace”haka ma kace kou?..to wlh idan bakazo yanxu ba baka kara ganina sai mub gama Clinical Posting”…da sauri ya wara idanu sosai yace”Subhanallah baby how could u do this plss?..ai abun bai kai nan ba gani nan tahowa yanxun amma bazan shigo ciki ba zan kiraki ki fito kinji?..”nan da nan ta saki kasaitaccen murmushi har dimples dinta suka lotsa tace”that’s my baby boo..ina nan ina jiranka plss and don’t keep me waiting”..yana murmurshin shima yace”wane ni?..am coming right away inshaAllah”…tace”ohk bye sai kazo”..shima yace mata”bye snn suka ajiye waya…ta mike daga wurin tana kokarin maida nata wayan cikin jaka idonta ya sauka a kanshi ya wani hakimce kan seat yana kallonta with his big eyes…gabanta taji ya fadi tayi saurin kawar da kanta tana salati…meya kawo wnn mutumin nan wurin kuma fisabilillahi?..sake dagowa tayi still taga idanunshi a kanta yana mata wnn kallon dake sata nutsuwa ko batayi niyya ba…sunkuyar da kanta tayi ta hadiye wani yawu da taji ya cika mata baki snn ta juya a hankali ta bar wurin fatanta Allah yasa baiji abunda take fada ba…ko wane irin asiri yakema idanunshi oho?..batasan ko kowa yanajin wani abu idan sun hada ido ba amma ita dai Allah ya gani tsoronshi ma takeji…ta tabbata ba karamin mara imani bane dan ko a fuska baiyi mata ruwan mutanen kwarai ba uwa uba kuma gashi inyamuri…duk dunia a ganinta babu azzalumin qabila kaman inyamurai shiyasa sam bata son tana hada harka dashi dan a cewarta da kyar idan baya daya daga cikin masu assasa yakin biafra.????
Shima a nashi bangaren kallonta kawai yake yana mamakin gangancin da yasa iyayenta suka turota karatu wani gari bayan sunsan halinta…duk mgnr da tayi a kunnenshi tayi su ya kuma tabbatar da cewa bayan sangarta dake damunta hadda rashin tarbiyya ma…idan ba haka ba why zata ringa behaving haka?..yanxu dubi yanda ta taho biki ko mayafi babu snn ta fito da gashi waje ga kayan jikinta sun matseta sbd tsabar rashin sanin darajar kai…ya saki wani hadadden tsaki shi baisan dalilinda yasa wasu matan ke neman maida kansu wawaye ba wlh..shi sam bazai iya auren mace mai irin halinta ba…macen da bata ajiye komai ba sai shegen shagwaba da rawar kai ai yanaga idan ya auri mai irin halinta kilan kullum sai yayi mata dan iskan duka sbd kular dashi da zatayi…tsakin da ya saki ne ya dawo da hankalin Nur daketa faman danna wayanshi kanshi…yace”hope lafia kake sakin wnn tsak haka?..”harara ya watsa mishi mai kyau ba tareda yayi mgn ba…kawai haushin kowa da komai ma yaji yanaji and he doesn’t know why…Nur da yaga kallon da yayi mishi sai yaci gaba da abunda yake cikin wayanshi yana fadin”easy dude ai bani na kar zomon ba and ko rataya ba wanda ya bani”..wani hararan Bobby ya sake maka mashi duk yaji zaman wurin ma ya gundureshi…mikewa yayi zuwa wurin da ya hango Mummy ya samu ya lalla6ata wai yanaso yaje gida ya huta sbd zai fita aiki da safe gobe…bata hanashi ba tace suma sun kusa tahowa gidan…yana barin wurin kai tsaye ya wuce waje dan ko second daya baison karawa nan ciki dan wani irin haushi yakeji from no where…text ya turama Nur yace ya fito su tafi snn ya karasa jikin motar nashi ya jingina dashi…har bayan 20 mins Nur bai fito ba ran Bobby duk ya gama 6aci na barinshi da yayi a tsaye cox key yana hannunshi balle ya bude mota ya shiga…yana kokarin sake dialing number dinshi wani mota yayi parking kusada nasu…baisan meyasa a kallon farko da yayiwa motar ya ganeta ba…it was the same car da suka shiga itada mutuminda yakeda tabbacin saurayinta ne ranan da sukayi reporting a Hospital dinshi…wani tsakin ya kara saki yanajin haushin Nur for not coming out har wnn mutumin yaxo ya sameshi a wurin…yayi kaman zai koma cikin hall din idanunshi suka hango mishi ita ta fito daga ciki ana tafiya kaman baza’a taka kasa ba…fuskan nan daukeda murmushin dake sa dimples dinta fitowa sosai dan yana iya ganosu daga nan inda yake tsaye..da yake inda yake babu haske sosai har ta karaso wurn bata lura dashi ba shi kuma baisan dalilinda yasa ya kasa dauke idonshi akanta ba duk kuwa da yanda yaso yin hakan…as usual tana karasowa ya bude mata mota ta shiga snn shima ya shiga ya rufe kofa…Bobby ya runtse ido yanajin wani zafi sosai a jikinshi…shi baisan wnn masifa ba da babu dama yaga yarinyar nan sai ranshi ya 6aci kuma duk laifin Nur ne dan daya fito sun wuce tun daxu yasan babu yadda za’ayi yaga wnn kayan takaicin…gaba daya yaji yanajin haushinsu daga ita har saurayin nata…wai babban mutum dashi ya rasa inda zai kare sai akan wnn fitsararriyar yarinyar sangartacciya ma da bata ajiye komai ba sai dan banzan shagwa6a…ganin time na sake kurewa Nur bai fito ba ya danna mishi kira…yana dauka yace”malam you should have told me if u are not going to leave now ba wai ka shanyani waje inata faman jiranka ba”..da sauri Nur ya mike daga inda yake zaune yace”wai kana nufin kana waje?..”tsaki kawai Bobby ya saki tareda kashe wayarshi…shi kuma Nur fitowa yayi dan sam bai lura da message daya tura mishi ba…yana karasowa ya bude mota suka shiga snn yayi reverse suka fita daga wurin fuskan nan na Bobby a dinke tsaf kaman wanda bai san me ake nufi da daria ba.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128Next page

Leave a Reply

Back to top button