Dr. BOBBY COMPLETE HAUSA NOVEL

Rano✨
Wnn littafin na kudi ne…masu buqatan siya zasu tura 300 zuwa 2208991344 Aisha Ahmad Tijjani Zenith Bank…sai a tura evidence of payment via 07063800556.
17
A bangaren love birds kuwa musayar kallo aka shigayi bayan an shiga motar…sai daga baya Prof yayi breaking silence din da fadin”baby girl kinyi more than kyau..i don’t how to put it but u look extraordinary gorgeous”…murmushi jin dadi ta saki tanata juya ido dan ba karamin dadin compliment din taji ba shiyasa ma ta dage mishi yazo dan bazata so tayi asaran duk wnn kwalliyan a banza ba tareda ya gani ba…sai kuma ya dan hade rai yace”amma baby haka kike yawo ko veil babu a jikinki?..look at yanda kika fito da gashinki kowa yana kallo this is not fair mana”…murmushi ta kara saki kafin tace”baby sbd biki nefa”yace”next time ko bikin wa akeyi banson ana ganinki a haka…banaso”…hannu takai tayi saluting dinshi still tana smiling tace”yes sir..ur wish is my command”…daria yasa sbd ganin yanda tayi itama tana tayashi…bayan sun gama daria kuma sai hira ya 6arke a tsakaninsu…labari sukesha sosai dan har ta mance da wajen biki suke tanata buga love abunta…yana fada mata zaiyi tafiya zuwa malaysia gobe ta dinke fuskanta tsaf kamar ba ita ke daria a while ago ba…shima nashi fuskan ya marairaice mata yace”baby bafa dadewa zanyi ba and believe me kullum zamu kasance tare a waya”…a takaice tace dashi”how many days?..”shiru yayi yana kallonta kafin a hankali yace”four weeks”…ganin zata fara mishi kuka yayi saurin matsawa kusada ita yana cewa”C’mon baby kar kimin kuka please…nima fa baa son raina bane ya zama dole ne shiyasa zanje but Allah kadai yasan how am going to miss u”…goge hawayenta tayi tana turo baki tace”kuma shine baka fadamin da wuri ba”..yace”am sorry kukan nan ne banaso amma am sorry kinji..pardon my manners”…sake turo bakin tayi wnn karon hadda dan murgudashi tace”kuma na dena kulaka”..ya saki murmushi yace”kicigaba da murgudamin bakin nan baby duk abunda ya biyo baya don’t blame me”…sake turo bakin tayi tana taleshi kaman zatasa wani kukan yayi saurin dakatar da ita da fadin”ohk ohk yi hakuri da wasa nake..am sorry okay?..”to cut it short Aysha daga nan ko cikin hall din bata koma ba bayan sun gama hiransu ta kira Billy a waya ta fito suka tafi…as usual yayi musu takeaway na kayan kwadayi snn yayi dropping nasu a hostel.
Dr.Bobby kuwa Nur na ajiyeshi a gida ya shige ciki ko sallama bai tsaya sunyi dashi ba…kawai gaba daya jinshi yake wani iri shiba mai lafia ba kuma shi ba mara lafia ba…wanka kawai ya sakeyi ya kwanta amma duk kokarinshi na ganin yayi bacci abun gagaranshi yayi…har su Mummy duka dawo bai runtsa ba…yanajinsu yaji fitowa yasan suma sunyi tunanin yayi bacci shiyasa basu nemeshi ba shi kuma bacci kiri kiri yace bazai daukeshi ba…har dare ya raba bai samu baccin ba haka yayita juyi kan gado yana faman tunanin abunda sam bai shafeshi ba sai can wajen 3 baccin ya lalla6o yayi gaba dashi…rashin samun bacci da wuri yasa ya makara sallahn asuba dan time din daya tashi an idar da sallah sai a gida yayi nashi snn ya sake kwanciya amma still baccin bai daukeshi ta dadin rai ba saida ya gama ja masa aji…can cikin baccin ringing din wayanshi ya tasheshi…a fusace yakai hannu ya dauko wayan yayi sliding yakai kunnenshi ko sunan mai kiran bai tsaya dubawa ba…daga can 6angaren Rayhan tace”uncle bobby”…ya runtse ido yanajin wani irin haushinta na lullu6eshi…yanxu dama duk uban kiran nan da ake jera mishi wnn yarinyar ce?…yana kokarin kashe wayarshi dan yasan yana bude baki mgn zai fada mata mara dadi yaji ta sake cewa”uncle bobby kayi hakuri plss…na kasa hakura ne…jiya Mummy ke cemin kaje wurin dinner kuma har ka tafi ban karaso ba…a wurin make up ne aka 6ata mun lokaci amma naso haduwa dakai sosai”…shiru ya sakeyi yanajin kaman yakai hannu ya kwada mata mari ta cikin wayan..he is just trying to control his temper sbd idan ta kaishi bango bazataji da dadi ba…jin shiru bai still baice komai ba tace”uncle bo…”bata karasa ba ya katseta da fadin”ke hold it plss..how dare u call me at this time of the day?..are u insane?..bakisan safiya bane ko bakisan i might be sleeping ba?..”kwantar da muryanta tayi sosai tace”kayi hakuri dan Allah..naga 8 ya wuce so i taught kana Hospital..am sorry”..tsaki ya saki bayan ya duba wall clock din dakin nashi yaga it’s 8:36 dan haka ya kashe wayan kawai tareda jan duvet ya lullu6e har kanshi dashi…kawai shidai gashi nan ne amma sam dadin jikinshi at all..wani irin weakness yakeji all over him ga kuma zuciyanshi da bai mishi dadi shima…haka nan ta kama kiranshi da sassafen Allah sai kace batada aikin yi…shi tunda yake bai ta6a ganin mayyar mace kaman Rayhan ba wlh…ace mace kaman chewing gum duk wulaqancin da yake mata har yanxu taki rabuwa dashi…haka yacigaba da juyi a kan gado shi bai koma bacci ba kuma shi bai tashi yayi abunda ya kamace shi ba…daga karshe dai da kyar ya iya mikewa yasa sport wears dinshi ya shiga jym wai ko zai dena tunanin abunda bai kamace shi ba.
Karfe uku dot yayiwa Aysha a Freedom Specialist Hospital…yau ko jiran bus bata tsaya yi ba besty ya kawota sbd tanaso ta wanke laifinta na jiya shiyasa ta fito as early as possible…tana shiga ward din taci karo da incharge na gaba daya maternity matron Salamatu sai midwife data rike mata aiki ranan da taje biki sai kuma wasu staff guda biyu da take ganinsu a eclamptic ward sai kuma alhaji Dr.Bobby dake tsaye hannayenshi zube a aljihu yana sauraronsu…wani irin dum taji gabanta ya fadi dan tasan taron bana lafia bane…Matron salamatu ceta fara ganinta dan haka tace”yauwa ga yarinyar nan doctor”..juyawa yayi a hankali ya kalleta sam baiyi mamakin ganin itace na sbd jikinshi ya bashi babu mai iya aikata wnn danyen aikin sai ita…gashi kuma hasashenshi ya zama gaskia..Aysha dai kasa tayi da kanta da sauri tana karanta lailaha illa anta subhanaka inni kuntu minazzalimun a cikin zuciyarta…har yanxu heart beat dinta bai dawo daidai ba…saida matron ta sake yi mata mgn snn tayi karfin halin daga kafarta ta karasa ciki…daga gefe ta tsaya kanta kasa tana karanto duk abunda yazo bakinta…idanunta lumshe tasan ko bata gani ba idanunshi ke yawo a kanta dan taji wnn hadadden tsoro da firgici da take shiga idan ya kalleta…Matron ce ta fara jifanta da tambayan da ya kusa sata sakin fitsari sbd tsoro..”meya hanaki zuwa aiki jiya?..”tayi shiru tana tunanin karyar daya kamata tayi…matron ta sake cewa”kinsan asarar da kika janyo mana kuwa?..kin tafi kin bar daki ba kowa snn ga patients duk babu mai kula dasu har daya daga cikinsu ta rasu sbd carelessness dinki”…a razane ta dago tana kallon matron din abunda ta fada..she can’t believe wata ta mutu sbd rashin zuwanta aiki jiya…”innalillahi wainna ilaihi rajiun mena janyoma kaina haka?..”ta fada cikin zuciyarta…lokaci guda hawaye suka ciko idonta yanxu hakan na nufin tayi kisan kai knn?…Dr.Bobby da tunda ya dora idanunshi kanta bai sauke ba ya daka mata wani tsawan daya sake firgita ta ganin yanda tayi banza da mutane kaman bada ita ake mgn ba…yace”bakida baki ne?..”da sauri ta shiga girgiza kai alamar tana dashi…ya sake tamke fuska snn yace”oya speak up..tell us exactly why u left them all alone har kika janyo mukayi asarar rai”…bakinta ta shiga motsawa tanason tace wani abu amma ta kasa…ta sai san ko kwaya takesha bazata yi karyan batada lafia ba tunda ya ganta jiya a wurin dinner… ganin batada mafita kawai ta shiga yarfa hannayenta hawaye na turereniya kan cheeks dinta tace”am…sor..ry”..Matron tace”ko dan gaba baa yin irin haka a asibiti..da kikasan bazaki zoba sai samu wata ta rike maki amma ba ki tafi ki bar patients on their own ba sbd ba wanda zaiyi tunanin su kadai ne…ba don Allah ya taimaka wadan nan sunzo jiyan ba da kilan asarar da zamuyi sai yafi haka”..kuka kawai takeyi tana gyada mata kai…Bobby ya zaro kudi a aljihu ya mikama mutum biyu da suka taimaka suka rike dakin snn yayi musu godia suka wuce…Matron da taga yanda ranshi ke 6ace tace”ayi mata uzuri dr kaga yarinya ce..zanyi mata fada inshaAllah bazata sake aikata makamancin haka ba”…bai ko kalleta ba bare tasa ran zai amsa idanunshi kan Aysha da har yanxu bata bar kuka ba yace”wuce muje”…a rikice ta dago tana kallonshi…ya zuba mata idanun nan nashi aikuwa ba shiri ta wuce gaba tana cigaba da kukanta…haka suka fito daga ward din tana gaba yana binta a baya har zuwa office dinshi…karasawa yayi seat dinshi ya zauna fuskan nan ba sarari yace”sbd bakida hankali kika wuce kika barmin patients su kadai dan bakisan aikinki ba koh?..anya kuwa bada malpractice kikayi passing Clinical skills dinki ba?..”dukda halin da take ciki mgnrshi ba karamin kular da ita yayi ba…wato ita yake nufi tana satan amsa amma Allah ya isanta wlh…cikin daga murya yace”are u deaf ina miki mgn zakimin shiru?..are u sick?..”runste idonta tayi sabbin hawaye na sake gangaro mata…itadai yau ta shiga uku da masifan wnn mutumin…sai ihu yakeyi mata kaman ita tajs ta shaqe matar ta kasheta…shima runste nashi idon yayi yana murza goshinshi trying very hard to control his temper don idan ya biye ta zuciyarshi yana iya gaggaura mata mari sbd haushin datake bashi…what did she think of herself da zai ringa mata mgn tana banza dashi…ganin bafa shiru zatayi ba ya buga table din gabanshi cikin karaji yace”kin rufemin baki ko sai na gaura maki mari a wurin…are u even alright da zaki sani a gaba kina min kuka?..are u mad?..”ya karasa mgnr cikin tsananin 6acin rai…sbd tsoratan da tayi batasan time data hadiye kukan nata tana toshe baki da hannayenta ba…shi kuma yacigaba da fadin”from today onwards aikinki ya dawo office dina…ke zaki dinga cleaning min office kullum kina wanke toilet dina…snn duk wani aike na office dina ke zaki dinga zuwa zan sallami cleaner da messenger dina har zuwa lokacin da zaki gama punishment dinki…if u like ki tafi gidan biki ku hadu da saurayinki kiqi zuwa aiki kiga yanda zanyi dake lazy fellow kawai”…har yanxun idanu a lumshe take sauraronshi…wato ma itace zata zama mishi cleaner kuma messenger sbd bashida imani…kuka kawai takeyi har yanxun batace mishi qala ba…shi kuwa kallonta yake har yanxu yana ganin yanda dimples dinta ke fitowa as a result of kukan da takeyi…ya sake daure fuska snn yace mata”go to the Nurses Station kice ina kiran Zarah”…ba tareda ta bude idon ba ta juya ta fita a office din…saida ta tsaya ta gama clearing face dinta dukda tasan a banza dan ana ganinta za’aga alamun kuka tattare da ita snn ta wuce nurses station din…tare suka fito sa nurse din zuwa office dinshi…Aysha taja gefw ta tsaya tana daure fuska dan a ganinta sbd tana mishi kuka ne yasa yake raina mata wayo…Zarah ta karasa bayan ta gaisheshi yace”how many files do we have?..”tace”they are many sir..”yace”ohk kuje da ita ki bata ta kawo and kina iya tafiya gida u are done for today”…nan da nan ta washe baki hadda risinawa tace”thank u sir”…Aysha ta maka mata wani harara a kan idon Bobby dake kallonta ta gefen ido…cikin ranta tace”azzaluma ba dole kiyi godia ba”…saura kadan daria ya subuce mishi sbd ganin yanda tayi hararan kaman idonta zasu fado kasa…tare suka sake fita Zarah ta hadata da uban files na patients din da zai gani yau snn ta koma office din nashi ta kai mishi da kyar take iya dauka sbd nauyinsu…ta ajiye mishi su nan gabanshi snn taja baya ta tsaya tareda rungume hannunta…yace”zo kiyi arranging files din according to their numbers”…sake daurw fuska tayi ta matsa ta janyo kujera zata zauna yayi saurin dakatar da ita da cewa”and who ask u to seat?..”shiru tayi tana kallonshi yace”C’mon get started before i loose my temper with u…ba dai aikinki tafia gidan biki kina barin patients su kadai ba?..as small as you are har kinsan ki hada Ap da saurayi ya sameki wani wurin sbd ba gaban parents dinki kike ba kou?..i know exactly how to deal with people like u..now start what i asked u see the other side of me”…a hankali ta matsa gaban table din ta kai hannu ta janyo files din gabanta…har zata fara dubawa ta tuna batasa glasses dinta ba dan haka ta mike zuwa inda bag dinta ke ajiye ta dauko glass din ta saka snn ta sake komawa ta fara abunda ya sata…shidai yana zaune yayi crossing hands dinshi a kirji yana kallonta…Allah ya taimaketa gaba daya files din a jere suke according to numbers dan haka ta dago tana kallonshi tace”Sir a shirye suke”…without looking at her yace”call the first person”…cikeda haushi sosai take kallonshi jin abunda yace..ta kalli bell dake gabanshi dannawa kawai fa zaiyi patients din su fara shigowa amma bazai iyaba sbd dole sai ya bata wahala…ganin wasu hawayen na sake ciko idonta ta dauki file din farko tareda juyawa ta fita sai gasu sun dawo ciki da me file din…ya nuna mata wuri ta zauna ita kuma Aysha ta kwashi files din gaba daya zata fita dasu yace”where do u think u are going?..”ba tareda ta juyo ba tace”waje..”yace”su kuma files din suyi mene a wajen?..and ke kanki waya baki permission din zuwa waje?..”saida ta hadiye tears dinta snn tayi qundunbala ta juya tana kallon tsakiyar idonshi trying so hard ta 6oye tsoronshi dake cikin nata idanun tace”sai nacigaba da turosu daga waje”…kallon tsakiyar nata idanun shima yayi kafin yace”zo ki ajiyemin files and if u dare step out of this office sai na baki mamaki wlh”…sauke idonta qasa tayi tareda lumshe su allowing tears dake ciki fitowa kan cheeks dinta…ai ita tasan ta gama yawo tunda ta fada hannun wnn azzalumin…bata damu data goge hawayen ba ta maida mishi files din gabanshi kaman yanda yace snn ta koma gefe ta tsaya tana cigaba da hawaye…hankalinshi ya maida kan patient dinshi yana mata tambayoyi…Aysha tayi mamaki sosai yanda taga yana interacting da patients din nashi sam batayi zaton haka daga wurinshi ba…gani take ko patients din ma zare musu ido zai ringayi yana daure musu fuska amma sai taga ba hake yakeyi ba sam…mgn yakeyi dasu full of attention da kuma concern kamar dai ba arrogant and wicked Proprietor dinsu ba…haka yacigaba da attending patients dinshi tana tsaye saidai idan ya gama yace ta kira next patient and ba yanda ta iya haka tayita sintiri from office dinshi zuwa waje…legs dinta har sun fara mata ciwo sbd tsaiwa ga wnn kai kawon da takeyi shima ba karamin wahala ne dashi ba…ga patients din da masifan yawa dan gani take kaman ma karosu akeyi ace tun dazu suna abu daya amma har yanxun sunki karewa…har aka kira sallahn magrib basu kammala ba…zuwa yanxun karfinta ya gama karewa tass neman wanda zata saukema kukan dake cinta kawai takeyi amma babu dan haka ta jingina da bango tareda kai hands dinta ta rufe fuskanta dasu ta shiga rera kukanta a hankali…Bobby na jinta baice komai ba har ya sallami wadda take gabanshi snn ya mike zuwa bathroom yayo alwala ya fito ko kallon inda take baiyi ba ya fice zuwa masjid…tana jin ya fita ta zauna nan kasa zaman dirshan ta dora hannu a kanta tana rushewa da wani matsanancin kuka…kuka take sosai dan idan ka ganta zaka ranste da Allah wani gagarumin abun akayi mata…saida ta shafe kusan minti goma tana abu daya kafin ta mike da sauri kaman wanda ta tuno wani abu ta dauki bag dinta tana goge hawayenta ta bude office din ta fita…a bakin kofa sukayi karo dashi yana tsaye ya zuba mata ido kaman yasan abunda take niyyar yi yace mata”waya baki permission din tafiya?..”takai hannu ta goge tears dinta ta bude baki da kyar sbd kukan da taci tace”Sir…dan..Allah…inje gida…wlh na gaji…kaina namin ciwo”…kallonta kawai yake yanda tayi mgn dama tun ba yanxu ba yasan sangartacciya ce so baiyi mamaki ba sam…baice komai ba yakai hannu ya bude kofar office din yana binta wnn kallon da bataso cikin stern voice dinshi yace”get in..”yarfe hannu ta farayi tana dan bubbuga legs dinta a kasa da alama abun ya motsa cikin shehssheka tace”Sir dan…Muhammdu…Rasulillahi…dan darajan…”kasa karasawa tayi sbd ido daya tsareta dasu…haka nan ta juya ta koma office din sabbin hawaye na sake antayowa fuskanta…shima shiya yayi ya maida kofan ya rufe snn ya karasa seat dinshi ya zauna…ya duba sauran files da suka rage mishi yaga guda uku yasan idan yace ta kirasu 6ata mishi time zatayi dan haka ya danna kararrawa ba dadewa wanda yake kan layi ya shigo…wuri ya nuna mata ta zauna snn ya shiga attending dinta…Aysha dai har yanxun tana tsaye tana kuka kaman wanda akama dan banzan duka…ganin bafa dena kukan zatayi ba daya sallami ta gabanshi sai ya juya yana watsa mata harara yace”ke kinada hankali kuwa?..office din nawa zaki maida wurin iskancinki are u insane?..”banza tayi dashi tana cigaba da kukanta…ya daka mata tsawa yace”are u deaf”…ai batasan lokacin data hadiye ragowar kukan ba sbd tsabar tsoratan da tayi…ya nuna mata wani seat dake kusada ita yace”seat down and keep shut…idan kika sake na sake miki mgn you will see the other side of me”…ba musu ta zauna kan kujeran tana kunshe kukanta…haka tayita zaune har ya karasa ganin patients din snn ya mike ya tattara kayanshi ya dau keys da wayoyinshi ba tareda ya kalleta ba yace”leave my office immediately..and make sure gobe ki fito da wuri kimin clearing office idan ba hakaba zakiga yanda zanyi dake”…tun kafin ya karasa ta bude office din ta fita da sauri tana sakin kukan da take rike dashi tun daxu.