Dr. BOBBY COMPLETE HAUSA NOVEL

Dr. BOBBY COMPLETE HAUSA NOVEL

Rano✨

Wnn littafin na kudi ne…masu buqatan siya zasu tura 300 zuwa 2208991344 Aisha Ahmad Tijjani Zenith Bank…sai a tura evidence of payment via 07063800556.
18
Parking lot ta zauna tacigaba da rusa kuka kaman wadda aka aikoma saqon mutuwa…tana nan zaune taga fitar motanshi aikam tabi motan da harara kamar idanun zasu fadi…saida tayi me isarta snn ta daga waya ta kira besty dan yazo yayi picking dinta…yana dauka ko mgn kasawa tayi kawai ta rushe mishi da kuka…a rikice sosai Sa’eed ke tambayan abunda ya sameta amma ko uffan batace ba sai azabar kuka take…daga karshe sai ya kashe wayan kawai snn ya dauki hanyan Hospital dama he is near by so within few minutes ya iso…da sauri ya karasa inda ya hangota zaune tana kuka shima ya zauna nan gefenta hankalinshi duk a tashe yace”besty dan Allah what is it?..why are u crying like this?..are u sick?..”girgiza mishi kai tayi meaning she is fine…yace”then what happened?..why are u crying?..”kuka tacigaba dayi kaman bazata yi mgn ba sai can daga baya tayi kokari ta tsayar da kukan nata snn tayi mishi bayanin duk abunda ya faru tun shigowarta asibitin zuwa yanxu…sauraronta yake saida ta gama tsaf snn yace mata”yanxu dai kiyi hakuri ki fara mikewa mu wuce kinga dare na karayi sosai…shi kuma proprietor kiyi mishi addu’a Allah zai saka maki kinji kou?..”gyada kanta tayi tareda mikewa a hankali suka nufi inda yayi parking…if u see how she is walking u will think irin tayi shekara da shekaru tana ciwon kafa…a haka suka isa inda motan yake ya bude mata ta shiga shima ya shiga suka fita daga asibitin…koda suka isa hostel saida ya kira Billy a waya wai tazo ta shiga da ita ciki aikuwa ta fito a rikice dan tana tunanin wani mugun abun ne ya faru da ita…mamaki ya kamata ganin yanda idon ‘yar uwar tata yayi ja sosai face dinta duk yayi red sbd kukan dataci kafin ma ta tambaya Sa’eed ya labarta mata abunda Ayshan ta fada mashi ya faru…jikinta yayi sanyi kalau ita kanta tausayin Ayshan takeji…tasan haduwa irin wnn da proprietor ba abun alkhairi bane mutumin da ko idanu ka hada dashi sai kaji a jikinka inaga kuma ace ya tsareka da a gaba yana suburbuda maka masifa…ai dole ma Aysha ta jigata wlh..ko ba don zirga zirgan da tayi ba ko zama at the same roof da wnn mutumin kadai ya isa yasa mata zazza6i balle kuma ga wahalar da ita da yayi…Allah kadai yasan adadin sau nawa cikinta na kadawa sbd wmn matsiyacin kallon nashi…a hankali ta kamata suka shiga hostel din shi kuma Sa’eed ya juya kan motarshi ya wuce gida…suna shiga ciki ta hada mata warm water ta taimaka mata zuwa bathroom snn ta dawo ta shiga kitchen ta hado mata thick tea shima mai zafi ta jiye mata kan study table…ta dauko pcm da ruwa shima ta ajiye mata nan kusada tean sai kuma ta bude wardrobe dinta ta dauko mata jessy dinta as usual na Man Utd fara qal da wandonta duk ta jiye mata su kan gado…tana fitowa ta dauki kayan ta saka snn tasha tea da magani snn ta nannade kan gado tana sauke ajiyar zuciya…kawai imagining take yanda zatayi spending three whole weeks tareda wnn azzalumin mutumin da baida imani da tausayi ko kadan.

Washegari da wuri ta tashi duk da ba wani baccin kirki ta samu ba amma she woke up as early as possible sbd gudun sake yin wani laifin…a gurguje ta shiga bathroom tayi wanka snn tazo ta shirya suka fita tareda Billy ko breakfast ta kasa tsayawa tayi sbd tsoron kar tayi latti ya samu daman ci mata mutunchi.
8:17 suka shigo Hospital ko sallaman kirki bata tsaya sunyi da Billy ba ta wuce sbd tsoron abunda zai iya mata…saida ta tsaya ta gama jero addu’o’inta a bakin office dinshi snn ta tura kofan ta shiga a hankali da sallamanta ciki ciki…yana zaune kan office chair dinshi sanye da suit as always yana filling wani file dake kan table dinshi…ko kallon inda take baiyi ba balle har tasa ran zai amsa sallaman da tayi..itama hakan bai dameta ba ta karasa inda ta tsaya jiya ta tsaya kanta a kasa…wayanshi ne keta ringing yana ciki file din amma yayi banza dashi kaman bashi ake kira ba…saida ya gama snn yayi sliding tareda putting nata on speaker da igbo yace”Sab bakada hankali kou?..why kaketa jeramin missed calls haka?..”daga daya bangaren Sab ya amsa mishi cikin igbo shima saying yanason mgn dashi ne…Aysha dai na tsaye tana jin yanda suke mgn da igbo dagashi har wanda ya kirashi a wayan…dukda ba fahimtan language din takeba for sure tasan masifa yake sbd yanda yake daga murya…can kasa kasa tace”duk wani inyamuri dai ya iya masifa..kilan abun a jininsu yake”…tayi nisa cikin tunaninda take har batasan ya kammalan wayan da yake ya dawo sa hankalinshi gareta ba…yana kallon yanda dan bakinta ke motsawa as a result of zancen zuci da take kawai sai yaji gabanshi ya fadi…ya lumshe ido yana karanta innalillahi cikin ranshi…ya dauki tsahon lokaci idon nashi a rufe har saida yaji heartbeat dinshi ya daidaita snn ya bude..still kuma idanun kanta suka fada this time around sai ya kasa dauke idanun daga kanta…he just keep staring at her like mirror…har yanxun bakinta mosti yake and he wonder what she’s saying da bakin ke motsawa haka…a hankali yayi sama da eyes dinshi zuwa forehead dinta da black thick hair kenan a kwance luf kaman na jaririya har zuwa sajenta da kuma dimples dinta da ko yaya cheeks dinta yayi motsi sai ya fito…sake lumshe eyes dinshi yayi yana dan murza goshinshi feeling somehow…baisan meya sameshi yau ya kasa dena kallonta ba and it’s not as if she’s beautiful kawai dai baisan dalili ba…wnn karon yana bude idon itama ta bude nata aikuwa idanunsu suka sarke cikin juna…Aysha da dauke nata da sauri sbd wnn abun dai da takeji duk ya zuba mata golden eyes dinshi a kanta…turo baki tayi murya can kasa tace”nidai Allah ya isana wlh..haka nan ya dinga zubama mutane idanun nan nashi sbd yasan ba’aso”…daure fuska yayi kafin yace”ke what are u saying?..”da sauri ta maida bakinta normal tareda kokarin daidaita face dinta kai a kasa tace”ba komai Sir…good morning”…bai amsa ba sai nuna forehead dinta da yayi yace”baki iya daura dankwali bane?..ko duk cikin rashin sanin darajar kai ne yasa kike yawo da gashi a waje?..”hannu takai ta dan janyo hijab din zuwa goshinta dukda ba rufe gashin yake ba dan kome zatasa sai ya fito shiyasa ma take barinshi..cikin ranta tace”na rasa a ina inyamurin nan yaji hausa wlh..he speaks like jakin kano”…kallon forehead din nata yayi yaga still gashin na nan waje kuma wai da sunan ta rufe kawai sai ya girgiza kai tareda sakin tsaki…mikewa yayi ya dauki phone dinshi snn ya kama hanyan fita yace mata”follow me”…ba musu tabishi a baya kaman body guard…eclmaptic ward taga ya nufa…ya jima suna mgn da wata nurse da doctors guda biyu kan wata patient da zasu shiga da ita theathre yanxu…after like ten minutes aka fito da matar zuwa theatre sauran doctors din suma duk suka shiga don shiryawa…shine karshen fitowa shima ya kama hanyan theatrn Aysha ta bishi a baya…daga bakin kofa ta tsaya ta dan daga murya yanda zai jiyota tace”Sir in koma knn?..”juyowa yayi yana kallonta da mamaki yace”go back where?..ba cewa nayi ki biyoni ba”…ta dan marairaice tace”to Sir naga zaku shiga theatre nefa”…ya daure fuska snn yace”C’mon come inside and get ready dake zamu shiga ai”…ta wani zarw idanu tana kallonshi hadda dora hannu a chest dinta tace”dani kuma?..”yace”ke don’t waste my time here.. i said dake zamu shiga kiyi resuscitating baby and don’t let me repeat myself”…hannu ta fara yarfewa zata kwaso magiya kawai ya zuba mata idanunshi yana yi mata irin kallon da yasan duk iskancinta bata isa ta sake yi masa musu ba…hakan ne kuwa ya faru dan kasa cewa uffan tayi..tayi kasa da kai cikin ranta tana mamakin tasirin da eyes dinshi suke dashi a kanta…kofa ya nuna mata yana kallonta alaman she should enter…ba musu balle gardama ta shigo ciki a hankali kaman mara lafia…changing room ya nuna mata ba tareda yace komai ba haka ta shiga ciki tanajin kaman ta dora hannu a kai tace wayyo Allah…bayan ta shiga shima ya shiga doctors changing room yayi changing zuwa theater outfit dinsu snn ya fito zuwa main theatre…matar tana kwance masu anaesthesia sun fara aikinsu a kanta sai doctor faith da doc gabriel da zasuyi aikin tare…ganin har zasu fara bata fito ba ya fita zuwa dressing room din…a tsaye ya sameta ta gama sa kayan sai kallon kanta take tana ganin yanda kayan sukayi mata yawa…tana turo baki tace”kayan ma over size n…”bata karasa idanunta ya sauka cikin nashi sai tayi saurin daidaita kanta da sauri tana cewa”am sir..d..dama yanxun..zan fito”…kallonta yayi from head to toe snn ya tsayar da idon nashi kan gashinta datayi parking a tsakiyar kai ta saki jelar yanata yawo tsakanin wuya da shoulders dinta…da sauri ta dauki hijab dinta ta rufe kan nata dashi baki a tunzure tana fadin”to babu hula fa”…baice mata komai ba ya karasa cikin dakin ya bude wani drawer ya zaro mata one of huluna da suke ciki snn ya wurga mata…saida ta daure fuskanta tsaf snn ta dau hulan ta saka cikin ranta tana zaginshi sbd cilla mata hulan da yayi…hanya ya nuna mata ba musu ta shige gaba yabita a baya…a bakin main theater suka tsaya ta zura wnn gunduma gunduman takalman snn suka shiga ciki…itadai a tsorace take dan bata ta6a shiga theatre ba..tsananin tsoronta ma bazai bari ta shigaba dan ko Allah ya san batason ganin ana yanka mutum sam…amma yau wnn inyamurin ya sanyata dole ta shiga dukda rashin son nata…saida suka gama shirya komai tsaf snn kowa yasa nose mask dinshi suka fara aikinsu…Aysha dai na tsaye tana faman runste ido don bazata iya gani ba wlh…Bobby dayaga yanda take runtse ido sai yayi mata alama da ta matso kusa…ta shiga yarfa hannu har ta fara hawaye shi kuma ya tsareta da ido yanda baza tayi mishi gardama ba…haka ta matsa inda ya nuna mata tana cigaba da hawaye har doc Gabriel nayi mata daria…kafin ta sake kulle idon yace mata”if u dare close those eyes again zakiga yanda zanyi dake wlh..and i mean it”…bata rufe din ba kuwa ta zuba idanu kawai tana kallon abunda sukeyi…kirjinta har sama da kasa yakeyi bata ta6a sanin tanada tsoro har haka ba sai yanxu…hankalinta bai sake tashi ba saida taga sun fara yanka matar…taga yanda suke cutting skin dinta layer by layer kawai sai taji wani hadadden jiri ya fara daukanta…kokari tayi ta rike gefen gadon gam still kuma taki kulle idon sbd kar yayi mata masifa…tun tana iya bakin kokarinta wajen ganin jirin baiyi tasiri a kanta ba har yakai limit din da bazata iya controlling dinshi ba kawai sai gani tayi dakin yana juyawa da ita…ta saki gadon da sauri tareda kai hannu ta dafe head dinta dashi idanunta a rufe still bata dena ganin jirin ba daga karshe ma sai ji tayi ta tafi luuu kaman zata fadi Allah ya taimaka akwai wani gado a bayanta kawai saita fada kanshi ji kake timm…a tare gaba daya doctors din suka dago suna kallonta don sunyi nisa a aikinsu that ba wanda ya lura da abunda ke faruwa da ita sai faduwan nata sukaji…dukda ta fadin kuma jirin bai dena daukanta ba har yanxun tana dafe da kanta hawaye na fitowa idanunta murya can kasa take fadin”wayyo Ammina..wayyo dadyna..wayyo Allahna”…gaba daya doctors din saida sukayi daria banda Bobby da baiga anything funny a nan ba…basubi ta kanta ba suka cigaba da aikinsu that last for 40 to 45 mins kafin suka gama…doc faith ce tayi resuscitating baby su kuma suka karasa duk wani necessary abu da zaa yima matar snn wanda zasu fita da ita sukazo suka dorata kan trolley sukayi waje da ita babynta kuma already an mikashi wa relatives dinta…sauran doctors din suma duk fita sukayi shi kuma Bobby bayan yayi sanitizing hannunshi ya nufi kan gadon da take thinking ko bacci take mishi a theatre and to his biggest surprise sai yaga ashe sumewa tayi…mamaki ne ya kamashi hade da daria at the same time…wato duk iskancin dan iska akwai abunda yake tsorata shi har ya sashi suman dole…shi tunda yake bai ta6a ganin Midwife irinta ba…wai matar dake dealing da kar6an haihuwa itace zata suma sbd Caesarean section “what a shame!..”ya fada trying to control his laugher cox he still can’t believe sumewa tayi…wato duk rashin jin nan nata she has this phobia of blood ne ko of the operation din ne gaba daya ma bai sani ba…saida ya gama dariyarshi snn yasa aka kawo ruwa ya watsa mata…ta mike a gigice idanunta kulle take fadin” dan Allah no…i don’t want to see it plss i beg u…wayyo Allah besty,Billy,baby come help me plssss”…ta karasa mgn new tears na rolling kan fuskanta…Dr.Bobby still can’t believe this…knn da gaske suma tayi sbd abunda ta gani…lallai kuwa tanada aiki a gabanta…a very huge one ma kuwa…a hankali ta bude idonta sai taci karo da smiling face dinshi aikuwa ta wara idanun da kyau tana kallonshi to make sure she is not dreaming…tadai san idan ba mafarki ba ba yanda za’ayi inyamurin nan yayi daria for it’s something she never seen..shi kuma ganin kallon da take masa sai ya dinke fuskanshi tsaf tareda matsawa daga inda yake yace”C’mon get dawn before i slap u lazy girl kawai…a haka zaki zama midwife kina painting sbd caesarean?..u are deceiving ur self”…goge tears dinta tayi ta sauko daga gadon tana fadin”ai ni ba ta6a gani bane shiyasa”…harara ya watsa mata yace”shiyasa nace u are deceiving ur self…now ki wuce ki jirani office and if u like kije wani wurin kiga idan na dawo banyi maganinki ba”…wucewa tayi tana sake turo baki sai kuma ta juyo zatayi mishi mgn yace”i said leave”…ba gardama ta sake juyawa ta fice daga wurin…duk jikinta ma wani iri take jinshi kaman na mara lafia…shiko Bobby bayan yayi changing zuwa normal outfit dinshi ya fita zuwa office…zaune ya sameta kan one of sofas dake nan ciki tayi wani dai dai kaman tana office dinta yana shigowa ta mike da sauri tana rarraba ido kamar munafuka…baice mata komai ba ya karasa gaban table dinshi ya dauki stethoscope ya rataya a wuya snn ya juya zai fita ya sake ce mata”Follow me”…banza tayi dashi tana binshi da harara har ya fita snn ta mike itama ta fita tana kwaikwayon mgnrshi” wani wai follow me…sai kace ajiyeni yayi in dinga yi masa bauta…mugu kawai”…ta karasa mgnr da guntun hawaye a idonta…ita dai zataga ranar da zatazo asibitin nan ta tafi bai sa tayi kuka ba…kullum burinshi ya sata yin abunda bataso ko ya wahalar da ita kawai sbd small mistake data aikata bayan ba kanta aka fara ba…Post natal ward suka je ya fara ward round ita kuma tana biye dashi a baya…data gaji da tsaiwa sai ta faki idonshi ta samu wuri zata zauna taji yace mata”zo kimin taking vital signs din wnn”…kamar ta kwada masa mari haka taji amma ba yanda ta iya haka ta mike ta fara taking vital signs din…a takaice ita ta dauki vital signs din duk patients din dake ward din shi kuma yana dubasu…kafin su gama kuwa jikinta yayi laushi liss kaman an nakada mata shegen duka…yau ma kamar jiya da kuka ta fita daga office dinshi bayan ya sallameta.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128Next page

Leave a Reply

Back to top button