Dr. BOBBY COMPLETE HAUSA NOVEL

Dr. BOBBY COMPLETE HAUSA NOVEL

Secretary na fita kai tsaye midwifery section ta nufa kaman yanda yace mata…duk wanda ta tambaya Lamido zaice baisan inda ta tafi ba…har class dinsu taje bata nan and gaba daya yan class din suna ciki suna lectures ita kuma ba wanda yasan inda take…gajiya tayi da neman nata ta sauka kasa ta sake dubawa nan inda classes din Nurses yake amma ba Aysha ba alamarta…tana fita daga wurin ta hangota can bakin gate ta shigo makarantan hannunta niki niki da ledoji kaman wadda taje kasuwa…da sauri ta karasa inda take tace”kece Lamido koh?..”kai tsaye ta gyada mata kai alaman eh…secretary tace”kizo office Dr.Bobby na nemanki”…Aysha ta wara idanu kaman taga abun tsoro tace”what!..ce mishi kikayi kin ganni?..”secretary bata sake cewa komai ba ta juya tace”nidai na fada miki..idan kuma inje ince mishi baki zuwa ne toh”…da sauri tabi bayanta tana turo baki tace”muje..ai dai duk abunshi bazai gutsuri naman jikina yayi pepper soup dinshi yaci ba..iyaka ya balbaleni da masifa wnn kuma shi ya sani”…secretary dai tafiyarta tayi bata ma jin abunda take fada sbd ciki ciki tayi mgnr…saida ta fara ajiye kayan dake hannunta nan kofar office din nashi snn ta tura kofar a nutse ta shiga bayan ta gama hade rai wai sbd kar ma yaga fuskanta a sake yace zai rana mata hankali…bayan ta shiga ciki ta juya tareda closing kofar tayi taking one step forward kafin idonta ya hango mata wanda ke zaune cikin office din…zare idanu sosai tayi looking at him kaman taga dodo dan har ga Allah ta dauka gizo yake mata…hannu takai ta murza idanunta sosai tana tunanin kodai sbd batasa glasses dinta bane ta fara gane gane kuma…bata tabbatar da gaske shine nan zaune ba saida taji voice dinshi na fadin”ni ne nan zaune ba daydreaming kike ba”…lokaci daya gabanta yayi wani irin faduwa irin wanda bai ta6a yin irinshi ba…juyawa tayi ta kalli Bobby taga shima idonshi a kanta snn ta sake juyowa ga daddy still shima kallonta yake fuska daure…nan take wani irin zufa ya fara keto mata…taya akai daddy yazo office din mutumin nan?..bata samu amsan tambayan ta ba ta sakejin daddy yace”ni kike jira in taso in gaisheki knn kou?..”da sauri ta karasa inda yake ta zube kan guiwoyinta murya a matukar nutse tace”daddy..barka da z…”bai bari ta karasa ba ya katseta da fadin”daga ina kike?..”wani yawu ta hadiye da kyar zufa na kara keto mata tayi qundunbala tace”da..daga class nake”kallonta yakeyi rungume da hands dinshi yace”really?..wato daga class kike?..”kai ta sake dagawa tareda cewa”eh..”sai kuma tayi saurin girgiza kan ganin irin kallon da yake mata tace”aah..”fuskanshi ba alamun wasa yace”kince eh kince aah..wanne zan dauka knn?..”hawaye na cikowa idonta tace”daddy wlh abinci naje na siyo”..yace”abinchi?..bakuda cafeteria ne cikin makarantan?..”tana girgiza kai tace”da akwai”…yace”then menen dalilinda zaisaki fita waje siyo abinci lokacinda students yan uwanki suke class..wato har yanxu baki dena irin wnn halayen ba koh Aysha?..kina ganin kaman tunda kina nesa damu you are free to do duk abunda kikaga dama kou?..”da sauri ta shiga girgiza kai tana hawaye sosai tace”daddy wlh ba haka bane…dan Allah kayi hakuri wlh Billy ce batada lafia tace in siyo mata shine na fita amma ba haka nakeyi ba wlh”…kallonta kawai daddy keyi baice komai ba…Bobby kam kusan suman zaune yayi sbd mamaki…bai ta6a tunanin haka takejin tsoron mahaifinta ba dan hasali ma shi kallon sangartatta yake mata ashe abun ba haka bane..ya tabbata da sangarta ta ake babu yanda zaayi ta shiga tashin hankali haka sbd ganin babanta…wnn kadai ya isa ya nuna cewar sam ba sangartata akeyi a gida ba kilan dai kawai halinta ne haka…amma kam albasa batai halin ruwa ba…jin kukanta ya fara cika office din daddy yace”ke denamin kuka a nana..ai bakisan da kukan ba kike aikata abunda kikaga dama sbd kinga bama ganinki kou?..”girgiza kai kawai takeyi tana kokari tsayar da kukan nata ko uffan ta kasa cewa…a dan fusace yace”bazakiyi shirun ba knn”…tun kafin ya rufe baki tayi diff kaman anyi ruwan sama an dauke…still fuskanshi a daure yace”ina Bilkisun take?..”da sauri tace”tana hostel..”yace”kun kaita asibiti ne?..”ta gyada kai tace”da safe muka kawota..an bata drugs da injections yace inshaAllah zuwa gobe zataji sauki”…gyada kanshi yayi alaman ya gamsu kafin ya sake dan hade ranshi yace”idan kin koma ki hadani da ita awaya and wlh wlh Aysha idan kika sake na gani ko naji labarin kin aikata abunda bashi kenan ba a cikin makarantan nan ko a waje Allah sai kinyi mamakin matakin da zan dauka a kanki tunda na fuskanci har yanxu akwai sauran rashin ji a tare dake..just dare me kiga abunda zai biyo baya”..kai a kasa taba matsar kwalla tace”inshaAllah zan kiyaye daddy..kayi hakuri”..baice mata komai ba ya juya yana kallon Bobby da yayi relaxing kan seat dinshi yana kallon su kaman movie..kawai mamakin yanda such a responsible and reasonable person kamanshi zai haifi tantiriyar yarinya kamar Lamido…ga dukkan alamu kuma yana iya bakin kokari kan tarbiyyarta kunnen qashi ne kawai Allah ya hore mata…muryan daddy ya dawo dashi daga duniar daya tafi da yace”son alfarma nake nema a wajenka”…wnn karon Aysha ce mai mamakin sbd sunan da taji daddy ya kirashi dashi”son dai?..”ta fada cikin ranta…murmushi Bobby ya saki cikeda girmamawa yace”ai babu alfarma tsakanimu sir..kawai ka fadi buqatarka”…shima daddy ya saki smile din jin dadi snn ya nuna Aysha da har yanxu ke zaune kan guiwoyinta yace”so nake kasamin ido a kanta plss..tanada fitina sosai..she is so stubborn that saida mahaifi na yasa baki before in amince ta taho karatu wani garin..batajin mgn sam kuma tun tana karamarta haka take…na yadda da tarbiyyarka shiyasa zan dora wnn responsibility din a kanka and inada tabbacin u can do it…i want u to put eyes on her idan kaga zata aikata abunda ba daidai ba kayi stopping dinta snn duk lokacinda kace tayi wani abu batayi ba just give me a call zakaga hukuncin da zanyi mata..i hope u can do that for me”…gyda kai Bobby yayi yace”inshaAllah sir”…murmushi daddy ya kara saki tareda mikewa ya isa gaban table dinshi ya mika mishi hannunshi yana cewa”thank u so much son..ubangiji Allah jikan mahaifinka”…Bobby da kunya ya hanashi mika nashi hannun yace”Ameen sir”…kamo hannun nashi dady yayi tareda shaking da nashi still smiling yace”we’ve already became family so meye na makale hannun?..”murmushin dai ya kara saki kanshi kasa ya kasa hada ido dashi…hakan da yayi ya sake burge daddy sosai ya kuma tabbatar da cewa ya damka amanar Aysha a hannun daya dace domin yasan har abada jinin Attahir bazai ta6a kasancewa bata gari ba..ya aminta da tarbiyyar yaron dari bisa dari…bayan ya saki hannun nashi ya zari card dinshi daga aljihu ya ajiey kan table dinshi tareda fadin”here is my card ka kirani da wuri sbd inyi saving numberka”..Bobby ya dauki card din yana fadin”InshaAllah sir..thank u so much”..daddy yace”always welcome son..will like to meet u again”…yace”inshaAllah Sir..Allah ya tsare”..daddy ya amsa da”Ameen”..kafin ya fita daga office din…hajia Aisha kuwa suma ne kawai batayi ba tsabar mamaki…har yanxu ta kasa fahimtan ta inda wnn sabon alaqa ya 6ullo tsakanin daddy da inyamurin mutumin nan..sam hakan bai gamsheta bane..dr Bobbyn da ba kaunarta yake ba shine yanxu zaa ba amanarta aikam tasan ta gama yawo..takura dai iri iri zata sha a wurinshi kuma batada bakin complain tunda umarnin mahaifinta ne…ficewa tayi itama yabi bayan daddy…yana dab da shiga mota ta cimmasa dan haka ya dakata tareda juyawa gareta ya zaro kudi masu yawa daga aljihun babban riganshi yayi dividing kudin into two tareda mika mata daya yace”ga naki”…ta amsa tana godia snn ya sake bata dayan yace”wnn kuma na Bilkisu..saura kuma ki bari inji labarin ya saki ko ya hanaki wani abun kinki yi zakiga yanda zanyi dake”…kasa cewa komai tayi kanta kasa…security dinshi dake tsaye ya nunama ya dauko mashi wani abu a mota nan da nan ya bude motan ya dauko wani bag mai kyau ya mika mashi…daddy ya amsa tareda mikawa Aysha dake tsaye kai a kasa yana cewa”take..”da sauri tasa hannu biyu ta karba tareda dan risinawa tace”Allah ya saka da alkhairi “..a hankali yace”Ameen”..snn ya shiga cikin mota…ta matsa jikin window tana dubanshi tace”daddy Allah ya kiyaye hanya..ina gaida su Ammi”..yace”zasuji inshaAllah..ki koma ciki”…a hankali tace”toh..”tareda barin wurin…tana kallo motan nashi har ya fita daga makarantan ta sauki ajiyar zuciya tareda dafe kirjinta da har yanxu bai dena bugawa ba…taso komawa ta dauko kayan data bari a kofar office dinshi amma bazata je ba haka kawai yayi ram da ita a wajen…yanda yake neman tan nan tasan ai idan suka hadu rashin mutunchi ne zata sashi musamman yanxu da daddy yace wai yasa mata ido…wucewa tayi class dinsu cikin ranta tana ayyana wai ita daddy zaice a sa mata ido sai kace wadda take aikata wani aikin ashsha.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128Next page

Leave a Reply

Back to top button