Dr. BOBBY COMPLETE HAUSA NOVEL

Rano✨
Wnn littafin na kudi ne ban yadda wani ko wata ya fitarmin dashi ba…masu buqatan siya zasu tura 300 zuwa 2208991344 Aisha Ahmad Tijjani Zenith Bank…sai a tura evidence of payment via 07063800556.
21
Tun daga wnn ranan bata sake yadda ta hadu dashi ba har tsahon sati guda shima kuma bai nemeta ba…gashi duk sukayi waya da daddy sai jaddada mata tayi mishi biyayya and ta ringa zuwa tana gaisheshi time to time ta amsa mishi ai already tana zuwa…gaba daya haushi takeji that daddy zai dinga hadata da wnn mutumin…ko a inama ya sanshi har ya yadda dashi haka oho?.
Yau Thursday suna zaune class dinsu tana koya ma wasu assignment kiran daddy ya shigo wayanta…excusing kanta tayi tareda daukan wayan tana gaisheshi..bayan ya amsa yace mata”where are u now?..”tace”ina class daddy”..yace”kinje kin gaida Attahir?..”shiru tayi tanaso ta gane waye Attahir yace”ur proprietor”…da sauri tace”eh..aah banje ba..amma zanje sai mun tashi daga class”..yace”to idan kinje ki hadani dashi a waya”..bai jira cewarta ba taji ya kashe wayan…tabi wayan nata da kallo tana mamakin abunda yace..tadai san bai yiwuwa ace har yanxu Bobby bai kirashi don akan idonta ranar yace yanaso ya kirashi a wuri so dole yanada number dinshi amma why zaice ta hadasu a waya?..”so yake ya tabbatar da kina zuwa gaidashi ko bakiyi”..cewar wani 6angare na zuciyarta..ta kuwa yi na’am da haka don dai tasan zaiyi wahala ace kiran wayanshi yayi bai shiga ba…komawa tayi suka karasa assignment din kafin lecturer dinsu ya shigo ta nufi office dinshi don tasan idan bata hadasu kamar yanda daddyn yace ba then zasu samu matsala gagaruma…tana isa bakin office dinshi kafin ta shiga secretary dinshi ta bita da wani irin kallo tace”wai ke me kike zuwa yi office din nan ne?..”wani kallo Aysha tabita dashi irin na rainin hankali kafin taja tsaki ta wuce…da sauri ta mike daga inda take tana fadin”ki bari a fada sanar dashi zuwanki kafin ki shiga”…ai ko tsayawa sauraronta batayi ba ta banka cikin office din itama tabita da sauri…tana shigowa secretary din itama ta shigo da surinta…Bobby dake zaune seat dinshi ya daga idanu yana kallonsu..ganin yanda kowacce ke huci yace”bakuda hankali ne?..why zaku shigomin office kai tsaye haka without my permission?..”da sauri secretary dinshi tace”Sir cewa nayi ta jira in fada maka idan kace ta shiga sai ta shigo shine taki tsayawa ta shigo ciki”..juyawa yayi yana kallon Aysha data wani hade rai yace”kan wane dalili zaki shigomin office kai tsaye?..are u mad?..”sake daure fuska tayi tana turo baki tace”raina min hankali zatayi shine kawai na shigo”…tsaki ya saki tareda juyawa ga secretary dinshi yace mata”u can leave”…ba musu ta juya ta fita daga office din…shi kuma ya maida dubanshi gareta fuskanshi cunkus yace”wato ke bazakiyi hankali ba kou?..duk wani abu da bai kamata ba bazaki dena yi ba kou?..”turo baki ta sakeyi tace”Sir ni me nayi?..”kallonta kawai yake yace”oh tambayana ma kike?..to bari na kira mahaifinki na sanar dashi shi sai kiyi masa bayani”…ai tun kafin ya karasa ta karasa kusa dashi da sauri tace”aa dan Allah kayi ban karawa”..harara ya watsa mata bai sake cewa komai ba…ita kuma taja kujera zata zauna yayi saurin katseta da fadin”who asked u to sit?..”ta wani marairaice tace”Sir dan Allah..daddy ne yace in hadaku a waya”…still bai sake cewa komai ba ita kuma ta zauna snn ta fiddo wayanta tayi dialing number daddy…yana fara ringing tasa a speaker snn ta mika mishi…ya kar6a ya wani 6alla mata harara tareda cirewa daga speaker snn yakai kunnenshi..tana ganin yanda har wani sunkuyar dakai yake yayinda suke gaisawa da daddyn…ta lura he have so much respect for him and hakan ko kadan bai burgeta ba don gani take duk ladabin kura ne…saida suka kammala wayan snn ya mika mata abarta yana hararanta yace”wato ce masa kikai kina zuwa gaisheni koh..”sake turo baki tayi tace”ai daga yanxu zan fara zuwa”…ya wani ta6e baki yace”kiyi zamanki bana bukata..now tashi ki bar min office”…mikewa tayi ta sake hade rai fa fita cikin ranta tana ayyana shegen son office inda kasan kanshi aka fara zaman office…komai sai ya wani ce office din,my office sai kace wani yace ba office dinshi bane…batafi 10 mins da fita ba Nur ya shigo office din…ya karasa ciki ya zauna yana duban abokin nashi yace”maza yane?..”Bobby yace”normal..kwana biyu..ya aikin”..yace”aiki fine yanxu ma mgnrshi ne ya kawoni”…Bobby yace”umhum inajinka”…”kan batun Festivities din nan ne”…gyara zama Bobby yayi before saying”ina sane dashi ai..next week za’a fara kou?..”Nur yace”yea and yanxun nayi receiving message daga social department that suna buqatar additional money for the preparations”…buda hannu Bobby yayi yace”then ka basu mana”…Nur yace”dama in fara mgn da kai ne..if kace a basu sai a basu”…wani kallo Bobby ya shiga binshi dashi kafin yace”seriously?..haka ka daukeni dama?..kenan har yanxun ban wuce wnn matsayin a wurinka ba?..”shafa kai Nur yayi yace”sam ba haka bane..kawai dai naga bai kamata in fara amsan kudi without permission dinka ba”..yana rufe baki Bobby yace”gaskia bakayi min adalci ba idan har yanxu baka bar irin wnn tunanin ba..now tashi ka bar min office”…dan murmushi Nur ya saki saying”abun hadda kora kuma?..”Bobby yace”yes tunda baka daukeni bakin komai ba ai banga amfanin zamanka nan ba so kindly leave”..gyara zama Nur yayi hade da fadin”to kayi hakuri ya wuce”…harara ya sake 6alla mishi shi kuma yasa daria yace”da gaske bazan karaba mana..sorry”.
Ranan Friday akayi pasting result dinsu na first semester wurin ya cika fam da jama’a kowa na kokarin duba nashi wanda sukayi passing mata murna while masu resitting suna jimami…Aysha dai na kwance a hostel dan ko fitowa batayi ba sai Billy ce tayi kokarin duba musu da taimakon Sa’eed sbd turereniya akeyi sosai a wurin…bayan ta samu fitowa daga hayaniyar ta samu waje ta zauna tareda dialing number dinta…cikin muryan bacci ta daga da fadin”Hello”..Billy tace”so u are still sleeping”..tace”eh mana ban dade ma da kwanciya ba”…cikin excitement Billy tace”anyi pasting results yanxun nan and gues what?..”a hankali tace mata”what?..”da sauri Billy tace”as usual ke kikayi overall..and this time around bestynki ma yayi abun kirki”…daria ta saki dukda baccin dake idonta tace”kema dai kinsan my besty is always intelligent kece dai kawai baki ganin haka”…ta6e baki Billy tace”oho ku kuka sani..am hanging up now”..da sauri Aysha tace”wait..baki fadamin naki ba ai”…wani murmushin Billy ta saki kafin tace”congratulations to me..inada 4.55″..tun kafin ta rufe baki Aysha ta saki wani ihu tana fadin”are u serious Billy?..gaskia am very happy bari in kira besty this calls for celebration”…murmushi Billy ta kara saki tana jin yanda take farin ciki ko nata result din bataima wnn murnan ba koda yake idan da sabo ai ya kamata abun ya zaman mata jiki dan tun shigowarsu college din bata ta6a scoring below 5 points ba…kafin ma ta jira jin ta bakinta tayi hanging kiran and for sure tasan bestyn nata zata kira kamar yanda ta fada.
Bobby da bai samu shigowa college din da wuri ba sai after jumu’at prayer motanshi na shigowa ya hangi crowd din dake wajen sai ya tuna ashefa Nur ya fada mishi cewa yau zasu kafe result…daga dan gaban inda aka kafe result din ya hango katon banner da suke kafewa duk shekara na best students of the year kowa da grade dinshi da department sai kuma picture dinshi a jiki…driver bai karasa inda ya kamata yayi parking ba yace ya saukeshi nan wurin..ba musu yayi parking daga gefe kafin ma yazo bude mishi kofan ya bude ya fita…inda aka manna babban banner ya nufa…haka nan yaji yanason ganin da akwaita a jiki ko babu…aikam yana karasa yayi ido biyu da pic dinta tana sanye da uniform da glasses dinta a ido…qasan pic din nata ya kalla baisan time daya wara idanu yana sake kallon points din nata ba…gani yake kaman karya ne bazata iya scoring wnn points din on her own ba…hoton su biyu ne kadai a jikin banner daga ita sai Sa’eed da yayi overall a Nursing department…dukda baisan yaron ba amma ya jinjina mashi sosai dan points ba kadan ba shima yakeda…ita kuwa nata har yanxun bai gama yadda ita taciyoshi da kanta ba…bayan ya gama kallon ya shiga takawa a nutse zuwa office dinshi saidai kafin yakai office din kusan mutum uku sukazo suna gaisawa dashi snn suka nufi office din tare…deep down wani irin feeling yakeji…like gaba daya sai baiji dadin ganinta da yayi jikin banner ba…not because yana mata bakin ciki but because yana ganin yin hakan kaman talla ne akeyi da ‘ya’yan mutane tunda yasan yanxu duk wanda ya shigo college din sai ya gani and hakan will make her popular da bai zama lallai parent inta su so haka ba..especially ita da dama ba wani cikakken nutsuwa gareta ba…ya fuskanci kanta na rawa shiyasa ko mahaifinta baya sassauta mata…har ya isa office dinshi bai bar tunanin ba and yanaso yayi ma Nur mgnr kuma yanajin tsoro kar yazo yayi misquoting dinshi amma seriously baiji dadi ba sam…sai yakejin kaman yaje ya yageta daga wurin amma ba hali…hakura yayi da yima Nur mgnr saidai ya kudirce a rai kafin next year zai samu yayi mgn dashi kawai a hakura da banner ma gaba daya…sam baiga amfanin yin hakan ba…dukda ba yanxu aka fara ba amma wnn karon kam abun baiyi mashi dadi ba.