Dr. BOBBY COMPLETE HAUSA NOVEL

Dr. BOBBY COMPLETE HAUSA NOVEL

Shirye shirye sukeyi sosai for the upcoming Annual Festival da ake gabatarwa cikin college din every year…shiri ba daga 6angaren students ba ba kuma daga 6angaren social department ba…week guda suke cinyewa suna abu guda and wnn year din ma kaman ko wacce shekara sun gama tsara duk yanda festivities din zasu kasance…ranan farko daya kama Monday zasu gabatar da dramas da wasu daga cikin students din zasu gabatar..da akwai English drama sai Hausa drama…rana na biyu kuma zasuyi cultural activities rana na uku ne ake inviting mawaqa daban daban suzo suyi performing a wurin sai rana na hudu wich is Thursday zasuyi Public Lecture and Fun Walk ma’ana za’ayi picking one among cututtuka da suke damun mutane a wnn lokacin sai daga cikin doctors da ake inviting zuwa wurin suyi fashin baqi akan cutan bayan an gama sai su fita fun walk dasu police bands da masu dj suna tafe suna waqa da rawa zasubi ta cikin gari har zuwa state road snn su dawo college din a qafa…ranan Friday wich is the last day of the festival sukeyin sport activities such football,volley ball,table tennis,snooker,basket ball dama sauran wasanni na maza dana mata.

Ranan Monday wich is the first day if the festival wurin 10 na safe auditorium dinsu na cike da students,doctors da kuma manya manyan baqi from every angle na kano da akayi inviting dinsu…kowa yana zaune a respective wurin da aka tanadar musu…mike na hannun mc yanata welcoming baqi tareda sanarwa cewan a jira wanda zasu gabatar da drama zasu bayyana in few minutes time…daga can waje masu yin draman ne a tsatsaye suna mgn da wani daga cikin organizers na festivals din…ba anko sukayi ba amma kowa cikin yayi kyau in his own way…saida ya gama musu karin bayani kan abunda zasuyi snn yace su shiga audit din…suka jera kansu a layi snn dj yasa musu waqa suka fara shiga wurin…Aysha na tsaye a gaba tana rikeda katon sign board da aka rubuta day 1 English and Hausa Drama…suna shigowa wurin ya kaure da sowa da tafi kowa sun burgeshi…Dr.Bobby dake zaune inda aka tanada domin shi a hankali ya dago idanunshi ya kallesu…as always idanunshi ita suka fara hango mishi…tana sanye cikin riga da straight skirt na atampa red da touches din black leaves a jiki…ta daura dankwalinta irin daurin da ake cewa Zara Buhari ta fito da gashinta ta qasan daurin snn ta kalmasheshi ya tsaya a wuyanta…daga bayan skirt din nata an dan tsagashi kadan ta kasa sbd yayi mata dadin tafia…takalmin kafanta flat ne sosai black sai veil dinta da tasa a kafadanta shima black…sai wrist watch da dankunnenta suma black…batasa sarqa ba dan haka fair wuyanta yana nan sai daukan ido yake…a hankali take takawa tana rikeda sign board a hannunta sai murmushi take dimples dinta na fitowa…wani irin abu yaji ya taso tun daga kwakwalwarshi yazo ya tokare mishi maqogaro shi bai tafi ba kuma shi matsa ya bashi sararin maqogaron ba…tunda yake bai ta6a tsintar kanshi cikin 6acin rai irin wnn ba..har wani zafi yaji yana rufeshi duk kuwa da sanyin ac dake wurin…lokaci daya kanshi yayi wani mugun sarawa kaman zai tarwatse..har yanxun kuma ya kasa dauke idonshi daga gareta har suka karasa suka zauna…lumshe idanunshi yayi yana karanta innalillahi a cikin ranshi wai ko zai samu sassauci…kai tsaye kuma yace ga abunda ke damunshi bazai iya ba dan shi kanshi bazaice ga dalilin wnn sudden change din nashi ba…sam baisan yaya zai misaltashi ba…kokari yayi sosai yayi kokarin danne abunda ke taso mishi ganin har za’a fara taron…yana kallo aka fara kiran sunan wanda zasuyi draman kawai ya runtse ido yana addu’a Allah yasa babu ita a ciki saidai kamar jiran addu’an nashi akeyi yaji mc na kiran “Aisha Ahmad Lamido”…sake runste idanun yayi yanajin wnn kuncin da yaketa kokarin 6oyewa yana sake neman hanyar dazai fito amma bai bashi dama ba dan kara dakewa yayi sosai wnn karon har yana dan muzurai snn ya bude idon…baisan ko shi yake kai idanunshi gareta ko kuma idanun ne ke kai kansu gareta ba dan yanxun ma ita ya sake gani bayan ya bude idon…karasawa sukayi suka zauna inda aka tanada domin yin draman…acting zasuyi itada Sa’eed matsayin mata da miji Billy kuma kishiyarta a cikin sauran kuma akwai yara snn akwai set of another couple da dai sauransu…cikin kwarewa da nutsuwa suka fara gabatar da draman nasu na English knn…wurin sai yayi tsit banda voices dinsu ba abunda akeji…gaba daya sun saki jiki suna acting dinsu sosai dan babu wanda zai gani yayi tunanin ba gaske bane sai wanda ya sani…dama kuma sunyi rehearsal sosai shiyasa basu samu wani problem ba…Bobby kuwa tunda yake bai ta6a sanin da akwai kunchi irin wnn yakeji a yanxu ba…kallon yanda suke acting itada Sa’eed kadai yasa yaji kaman zazzabi na neman kamashi…baisan meyasa yake feeling what he’s feeling ba…baisan why zai damu da rayuwar yarinyar nan ba…”sbd amanarta da mahaifinta ya baka”..cewar wani sashe na zuciyarshi…babu wata wata kuwa yayi na’am da wnn amsa don yasan da gaske kuwa ba abunda ya hadashi da ita bayan wnn…da wnn amsa na zuciyarshi ya dan samu sauki kadan daga cikin abubuwanda ke damunshi…haka yacigaba da daurewa yana kallonsu har wani murmushin yake yakeyi sbd kar mutane su dago halin da yake ciki…draman nasu ya dauki kusan one hour kafin su gama…wanda zasu gabatar da na Hausa akace su zama ready kafin mc yacigaba da surutanshi…sauran kuwa tafi aka shigayi musu sosai dan ba wanda basu qayatar ba a wurin Bobby kam shi kadai yasan halinda yake ciki…bayan lokaci mai tsayi masu draman Hausa suka shigo and to his biggest suprise wnn karon ma da ita a ciki…lokaci guda face dinshi ya sauya yana kokarin mance jarumtar da yace zai nuna…wnn karon kuma matsayin budurwar wani ta fito hakan kuma ya 6ata masa rai fiyeda tunaninshi…haka nan ya sake daurewa ya kalla har suka gama amma fa kafin a gama ya saki tsaki yafi cikin carbi…6acin ranshi kuwa ya ninka na dazu ninki ba ninki…gaba daya yaji zaman wurin ya gallabeshi burinshi kawai a tashi ya samu yarinyar can ya zabga mata rashin mutunchi…kwata kwata baisan dalilinda yasa bayason ganinta cikin irin wadan nan abubuwan ba…bayan sun gama masu jawabi duk suka tayi sukayi kayansu…wanda zasu bada kyauta ma duk suka bayar and Lamido na daya daga cikin wanda suka samu kyautar 50k da wani attajirin mutumi ya bayar…ran Bobby idan sun kai dubu duk a 6ace suke…ji yake inama yanada hali ya kar6e kudin daga hannunta gaba daya sai yaga ta gidan uban da zatayi amfani dashi dan yaga sai wani fara’a take tana jujjuya ido ita bata yadda ba celebrity…InShot har aka tashi daga wajen Bobby baisan ina kanshi yakeba…a zafafe ya koma office dinshi ya dauki waya da niyyan kiran secretary dinshi tasa a nemo mashi ita nan take kuma wani tunani yazo masa…”to idan na kirta ince mata me?..”ya fada a fili kaman he’s talking to someone…nan take kuma ya shiga girgiza kai yana fadin”no yanxu idan na fadi wani mgn tana iya misquoting dina ma tunda ba hankali gareta ba”…ya sake fadama kanshi…can kuma yace”amma ai sbd babanta zanyi hakan kou?..”yayi shiru kaman yana sauraran amsan da zuciyarshi zai bashi kafin yace”No I won’t talk to her…wai ma ina ruwana da ita taje taita haukanta mana is not as if i care”…ya fada yana daddaure face dinshi kaman tana zaune nan kusa dashi…da wnn shawara yayi amfani don bai kiratan ba a cewarshi wai baison raini…haka yayi dakon bakin cikin daya kwasa ya kaishi gida su Mummy sukaita aikin fama.????

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128Next page

Leave a Reply

Back to top button