Dr. BOBBY COMPLETE HAUSA NOVEL

FCNM Female Hostel,Apartment C Room 2a.
Zaune take tsakiyar gado ta zuba tagumi da duk hannayenta…gaba daya hankalinta naga Macbook dinta dake ajiye gabanta suna video call da yan gidansu…kana ganin yanda ta daure fuska take faman turo baki zaka fahimci fada akeyi mata…fara ce sosai kamar ka tabata jini ya fito kuma kallo daya zakayi mata ka gane Fulani blood ke running a cikin veins dinta dan she is full blood Fulani of Gombe state…face dinta daukeda siririn pointed nose da cute red lips masu masifar kyau sai kuma sexy idanunta da suke nan farare tas dasu kaman na larabawa…gashin kanta nada tsawo sosai tayi parking dinshi a tsakiya ta saki jelan nata yawo a gadon bayanta…red jessy ne a jikinta mai daukeda tambarin Manchester United a kirji sai black trouser dinta three quarter…daidai da bedsheets da pillow case dake shimfide kan bed dinta Red ne mai daukeda tambarin Manchester United ko ta ina…wnn alama ne na she is a die heart fan of MUFC…babu dankwali ko hula a kanta hakan kuma ya bayyanar da silky black hair dinta da yake nan a barbaje…ganin yanda ta bada hankalinta kacokam ga vidoe call datake yasa nima na karasa dan inga da wanda take magana…wata mace ce da kallo daya zakayi mata ka gane mahaifiyarta ce sbd tsananin kama da sukeyi da ita…hatta dimples dinsu da yake lostawa duk sukayi motsi da cheeks dinsu iri daya ne…dukda ba a zahiri nake ganinta ba dimples din are so visible da kana dora idanu a kanta zaka gansu…cikin fushi takeyi mata fada snn ta karkare da fadin”kuma wlh duk na sake jin ance kinyi irin wnn rashin hankalin sai ranki yayi mummunan baci tunda ke har yanxu bazakiyi hankali ba…kece babba amma kullum rashin hankalinki karuwa yake…na tabbata ko Yusra da take karama bazatayi wnn iskancin da kikeyi ba kawai sbd zaayi maki allura sai kiyita zubama mutane ihu kina musu kuka sai kace karamar yarinya?..dont worry daddynku yana dawowa dama zan fada masa ga abunda kikeyi a makaranta”…tunda Mom dinta ta fara fada batace wani abu ba sai yanxu…hankali a tashe murya tamkar zata fashe da kuka tace”Ammi dan girman Allah karki fadama daddy kinji wlh bazan karaba…Ammi kinsan yanda allura yakemin shiyasa nayi kuka wlh amma i promise bazan kara ba pls pls plssss”..ta karasa mgnr hawaye na wanke mata fuska…tasan muddin mgnr nan yaje kunnen daddy ta gama yawo…ta sanshi sarai mutum ne shi mai zafi shiyasa baya daukan nonsense kuma ta tabbata idan yaji mgnr nan yana iya zuwa har Kano yayi maganinta tunda tun tasowarta ake wnn rikicin da ita akan allura…tun tana yarinya dama duk zaayi mata allura saidai ya tsaya a gabanta rikeda bulala snn zata yadda…har zuwa yanxun kuma ta kasa sabawa dashi…tana rufe baki Ammi tace”to wlh na sakejin mgn makamancin haka sai kinci ubanki kuma itama Bilkisun zan fada mata duk kika fara period sai su barki da abunki tunda ke har yanxu bakisan annabi ya faku ba”…da sauri ta sake cewa”am sorry ban karawa”..Ammi bata sake cewa komai ba sai tsaki data saki tareda mikama sisters dinta dake zaune tun dazu suna jira suyi mgn da ita Macbook din hannunta kafin ta fita daga parlorn…da sauri ta goge hawayenta dan bataso su gani…immediate sister dinta mai suna Husna ta shiga duban screen din fuskanta da wani murmushi tace”hajia Adda mai kukan allura”..da sauri ta dago idanunta tana watsa mata harara tace”so na zama abokiyar wasanki ko Husna?..raini ya fara shiga tsakanina dake ba?”…Husna ta shiga girgiza kai tace”kai Adda dan Allah nidai bance haka ba…kawai dan nace mai kukan allurr”..bata karasa ba ta daka mata wani hadadden tsawa tace”Husna kina hauka?..ni kike fadama mgn haka koh?..”Husna tayi shiru tana duban yar uwar tata baki a tsuke tace”Allah ya baki hakuri..laifina ne ma dana dage sai nayi mgn dake..sai anjima”..daga haka ta mike da sauri ta ajiye Macbook din ta tafi dakinsu abunta…Yusra ta matso da fara’arta sosai tace”Adda don’t mind her kinji?..she is not a good girl”..lokaci daya murmushi ya maye gurbin face dinta tace”of course she is not habibty..how are you?..”Yusra tace”ina lafia Adda..ya karatu”…saida ta dan bata rai snn tace”karatu ba dadi habibty kuma ina missing dinku sosai”..tace”muma muna missing dinki Adda amma Hammanmu yace duk zai sake zuwa wurinki damu zaizo”…tace”to shikenan habibty i can’t wait to see you…yanxu ki bama Hamma Macbook muyi mgn dashi”..ba musu ta mike zuwa inda Hamman nasu ke zaune yana sararonsu ta mika mashi MacBook din…yana amsa yaja cheeks dinta tareda mikewa ya fada dakinsa…saida ya zauna akan bed snn ya daidaita screen din yana dubanta da kyau yace”so you are done”…tana wani tale baki tace”Hamma Ammi kaman zata cinyeni sbd fada…hadda cewa saita fadama daddy nidai dan Allah kace mata kada ta hadani dashi kaji”…murmushi ya saki yana cigaba da kallonta yace”ai ke dince Maama bakya jin mgn…na rasa gane wane irin tsoro kikema injection da duk akazo yi miki sai kin tarama kanki jama’a sai kace ba health personnel ba”…tana sake turo bakinta tace”Hamma dan ina health personnel dole sai naso allura ne?..”yace”ya kamata kiso ta mana tunda kina yiwa mutane”..ta rungume hannunta a kirji tana girgiza kai tace”nidai aah wlh..dan inayi bashi yake nufin dole nima sai anyi min ba…yanxun yaushe zakazo ka ganni kaga fa yau almost 6 weeks knn baka zo ka ganni ba”..yana murmushi yace”i will come inshaAllah nima ba karamin missing dinki nakeba…aiyuka ne kawai sukamin yawa suka hanani zuwa ganin qanwata”…nan da nan ta saki smile daya bayyanar da dimples dinta tace”to yaushe zakazo Hamma?..”yace”zanzo Maama amma ba yanxu ba…kinga wnn week din daddy zai dawo amma inshaAllah yana tafiya zamuzo har su Husna”..tace”to shikenan Hammana thank you”..shima yace”thank you cutie pie amma yanxu qafan ya warke koh?..”tana gyada mishi kai tace”ya warke wlh…kuma ko injection din ma bayamin ciwo kaman yanda yakeyi da…kilan proprietor dinmu bashida zafin hannu”…murmushi kawai Hamman nata yayi kafin yace”ohk ki samu ki kara hutawa yanxu and kice ina gaishe da Billy da kyau”..da sauri tace”zataji inshaAllh…besty fa?..”saida ya danyi jim snn yace”shima ina gaisheshi”…ta sake amsawa da zaiji snn sukayi sallama…ta ajiye Macbook dinta a gefe tana sauke ajiyar zuciya tace”Finally”…tana kokarin kwanciya Billy ta fito daga kitchen hannunta rikeda bowl data dama custard a ciki…tana karasowa ta janyo table ta dora mata akai snn tace”ga custard din nan idan zakisha”…Aysha ta dan daga ido ta kalleta sai taga fuskanta daure tace”haba mana Billy…haba my besty..fushin bai kare bane har yanxu?..”harara Billy watsa mata tace”kije ki nemi inda bestynki yake dai amma ba a nan ba…kawai dazu kikasa mutumin nan yayita watsa mana wadan nan shegun idanun nashi masu kama da na aljanu…saura kadan na saki fitsari wlh sbd tsabar tsoro”…Aysha na kokarin fashewa da daria tace”haba Billy fitsari kuma sai kace wanda taga mala’ika”…Billy tace”ba gara mala’ika ba Lamido shi yanada imani snn aikin Allah yakeyi…amma Proprietor fa kullum fuskanshi a haka yake sai kace namijin saniya”…wnn karon daria Aysha ta saki sosai sai kace ba itane me kukan allura ba dazu…saida tayi me isarta tace”wlh ni kaina bansan sanda na shiga hankalina ba…gaskia idanun mutumin nan basuyi ba a rayuwa…kawai kuna hada ido da mutum kiji kmr yayi miki asiri”…Billy ta sauke ajiyar zuciya tace”shiyasa ni ko hanya bana son hadawa dashi ballantana mu hada ido hantar cikina tazo tana kadawa”…kafin Aysha tayi mgn wayanta ya dauki ringing…ta dan tsayar da dariyanta snn tayi picking tareda fadin”my bsty”..a daya bangaren yace”besty ya jikin naki?..”tace”na samu sauki sosai besty”…yace”to Alhamdulillah wajen injection dinfa?..”saida ta kalli Billy taga yanda take ta wani tabe baki snn tace”shima da sauki sosai…Billy tace wai ita bazaka tambayi yanda take ba”…da sauri Billy tace”Allah ya kiyaye yaushe na fada miki haka?..me ma akai akayi wani Sa’eed da har zan damu dan bai tambayeni ba…ya dade baiki tambayata ba wnn matsalarku ce ba nawa ba”…Aysha najin Billy ta fara mgn tayi putting nata on speaker tace”besty kanajin mutumiyar taka koh”…yace”inaji rabu da ita besty duk wnn maganganun da take fada basu kai zuci ba…i know she is boiling inside sbd mai girma Sa’eed bai tambayi ya Bilkisu take ba”…tun kafin ya rufe baki Billy ta sake fadin”nikam Allah yayi min tsari da ganin wnn rana…kudai kuje can kuyita abunku amma bada Bilkisu ba”..Aysha dai na zaune gefe tana sauraronsu tanata yi musu daria…ta kasa gane wnn ‘yar tsama dake tsakanin Billy da Sa’eed tun tale tale…tun farkon haduwarsu basa jituwa sam suna haduwa zasu fara tsokanar juna sai kace mage da bera…Friendship dinsu kuma ba karamin sake karfi yakeyi ba…dukda kasancewar kowa state dinshi daban karatu ne kawai ya hadasu a kano ba karamin shakuwa sukayi da junansu ba…shi Sa’eed dan kaduna ne sunanshi Sa’eed Mukhtar Makarfi…shekarunshi 25 yana karantar basic Nursing a FCNM dukda cewa saida ya kammala Bsc dinshi kawai sbd sha’awan Nursing profession yayi joining FCNM kuma sai Allah ya hadashi dasu…yanxu haka yana final year…Billy kuma asalinta jihar Bauchi…Bilkisu Ibrahim Muqaddas shine cikakken sunanta…she is a 2nd year student of Basic Midiwifery…class dinsu daya da Lamido likewise hostel dinsu..ita kuma Aysha Ahmad Lamido shine complete sunanta…suna kiranta Lamido kasancewar almost kowa a school abunda yake kiranta dashi knn…mahaifinta bafulatani ne Alhaji Ahmad Adnan Lamido shine present deputy controller general na Nigerian Custom Service snn shine ‘da na biyar cikin jerin ‘ya’yan Lamidon Gombe Alhaji Muhammad Adnan Lamido…mahaifiyarta kuma Maimunatu itama asalin bafulatanar Gombe ce…yara uku garesu Aysha itace babba sai Asma’u da suke kira Husna sai kuma Yusra data kasance ‘yar auta…shi Kuma Hamma Najeeb cousin brother dinsu ne da mahaifinsu ya rike tun kafin a haifi Aysha shiyasa suka saba dashi sosai dan idan ba fada akayi ba bazaka taba tunanin Cousin dinsu bane.
Wnn knn…