Dr. BOBBY COMPLETE HAUSA NOVEL

The next day which is Wednesday ranan ne ake inviting mawaqa from different states suzo suyi performing a makarantan…Bobby na kwance tun safe a daki ko parlor ya kasa fitowa…kawai jin jikinshi yakeyi wani iri that har yake tunanin kilan hakura zaiyi da shiga college din nan kawai…dukda yayi mata mgn jiya and yanada tabbacin ta tsorata sai yakejin kaman yayi zamanshi a gida or better still ya tafi Hospital dinshi kawai ba sai yaje ba balle yaga abunda zai 6ata mishi rai…haka yayita kwance a daki bai fito ba saida Mummy ta aiko a kirashi…yana saukowa daga gado ya fada bayi yayi wanka snn ya fito ya shirya kanshi cikin wata armless shirt da wando three qtr snn ya nufi parlor…parlon Mummy ya samesu zaune gaba daya as aunty sumy na gida itama ranan bataje aiki ba Miemie ma bataje sch ba sbd fever data kwana dashi ita kuma ilham tun 1 aka tashesu…karasawa yayi ciki ya zauna da igbo ya gaida Mummy itama ta amsa da igbo snn tayi adding da”yau baka fita ne naga har yanxu baka shirya ba?..”dan ta6e baki yayi yace”i just don’t feel like going out..i think zamana zanyi a gida in huta”…Aunty Sumy tace”aikam bai kamata kaki zuwa ba Bobby..remember it’s a Festival week and abune wanda yake taking place once in a year sai nakega kaman bai dace kaki zuwa ba ko don sbd guests dinku”…Mummy ma na gyada kai tace”sumayya gaskia ta fada Bobby”..shiru yayi cikin ranshi yana ayyana bazaku gane bane…abun kaman hadin baki kawai sukaji sallamr Nur a parlon…Bobby ya kulle ido tareda fadin”the fool is here..nasan yanxu ko banida intention din fita saina fita ko don nacinshi”…daria Mummy sa aunty sumy suka saka jin abunda yace…Nur daya karaso ciki ya zauna ya shiga gaisawa dasu Mummy shima cikin igbo…aunty sumy tace”wlh har mantawa nake Nur yanajin igbo sbd bai cikayi ba unlike abokinshi da mgn daya biyu sai ansa igbo a ciki”…murmushi Nur yayi yana shafa kanshi yace”wlh ni kaina ina manta inajin yaren aunty…gaba daya hausawa sun janyeni”…daria suka sake yi Mummy tana ai dole hausawa su janyeshi tunda yake zaune a kano…bayan sun gama Nur ya juya yana kallon Bobby kafin yayi mgn Bobbyn ya mike yana cewa”ba saika 6ata bakinka ba nasan meya kawoka..ka bani just 5 mins zan shirya in fito”…daria gaba daya suka kara sawa Bobby ya wuce flat dinshi…aunty sumy tace”Nuru kai kadaine maganin Bobby gashi tun kafin kayi mgn an tafi shiryawa”…dariyan shima yasaka yace”kinsanshi baya son naci ai..ni kuma indai inason yayi abu bana barinshi har saina samu abunda nakeso”…bayan 5 mins ya fito a shirye kaman yanda ya fada…Nur na ganinshi ya mike yana sallama dasu Mummy Ilham tace”uncle bobby inaso inje plss”..kallonta bobby yayi sai kuma yace”no kiyi hakuri sai gobe kuje tareda su aunty kinji”..makale shoulder dinta tayi tana fadin”oh oh inaso inje yau”…kallonta kawai yakeyi totally speechless..shi ba son zuwan nan nasu yakeba wlh..ko gobe da aunty sumy tace zasuje suji lecture da za’ayi ba so yakeyi ba…Nur da yaga tana shirin sakin musu kuka yace”zamuje dake baby don’t cry”…nan da nan ta washe bakinta tana tsallen murna…”uncle Nur”..yaji Miemie ta kira sunanshi…a hankali ta juya yana kallonta sai yaga tayi narai narai tana kallonshi…murmushi ya saki dan ya gane mgn take mishi a haka..so take taje itama and tana tsoron furtawa sbd Oga Bobby kada ya hana…saida ya dan saci kallon Bobbyn snn ya dubeta yace”kema zakije kou?..”daga mishi kai tayi da sauri..yace”to je dauko mayafinki”..da sauri ta mike zuwa dakinta ta dakko veil da phone dinta ta fito…Bobby da haushi ya isheshi ya bude baki zai fara masifa Mummy tace”don’t say anything plss..kuje dasu su gani ai ba dadewa zaayi ba”..gum ya maida bakin nashi ya tsuke ba tareda ya fadi abunda yayi niyya ba…sallama sukayi musu suka fita Bobby ya shiga motanshi tareda driver da kuma ilham shi kuma Nur ya dauki Miemie a nashi motan suka tafi.
Tsaye take gaban mirror dinsu tanata kallon kanta kaman bata ta6a ganin mirror ba…straight gown ce a jikinta na wani lace mai kyau..dinkin yabi jikinta ya kwanta luf luf hakan kuma ya baiyanar da beautiful figure dinta…daurin dankwalinta Zara Buhari as usual gashinta ya leko ta karkashin daurin..gaba daya ranta ba dadi duk ma tasan ba jin dadin yau din zatayi ba sbd Bobby..duk ta tuna kashedin da yayi mata jiya na idan tayi wani abu zai hadata da daddy sai taji kaman tasa kuka wlh…yanxu haka yakeso taje tayi zaune a wurin tayita kallonsu knn ita bazatayi rawa ba…da yasan yanda take kaunar rawa da baiyi mata haka ba wlh..kawai rawan yakema bala’i jiya kaman zuwa tayi club ta kwana…Billy ta shigo dakin tana sanye cikin kayanta irin na Aysha sak har dinki da daurin dankwalinsu iri daya…batace mata komai ba ta karasa cikin dakin ta dauko veils dinsu da suke zube kan bed dinta ta hada da wayoyinsu snn taja hannun Aysha suka fita daga dakin…binta kawai takeyi har suka isa compound snn ta saketa ta mika mata veil da wayanta ba musu ta kar6a ta yafa itama Billy ta yafa nata snn tace”nasan in muka daka ta taki zamu iya kwana nan ciki baki gama kallon madubi ba..na fada maki idan kika kiyaye babu abunda ya isa ya maki amma har yanxun kinki kwantar da hankalinki”..juyawa Aysha tayi tana kallonta kaman zatasa kuka tace”yandu fisabilillahi saidai inje inyi zaune kaman gunki ni bazanyi abun arziki ba?..ai wnn rashin imani ne wlh”..ta karasa mgn hawaye na cikowa idonta…daria yaso kufcewa Billy amma ta gimtse suka fita daga wurin…inda Sa’eed ke tsaye suka nufa kafin su karaso ya bude musu mota Aysha ta shiga gaba Billy kuma baya snn shima ya shiga ya tayar da motar suka tafi…a hanya ya dubi bestyn tashi yaga fuskan nan cunkus sai ya kallo Billy ta mirror yace”waya ta6amin besty ta?..”daria Billy ta saki tace”akan mgnr jiya nefa”..dan murmushi shima ya saki yana kokarin controlling dariarshi yace”besty har yanxu mgnr rawan ne dai?..”a fusace ta juya tana kallonshi tace”malam ba ruwanka dani tunda biyewa Billy kake kunamin daria…kawai sai inje inyi zaune ni bazanyi rawa ba sbd rashin imani”…ta karasa mgn hawaye na sake ciko eyes dinta…wnn karon kasa 6oye dariar sukayi dan dagashi har Billyn basu san sanda ta fito ba…daria sukeyi sosai sai kace ta6a66u Aysha kuma ta shaqa iya shaqa kawai sai ta rufe fuska da hands dinta ta wani rushe da matsanancin kuka…ganin kukanda take sai darian ya sake zuwa musu aikam sukaita yinshi knr sabbin kamu saida sukayi me isarsu snn suka bari…Sa’eed ya dan juya yana kallonta with a little smile yace”besty dan Allah kiyi hakuri kinji..nifa bake nakewa daria ba”…yana rufe baki Billy ma tace”nima na ranste ba dake nake ba dan Allah ki bar kuka”…ai kaman ma sunce tacigaba don kara sautin kukan tayi hadda su buga kafafu a kasa ba shiri Sa’eed ya gangara gefen titi yayi parking…juyawa yayi yana kallonta ya wani marairaice yace”yanxu besty dan girman Allah bazakiyi shiru ba?..nace fa am sorry kuma da gaske ni ba dake nake ba”…banza tayi dashi tana cigaba da kukanta…yana mata ciwo idan ta tuna saidai kawai taje wurin a matsayin hoto bazatayi rawa ba…gashi ance hadda favorite mawaqinta aka dauko Ado Gwanja kuma ace bazatayi rawa ba ai wlh an cuceta…wayanta dake ajiye kan dashboard ne ya fara ringing Sa’eed yakai hannu ya dauka ganin yanda tayi banza da wayan…Baby boo ya gani kan screen din dan haka ya juya screen din yana nunawa Billy..da sauri tace”yauwa dauka kace masa yazo ya rarrashi kayarshi tunda mu taki ta sauraremu”…ba musu Sa’eed yayi sliding tareda sawa a speaker…on the other side Prof Ahmad yace”my baby girl”…hada ido Sa’eed sukayi da Billy suna kunshe daria kafin ya maze yana cewa”ahm ba ita bace sunana Sa’eed”…Prof yace”ai besty zaka cemin yanda zanfi ganewa”…Sa’eed ya kara sakin murmushi before yayi adding”besty ce dama tun daxu take kuka wlh kuma munyi iya bakin kokarinmu taki tayi shiru”…hankalinshi har ya fara tashi yace”wait voice dinta ne nakeji tana kuka yanxu?..”da sauri Sa’eed yace”itace wlh…mun rasa yanda zamuyi da ita”…Prof yace”bata waya muyi mgn”…ba musu Sa’eed ya ajiye wayan kan laps dinta…voice dinshi taji yana fadin”hello baby girl”…dan dakatar da kukan tayi tana goge tears dinta tace”umhum”..yace”why are u crying baby girl..waya ta6amin ke?..”saida ta sake goge tawagar hawaye da suka biyo fuskarta tace”ba komai”…yace”no ban yadda ba baby kodai inzo ne?..”girgiza kai tayi tace”aah..”yace”then promise me u will stop crying inba haka ba kuma am coming”…a hankali tace”I promise”…yace”yauwa my little baby girl i love u kinji?..and zanzo da daddare sakin fadamin wanda yasa babyna kuka”…kai take gyadawa kaman yana ganinta kafin tace”toh..”yace”ohk bye”…itama tace”bye..”snn ta ajiye wayar…Billy da Sa’eed hanci da baki suka saki suna kallon ikon Allah ganin har ta dea kukan kaman ba itane suke roki ta dena ba amma taki…bata kalli kowadaga cikinsu ba ta maida kanta jikin window…suma basuce mata komai ba as suna tsoron su sake mgn ta kuma langabe musu Sa’eed ya koma seat dinshi ya zauna snn tada motar suka karasa cikin makarantan.