Dr. BOBBY COMPLETE HAUSA NOVEL

Wucewa sukazo yi ta daidai inda suke tsaye da alama wani suke jira…Bobby rikeda hannun Ilham Miemie kuma na tsaye kusada Nur don ko kadan batason hada ido da Bobby data tabbatar haushinta yakeji for following them…Bilkisu da Sa’eed ne suka fara tahowa suna zuwa inda suke gaishesu snn suka wuce ita kuma tana baya dan cewa tayi bazata jera dasu ba…ganinshi tsaye a wurin ta sake dinke fuskanta tsaf tana cigaba da tafiya kaman batasan suna wajen ba…kafin ta wuce Nur ya kira sunanta”Lamido”…a hankali ta juya tana kallonshi with a little smile kan face dinta tace”Sir good afternoon”..yace”afternoon ya gajia”…murmushi kawai tayi batace komai ba…Miemie da a kallon farko taji ta burgeta sbd kyanta itama ta gaisheta..Aysha ta amsa ta murmushi tana mamkin inda provost ya samo yarinyar me kyau haka…so tayi ta wuce batareda ta gaishe da Bobby ba amma sai taga bai dace ba kuma yana iya hadata da daddy dan haka ta dan juya tana kallonshi a kaikaice fuskan nan ba fus tace”ina yini”…ko kallon inda take baiyi ba balle ya amsa mata…ita kuma jin yayi shiru ta daga ido sai taga wayanshi ma yake dannawa aikuwa ta daddage ta murguda masa baki sai kuma karaf a idanunshi…idanunta na sauka cikin nashi tayi kasa da nata da sauri…kallonta yayi for like 2 minutes snn ya dauke kai…ita kuma juyawa tayi zata tafi Ilham da har yanxu ke rikeda hannunshi tace”Ehihie Oma”…juyawa Bobby yayi yana kallonta da mamaki jin tayi mata igbo..kafin yayi mgn Aysha data juyo itama tana kallonta with smile tace”hey I don’t understand igbo…how are u”..ilham ta saki murmushi tace”am fine”…Aysha ta gyada kai dan yarinyar sosai ta burgeta sai ta ganta kaman Yusra don itama akwai surutu…tace”ya sunanki?..”da sauri ilham tace”sunana Nadia amma ilham ake cemin..mamana kuma sunanta Sumayya muna cemata aunty…wancan kuma sunan…”bata karasa ba Bobby ya toshe mata baki yana hararanta yace”and who asked u all these?..”turo baki tayi tace”Uncle Bobby let me finishi plss”…bai bari ta sake mgn ba ya kama hannunta suka bar wajen…Aysha ta bisu da kallo tana hararan bayanshi kaman idanun zasu fado…tsaki taja tacigaba da tafia itama…tana shiga inda hall din yake kafin ta karasa Bobby dake tsaye yana jiran shigowanta yace”come here”…juyawa tayi a tsorace tana kallonshi don batasan da mutum ba a wurin…ya wani hade rai yace”bazaki zoba?..”turo baki tayi ta wuce inda yake…tana karasawa ta rungume hanu tana ciccin magani and hakan bai dameshi ba ya nuna gashinta dake a waje fuska babu alamun wasa yace”maida wnn gashin da kika fito dashi”…dagowa tayi ta kalleshi hawaye har sun ciko idonta sbd haushi…har yanxu idan ta tuna batada daman yin rawa a wurin nan sai taji kaman ta shakeshi ya mutu…ganin yana mata wnn kallon da bata so takai hannu ta tura gashin nata ciki…ya bita da wani irin kallon kafin yace”now leave”…ba misu ta juya ta tafi daga wurin hawayen dake cikin idonta na gangarowa kasa…shima ya kama hannun ilham zasu shiga saiga Miemie da Nur sun shigo…Nur ya kalleshi da mamaki yace”wai dama baka shiga ba?..meka tsaya yi a nan toh?..”banza yayi dashi yaja ilham suka shiga ciki…shima shiga cikin sukayi yana mamakin abunda ya tsaidashi a waje bayan tun daxu ya shigo.
Rano✨
Wnn littafin na kudi ne ban yadda wani ko wata ya fitarmin dashi ba…masu buqatan siya zasu tura 300 zuwa 2208991344 Aisha Ahmad Tijjani Zenith Bank…sai a tura evidence of payment via 07063800556.
23
Suna nan zaune daya daga cikin mawaqan da sukazo ya fara performance dinshi…hajia Aysha na zaune tana kallo kaman tayi kuka…yana kammalawa favorite din nata ya shigo tareda ganguna da ‘yan rawarshi aikuwa gaba daya hall din ya rude da sowa da tafi…kaman yasan halinda take ciki saida ya samo favorite dinta a cikin waqoqinshi nashi ma snn akayi playing ya fara miming…nan take hall din ya sake rudewa da muryan mata duk suna bin waqar wasu kuma suna zuwa suna mishi liki…itadai tana daga gaba gaba tana kallonsu tanajin ciwon da bata isa ko dan liki taje tayi ba…tana kallon su Billy sukaje sukayi liki snn suka dan taka rawa suka fito…hawaye taji suna ciko mata ido kawai saita rufe fuska da hannayenta tana kokarin mayar da hawayen…Bobby da tun daxun hankalinshi ke kanta daga inda yake yana ganin yanda ta rufe fuska fuska ya wani ta6e baki cikin ranshi yace”ko kukan jini zakiyi bazakiyi rawa a wurin nan ba wlh”…ita kuwa bata ma san yanayi ba saida ta gama goge tears din snn ta bude fuska…daga karshe ma mikewa tayi ta fita a wurin don bataga amfanin zamanta ba…duk akan idon Bobby da kona one second bai dauke idonshi kanta ba sbd yasan tsaf zata iya fakar idonshi ta shige cikin ‘yan rawa idan taga baya kallonta…can waje ta fita ta samu wuri tayi zamanta tana jera masa Allah ya isa a cikin ranta kmr daga sama taji sallaman mutum a kanta..idonta ta lumshe tasan yanxu zuwa zaiyi ya kara mata kan abunda take ciki dan ko ba’a ba tasan shine…muryan kadai taji ta gane Sir Abdool ne…kallon yanda ta kulle idanu yake kafin a hankali yace”may i?..”kai ta gyada mishi ba tareda ta bude idon ba…zama yayi nan kusada ita yana sake kafa mata eyes dinshi yace”Lamido wai bakida tausayi dama?..ace duk tsahon lokacin nan inata faman baki hakuri amma kinki hakura”…bude idon tayi tana dan turo lips dinta tace”Sir nifa ba fushi nakeyi dakai ba”…tana rufe baki yace”idan ba fushi kikeyi dani ba meye wnn toh?..meyasa har yanxun bakya picking calls dina?..”dan juyawa tayi tana kallonshi tadan marairaice tace”da gaske ba fushi nakeyi ba”…yace”then fadamin idan sona ne bakyayi I won’t force you”…sake narkewa tayi tana dubanshi tace”inada wanda zan aura ne”…hannu yakai ya dafe chest dinshi tared runste ido yace”that hurts”…a hankali tace”am sorry”…bude idon yayi yana kakalo murmushi yace mata”as i have said I won’t force u to love me and congratulations to the lucky guy”…dan murmushi kawai tayi batace komai ba..she’s happy yayi understanding dinta…muryanshi taji yana cewa”but akwai alfarma da zan nema wurinki”…tana gyada kanta tace mishi”inaji”..yace”if I can’t be ur lover at least i will be glad to be ur friend”…bright smile ta saki tana dubanshi tace”then we’re friends”…murmushin shima ya saki yace”yes we’re friends..thanks for accepting my offer”…daria kawai takeyi tana kallonshi..taji dadin yanda ya fahimce ta har hakan yaso yawa ta manta baqin ciki hanata rawa da akayi…shima darian yakeyi yana kallonta deep down yanajin ciwon rashin samun soyayyanta amma ya ya ita tunda bata sonshi?..kaman ance ta daga ido sukayi ido hudu da Bobby daya wani hade rai yana binta da tsinannen kallon nan bata qauna…darian da takeyi ya tsaya cak itama ta hade rai tareda dauke idonta daga gareshi…shi kuma wucewa yayi zuwa office dinshi yanajin haushin yanda heart dinshi ke neman deceiving dinshi yana sashi jin abunda sam bai kamata ace yajishi akan jinin Fulani ba.
A takaice ranar haka aka tashi taron nan batayi rawa ba sbd tsoron kar ya fadawa daddy…haka suka koma hostel itada Billy tanata ciccin magani Billy batabi ta kanta ba ta shiga sabagar gabanta…sai dare da babynta yazo snn ta dan samu nutsuwa dan bai bar hostel dinba saida ya tabbata yayi flushing away wnn damuwan da take ciki.