Dr. BOBBY COMPLETE HAUSA NOVEL

The next day around 10 suka fita sbd da wuri ake fara lecture din…dress code dinsu na ranan white ne dan basuyi anko ba saidai ance everybody should wear white cloth…itada Billy black straight skirt suka saka da farar shirt sai farin kimono da suka dora akan kayan itama white da digi digon black a jiki suka yafa black veil…ita Billy tasa turban snn tayi veiling da mayafin while hajia indo batasa komai ba sai dan mayafin data yafa akanta…daidai sa bags da suka rike iri daya ne suma duk farare…suna shigowa cikin school kiran Husna ya shigo wayan Billy nan ta dubi Aysha da sauri tace”Lamido ina tunanin su Hamma fasun karaso kinga Husna na kirana”…Aysha tace”to mu karasa parking space muga ko suna can”..daga haka suka wuce zuwa parking lots din…tun daga nesa suka hango motanshi dan haka suka nufi inda take…Hamman nasu ya shiga binsu da kallo yana murmushi yace”lallai ashe gayunku kawai kukeyi a makarantan bamu saniba”..Aysha tace”kai Hamma meya wani gayu a nan”..yana kallon Billy yace”gayu ne mana..dan bakiga yanda kukayi kyau bane”…kafin Aysha tayi mgn Husna tace”Hamma mudai dan Allah mu karasa ciki kar a fara abun arzikin bamu shiga ba..nasan anjima nayi zaka fara cewa azo a tafi daddy yace kar ayi dare”…murmushi kawai yayi gamida girgiza kai snn suka dunguma zuwa hall din…da yake yau kusan kowa yana inviting family ko friends dinshi sai hall din ya cika yayi taf fiyeda sauran ranakun…wuri suka samu suka zazzauna daga gaba gaba yanda za’ayi komai akan idonsu snn suka cigaba da kwasan hira kaman sun shekara basu hadu ba…suna nan zaune gab da za’a fara Sa’eed shima ya shigo tareda lubna aikam suna ganinta suka mike zuwa inda take sukayi hugging dinta..shi kuma Sa’eed ya karas shna gaisawa da Hamma dasu Husna…bayan sun gama rungume rungumensu suka karasa suma suka zauna Lubna nata jadda musu sai sunzo kd bikinta nanda few weeks sukace zasuje inshaAllah…saida kowa ya gama shiga snn Proprietor,Provost da kuma manya manyan doctors da zasu gabatar da lecture suka fara shigowa…duk yawan jama’an dake wurin baisan meyasa idanunshi suka hango mishi ita zaune a tsakiyar wasu maza ba…ranshi yaji ya 6aci sosai yanxun duk space dake cikin hall din nan ta rasa inda zata zauna sai ta shiga cikin maza?..wai wace irin yarinyace ne wnn?..wane irin shegen rashin hankali gareta?..har suka isa high table da aka tanada dominsu suka zauna bai denajin ciwo ba…sai a lokacin Aunty Sumy dasu Miemie suka karaso…Nur ne ya amsa mike daga hannun mc yayi welcoming guests dinsu snn ya gabatar da sunan disease da za’ayi lecture a kanshi Sickle Cell Anaemia wanda akafi sani da Sickler…tafi wurin ya dauka kowa yana ganin dacewar gabatar da lecture akan Sickler sbd yanda masu ciwo irinshi suke facing challenges a rayuwarsu na yau da kullum…bayan hall din ya danyi tsit ya dora da fadin”and before i hand over the mike to our qualified doctor Olusola Bulus…i will like to invite Aisha Ahmad Lamido for a brief introduction of Sickle Cell Anaemia”…fuska daure Bobby ke kallon abokin nashi ko meye ma’anar hakan da yayi oho?..meye amfanin wani kiranta tayi bayani tunda ga doctor zaiyi lecture a barshi ya gabatar da abunshi mana…Aysha da taji sunanta unexpected kasa mikewa tayi daga inda take zaune…Hammanta ne ya sunkuya yayi mata mgn a kunnenta kan idon Bobby da idanunshi ke wurin…a hankali ta mike daga inda ta fito zuwa kan stage…tana isa ya ba ta mike dake hannunshi ta amsa ta fara da gaishe da manyan baqi da colleagues dinta dake wurin snn ta shiga yi musu brief introduction ko ince explanation na Sickle Cell Anaemi kaman yanda aka bukaceta…ta burge mutane da dama a wurin domin tun daga kan yanda take mgn with courage and confidence zaka san ba karamar mai kwanya bace…uwa uba kuma dressing dinta daya sake fito da ainihin kyawunta hatta yanda take mgn ma abun kallo ne…hall din yayi wani irin tsit ko tari babu sai sweek voice dinta dake tashi ta cikin speakers…bata shiga deep ba ta tsaya iya introduction kmr yanda akace tayi snn ta sake miqawa Nur mike din ta sauka daga wurin..tafi sosai aka shiga yi mata hatta doctors dake wurin saida suka jinjina mata dan tayi kokari sosai ba kadan ba…tana karasawa inda take Hammanta ya mika mata hannu suka tafa and again kan idanun Dr.Bobby da yabita da wani hadadden harara data sauka daga stage…kawai haushi yakeji and ya rasa dalili…gaba daya mutanen wurin ma haushinsu yaji yanaji for clapping mata da sukayi ballantana kuma Nur dashine wanda ya haddasa komai…aunty sumy dake zaune daga dan gaba itama kallonshi kawai take tana mamakin abunda aka mashi yake wnn cin kunu haka…ta lura ko noticing zuwansu ma baiyi ba hankalinshi na can wurinda batasan me yake kallo ba…text tayi typing a wayanta”what’s wrong?..why are u frowning ur face?..”ta tura mashi…wayan na aljihunshi yanajin shigowan text bai duba ba..ta sake tura mashi”Bobbyyyy”…zaro wayan yayi cikeda haushin damunshi da akeyi zaisa a flight mode idonshi ya sauka kan sunanshi data kira…sender ya duba yaga itace sai ya bude message din da sauri shi sam ya mance sunyi mgn daxu tace mishi suna hanya…yana gama karantawa ya daga kai yana duban wurin wai ko zai hangota amma bai ganta ba…text ne ya sake shigowa wayan ya duba sai yaga tace”ba ganinmu zakayi ba kawai ka bar frowning face dinka haka kar guest dinka suyi tunanin wani abu”…ajiyar zuciya ya sauke yana sake wurga idonshi still bai gansu ba dan haka yayi typing”ohk na dena”shima ya tura mata…yana gama tafiya ya maida wayan aljihu yana kokarin daidaita face dinshi kmr yanda tace kar guest dinshi suyi tunanin wani abu…doctor Olusola ne ya fara bayani kan yanda Sickler yake..yanda yara ke samu ta hanyar iyayensu and hanyoyin daya kamata abi don ganin sun zauna cikin koshin lafia…saida ya dauki more than one hour yana abu daya kafin ya gama…bayanshi wani doctor Solomon shima yayi bayani stigmatization da suke fuskanta a society da kuma hanyoyin daya kamata abi don kiyaye wnn stigmatization din and lastly doctor Nuruddeen wato Provost yayi bayani kan hanyoyin da za’abi wajen preventing haihuwan yara masu sickler snn idan an haifesun hanyoyin da za’ayi taking proper care of them tun daga neonatal stage zuwa child har zuwa adolescent…daga nan kuma ya sake mika godia wa duk wanda suka halarci taron a matsayinshi na Provost na FCNM tareda fatan komawa gida lafia…daga nan kuma sai aka hau raba drinks da snacks each table aka ajiye musu nasu snn aka faraci…bayan sun gama Provost ya sake amsan mike yace yanaso su zama ready for the Fun Walk don in the next 10 minutes zasu fita…haka kuwa akayi duk mutane suka fara mikewa suna fita daga hall din…Bobby ma ya taso daga inda yake zuwa inda ya hango su aunty sumy zaune…tun kafin ya karasa Ilham ta mike tana rungumoshi..shi kuma yajata suka karasa wurin yana kokarin dora smile kan face dinshi yace”wai yaushe kukazo?..kinsan banga shigownku ba?..”aunty sumy tace”dama ya zaayi kaga shigowanmu hankalinka na wani wajen..wai mema kake kallo ne kam?..and meya 6ata maka rai da kaketa cin magani haka?..”dan shafa kanshi yayi yace”bafa wanda ya 6atamin rai kawai zaman wajen ne ya isheni..kuma zakuyi walk din ne ko bazakuyi ba”..mikewa aunty sumy tayi hannunta rikeda bag dinta tace”rufamin asiri da wnn tafiyar Bobby..komawa gida zamuyi dama lecture mukazo ji kuma an gama so we are going back home”…gyada kanshi yayi cikin jin dadin tafiyar da zasuyi yace”gara ku koma ai dan wnn walk din wahalar banza ne kawai”..aunty sumy ta wuce suka fara tafia tace”wnn karon ma bazakaje ba knn?..”yace”haba!.Allah ya kiyaye ai bazan iya wnn wahalar ba”..murmushi kawai ta sakeyi batace komai ba…saida ya rakasu har mota yaga sun shiga sun fita daga makarantan snn ya juya zuwa office din Nur don yasan da yawa daga guest din da basu tafi ba suna can…snacks ya samu sunaci da drinks dinsu sunata kwasan hira kaman basu ba…daidai lokacin da ya shiga yaji Gabriel na fadin”ni wlh yarinyar nan cema ta burgeni gaba daya tunda na ganta naji na gagara sukuni…yaya ma sunanta kace?..”yayi referring tambayar to Nur dake sauraronshi yana daria yace”kai wnn yarinyar tafi karfink wlh..Lamido matar manya ce ba yara irinku ba”..daria suka saka Gabriel din na cewa kodai shima Nur sonta yake Nuru yace ai babu mamaki ma idan yana son nata…Bobby dake tsaye jikin kofa yana sauraran conversation din nasu kasa karasawa ciki yayi..haka nan yaji wani irin faduwar gaba dajin abunda Nur ya fada..shi sam mgnr Gabriel bai daukeshi da wani abu kaman na Nur ba..da dadewa dama yana zargin Nur sonta yake and now ya tabbatar da zarginsa..dukda ba fitowa fili yayi ya furta yana sonta ba a iya mgnr daya fada ya fahimci da gaske son nata yakeyi…juyawa yayi ya bar office din yana sakin tsaki a fili ya furta”ko uban me Nur zaiyi da wnn yarinyar oho?..”shidai wlh wnn yarinyar yana ganin ko daura masa ita akayi a kafarsa zai kwance ya wurgar don baiga amfanin auren mace mai shegen rawar kai da kula samari ba..jiya ma ya ganta da Abdool and a yanayin da yaga suna mgn yasan da kyar idan shima ba saurayinta bane..daxun ma ya ganta zaune tsakiyar maza su dinma kuma ba abun mamaki bane idan ance samarinta ne shi kam me zaiyi da mace kaman wnn da take daukan maza kaman ‘yan uwanta mata?..a fili ya sake furta”God forbid”..harda tsartar da saliva.????