Dr. BOBBY COMPLETE HAUSA NOVEL

Bayan few minutes gaba daya wanda zasuyi walk din suka fita masu police band nata kida haka masu dj sunyi playing music sauran kuma ana tafe ana rawa kowa rikeda banner da akayi rubutu a jiki…dukda tafiyan akwai nisa ba karamin enjoying dinshi sukayi ba don suna tafe suna takawa hadda Aysha data gama dubanta tsaf bataga proprietor a wurin ba…duk inda suka wuce anata kallonsu sbd yawansu haka duk titin da suka hau suke rufeshi gaba daya saidai masu wucewa su nemi wani hanyan…suna tafe sunata daukan pics da videos abundai sai wanda ya gani…haka suka gama zagayensu suka dawo college din a kafa.
Suna shigowa college din can bayan classes dinsu dake nan kmr garden suka wuce kai tsaye suka shimfida manyan carpets a wurin snn suka fiddo abincin da sukazo dashi daga gida suka zazzauna nan sunaci sunata kwasan labari…idan kaga yanda suke hira zakayi zaton duk ‘yan uwan juna ne irin wanda suka shaqu da juna sosai…Lubna da Aysha da Billy sunacin nasu tare..Hamma da Sa’eed suma sunacin nasu sai Husna da Yusra…Billy ce kadai ba ‘yan uwanta kasancewar ita kadai ce mace a gidansu duk sauran siblings dinta maza ne…bayan sun gama ciye ciyen sai suka fara daukan pictures da videos Aysha nata ma Hammanta da bayason daukan hoto daria…a takaice basu suka bar FCNM ba sai after five…suka rakasu har mota suka tafi snn suka dawo ciki ya rage daga Aysha da Billy sai Sa’eed da Lubna…daga nan ya kwashesu zuwa hostel don Lubna cewa tayi ita sai dare zata koma gidan Hajia..hakan kuwa akayi don bai dawo ya dauketa ba sai around 9 na dare..haka suka rabu sunata zullumi kaman bazasu sake haduwa ba bayan ko gobe tace zata dawo kallon sports da zasuyi.
Washegari Friday basu fito daga hostel ba sai wajen 11…lokacin already wanda zasuyi sports suna can field sun fara abunsh…karasawa suma sukayi inda babban sports field din nasu yake…waje suka samu suka zauna suna kallon football da maza keyi…Bobby kam zamanshi yayi a gida sam baiyi niyyar fitaba amma yana tuna zata iya zuwa ta aikata wani abunda ba shikenan ba idan baya nan sai ya mike da sauri sairi ya gama shiryawa ya fita…office din Nur ya tsaya suka tafi field din tare…suna karasawa ciki as usual ya hangota zaune tareda Lubna da Billy sai kallon ball suke suna ihu..muryanta mayafi na kowa tashi a wurin sbd bestynta yana kokari…yana daukan ball zakaji ta fara fadin”yes..yauwa besty na go on..yauwaaa”..Lubna sai daria take mata yayinda Billy tace”ai wlh zaki gaji kuwa indai Lamido ce..haka nan take kallon ball dinta tana ihu idan suna abun arziki knn..idan kuma abun tsiya sukeyi tsit zakijita kaman ba itaba”…Lubna dai dukda haka ta kasa dena daria…Bobby da suka zaune opposite dinsu yana kallonta tana ihu sai kace namiji..ranshi ya 6aci sosai ya rasa wace irin yarinya ce ita…yana kallo da aka tafi half time wnn saurayin da sukayi drama tare yazo inda suke ita kuma ta mike da sauri ta mika mishi dan towel ya goge jikinshi snn ta bashi ruwa yasha sai doka masa murmushi take tanajin kaman ta goyashi sbd farin cikin yana performing…yana gamawa ya maida mata towel da goran ruwan snn ya sake komawa ciki…zuwa yanxu Bobby a kule yake tsaf ji yake kaman ya mika hannu ya kwada mata mari..sbd kazanta har amsan towel daya gama goge guminshi takeyi?..wnn wane irin kazanta ne?..duk kokarinshi na yaga ya manta da abun kasawa yayi dan haka ya mike bayan yacewa Nur yana zuwa ya fita daga wajen…kai tsaye office dinshi ya nufa snn ya zaro wayanshi yayi dialing number dinta da ranar yayi saving as Lamid…wayan na cikin jaka yanata ringing bata gani ba shi kuma bai fasa kiraba sai a karo na uku tayi picking…murya a cushe yace mata”come to my office”…zatayi mgn yace mata”now..”da sauri ta matsar da wayar daga kunnenta sbd ihun da yayi…su Billy ta kalla rai a 6ace tace musu zataje proprietor na nemanta daga haka ta fita daga wurin da sauri tana zullumin ko wani abun ta sakeyi…tana shiga office din ya bita da wnn kallon as always..saida ta karasa gaban table dinshi ta tsaya kafin tayi mgn yace”waye wnn da kike mikawa ruwa daxu?..”da sauri ta dago tana kallonshi sai kuma tayi kasa da ido tace”besty na ne”…da mamaki sosai yake kallonta yace”bestie?..”gyada kai tayi tace”eh..”ranshi ya sake 6aci wato har bude baki ma takeyi tana ce mishi bestynta ne?..a fusace yace”ke yanxu ko kunya bakiji kike kiran wani qato da besty?..are u madd?..”turo baki tayi tana marairaice mishi tace”Allah Sir besty na n…”bata karasaba ya daka mata tsawanda yasata shiga taitayinta sbd firgici…yana huci yacigaba da fadin”wato ke gaba daya bakida aikinda ya wuce kule kulen maza koh?..jiyama na ganki da Abdool shi kuma meye tsakaninki dashi?..”kai tsaye tace”sona yakeyi”..wani irin dumm Bobby yaji gabanshi ya fadi..baisan meyasa duk yaji kalmar wani na sonta sai yaji wnn faduwar gaban ba…bazai manta ba jiya ma haka yaji da Gabriel yace yana sonta..amma why yake jin irin haka?..ganin baida amsan tambayan ya sake daure fuska yana kallonta yace”wato sonki yakeyi?..sbd bakida hankali ke kowanne namiji yace yana sonki saiki biye mashi kuna shashanci koh?..are u even alright?..”turo baki ta sakeyi cike da gajiya da wnn masifan nashi tace”nifa ba sonshi nakeyi ba..kuma ni bana kulashi ko jiyan ma daka ganmu hakuri yake bani ai”..yace”hakuri yake baki shine naga kuna daria?..ni zaki maida mahaukaci?..”kaman zatasa kuka tace”Allah hakuri yake bani kuma na ce mishi inada wanda nakes…”bai bari ta karasaba ya katseda fadin”just stop it okay?..stop it”..tsorata tayi sbd ganin yanda yanayinshi ya sake sauyawa lokaci guda..shi kuma ya dakatar da ita ne ba don komai ba sai don bayason jin wnn faduwar gaban da yakeyi idan yaji ana sonta…yanxun da take kokarin ce mishi tana son wani yasan zai iyajin fiyeda na baya…idanunshi a kanta yana kallon yanda take turo baki kawai sai ya runtse nashi idon don a yanda yakejin zuciyarshi yana iya gaura mata mari sbd zafin da yakeji…kofa kawai ya iya nuna mata ba tareda ya bude idon nashi yace”fita..”kaman jira takeyi ta mike zata fita har takai kofa yace”kuma idan baki maida gashin nan da kika fito dashi waje ba you will see the other side of me”..turo baki tayi ta zake juyawa zata fita yace”ba mgn nayi maki bane?..”dakatawa tayi da tafiyar ta janyo mayafin kanta zuwa inda gashin goshinta ya fito…bai tareda ya sake kallonta ba yace”now leave”..da sauri ta bude kofar ta fita tana fadin”mutum sai shegen baqin hali..ko ina yaji hausa haka maoho?..he speaks kaman hausawa ne suka haifeshi”.
Bayan sati hudu…
A cikin four weeks din nan sau biyu suna zuwa gida weekend…karatunsu kuma yanxu ya dauki zafi as suna dab da gama 2nd semester year 2 daga nan kuma sai final year…Sa’eed kuwa shirye shirye sukeyi sosai na Council Exam dinsu daya gabato..Hospital Final Exam zasu fara daga nan kuma wanda yayi passing ya wuce School final inda daga nan kuma za’a turasu asibiti waiting results…har basu son tuna Council din nan sbd hakan yana nufin sun kusa rabuwa da besty…hatta Billy da ba wani shiri sukeyi sosai ba tana tunanin rabuwar nan sbd Sa’eed is one of the best things that have ever happened to them in Kano..sam basu san ya rayuwa zai kasance bayan babushi ba..wnn dalilin yasa Aysha har kuka takeyi idan ta tunada haka…kawai she is going to miss him like crazy…a 6angaren Bobby kuwa fita harkanta yayi completely sbd kwata kwata baison jin abubuwan da yakeji gameda ita…so yake ya dawo da tsanar da yayi ma Fulani ya dora mata amma sam zuciyarshi taki bashi hadin kai and baisan meyasa ba…sai suyi sati ma basu hadu ba sai idan da wani dalili idan sun hadun ma kuma dinke fuskanshi yakeyi tsaf wai kar ta rainashi…tsakaninshi da daddy kuwa zumunchi suke sosai don every Friday yana mishi sending friday text message snn yana kiranshi yana gaishesheshi once in a while haka..sosai yakejin mutumin na sake kwanta mishi a rai sbd mu’amala da yake dashi me kyau da mutane…har yanxun kuma bai dena mamakin how he end up giving birth to Lamido da tunda yake bai ta6a ganin fitinanniyar yarinya irinta ba.