Dr. BOBBY COMPLETE HAUSA NOVEL

Cikin ikon Allah washegari haka ta tashi garau kaman ba ita ke kukan ciwo ba jiya…kuma abunda mamakin shine yanda ko injection site din baya mata ciwo unlike before da duk akayi mata injection sai wajen ya kusa shekara yana damunta amma shi nashi yana gamawa ta dena jin ciwon wurin…she remember last time daya mata alluran ma hakan ya faru don a ranar ta warke garau babu ciwon kafa ko ciwon bayan snn kuma babu ciwo da dan swelling din da wajen allura keyi mata…tunda take bai ta6ayin wani abu ya burgeta ba amma this time around ta jinjina mashi kwarai don tunda aka haifeta ba’a ta6a mata allura wurin baiyi ciwo ba sai a kanshi…hakan ya nuna mata he isn’t only a qualified doctor he has magic handa too…tana zaune daki ta tasa pringles da babynta ya kawo kawo cikin shopping da yayi mata daxun saici takeyi kaman ba gobe…Billy suka shigo dakin tareda wata ta karasa ta dauki iron dinsu dake ajiye ta bata snn ta juya ta fita ita kuma ta karasa kusada Lamido ta zauna tana murmushi tace”wai Lamido har yanxu fushin ne?..”murguda baki Aysha tayi batace komai ba…Billy ta kara sakin smile kafin tace”dama Ammi ne tace idan baki kulani ba in kirata in fada mata”..tun bata karasa ba Aysha ta juyo tana kallonta da mamaki sosai tace”yanxu zuwa kikayi kika hadani da Ammi Billy?..sai kace bakisan halin fadanta ba?..”daria Billy ta saka tana mikewa daga inda take tace”dama mgn nakeso kiyi kuma kinyi..ba wata Ammi dana fadawa”…pillow dake kusada ita Aysha ta dauka ta wurga mata shi kaman zatasa kuka tace”amma kin shiga haqqina wlh..kinsan irin tsoron da naji kuwa?..”daria kawai Billy keyi ta fara rage kayan jikinta ta shiga bathroom.
Zaune yake a parlonshi waya rike a hannunshi sai jujjuyashi yake kaman wanda yake tunani…tun daxun yake zaune nan wurin yanaso ya kira yaji ya jikinta yake amma wani zuciyan na hanashi wai idan ya kira zata iya misunderstanding dinshi…yayi kokarin kira kusan sau goma yana fasawa sbd zuciyarshi dake raya mishi cewa kar ya kira…tsaki ya saki yayi wurgi da wayan snn ya kwanta nan kan sofa da yake zaune yana wani daure fuska kaman Lamidon tana gabanshi yanxu haka…sam bayason yanda zuciyarshi ke saqa mishi abubuwa a kanta…ya rasa dalilinda yasa tun jiya ya kasa macewa da halin daya barta a ciki kiri kiri yana son kira kuma ya hana kanshi…har yanxun bai dena jin uban laushin gashinta a hannunshi ba kaman yanda bai ta6a mance cute face dinta dake tsaya mishi a rai ba…lumshe ido ya sakeyi cikin ranshi yana ayyana ko mutuwa zatayi bazai kirata ba..to meye ma ruwanshi da rashin lafiyarta da har zai bi ya damu kanshi?…juyi ya sakeyi yana dafe head dinshi duk a kokarinshi na ganin ya hana kanshi kiran nata saidai abunda bai saniba shine duk taurin kanshi heart dinshi bazai dauka ba sbd yafishi taurin kai don haka dole ne yayi mata abunda takeso idan har yana son zaman lafia…kasa daurewa yayi daga karshe ya sake mikewa zaune ya dauko wayan nashi…yayi dialing number dinta yana wani hade rai kaman tana ganinshi…tana kwance daki suna waya baby kiran nashi ya shigo sbd tsabar dadin hira ko noticing kiran nashi ma batayi ba…Bobby da yaji an buga masa wani abu kaman guduma a cikin heart dinshi sakamakon busy da yaji alaman tana waya…haka har ya gama ringing dinshi bata dauka ba hakan kuma ya mugun 6ata masa rai dan yasan da kyar idan bada namiji take wayan ba…sake kira yayi still bata dauka ba sai a na uku ne akayi sa’a taga shigowan call din dan haka tacema baby ya bata two minutes zata kirashi…picking call din tayi da sauri bayan tayi hanging wancan tana wani turo baki kaman tasan yanda ya hade ranshi shima…tana kokarin gaisheshi taji yace”dawa kike waya?..”murguda baki tayi cikin ranta tace”ina ruwanka?..”a fili kuma tace”Hamma na ne”..shiru yayi ba mgn as gaba daya ma mgnr baisan sanda ta fito ba..shi kanshi saida yaji wani iri daya tambayeta amma ba yanda zaiyi ne shiyasa ya tambaya…baisan meyasa abubuwa irin haka suke son su dinga faruwa dashi ba yanxu..shi da sam ba haka yake ba wlh…jin bai sake cewa komai ba tace”hello”…wani mgnr ne ya sake su6ucewa daga bakinshi ba tareda ya shirya ba yace”ya jikinki?..”ita kanta saida tayi mamaki jin tambayar amma bata nuna ba tace”naji sauki”..bai sake cewa komai ba ya kashe wayarshi yana dafe kanshi da yaji kaman zai rabu biyu sbd ciwo…da yasan abunda zai faru knn da bai kirata ba wlh…kawai yana zaman zamanshi ya janyoma kanshi 6acin rai..ko waye Hamman data fada ma oho..a iya saninshi dai idan ance Hamma ana nufin yaya namiji saida i baisan meyasa jikinshi ya kasa amincewa da yayanta take waya ba…sam yasan ba haka bane ta fada ne kawai don ta gujema fadanshi amma zaiyi wahala idan bada daya daga cikin boy friends dinta take wayar ba…wnn tunanin kadai ya sake dagula mishi lissafi.
Kwanakin da suka biyo baya shirye shirye sukeyi sosai na End of Year Presentation da suka saba gabatarwa duk end of session.
Bobby kuwa tun daga wnn ranan bai sake kiran Lamido a waya ba..ko a hanya suka hadu ko kallonta baiyi dan ko gaisheshi tayi bai amsawa wai duk a kokarinshi na ganin yayi yaki da abunda yake ganin bai kamata ace yanaji ba kuma a kanta…yau friday tun safe ya shigo college din sbd meeting da yake dashi da entire staff karfe 10…bayan sun fito Nur ya biyoshi har office dinshi yana mishi bayanin Presentation da za’ayi next week…ya gama sauraranshi tsaf snn ya bar office din shi kuma sai a lokacin wani tunani ya fado masa…yasan zaiyi wahala wnn abun ace ba’ayi selecting Lamido ba dukda dai kowane department voting sukeyi a tsakaninsu ko wanne class tun daga year 1,2 da 3 zasu bada mutum daya da suka yadda da brain dinshi sai a hadasu su ukun ayi masu test kowa akan gaba daya courses dinshi na shekarar duk wanda yayi winning a cikinsu shine zaiyi representing gaba daya department…baisan meyasa haka nan jikinshi ke bashi ita zatayi winning ba..kawai shidai baya sonta da wnn abubuwan ba don komai ba sai sbd shegen rawar kan daya lura tana dashi snn abune wanda a gaban mutane za’ayi shi hadda wanda ba daga makarantan suke ba..shi kuma yanxu baisan meyasa yaki jinin yaga tana wnn abubuwan ba..sam bai son yaga tanata wnn rawar kan nata a gaban mutane suna kallonta hakanba karamin 6ata mishi rai yake ba…sanin zaiyi wahala idan batayi din ba ya lalabo numberta ya danna mata kira don yayiwa tufkar hanci…shiganta class knn taga kiran nashi ta wani zare ido sosai tana sake kallon screen din to make sure ba idonta ke mata gizo ba…to me yake nema a wurinta yanxu kuma?..ta samu ta huta da masifarshi a yan kwanakin nn shine yanxu zai wani kama ya kirata salon ya wargaza mata jin dadi…ganin ya kusa tsinkewa ta daga tareda kai wayan kunne tana turo baki..kai tsaye yace”meet me now”…bai jira cewarta ba ya kashe wayar..ita kuma ta mike tana kwaikwayonshi”wani wai meet now…as if i am his child..inyamurin banza dan rainin hankali kawai”…mikewa tayi tanata sababi ta fita zuwa office din nashi…secretary dinshi na ganinta ta dauke kai bata kulata ba itama batabi ta kanta ba ta tura kofa ta shiga da sallama…yana zaune kan seat dinshi yana dan juyawa a hankali idanunshi kan kofa…kai a kasa ta karaso gabanshi ta tsaya snn ta gaisheshi still ba tareda ta dago idonta..shima bai damu da ta dago din ba ya nuna mata seat dake bayanta a nutse yace”seat..”dagowa tayi ta kalleshi da mamakin abunda ya fada dan bata ta6a zuwa office dinshi yayi mata tayin seat ba sai yau…janyo kujerar tayi a hankali ta zauna still idanunta a kasa tana wasa da fingers dinta…ba yabo ba fallasa yace”akwai end of year presentation da za’ayi next week nasan kin samu labari koh?..”gyada mishi kai tayi alaman ta sani…yace”then so nake koda anyi selecting dinki a cikin participants kice you won’t do it”…sake dagowa tayi tana kallonshi da mamaki tace”but why sir?..already an riga anyi choosing dina and I can’t say no because I don’t want my department to loose”…kallonta kawai yakeyi yanda take wani explaining mishi bata san kome zata ce ba ganewa zaiyi ba…ya wani hade rai yace”i said you are not going to do it and that’s final”…sake dagowa tayi tana kallonshi da mamaki shima kallon nata yakeyi wai ko zata fahimci abunda yakeji ta cikin idanunshi amma sai yaga ta kauda kanta tareda daure fuskanta itama tace”nidai I can’t say no”…tun kafin ta rufe baki yace”haka kikace?..”shiru tayi tana kallonshi ya sake fadin”haka kikace kou?..fine..we shall see”..dan marairaicewa tayi tana mishi puppy eyes tace”yanxu sir fisabilillahi kawai sai inje ince musu bazanyi ba bayan an riga anyi selecting dina?..”cikin fushi yace”na fada maki baza kiyi ba and if u like go and do it kiga what will happened..just try me and see”…kallonshi kawai takeyi yanda yake mgn ita kam kome zaiyi saidai yayi wlh amma bazata fasa yin abunda tayi niyya ba..besides ko daddy zai fadama tasan bazai hanata ba tunda ba wani abun rashin kyau bane and sai tayi abunta wlh…ganin kallon da yake mata sai tayi kasa da idonta a hankali tace”shikenan zan fada musu su samu wani”…ajiyar zuciya ya sauke a 6oye dan wani irin relieve yaji ya samu jin abunda ta fada ita kuma ta sake dubanshi cikin nutsuwa tace”ina iya tafiya?..”baice komai ba sai kofa daya nuna mata alaman she can…mikewa tayi a hankali ta fita saga office din cikin ranta tace”in your widest dream ba..ai wlh sai nayi abuna saidai kawai ka ganni kan stage..shknn sai ince na fasa kilan aje a dauko wanda bata iyaba ta kayar da department dinmu..to bada A’i za’ayi wnn wautan ba..dan rainin hankali kawai”.