Dr. BOBBY COMPLETE HAUSA NOVEL

A can makaranta kuwa Billy da Sa’eed hankali tashe suke nemanta sun kuma rasa inda ta shiga…duk inda suke tunanin zasu ganta sun duba basu ganta ba…wasa wasa har yamma yayi likis basu dena nemanta ba kuma basu ganta…hankalinshi idan yakai dubu duk a tashe suke gashi mutane har sun fara raguwa cikin makarantan ba Lamido babu dalilinta…Billy kaman zata sa kuka take dubanshi tace”nidai wlh ba ruwana kaine ka farayi mata daria bani ba..kan wane dalili ma zaka fara mata daria bayan kasan bataso?..”da mamaki sosai yake kallonta yace”Seriously?..gaba daya laifin zaki dora a kaina sbd ga sarkin laifi koh?..”cikin tsiwa tace”laifinka ne mana tunda ka fara mata daria..yanxu idan bamu ganta ba ya zanyi ni Bilkisu?..dan Allah ina kake tunanin zataje?..”shiru Sa’eed yayi yana tunanin inda zata iya zuwa can yace”bakida number babyn nan nata?..”girgiza kai Billy tayi tace”bani dashi”..shiru ya sakeyi yana tunani Billy tace”ko Proprietor din zamu kira ko yasan inda take?..”girgiza kai yakeyi yace”i don’t think zaisan inda take gaskia..besides ke kanki kinsan besty ba fada mai zatayi ba”…cikin hankalin dake karuwa Billy tace”nasan bazata fada mashi ba amma at least zai iya taimakawa wajen gano inda take..dole muna buqatan taimakon wani babba and sanin kanka ne bazan iya kiran gida in fada ba amma shi idan na fada mishi na tabbata zaiyi wani abu akai tunda daddy ya bashi amanarta kuma shine yayi sanadin komai dake faruwa”…gyada kai yakeyi cikeda gamsuwa yace”yea kinada point..amma a ina zamu number dinshi?..”tace”bamu dashi amma sai mu tambayi provost ya bamu”…zaro waya Sa’eed yayi daga pocket dinshi yace”let me call Dr Aslam nasan bazai rasa numbershi ba”..daga haka yayi dialing number da yayi saving as Dr Aslam a wayarshi…yana fara ringing doc Aslam ya daga nan Sa’eed yace mishi number Dr Bobby yake nema babu 6ata lokaci kuwa ya turo mashi…message din na shigowa ya dubi Billy da har yanxu hankali ke tashe yace”yauwa gashi ya turo..dauko wayanki ki kirashi”…ba musu Billy ta dauko wayanta ta kwashi numbers din da aka turo snn tayi dialing…har ya gama ringing bai dauka ba sai ta sake kira…a takaice saida ta jera missed calls kusan 7 bai dauka ba hakan kuma ya sake tada hankalin hajia Bilkisu…bata hakura ba haka tayita jera masa kira har saida taji ya daga…tana jin ya dauka tayi saurin cewa”Sir sunana Bilkisu Muqaddas nice muke tareda Aysha Lamido..sir wlh tun daxun muke nemanta school din nan bamu ganta ba gashi har dare ya fara shine nace we should call ko akwai taimakon da zaka iyayi mana”…tunda ta fara mgn Bobby da har yanxun yake kwance baice mata qala ba..sauraronta kawai yakeyi yanajin yanda maganganunta ke shiga direct to his heart suna sake lalata mishi ita…ciwon kan daya fara mishi sauki nan take ya sake dawowa…da kyar ya iya bude bakinshi yace”where are u now?..”da sauri tace”school..”yace”will be coming right away”…da sauri tace”mun gode sir..Allah ya saka da alkhairi”..shidai bai sake cewa komai ha ya kashe wayarshi.
Rano✨
Wnn littafin na kudi ne ban yadda wani ko wata ya fitarmin dashi ba…masu buqatan siya zasu tura 300 zuwa 220891344 Aisha Ahmad Tijjani Zenith Bank…sai a tura evidence of payment via 07063800556.
26
Mikewa ya samu yayi daga kwancen da kyar yanajin yanda ciwon kan daya samu ya fara raguwa na sake dawowa sabo…shikam baisan dalilinda yasa Allah ya hadashi da Lamido ba amma for sure ya fara tunanin ba alkhairi bane haduwan nashi da ita..gaba daya nema take ta zame mishi tauraruwa mai wutsiya da tunda ta shigo rayuwarshi take kokarin canxa mishi ita…yana mikewa wani jiri ya sake daukanshi don saura kiris ya fadi a kasa yayi saurin dafa wall da yake tsaye kusa dashi…da kyar ya karasa first aid box dinshi ya dauki maganinda yasan zaiyi saurin saukar mashi da headache da dizziness din yayi dispensing ruwa yasha snn ya koma kan sofa ya sake kwantawa for like 10 mins kafin ya dan ji dizziness din ya ragu dan haka ya mike ya dauki car keys dinshi ya fita…Mummy da har yanxun ke zaune parlor tana ganinshi ya fito da keys a hannu ga kuma yanda yake tafiya shows har yanxu akwai sauran matsala tattare dashi tace”ina zakaje kuma?..”kallon inda take yayi kafin yace”Hospital zanje Mummy…ba dadewa zanyi ba”…cikeda concern tace”amma bazaka iya driving a haka ba Bobby..kaga yanda kake tafia kuwa?..”dan murmushi ya saki ba karfin hali yace”Mummy don’t worry ba abunda zai faru..ya zama dole ne fitan shiyasa zanje”..bata sake cewa komai ba sai kai kawai data gyada mishi…shi kuma ya juya ya bar parlon walking slowly sbd kar taga yanda jirin da yakeji ke neman affecting tafiyan nashi…yana fita ya fada mota yayi mata key ya fita daga gidan…a hankali yake tafia sbd gudun problem don yasan idan yace zaiyi gudu a halinda yake ciki tsaf za’a iya samun matsala…cikin 35 mins ya iso makarantan bai shiga ciki ba yayi parking nan bakin gate snn ya kira number da Billy ta kirashi dashi daxu…tana dauka yace”am at the gate”..snn ya kashe wayan…Billy ta mike da sauri tana duban Sa’eed tace”kaji proprietor har yazo..yana bakin gate”…Sa’eed baice komai ba ya mike suka fita bakin gate din…suna tsallako titi suka nufi inda suka hangi motarshi…kanshi na hade da starring motan ko noticing dinsu baiyi ba saida Billy tayi mgn…da kyar ya iya dago kan nashi yana kallonta da eyes dinshi da sukayi jaa sbd headache da kuma damuwa yace mata”so kince kun duba ko ina baku ganta ba?..”da sauri tace”eh wlh tun dazu muke nemanta bamu ganta ba”…da kyar ya sake fadin”kuma baku tunanin she might have gone to someone a nan cikin gari like a friend or family?..”gaba daya shiru sukayi can Sa’eed yace”ina tunanin zata iya zuwa wurin baby”…juyawa Bobby yayi yana kallonshi da kyau yace”who was that?..”kai tsaye Sa’eed yace”saurayinta ne..sunanshi Professor Ahmad”…kallonshi kawai Bobby keyi yana kankance idanu tsabar bala’i…yanxu rashin hankalinta har yakai ta dauki kafa takai kanta wajen saurayi?..innalillahi wainna ilaihi rajiun?..wnn wace irin yarinyace?..lokaci daya ciwon kan daya samu saukinshi ya sake dawo mishi kaman zai rabe biyu…shima dizziness din kaman jira yake a fadi wnn mgnr sai ya ninku akan wanda yakeji a baya…6acin ranshi ya fito karara wanda hakan ya basu mamaki sosai…maida kallonshi yayi ga Billy dake gefe murya a cushe yace”have u tried calling her?..”da sauri Billy tace”tun daxu naketa kira bata picking”..”ki sake kira”…ya fada mata feeling extra hot inside…ba musu Billy ta dauko waya ta sake dialing numberta..tana kokarin kaiwa kunne yace”put on speaker”..still batayi mashi musu ba tayi putting a speaker din nan sukaji kiran ya fara shiga amma har ya katse bata dauka ba…ta sake kira still no answer sai a karo na kusan takwas Prof da yaga anata jera mata kira tun daxu yace”yanxu baby bazaki picking calls dinki ba?..”turo baki tayi tace”nidai bazan dauka ba nasan Billy ne ko besty ke kira kuma fushi nakeyi dasu ni”..girgiza kai kawai Prof yayi tareda kai hannunshi ya dauki wayan..daidai lokacin wani kiran ya sake shigowa dan haka ya dauka ganin Billy ce ke kira…a daya 6angaren sunajin an daga Billy tayi saurin cewa”Lamido ina kika tafi kika barmu cikin tunani haka?..and why aren’t u picking my calls?..”dan murmushi ya saki jin yanda take mgn da damuwa yace”Bilkisu relax kinji koh?..tana tare dani yanxu haka”…wani irin darammm Bobby yaji kaman saukan aradu a cikin ziciyarshi..knn da gaske wurin saurayin nata ta tafi?..Billy da taji abunda ya fada ta sauke ajiyar zuciya kafin tace”shiknn Prof nagode..tell her idan ta bari raina ya 6aci saina hadata da Ammi ko daddy wlh”…Prof yace”No inshaAllah bazai kai ga haka ba…yanxu xan dawo muku da ita”..gyada kai kawai Billy tayi ta kashe wayarta Sa’eed kuma na daga gefe baice komai ba…juyawa sukayi ga Bobby daya jingina kanshi da kujera ya dora right hand dinshi kan chest dinshi daidai saitin heart dinshi da yaji kaman zai faso kirjin ya fito sbd irin bugawan da yakeyi…wani irin zafi yakeji that har zata kwashi jiki taje inda saurayinta..abun yanayi mishi ciwo sosai fiyeda tunanin mai karatu…har yanxun eyes dinshi are closed don ji yakeyi kaman duniyan na zagayawa dashi…kanshi kuma na wani irin sarawa kama ana doka guduma akai…duk wani abu da yake tunanin yanaji daxun wnn da yakeyi yanxu is far more than wancan…ashe daxu somin ta6i ne kawai akayi mashi dan bai farajin komai ba sai yanxu..yanxu ne yakejin real ciwon kai da zuciya suna neman su hallakashi…daga Billy har Sa’eed tsayawa kawai sukayi suna binshi da kallo..yanda yake jujjuya kanshi from side to side da kuma hand dinshi dake dafe da his heart shows ba karamin ciwo yakeji ba…kamar yasan tunaninda sukeyi ya samu ya dago kanshi da kyar ya bude idanunshi a kansu wanda ba shiri gaba daya sukayi kasa da nasu don idon babu kyawun gani sam..idanunshin that ko lafia lau ma suke firgita mutum inaga kuma sun sauya launi haka?..bai damu da dauke idon nasu ba ya maida glasses dinshi sama tareda kwantar da kanshi jikin starring su kuma ganin haka sai suka tsallaka titi suka koma makaranta abunsu…saida ya dauki lokaci mai tsaho yana fama da kanshi kafin ya dago yana kokarin kunna motan…kawai haushin kanshi yakeji na fitowa da yayi ma at the first place..yasan da baizo ba ba yanda za’ayi yaji labarin tana wurin saurayinta ma balle ya karama kanshi bala’i cikin masifan da yake ciki…tada motan yayi ya haura kan titi yana tafiya slowly sbd yanda yakejin jikinshi…tafiyan minti uku kadai yayi yaji motan na barazanar kwacewa daga hannunshi sbd dizziness da har yanxun bai sakeshi ba..dole haka ya gangara gefen titi yayi parking tareda kashe motan ya sake kwantar da kanshi da starring…tunanin wanda ya kamata ya kira yake tunda dai yasan ko yasha giyan wake bazai fara daukan hanya yana a wnn halin ba..shidai wnn yarinya Lamido take ko Gidado ta cuceshi wlh..sam ya rasa abunda tayi mashi da yakejin irin wnn abun a kanta…sunyi fada da Nur daxu so bazai ma fara kiranshi ba..driver dinshi kuma yasan yanxu yana gida tareda iyalinshi shi kuma sam bai son ya katse mishi jin dadi ga Sab yana school da sai ya kirashi..Mummy kuma koda wasa bazai fara kiranta ba sbd yasan tambayoyi ne zai shasu kaman yana court…daga karshe dai daukan wayanshi yayi ya kira aunty sumy ya fada mata inda yake yace tazo ta daukeshi that he can’t drive…hankali tashe kuwa ta fita daga gida ta dauki drop din napep har zuwa inda yake…tana sauka ta biya mai napep kudinshi snn ta nufi inda ta gano motan nashi..saida tayi knocking sau uku snn ya samu ya bude mata…tana shigowa ciki ta shiga binshi da kallo ganin yanda lokaci daya kamanninshi suka sauya cikin igbo tace”Bobby lafia kuwa?..meya sameka haka?..”da igbo din shima ya amsa mata da”it’s nothing serious..just headache”…girgiza kai ta shigayi tace”ban yadda da abunda ka fada ba gaskia..you seems disturbed..kodai you are hiding something?..”girgiza kai ya shigayi shima cikin karfin hali duk a kokarinshi na kar ta dauki abun da zafi yace”aunty sumayya i am fine believe me..headache ne kawai ke damuna and am sure it’s stress..da zaran na samu bacci zai dena”…kallonshi kawai aunty sumy keyi kaman bata yadda da abunda ya fada ba…shi kuma bude motan yayi ya fita daga driver seat ya zagaya inda take zaune itama ta fito ta nufi driver seat shi kuma ya bude nan inda ta fito ya shiga ya jingina kanshi da kujera yana lumshe ido..bayason jin another tambaya da zai fito daga bakinta dan baisan amsan da zai bata ba…right now ba abunda yake bukata kaman yajishi alone..so yake ya ke6e shi kadai koya samu yayi jinyar zuciya da gangar jikinshi da kyau dan ji yake kaman sun dena aiki na wucin gadi…shi kadai yasan what is taking place in his heart sai kuma Allah daya halicci zuciya ya kuma baiwa kanshi kadai daman ganin abunda ke cikin kowacce zuciya…itama lura da hakan da tayi yasa ta tayar da motar kawai ta harba kan titi…har suka isa gida ba wanda ya sake mgn cikinsu..bayan tayi parking kafin ta bude ta fita yace mata”aunty karfa ki gayawa Mummy wani abu please..kinsan yanda take yanxun kina ce mata kinzo kin daukeni duk tashin hankalinta zatayi”..girgiza kanta tayi tace”bazan fada mata ba amma da gaske ban yadda da abunda ka fada ba Bobby..sam ban yadda onlh headache ke damunka ba..kaga yanda ka koma kuwa?..”dafe head dinshi yayi yanajin yanda ciwon kan ke neman karuwa sbd wnn maganganun da yake..kwata kwata ko bude bakinshi bai sonyi sbd azaba..shi kadai yasan halinda yake ciki…aunty sumy ta bude mota ta fita shima ya fito suka nufi entrance din gidan…Mummy na zaune parlor itada su Miemie da Ilham su suna kallo ita kuma hankalinta gaba daya na wani wajen data kurama id tana tunani…tanajin sallamarsu ta dago tana kallonsu Bobby bai yadda ya hada ido da itaba ya wuce flat dinshi sbd bayada amsan tambayoyin da yasan matukar yaje inda take sai tayisu…idonta a kanshi har ya shige flat dinshi snn ta maida hankali kan aunty sumy dake karasowa parlon..tana zama ta dubi su Miemie da suka hada kai suna kallo tace”Miemie kuje parlona ku cigaba da kallon”…ba musu Miemie ta mike ta kama hannun ‘yar uwarta suka bar parlon…bayan sun fita Mummy ta dubi aunty sumy hankali tashe tace”ya fada maki abunda ke damunshi?..”girgiza kai kawai aunty sumy tayi tace”yaqi fada Mummy..wai headache ne kawai ke damunshi amma ni nasan karya yake there is more to it..Mummy ko zaki gwada tambayanshi ko zai fada maki?..”sauke ajiyar zuciya Mummy tayi tace”nima dazu dana tambayeshi bai fadamin komai ba amma i will try again zuwa safe ko zai fada”..cikeda gamsuwa aunty sumy tace”eh hakan ma yayi..and Allah sa ya fada”..Mummy tace”Ameen”..cikin raunin murya sosai..kwata kwata batason abunda zai ta6a mata yaranta ko kadan musamman shi daya kasance guardian dinsu..kuma bata ta6a ganinshi cikin yanayi irin wnn ba tun bayan rasuwan mahaifinsu..to menene wnn dayasa shi fita daga hayyacinshi haka?..me yake damun yaron nan ne?..(nidai nace da kyar idan ba love bane mummy).????