Dr. BOBBY COMPLETE HAUSA NOVEL

Dr. BOBBY COMPLETE HAUSA NOVEL

Bobby bai samu dawowa gida ba sai after magrib…haka kuwa ya shigo gidan rai a hade sbd tsabar gajia da yayi…driver na shigowa ya samu wuri yayi parking snn ya bude motan ya fito saidai tun kafin ya zagaya ya bude mishi kofa mai gadi yazo ya bude yanata faman mishi kirari sai kace wani sarki…Bobby bai iya ce mishi komai ba sai hannu daya daga mishi kafin ya nufi entrance…tun daga compound din gidan zaka gane mamallakinshi ba karamin mai kudi bane duba da girma da kuma tsagwaron kyau da kuma tsaruwar gidan…katoton Mansion ne daya amsa sunan Mansion saidai abu daya daya bani mamaki is yanda naga gidan shi kadai ne kaf girman layin nasu..ko makota basu dashi dan sai kayi tafiya mai nisa daga nan kafin ka fara hango gidajen mutane…cikin raina nace kilan mutanen gidan basu son zama cikin mutane…ga uban motoci zube cikin compound din bila adadin sai kace ba kudi ake sawa ake siya ba…hatta plate number dake jikin motocin nashi duk sunanshi ne a jiki tunda daga Dr.Bobby 1,2,3 har zuwa ba adadi dan ban samu damar irga adadin yawan motocin ba…ajiyar zuciya na sauke ina jinjina baiwar kudi da Allah yayi masa at such young age snn nabi bayanshi zuwa cikin gidan…bai samu kowa a central parlour ba sai tv dake aiki sai kuma sanyin ac da qamshin freshener da suka hadu suka bada wani sassanyan qamshi a dakin…shi kanshi palorn abun kallo ne…bai tsaya wasting time ba naga ya nufi wani corridor suit dinshi rataye a shoulder dinshi…another parlour naga ya shiga wnn karon dai da akwai mutane a ciki…ya karasa ya zauna kusada wadda kallo daya nayi mata na gane Mom dinshi ce…if you see yanda yayi da face dinshi zai baka daria sosai…ya lumshe eyes dinshi tareda dora kanshi shoulder dinta voice dinshi can kasa cikin igbo yace”Mummy am home”…Mummy na shafa kanshi fuskanta daukeda wide smile itama da igbo din tace”welcome back son..akwai gajiyan aiki koh”…ya danyi pouting lips dinshi before saying”gajia sosae Mummy…kawai Aunty Sumy tace lallai sai naje na duba yarinyan friend dinta a hospital”..Mummy na cigaba da shafa kanshi ta maida dubanta kan Aunty Sumy dake zaune gefe tana aiki cikin system dinta tace”gaskia Sumayya baki kyauta min ba..haka nan kin wahalar min da yaro”..aunty sumy daria tasa sosai kafin tace”Mummy dan yaga kina biye mishi nefa yake wnn abun…ko Sabeer da yake dan auta baya wnn shagwaban da yakeyi..you better grow up wlh wnn shagwa6an babu inda zai kaika”…ta karasa mgn referring to him.

Littafin Dr.BOBBY na kudi ne…masu bukatan siya zasu tura 300 zuwa 2208991344 Aisha Ahmad Tijjani Zenith Bank… sai a tura evidence of payment through 07063800556.

Rano✨

????Dr.BOBBY????

By Aysha Rano✨

Wattpad@aysharano22

03

Sake pouting lips dinshi yayi yace”Mummy blackmailing dina fa tayi wai idan banjeba friend dinta will think bata isa dani ba”…Mummy na kokarin bude baki tayi mgn wata yarinya da batafi 16 years ba ta shigo parlorn da wani mugun gudu kaman wadda kura ko zaki ya biyota…ta tsallaka ta boye bayan Mummy ba tareda ta lura da Bobby da har yanxun ke rungume jikinta ba cikin sauke numfashi tace”Mummy talk to uncle Sab plss…haka nan ya sameni a dakina wai na shiga mishi daki na taba Macbook kuma nidai Allah ban taba mishi komai ba..ko hanyan dakinshi ma banjeba”…tana rufe baki sai ga Sabeer din ya shigo parlorn shima a sukwane yanata kalle kallen inda zai hangota ya fara cewa”Mummy kinga Miemie kawai na ajiye abuna taje ta tabamin koh?..Mummy Allah kiyi mata mgn idan ba haka ba i will…”Bobby bai barshi ya karasa ba ya daka mashi wani tsawan da hatta Miemie dake boye bayan Mummy batasan time da ta fito tana rarraba idanu ba…ya shiga binsu da wani mugun kallo gaba dayansu aikuwa ba shiri duk sukayi kasa da idanunsu domin babu mai karfin zuciyar da zai iya jure wnn kallon da idanun Bobby ke binsu dashi…lokaci daya duk suka shiga taitayinsu dan ba karamin tsoronshi sukeji ba..haka zalika idanunshi ba karamin ladabtar dasu sukeyi ba musamman Miemie da duk ya zuba mata su sai taji kaman ta saki fitsari a wando sbd tsoro shiyasa duk gidan ba wanda suke tsoro kamanshi dan ko kadan baya saurara musu sbd yanda kullum cikin rikici suke yanda kasan tom and jerry…kullum cikin one rigima or the other suke duk kuwa da tazaran shekarun dake tsakaninsu aikinsu knn…saida ya gama binsu da matsiyacin kallo snn ya sauke idanun kan Miemie yana sake tamke fuska yace”meya kaiki dakinshi?..ban ma hanaki zuwa dakinshi ba?..”jiki na rawa Miemie tace”ka hana Uncle Bobby amma wlh nidai banje dakinshi ba…ina cikin zamana fa kawai yazo yace wai na shiga mishi dakinshi”…saida ya bari ta gama tsaf snn ya maida dubanshi ga Sab still fuska daure yace”kai ya akai kasan ta shiga maka daki?..”da sauri yace”Uncle Bobby na gama aiki cikin Macbook dina ko saving banyi ba na tafi masjid shine ina dawowa kawai naga tayi deleting”..yana rufe baki Miemie tace”Uncle Bobby i swear he’s lying ni ban taba mishi komai b…”bata samu sararin karasawa ba sakamakon wani kallo da Bobby ya shiga binta dashi…yana pointing Sabeer yace”mate dinki ne shi da zakice yana karya?..”da sauri ta girgiza mishi kai alaman aah…Bobby yacigaba da fadin”menene sunanshi?..”hawaye na cikowa idonta tace”Uncle Sabeer”…ya sake fadin”who is he to you?..”hawayen da suka cika idanunta na zuba kan fuskanta tace”he’s my Uncle”..wani kallon Bobby yacigaba da binta dashi ba shiri ta sake cewa”he’s my mother’s brother”..Bobby yace”good..ko don sbd wnn matsayin baiyi deserving respect dinki ba?..”wnn karon da kyar ta iya bude baki sbd kukan dake cin karfinta tace”he deserve”..yace”then why are you not respecting him?..”tayi shiru…ya sake cewa”am talking to you”..still kasa mgn tayi sbd kuka da yaci karfinta…shi kuma ya sake juyawa ga Sab ya sakar mashi wani kyakykyawan harara tareda nunashi da finger dinshi yace”and you…kaima baka kama girmanka..kawai sbd anyi maka deleting abu sai kace ita tayi?..kasan kanason abun mai yasa bakayi saving before going out ba…this is going to be the very last warning da zan baku wlh…duk na sakeji wani cikinku yace wani yayi mashi wani abu duk sai nayi maganinku…C’mon get lost”..tun kafin ma ya rufe baki duk suka juya sum sum suka koma inda suka fito…Aunty Sumy da har yanxun hankalinta ke kan abunda takeyi tace”na rasa wnn rigima dake tsakanin Miemie da Sab a gidan nan…ace yara kullum cikin fada kaman wanda aka haifesu a iraq?..”Mummy ma girgiza kai ta shigayi tana fadin”har yanxun akwai sauran yarinta a tattare dasu ne amma inshaAllah watarana zasu daina just continue praying for them…kai kuma Bobby go and freshen up sai ka fito kaci abinci”…baiyi mata musu ba ya mike tareda kama hanyan Flat dinshi walking majestically like a king…wani dogon corridor naga ya shiga snn yabi ta wani kofa kawai sai ganinshi nayi cikin wani parlon…fadin haduwa da tsaruwar wurin is a waste of time…bai tsaya nan parlorn ba ya wuce bedroom dinshi kai tsaye ya rage kayan jikinshi tareda fadawa toilet…ni kuma nayi amfani da wnn daman na shiga karema dakin nashi kallo…komai na cikin dakin white ne daidai da curtains,sofas da carpets duk farare ne…snn dakin yanada girman da zai iya daukan almost 2 sets of bed bayan wanda already suke zube a cikinshi…ko ina tsaf tsaf dashi ga wani kamshi dake tashi ko dakin amarya albarka…a jikin bangon dakin katon picture ne na wani mutumi dake sanyeda Uniform na Nigerian Custom da alama yana tafiya aka dauki hoton…a can kasa an rubuta COL ATTAHIR ADAMU WAZIRI sai in bracket aka rubuta CONTROLLER GENERAL NIGERIAN CUSTOM SERVICE 2014-2018…a kallon farko da nayiwa mutumin na tabbatar da shine mahaifin Bobby dan yana kama dashi sosai unlike Aunty Sumy da Sabeer da sukafi dauko kamannin Mummy…asalinshi bafulatanin Gombe ne mahaifinshi Alhaji Adamu Abdullahi Wazirin Gombe…shine first son din waziri snn yanada tarin siblings maza wanda suka hada uba daya domin bayan shi mahaifiyarshi saida ta dauki lokaci kafin ta sake haifan qanwarshi Munubiya wanda tun daga ita kuma Allah bai sake bata haihuwa ba…ya hadu da Mummy(Nadia)a kano lokacin tana karatu a Buk nan take kuma yaji yana kaunarta…saida aka kai ruwa rana sosai kafin aka bari ya aureta kasancewar ba bahaushiya bace…Sumayya itace first daughter dinsu an sa mata sunan only sis din Mummy data rasu gab da haihuwarta sai Bobby da yaci sunan Dad dinshi Attahir shi kuma auta Sabeer yaci sunan Waziri Adam knn…Miemie kuma daughter din Aunty Sumy ce da younger sis dinta mai suna Ilham(idan muka juya labari zakuji bayanin komai in detail..this is just an introduction).

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128Next page

Leave a Reply

Back to top button