Dr. BOBBY COMPLETE HAUSA NOVEL

Washegari ganin har wajen 11 bai fito ba Mummy ta hada breakfast dinshi ta nufi flat din nashi…yana zaune kan gado ya jingina jikinshi da jikin gadon idanunshi a lumshe dagashi sai singlet da shorts a jikinshi…Mummy ta karasa ciki ta ajiye abincin data shigo dashi kan table snn ta karasa gefen gadon nashi ta zauna kuma har ta zauna din baisaniba sbd nisa da yayi cikin tunani…kallonshi Mummy ta tsaya yi for like 5 mins tanajin tsananin taysayinshi yana ratsata…dukda bata san ainihin abunda ke damunshi ba ta tabbata abune mai girma tunda har ya saka abun cikin ranshi haka…yanada sa abu a rai sosai shiyasa duk wani abu da zai zame mishi damuwa bata kaunar ya ra6eshi sam..hannu takai ta dora forehead dinshi tanaso taji ya temperature dinshi yake aikam taji shi zafi zau kaman ana hura huta…a hankali ya bude idonshi yana kallonta hankalin Mummy ya tashi sosai da ganin idanun nashi…tun yana yaro tasan idan har idanunshi suka sauya din nan to ciwon da yakeji yakai ciwo knn…nan take hawaye ya cika idonta tana kallonshi da kyau tace”Attahir…”da kyar ya iya bude idanunshi ya saukesu a kanta..tace”meyake damunka?..”idanunshi ne suka ciko da hawaye dan yana ganinta yaji wani irin rauni ya dirar mishi kawai sai ya matsa jikinta ya rungumeta yana runste ido…kwalo idanu Mummy tayi waje tanajin yanda ya matseta jikinshi kaman zai 6allata wnn ma is another reason da ya sake tabbatar mata da cewa yana cikin damuwa…hannu takai tana shafa kanshi a hankali tanajin yanda heart dinshi ke beating da karfi kaman zai fito waje…shiko Bobby bakin kokarinshi yake na ganin bai fito da hawayen daga idonshi ba sbd a ganinshi yin hakan ba karamin abun kunya bane a gareshi..wai duk fadin dunia ya rasa wanda zai zubda hawaye kanshi sai Lamido?..yarinyar da dama ya tsaneta from the beginning..jiya ko baccin kirki kasayi banda abubuwanda suka faru ba abunda yake tunawa..gaba daya komai yayi masa tsaye cak and abunda yafi bashi haushi knn sbd yana ganin kwata kwata bai cancanta yana jin wani abu makamancin haka a kanta ba..sam bai dace ba shiyasa shi kanshi yakejin haushin kanshi kuma dui kokarin na yaga yayi stopping abun kasawa yayi…saida suka dauki lokaci mai tsaho a haka kafin ya dago daga jikinta a hankali yana yin kasa da ido sbd kar ya hada idanu da ita..Mummy takai hannu ta dago idanun nashi tana dubanshi sosai tace”fadamin..what is the matter with u?..”hannunta ya kamo ya rike cikin nashi yana kallonta shima ya rasa abunda zai fada..kawai tunani yake me zaice mata yana damunshi dan dai da kunya yace mata kan yarinya karama yake wnn abun…shidai zuciyarshi batayi mashi adalci ba wlh…ganin kallon da ya zuba idanu yana mata ta sake kiran sunanshi…ya lumshe ido ya bude cikin ranshi yana addu’an Allah yasa ta bar zancen amma sam Mummy ta dage sai taji damuwanshi…ganin ba hakura zatayi ba ya tattaro duk wani karfin hali da dakiya irin nasu na maza kafin yace mata”dama..mummy..it’s about a girl”…tun bai rufe baki ba Mummy ta wara idanu tana kallonshi tace”u mean kana son wata yarinya?..”girgiza kai ya shigayi da sauri yana wani ta6e baki jin abunda ta fada yace”Mummy Noo..wata yarinya ce kawai mahaifinta ya bani amanarta shine ita kuma take kokarin tasamin ciwon zuciya”…kallonshi Mummy keyi full of suprise don har yanxu bata fahimci inda zancenshi ya dosa ba..shima ganin kallon da take mishi sai ya shiga bata labarin tun haduwar da sukayi da daddy a college zuwa yanda ya gane shi son din Col Attahir ne da irin maganganun daya fada kan mahaifin nashi har zuwa yanda yace ga amanarta ban ya bashi yanaso ya kula da ita sbd batajin mgn…Mummy tayi shiru tana sauraronshi har ya gama kallonshi kawai takeyi dan she smells something cikin maganr nan nashi…tasan wanene shi sarai dan haka tafi kowa fahimtan halinda yake ciki fiyeda kowa a dunia and cikin maganganun daya fada ta tabbata ko ba son yarinyar yakeyi ba tabbas yanada interest akanta har tunda yake kishinta haka?..ita kuwa inama zataga wnn yarinya ta samu tayi mgn da ita?..inama Allah zai kar6i addu’anta ya zarginda takeyi ya zama gaskia?..inama zat…bata kai ga karasawa ba taji hannunshi a jikinta yana dubanta yake fadin”Mummy tunanin me kikeyi ne wai?..”dan murmushi ta saki tareda kama nashi hannun itama still tana smiling tace mishi”yama sunan yarinyar kace?..”hade rai yayi yana kallonta yace”Mummy me zakiyi da sunanta kuma?..yarinyar da ina fada maki tana kokarin halakani shine kikeso kiji sunanta?..”murmushi ta kara saki tace”nidai fadamin sunanta plss..watarana ma so nake ka kawomin ita mu gaisa”…da mamaki sosai ya tsaya yana kallonta jin abunda tace…shi bai gane me take nufi ba sam ya ya kawo mgnr da ya kamata ta tayashi jaje amma sai behaving take kaman wani abun celebration ne ya faru…daddagewa yayi ya kwa6e fuskanshi kaman zaisa kuka yace”Mummy manaa..meye haka kikeyi plss?..”daria sosai ta saki kafin ta dakatar dashi tana sake dubanshi tace”to yanxu tell me meya kamata muyi?..”gyara zama yayi yana dubanta in a serious tone yace”shine abunda ban saniba Mummy..na rasa wace irin yarinyace ita..wlh jiya ko bacci banyi ba sbd haushin data kunsamin shiyasa har yanxu kaina bai dena ciwo ba..na rasa meyasa na kasa mantawa da komai har zuwa yanxu”..sake kamo hannunta yayi ya rikesu gam idonshi na sake canxa launi yace”Mummy ya zanyi in manta plss…inaso in manta”…ajiyar zuciya ta sauke tana kallon yanda duk yanayinshi ya sake sauyawa dan haka ta kwantar da murya tace”karka damu watarana zaka manta inshaAllah..ni wnn damuwan naka ne banaso kaga har yanxun jikinka akwai fever..inaso ka nutu ka kwantar da hankalinka sosai snn kayima kanka treatment kuma ka dena damuwa dan idan baka denaba ko kayi treatment dinma a banza zai tashi..ko kanaso wani ciwon ya kamaka ne?..”girgiza kanshi yayi da sauri yace”definitely not because of that stupid girl”…Mummy tace”then ka dena damuwa..yanxu ga breakfast na kawo maka ka shiga kayo brush zanyi serving dinka”…baiyi musu ba ya mike tsaye da kyar snn ya shiga takawa a hankali zuwa bathroom dinshi…mummy tabishi da kallo tana tausaya mashi..cikin ranta tana addu’an Allah yasa dai ba soyayya ne zai wahalar dashi ba don a yanda taga alamunshi soyayya zaiyi matukar bashi wahala sbd yanda yake da riko da kuma sanya damuwa cikin ranshi.
Bayan sati daya…
Tun daga wnn rana Lamido bata shiga sabgarshi ba..dan gaisuwan ma da take mishi idan sun hadu a hanya ta dena snn idan zai shekara kiran wayanta bazata dauka ba…yau tsahon kwanaki uku knn dayake kiranta bata dauka..tana ganin wayan zaiyita ringing amma ko kallonshi bazatayi da sunan dagawa ba…yanayi mata ciwo duk ta tuna da kalmar daya jefeta dashi ranan..wai tana biye biyen maza bi ma’ana dai tana karuwanci..lokaci daya duk wnn tsoron nashi taji ya ragu dan cikin kashi dari tasan yanxu da kyar za’a samu kashi hamsin a cikinshi…su Billy kuwa saida suka dauki lokaci kai tsah suna bata hakuri snn suna saku ta hakura suka cigaba da gudanar da rayuwarsu…shirye shirye sukeyi ma na zuwa Kd bikin Lubna fa za’yi next week suna dawowa kuma ba dadewa zasu fara exams daga nan sai Clinical posting sai kuma su shiga level 3…tsakaninta da babynta kuwa sai sambarka dan soyayya sai kara karfi yakeyi kullum.