Dr. BOBBY COMPLETE HAUSA NOVEL

Tun daga ranan sai suka koma mutunchi sosai da Proprietor dan yana daukan lokaci mai tsaho baiyi mata bala’i ba amma yanajin zancen saurayi ko something like that bai iya daurewa sai ya dan zazzaga mata yakejin dadi…yanxun ya koya mata duk ta shigo college da safe taje ta gaisheshi idan yana cikin makarantan..haka kuwa take zuwa ba don ranta naso ba..wani lokaci idan yana nemanta ko ta kashe waya ko bata shigo cikin makaranta dashi ba saidai kawai ta ganshi a class dinsu yazo ya wani hade rai yace yana nemanta..haka zatayita ture turen bakinta tabishi tana zabga mai harara ta baya..wnn dalilin yasa da yawa daga ‘yan class dinsu ke zargin akwai wani abu tsakaninsu wasu kuma sunyi zaton dan uwanta ne kamar yanda idan aka tambayeta sai tace”dan uwan daddyna ne fa”.
Yau Thursday tun 3 Sa’eed ya daukesu zuwa gidan lalle sbd gobe zasu wuce kaduna bikin Lubna…amarya sai damunsu take da kira wai suyi sauri suje itafa ba wasu qawaye gareta ba…basu samu gamawa da gidan lallen ba sai after six dan haka Sa’eed na daukosu direct ya kama hanyan college dinsu..a hanya yaketa kallon lallen da Aysha ke nuna mashi tana fadin”besty lalle na yayi kyau koh?..”Sa’eed dake driving dinshi yace”sosai ma kuwa besty..aike din dama mai kyau ce so duk wani abu da zakiyi dole ma yayi suiting dinki”…Lamido ta saki murmushi tanata blushing tace”godia nake besty nah..shiyasa nake sonka wlh..besty bansan wane irin missing dinka zamuyi idan ka tafi ba”..ta karasa kmr zatasa kuka…shi kuma dan murmushi ya saki ba tareda yace komai ba don kuwa shi kanshi yasan dole yaji a jikinshi duk ranan da akace ya bar FCNM..yasan duk lokacinda yaso ganinsu bazaiyi mishi wahala ba ya dauko mota ya taho kano amma yasan bazai ta6a samun enough time dasu kaman yanda suke samu a yanxu ba…bayason zancen yayi tsayi sbd karyar mishi da zuciya suke dan haka ya kallo Billy ta mirror yana sakin smile yace”Billy banji kince komai ba”…harara mai kyau ya samu daga wurinta hakan kuma ya bashi daria sosai dama yasan abunda zatayi knn..shi tunda yake bai ta6a ganin wanda abun harara bai mata kadan kaman Hajia Bilkisu ba..ya tabbata zaiyi missing dinta fiyeda tunaninshi sbd wnn draman dake tsakaninsu…har suka karasa hostel ba wanda ya sake cewa komai a cikinsu..suna zuwa ya saukesu sukayi ciki shi kuma ya juya kan motarshi ya koma gida.
Washegari suna room dinsu sunata faman hada kaya a akwati yau ko makarantan bazasu shiga ba sbd da wuri zasu wuce…Aysha nata kiciniyar kulle akwatin da suka cikashi 6am da kaya kaman wanda zasuyi shekara a kaduna yayinda Bilkisu ke zaune gefen bed dinta ta zuba uban tagumi tana tunani..kamar daga sama taji tace”Lamido nifa har yanxu tsoro nakeji wlh..ina tsoron wani abu ya samemu a hanya bayan ko gida basu san zamuje kaduna ba”..tsaki Lamido ta saki tana cigaba da sabgar gabanta tace”matsalana da Billy dawo da mgn wlh…tun jiyafa muka gama mgnr nan na fada maki wlh kika sake gida sukaji zancen tafiyar nan bazasu bari muje ba kuma dai kinga idan mukayi haka bamuma Lubna adalci ba tunda da kunnenki dai kikaji tace batada qawaye sai mu..and koba wnn ba ko don besty bai kamata muki zuwa bikin nan ba nasan in Allah ya yadda lafia zamuje mu dawo lafia kawai dan kinsama ranki abun ne amma inshaAllah lafia zamu dawo kuma ba tareda kowa ya sani ba”…gyada kai Billy tayi cikeda gamsuwa dan har wani ajiyar zuciya ta sauke kafin ta sake cewa”to Proprietor kuma fa?..did u tell him?..”da sauri Aysha ta shiga girgiza kai tace”waye ya aikeni in fada mishi salon yace babu inda zamuje knn..kema dai kinsanshi Billy wlh indai ya samu labari bazai bari ba”..Billy tace”amma kina ganin baza’a samu matsala ba?..ina nufin zai iya yuwa har muje mu dawo baiyi noticing ba?..”Aysha na gyada kai tace”of course mana..ai kinsan ba kullum yake zuwa makaranta ba gobe ne kawai mu kuma monday inshaAllah zamu dawo so he won’t know in Allah ya yadda”..gyada kai kawai Billy tayi saidai har yanxun cikin zuciyarta tanajin tsoro..har mamakin yanda ita Aysha bata damu ba take sai wani shiri takeyi tanajin dadi zataje garinda bata ta6a zuwa ba..tsakaninta da kaduna saidai ta wuceshi idan zasuje Abuja amma bata ta6a shigan garin ba.
Karfe 10 da wani abu suka kama hanyan kd…ita da Billy ne sai wani cousin din Sa’eed suka tafi gaba daya a motar Sa’eed din…ko a hanya Billy hankalinta ba kwance yake ba dan koya taji sun shiga gargada zata hau sallallami tana zare idanu wai a tunaninta ko hatsari ne zai ritsa dasu.????
Basu samu isa kaduna da wuri ba sbd holdups da sukayita cin karo dasu a hanya sai kuma shi kanshi hanyan da ba wani kyawu kwarai ne dashi ba…lokacin da suka shigo kd was after one sosai dan har wasu masallatai sun fara sallahn jumu’a…kai tsaye unguwansu ya wuce dasu bayan ya kira Lubna ta shaida mishi cewa tana gidan wani uncle dinsu dake nan kusada gidan nasu…saida ya isa har kofar gidan snn ya sake kiranta nan da nan kuwa sai gata ta fito tana ganinsu ta daka tsalle ta wani cacimesu sai kace ba amarya…bayan sun gama cacime cacimensu suka karasa cikin gidan Sa’eed yabisu da kayansu ciki snn ya fito zuwa gidansu don yaje ya shirya sharp sharp ya wuce masallaci don ana idar da sallahn jumu’a za’a daura aure.
Suna shiga ciki Lubna ta kaisu suka gaisa da matar gidan snn ta jasu zuwa dakinda take ita kadai din da gaske ba wasu qawayen kirki gareta ba…mai make up na zaune tana jiranta tun daxu akaso farawa tace sai sunzo tukun za’a fara…zaunawa tayi aka fara mai aikin gidan kuma ta kawo masu abinci da drinks bayan sun gabatar da sallah suka zauna suka faraci…ko kafin a gama mata make up sun gama dan haka kowacce ta mike ta fara shiryawa don ‘yan daurin aure suna gab da dawowa.
Tare suka shiga gidan gaba daya su ukun bayan an gama cancada ma amarya kwalliyarta…Sa’eed da kanshi ya kaisu suka gaisa da Mom dinshi dukda taron jama’a dake gidan…daga nan kuma angwaye sukazo aka shiga daukan hotuna…su Lamido sai iyayi akeyi to abun nema ya samu…sai bayan sallahn asr suka koma can gidan uncle din amarya tareda few daga cikin friends dinta…karfe takwas na dare aka fara tafiya dinner…sudai suna tareda amarya tace qafarta qafarsu shi kuma Sa’eed yace lallai saidai ya tafi dasu..haka sukaita fafatawa daga karshe dai dole Lubna tayi hakuri ya wuce dasu bayan sun gama shiryawa…suna sanye cikin lace dinsu sea green iri daya duk cikinsu ba wadda tayi make up amma fadan kyawun da sukayi is a waste of time…tun daga mota Aysha ta dauko wayanta ta fara musu snap kala kala wani suyi gaba daya su ukun wani itada Billy wani kuma itada besty…koda suka isa hall din dinner ma cigaba da gashi sukayi…basu bar nan wurinda suke ba saida amarya da ango suka karaso…bayan an gama tsara masu shiga dasu Billy taja baya zatayi musu video Lamido kuma as usual tana sahun farko na wanda zasuyi rawa…ana sakar musu kida suka fara takawa zuwa ciki..Billy dai na gaba tana tafiya da baya baya tanata daukan video a wayanta…har suka raka bride and groom mazauninsu bata dena dauka ba…Aysha kuma bayan amarya da ango sun zauna ta nufi table din da ta hangesu zaune..videos din Billy ta hau nuna mata suna daria..Sa’eed ya kalli yanda take rawa yace”besty knn..na rasa wane irin soyayya ke tsakaninki da rawa wlh”…murguda mishi baki tayi batace komai ba…a takaice kafin a bar wajen dinner Aysha tayi rawa har jikinta saida ya gaya mata…pictures da videos kuwa tasha su a wajen Billy har ma da wanda bai kamata ba…saida suka koma gida suka nutsu kowa yayi shirin kwanciya snn Aysha tayi selecting wasu daga pics da videos da sukayi tayi posting a status dinta bayan tayi blocking duk wani wanda tasan idan ya gani labarin zai iya isa ga parents dinta…tana gamawa da whatsapp ta shiga instagram nan ma tayi posting snn ta kira babynta a waya sukasha hira abunsu..suna gamawa kuma bacci yayi awon gaba da ita.