Dr. BOBBY COMPLETE HAUSA NOVEL

Kano…
Tun safe Bobby ya shigo College dukda cewa saturday ne koda ya shigo bai samu zama ba don meeting suka shiga da staff bayan sun fito shi da Nur suka sake zama da wasu masu fili da yakeso ya siya a kusada college din daga nan kuma suka shiga hostel so gaba daya bai samu zama ba saida suka dawo daga sallahn jumu’a…yana shiga office driver ya kawo lunch daga gida snn ya fita…baa jima ba kuma sai ga Nur ya shigo..tare sukaci abincin a nan bayan sun gama ya kira driver ya tafi da ragowan shi kuma ya zaro phone dinshi ya shiga whatsapp sbd tun safe bai duba messages dinshi ba…reply ya farayi duk wani message mai muhimmanci yayi replying har zai ajiye wayan sai kuma ya fasa ya fara duba status..he is not a fan of viewing or uploading status amma yau haka nan yaji he should just check yaga what people are posting…na aunty sumy ya fara dubawa yaga picture dinshi ne a farko sai na ilham sai kuma na Sab da Miemie a hade…daga nata ya duba na Nur yaga pictures da Public Relation Officer na college din yayi musu daxu during meeting da sukayi ne duk yayi posting..dan ta6e baki yayi snn ya sake yin gaba har zai bude na wani colleague dinshi Dr Michael sai kuma ya fasa sbd ganin sunanta da yayi cikin jerin wanda sukayi posting…ba tareda tunanin komai ba ya danna sunanta nan take kuma picture din farko ya bayyana..ita kadaice a pic din tayi daria both dimples dinta sun fito..wani irin abu mai nauyi yaji yazo ya tokareshi a throat..dannewa yayi ya wuce gaba sai yaga itada Billy suna kallon juna still suna daria har dimples dinta sun fito…wnn karon zafi ya faraji all over his body ganin again ko mayafi babu a jikinta and ta fito da gashinta waje as usual..the next one kuma su uku ne a jiki ta turo bak tana kokarin sanya glasses dinta Billy kuma nayi mata mgn Sa’eed yayi musu selfie..na gaba kuma video ne ita kadai tanata dirkan rawa Billy tayi mata…sbd tsabar 6acin rai baisan lokacin da ya buga table dake ganashi ya furta”what the hell”da mugun karfi ba…daga shi kuma sai another video data daukesu su uku sunata murmushi sun sanya Sa’eed a tsakiya sai wanda aka daukesu tareda amarya da ango…haka dai yayita binsu daya bayan daya yana gani har saida ya gama gani tsaf snn ya ajiye wayar kan table ya dafe kanshi da both hands dinshi…Nur da tunda yaji abunda ya fada dazu ya dago yana kallonshi amma sai yaga all attension dinshi yanaga wayanshi yace”lafia dai?..”banza Bobby yayi dashi yana dafe da kanshi…wani irin zafi yakeji tun daga cikin zuciya zuwa gangar jikinshi..shidai ya rasa wace irin fitinanniyar yarinyace ita?..baisan wane irin rashin ji gareta ba?..yanxu kuma fisabilillahi ina taje sukayi wann pictures haka?..sbd tsabar batada hankali har rawa taje tayi a bainar jama’a..yasan kusan duk wanda ke wurin ya gama ganinta kilan ma baza’a rasa wanda yace yana sonta ba…tunanin hakan yasa yaji wani irin abu mai nauyi yazo ya tsaya mishi a kahon zuci…numfashi ma da kyar yake yinsa sbd azaba..shidai yasan Lamido idan ba nutsuwa tayi ba tana iya haifar mashi da ciwon zuciya watarana sbd abubuwan nan da yakeji a kanta sun fara wuce tunaninshi…duk wani jarumta da karfin halinshi na yaga ya 6oye abunda yakeji sbd Nur dake zaune wurin kasawa yayi…wani irin tari ya farayi sosai yana dafe da chest dinshi..Nur ya mike daga inda yake da sauri ya dauko ruwa daga fridge ya mika mishi yana cewa”sannu..have this zakaji sauki”…baiyi masa musu ba ya amsa ruwan dan shi kanshi yasan yanada buqatan duk wani abu mai sanyi a halin yanxu sbd turirin dake fita daga cikin zuciyarshi…tunda ya kafa goran ruwan a baki bai sauke ba saida ya shanyeshi..Nur dai na tsaye yana kallonshi har yaga ya dan samu nutsuwa snn ya zauna nan kusa dashi yace”mene wai..meka gani ya tayar maka da hankali haka?..”girgiza kai kawai Bobby yayi don baijin zai iya bude baki yayi mgn a halin da yake ciki…hannu Nur yakai ya dauki wayan nashi sai yaga sunan Lamido a jerin status da yayi viewing…bai tsaya wata wata ba shima ya shiga ya fara gani..saida ya gama tsaf snn ya dago yana kallon Bobby da har yanxu idanunshi ke lumshe yana dafe da head dinshi yace”so kishi ne ya motsa knn?..”wani irin kallo ya watsa masa kafin ya sake maida idonshi ya rufe…Nur ya fashe da daria yana cewa”idan ba kishi ba me kakeyi Dr Bobby?..you better wake up wlh”..ya karasa yana sake kwashewa da daria…Bobby dai diff yayi yana sake jin 6acin ranshi na karuwa…a fusace ya nunashi da yatsa yace”how dare you zakazo ka sani a gaba kanamin daria?..are u madd?..”ya karasa mgn da wani irin ihuu da saida Nur ya dora hannu a kunnenshi…bayan ya gama dariyarshi yace”continue deceiving urself kaji?..just keep on denying the fact that u love her..idan bakayi wasa ba kana zaune zata auri wani and ba yanda ka iya”…tun bai karasa ba Bobby ya sake buga table dake gabashi cikin karajii yace”how dare u?..how dare u talk to me like this?..nina fada maka ina sonta?..”gigiza kai Nur ya sakeyi yana shafa gemu cikin shakiyanci yace”har yanxu baka wahala ba shiyasa kake wnn kumfan bakin..idan kaji wuya da kanka zakazo ka sameni kayi kasa da voice dinka kace Nur i don’t know what to do plss help me..bansan yaushe na fara son yarinyar nan Lamido take ko Gidado?..”.Ya karasa mgnr yana wani ta6e baki exactly irin yanda Bobbyn keyi kafin ya sake fashewa da daria…qala Bobby bai iya cewa ba ya mike ya kwashi wayoyinshi ya fice daga office din..idan ya tsaya ya tabbata za’a iya taruwa azo kallonsu don yanda zuciyarshi ke a kusa yana iya kwada mashi mari wlh..kawai takaici yakeji na wnn pictures da tayi posting ?..is she mad or something?..kwata kwata bata san kishin kanta ba..wai ma ina sukaje har sukayi pictures din at the first place?..yana buqatan ya kirata amma a wnn lokacin idan ya kirata kilan zaginta kawai zaiyi sbd yanda yakeji…kai tsaye motanshi ya nufa driver ya bude mishi ya shiga snn shima ya shiga suka fice daga makarantan..dama duk abubuwan da suka kawoshi college din ya gama..rabon zaiga wnn bakin cikin nema kila ya zaunar dashi.
Wnn littafin na kudi ne ban yadda wani ko wata ya fitarmin dashi ba…masu buqatan siya zasu tura 300 zuwa 2208991344 Aisha Ahmad Tijjani Zenith Bank…sai a tura evidence of payment via 07063800556.
28
Kai tsaye gida driver ya nufa dashi..suna isa ya bude mota ya fita zuwa ciki..yayi sa’a ba kowa central parlor dan haka ya wuce flat dinshi..yana shiga ya ajiye wayoyinshi gefen gado ya shiga rage kayan jikinshi sbd azabar zafi da yakeji cox ba zuciyanshi kadai ke mashi zafi harda ilahirin jikinshi…saida ya tabbata ya cire komai shorts kawai ya bari da singlet snn ya shiga bathroom ya sakar ma kanshi ruwan sanyi duk a kokarinshi na ganin ya dena feeling zafin da yakeji amma a banza…saida ya kwashe almost 30 mins bayi yana abu daya kafin ya fito daure da towel yana goge gashin kanshi…turare kadai ya isa fesawa ya shiga closet ya sako amrless da three quarter snn yazo ya dauki one of wayoyinshi dake zube nan kan bed din nashi ya ya zauna yana kokarin kiranta..if u see how he’s frowning his face zakayi tunanin bai ta6a yin daria ba..he looks more angry than ever…kiran na shiga amma har ya gama ringing bata dauka ba saida ya sake kira ta daga tana wani tattaro duk nutsuwarta tace”Sir good evening?..”bai amsa mata ba sai cewa yayi”where are u?..”shiru ta danyi tana tunanin dalilin tambayar sai kuma tace”Sir banji me kace ba”…yace”i said where are u now?..”Aysha ta hadiye wani yawu praying Allah yasa ba asirinta ne ya tonu ba tace”sir..ina..hostel..mana..bacci nake daka kira shiyasa ban dauka ba”…dukda halinda yake ciki saida ya saki murmushi ganin raina mashi hankali zatayi yace”oh really?..kina hostel right?..”cikin dakiya tace”ehh..”yace”then come outside gani nan zuwa hostel din naku yanxun nan”..zaro ido Aysha tayi tana dafe chest dinta tace”na shiga uku”..Bobby da yaji sarai abunda ta fada yace”ki fito waje yanxun nan am coming right away”..da sauri tace mishi”sir dan muhammadu rasulillahi kayi hakuri..tsakanina da Allah bana cikin hostel yanxu haka?..”kai tsaye ya sake fadin”then ina kikaje?..”wani yawu ta sake hadiya kafin tace”gidan biki”..Bobby yayi shiru yana sauraronta baisan mema zaice mata ba…so yake ya sauke mata kwando kwando na rashin hankalin da tayi amma yafiso ya ganta a gabanshi tukun…ita kuma jin yanda yayi shiru sai ta sakeyin kasa da murya tace”sir please!..”ajiyar zuciya ya sauke kafin yace”kina dawowa ki sameni office tunda ke bakida hankali?..kuma kika bari na sake kiranki zakiga abunda zai faru?..”hawaye sosai suka ciko idanun Aysha tace”sir nifa gaba daya bana gari”..wnn karon shine ya zaro eyes dinshi tamkar tana gabanshi yace”ban gane bakya gari ba..explain urself”..murya can kasa yaji tace”muna kaduna”..ya bude baki zai kwaso masifa kawai yaji diff ta kashe wayarta…Bobby yabi wayarshi da kallo yana mamaki..sake dialing yayi yaji ta kashe wayan gaba daya nan take ya runtse ido yanajin zafin da yakeji yana sake karuwa…nan take zazza6i yace salamu alaikum..can saiga ciwon kai da jiri duk sun dirar masa at once..har wani irin sanyi yana kadashi ga temperature dinshi da yayi rising…da kyar ya iya daga legs dinshi ya dora kan gadon snn ya kwanta a hankali ya lullu6e da duvet..lokaci daya yaji kaman an kanainayeshi ya kasa koda daga finger dinshi..sake runtse ido yayi yana mamakin yanda duk ciwon suka saukan mishi at once..few minutes ago baijin komai ba in banda slight headache da 6acin rai amma yanxun ji yake ko mikewa tsaye bazai iya yi ba sbd ciwo…koda yake ba abun mamaki bane dan yanxu zakaga mutum lafia qalau anjima kadan ace maka ya mutu so wnn ba komai bane daga cikin qudurar ubangiji…jikinshi har shivering ya fara gashi ko kwakwaran motsi bai iya yi balle ya tashi ya kashe acn da yake zaton ita ke kara mashi sanyin da yakeji…su Mummy kam ba wanda yasan ya dawo a cikinsu don time din da ya shigo bai hadu da kowa ba dan haka yamma nayi suka shirya Sab ya fita kaisu unguwa a motan Mummyn…basu suka dawo gidan ba sai after magrib sai a nan ne Mummy ta fara mamakin rashin dawowarshi har yanxu sbd yace mata yau ko Hospital bazai shiga ba yanaso ya huta…ganin har anyi sallahn isha tara na neman wucewa sai ta dauki wayanta ta shiga kiranshi…yanata ringing bai dauka ba har tayi mishi 4 missed calls ba wanda yayi answering a ciki…nan kuma hankalinta ya fara tashi dan tasan lafia lau dai baza’a yima Bobby har 4 missed calls bai gani ba..sake kira tayi for the fifth time ganin still no answer saita dannawa Nur kira hoping ko basa tare yasan inda yake…Nur dake kan hanyan komawa gida yana ganin kiran nata yayi parking snn ya daga kafin yayi mgn Mummy tace”Nuru kuna tareda Bobby kuwa?..”girgiza kai Nur yayi kaman tana ganinshi yace”No mun rabu tun daxu Mummy..ai tun around 4 ya baro college saidai ko Hospital ya wuce”..Mummy tace”anya kuwa?..na kira wayanshi bai dauka ba and yau yacemin yana gama da college dawowa gida zaiyi ya huta bazaije ko inaba”..shiru Nur yayi yana tuna a halin da ya bar college din yasan zaiyi wuya yaje wani wurin idan ba gida dan haka yace”Mummy a duba flat dinshi dai..zai iya yiwuwa ya dawo yana ciki bai fito ba shiyasa baku san yana nan ba”..gyada kai Mummy keyi before tace”shknn let me check”..daga haka ta kashe wayar snn ta juya zuwa flat dinshi…tana tura kofan tajishi a bude tasan yana ciki knn dan haka direct ta wuce bedroom dinshi..a kwance can karshen gado ta hangoshi ya kudundune kanshi kanshi cikin duvet dukda haka kuma jikinshi bai bar rawa ba…karasawa tayi da hanzari ta yaye duvet din tana ganin yanda ya dunkule waje daya saida gabanta ya fadi dan Bobby ba mai yawan rashin lafia bane..yana dadewa baiyi ciwo ba amma duk ya tashi yi sai ya kusan mutuwa sbd wahalan da yakesha…zaunawa tayi nan kusa dashi hankalinta duk a tashe in igbo tace”Bobby meke damunka?..yaushe ma ka dawo gidan bamu sani ba?..”da kyar ya iya bude idanunshi ya zubasu a kanta sai kuma ya sake maida su ya lumshe sbd baison ganin tashin hankalin dake rubuce kan fuskata…hankali tashe ta sake fadin”ba mgn nakeyi ba?..meya sameka?..”daurewa ya mike zaune da kyar yanajin yanda sanyin dakin ke sake ratsa mashi jiki Mummy data lura da hakan tayi saurin mikewa ta kashe ac snn ta sake dawowa ta zauna tana dafa forehead dinshi tace”u look seriously sick Bobby..meke damunka?..”hannunta kawai ya iya kamawa yana zuba mata idonshi dake mata nuni da bayason ganin damuwar nan da takeyi shiyasa tun daxu yaso ya tashi yasha magani kafin ta shigo amma ko motsi kasawa yayi…ganin kaman bazai iya mgn ba ta dauki wayanta data shigo dashi kai tsaye ta sake dialing number din Nur tace”bari in kira Nuru yazo ya dubaka idan abun bai yiwu ba kawai mu wuce asibiti”..tun kafin ta rufe baki yaji wani new 6acin rai na diran mishi jin ta ambaci Nur sbd tunawa da iskancin da yayi mashi daxun yace”Mummy..dont..call him..plss”..Mummy tace”why zakace haka?..kaji yanda temperature dinka yayi rising kuwa?..”lumshe idonshi yayi dan baisan me zaice ba again…kafin Mummy ta kira Nur sai ga aunty sumy ta shigo dakin tan sanyeda dogon riga da hula itama duk a gigice tace”Mummy wai jikin nashi ne har yanxu?..”Mummy tace”wlh har yanxu sumayya..ungo wayan nan ki samu ki kira Nuru yazo ya dubashi wnn high temperature bana lafia bane”..da sauri aunty sumy ta amsa wayan da Mummy ke mika mata ta zauna tareda dialing number Bobby sbd takaici kawai ya zare hannunshi daga cikin na Mummy hade da komawa ya kwanta ya juya musu baya…hada ido sukayi kafin aunty sumy dake sake trying number Nur tace”ni ban ta6a ganin likita da baya qaunaf treatment ba irin Bobby..duk rashin lafia ya kamaka saika bamu wahala wajen zuwa asibiti ko kuma kiran doctor”..shidai baice mata komai ba sbd shi kadai yasan abunda yakeji…Nur na ganin kiran yayi picking tareda fadin”yauwa Mummy yana gidan kou?..”aunty sumy tace”yea yana nan amma fa bashida lafia..he’s seriously sick inaga u should come forward ka duba jikin nashi”…da sauri Nur yace”ok gani nan zuwa yanxun nan”..daga haka ya kashe waya tareda juya kan motarshi zuwa airport road…aunty sumy na gama wayan itama komawa tayi ta zauna kusa dashi suka wani sanyashi tsakiya itada Mummy sai kace wanda ke fama da cutar ajali.????
Ko cikakken 30 minutes baayi ba Nur ya karaso gidan..yana shiga ciki kai tsaye ya wuce flat din Bobby don bai samu kowa central parlor ba…saura kiris daria ya kufce mishi sbd ganin yanda sukayi wani tsuru tsuru suna kallonshi sai kace wanda akace musu ya mutu…karasawa yayi ciki yana kallonsu with smile yace”ya jikin nashi?..”Mummy ce ta mike daga inda take tana nuna Bobbyn da har yanxun ya juya musu baya tace”gashi nan dai..ka fara dubashi muga”…baiyi musu ba ya isa inda sphygmomanometer da stethoscope din Bobby ke ajiye ya daukosu snn ya dawo gefe gadon ya zauna ya ajiye kayan snn yakai hannu zai ta6a forehead dinshi ya wani daddage ya kwade mishi hannun aiko Nur ya fashe da daria sosai..bashi ba hatta su Mummy ya basu daria ganin yanda yakejin jiki amma har yanada energy din rigima haka…yana sake kai hannu Bobby ya kuma make hannun nan kuma Mummy ta daure fuskanta tace idan bai tsaya an dubashi ba zataci mutuncinshi..ba yanda ya iya haka ya mike zaune yana cika yana batsewa fuskan nan ba sarari kaman wanda aka aikoma sakon mutuwa…Nur bai damu da hade ranshi ba ya bude sphyg din ya zaro curf din ciki snn ya zurashi hannun Bobby yana tieing dinshi a hankali…bayan ya gama ya makale stethoscope dinshi a kunne tareda kama hannun nashi snn ya fara pumping…yana gamawa ya zare abun daga kunnenshi snn ya shiga kwance curf daya daura mashi yana duban su Mummy yace”Blood pressure dinshi is normal amma idan bai dena sa damuwa ba yana iya hawa nan gaba kadan”..Mummy ta gyada kai alaman ta fahimta shi kuma Nur ya mike zuwa first aid box dinshi ya dakko wasu drugs snn ya koma inda yake..Mummy tasa aunty sumy zuwa ta hado tea shima ya wani sake hade rai yace bazaisha ba saida Mummyn ta zauna da kanta itama ta daure nata fuskan snn aka samu ya sanyeshi tas ta amsa drugs din suma ta bala mashi yasha snn tace ya kwanta…ba musu ya sake juya musu baya ya kwanta yanajin yanda zuciyarshi keta harbawa sbd kular dashi da sukayi…bayan few minutes bacci ya daukeshi dan hadda maganin bacci aka hada mishi sai a lokcin suma suka fita daga dakin…kafin Nur ya tafi Mummy ta zaunar dashi tana tambayan ko wani abu ya hadashi da Bobbyn…Nur da har yanxu attitude din abokin nashi bai dena bashi daria ba yace”wlh ba wani abu Mummy love ne kawai yake dawainiya dashi kuma yaki admitting “..kallonshi Mummy keyi nan take kuma jikinta ya bata akan Lamido ne dan haka tace”u mean akan wnn yarinyar ne?..”Nur yace”a kanta ne wlh..kinsan halinshi da kafiya na fada mashi sonta yake yana maidani dan iska and the most funniest part of al’amarin shine azabar kishinta da yake wai amma har yanxun yaki accepting the fact that yana sonta..pics dinta fa kawai tayi posting a status shine yake wnn zazza6in”..gyada kai Mummy ta shigayi cikin ranta tace”lallai biri yayi kama da mutum”..a fili kuma sai tace”yanxu ya kake ganin za’ayi?..ni bansan irin Bobby ba wlh”..su Nur hadda gyara zama yace”nidai ina ganin dena mishi mgnrta kawai zamuyi..kuma idan kunayi ku dena nima daga yau ban kara fada mishi yana sonta..mu zuba mishi ido kawai na tabbata idan abun yafi karfinshi da kanshi zaizo ya fada”…shiru Mummy tayi tana nazari kafin tace”amma kana ga baza’a samu matsala ba?..”Nur yace”inshaAllah ba matsalan da za’a samu..a yanda halinshi yake indai za’a cigaba dayi mishi zancen yana sonta to ita kanta yarinyar zaiyita sauke mata masifanshi ne sbd zaiga kaman ita take janyo ana fada mishi haka..amma idan mukayi biris da al’amarin watarana da kanshi zaiyi admitting yana sonta”…gyada kai Mummy tayi tace”shknn Allah ya zaba mana mafi alkhairi..ni da zaka taimaka ka kawomin yarinyar ma in ganta”…yace”Kaii Mummy kinaso Bobby ya dena kulani knn?..a yanda yakeda kishin nan idan yaga na daukota a motata ai inaga kisan mutuwa zaiyi”..ya karasa mgn yana daria…aunty sumy da batsan da zancen ba sai yanxu tace”lallai Nur kasan kan abokin nan naka da yawa”…yace”ai aunty qanin naki ne kinsan zuma ne saida wuta”..daria suka saka kafin Nur yayi musu sallama ya wuce suma kowa ta nufi dakinta kafin a jima su sake zuwa ganin jikinshi.