Dr. BOBBY COMPLETE HAUSA NOVEL

Har gari ya waye Bobby bai denajin zafin da yakeji ba…ya samu dai headache da fevern sun sauka amma zuciyarshi dai tana nan a jagule yanda take tun jiya kuma duk kokarinshi na ganin yayi maganin hakan gagararshi yayi…ko yau da safe sau uku yana kiran numberta switch off hakan kuma ba karamin sake tunzurashi yayi ba..sbd batada hankali ta kwashi jiki ta tafi har kaduna biki sai kace bikin ‘yar uwarta?..kuma yanada tabbacin a gidansu ba’a sani ba dan haka jira kwai yake ta dawo ya sauke mata nauyin dake cikin zuciyarshi.
A can kaduna kuwa Lamido tunda tasan yasan inda sukaje hankalinta bai sake kwanciya ba dan ko bikin ma dena enjoying dinshi tayi..tsoronta Allah tsoronta kada ya kira daddy ya fada masa tasan yana fada itakam ta gama yawo..da farko kin fadawa Billy da shi kanshi Sa’eed din tayi sbd tasan zasu dora mata laifi musamman Billy amma daga baya dole suka gane akwai abunda ke damunta dan haka ta fada musu exactly yanda sukayi dashi…hankalin Billy ya tashi matuka dan ko ita Lamidon bazata gaya mata shiga tashin hankali ba dama yanda kasan farar kura haka take wajen tsoro…basuyi niyyan barin kd ranan sunday ba amma haka Sa’eed ya tattarosu suka wuce sbd yana guje musu matsalan da zasu iya fuskanta wajen proprietor dama kuma biki ya kare tunda ankai amarya…haka suka tafi ko sallama basuje sunma amaryan ba…karfe uku da wani abu suka dauki hanyan kano and basu suka shigo birnin dabo ba sai around six..suna ganin an dauki hanyan FCNM hankalinsu ya sake tashi musamman Aysha da cikinta har wani juyawa yake sbd tashin hankali…har tsoron kunna wayanta take sbd tasan tana kunnawa zai kira and hakan na nufin masifa da bala’i dan kuwa tasan idonta idon Dr Bobby saiya cinye mata mutunci tas tunda dama ba yanxu ya saba ba..kawai tsoronta kada ya hadata da babanta amma dan ta masifarshi mai sauki ne dan idan da sabo yaci ace ta saba dukda cewa yanxu sam bai cika mata ihu ba..wani lokaci ko abu ya kama na fadan ne da idan baiyiba bazaiji dadi ba sai yayi mata shi a nutse kaman ba fada yakeyi ba amma yau kam tasan idan akwai abunda ya wuce ihu ma zaiyi shi tunda ta gama kular dashi…har suka isa hostel babu mai kwarin guiwar yin mgn cikinsu shi kanshi Sa’eed din addu’a yakeyi Allah yasa bazasu samu matsala sbd shi ba tunda shine wanda ya daukesu zuwa kadunan and Allah ya sani da yasan basuyi informing parents dinsu ba ba dalilinda zaisa ya kwashesu har kd saidai rashin sani…kafin su rabu ya sake kwantar musu da hankali tareda assuring dinsu cewa inshaAllah komai zai tafi normal..sukam gaba dayansu jinshi kawai sukeyi amma gani suke dole fa sai wani abu ya faru either big or small.
The next day sukayi shirin school kowa tasa uniform dinta suna jiran school bus saidai ba wanda takeda walwala a cikinsu…baa jimaba bus dinsu yazo ya kwashesu sukayi cikin makarantan…ana ajiyesu suka fice yau har rige rigen fita daga bus din suke a takaninsu sbd gudun haduwa dashi dukda ma sunsan monday ba ranan shigowarshi bane…daga nan direct class dinsu suka wuce basu sake fitowa ba har suka fara lectures.
Karfe tara daidai yayima Bobby a college din dukda cewa Monday ne ga kuma jikinshi da bai gama sauki ba amma ko hospital ya kasa zuwa sbd yanaso ya ganta…kai tsaye sama ya haura zuwa class dinsu don yasan idan yace har saiya sameta a waya to bazai taba samunta ba dan ba kunna wayan zatayi ba…wani lecturer ya samu a class din yana musu lectures dan haka kai tsaye ya fada class din fuskan nan a tamke kamar baisan menene daria ba…hannu ya mikawa lecturer din suka gaisa snn ya maida hannun aljihu yana baza idanu yanaso ya hangosu amma ko daya daga cikinsu bai gani ba…hankalinshi ya maida kan ‘yan class din fuska ba fus yace”where is Lamido?..”da sauri suka nuna inda take can baya tana sunukuyar dakai..baice kala ba sai takawa da yayi har gaban seat din nata ya zuba mata idanunshi ko kadan bata sonsu snn a kausashe yace mata”mike..”ba musu ta mike tsaye kai a kasa..ya sake cewa”ina Bilkisu?..”da sauri itama ta nuna seat dinda Billy ke zaune itama kallon nata yayi tayi saurin dukar da nata kan snn ya juya still hands dinshi a aljihu yace musu”follow me”..sum sum suka bi bayanshi kaman marasa gaskia..yana gaba suna binshi dukda bai juyaba yanajin footsteps dinsu ta bayan nashi dan haka kai tsaye ya wuce office dinshi suna biye dashi..a hanya ya kusa cin karo da Nur ya wani wara ido yana kallonshi then su Lamido dake biye dashi sai kuma ya saki dan murmushi yana maida dubanshi gareshi yace”so ka warke knn?..”ko kallonshi Bobby baiyi ba ya wuce office dinshi…yana isa ya bude kofa da yake bai shigowa Monday so secretary dinshi bata zoba…shine ya fara shiga ciki snn sukabi bayanshi…a kan sofa ya zauna yana kallon yanda sukayi wani cirko cirko a gabanshi sai ya sauke idanunshi kan Billy da yake ganin kamar tafi hankali yace”Bilkisu hadda ke?..”da sauri Billy da kanta ke kasa tace”wlh sir ba laifina bane ba yanda banyi da ita akan mu fada a gida ba tace wai baza’a fada ba”..yace”then meya hanaki kirani ki fadamin?..”Billy da har ta fara hawaye tace”shima cewa tayi bazan fada ba wai sbd hanawa zakayi?..sir dan Allah kayi hakuri wlh bazai sake faruwa ba”..gyada kai yayi dan ya yadda da ita yace”next time kina ganin zatayi anything stupid just give me a call ai kinada number na”..gyada kai Billy tayi tace”inshaAllah sir”..yace”shknn u can leave”..Billy tayi godia snn ta juya zata fita Aysha tabi bayanta da sauri wai tunaninta ya sallamesu gaba daya amma sai taji cikin cunkushashen voice dinshi yace”who ask u to leave?..”juyowa tayi a hankali tana dubanshi kaman zatasa kuka tace”sir dan girman Allah in tafi”…ya sake hade rai yace”C’mon comeback here before i loose it with u”..juyawa tayi a hankali ta daw ciki idonta na cikowa da hawaye…kallon hawayen dake silalowa daga idon nata yayi nan take ya lumshe ido yanajin yanda hawayen ke sauka har cikin zuciyarshi…baisan meyasa these days ko tayi laifi tana fara kuka jikinshi ke mutuwa ba..so yake yayi mata masifa son ranshi amma yana ganin hawayen nan yaji zuciyrshi yayi waji weak…kujera ya nuna mata idanunshi a kanta yace”seat”…batayi musu ba ta zauna inda ya nuna mata tana hawaye na sake ambaliya akan face dinta…dafe goshi Bobby yayi hade da lumshe ido yanajin yanda takeso ta sake haddasa mishi ciwon kai da wnn kukan nata yace”For Gods sake me akayi makai na kuka ne wai?..nayi maki wani abun ne?..”girgiza mashi kai tayi still tana hawaye yace”then why are u crying?..nida kika haddasa ma rashin lafia banyi kuka ba saike zaki sani a gaba kinamin kuka?..kinama da hankali kuwa?..”turo baki tayi jin abunda ya fada wai ta haddasa masa rashin lafia..ta sake tale baki tana dan kallonshi ta gefen idonta tace”nidai dan Allah karka fadawa daddy plss”…kallonta yakeyi yace”naji I won’t tell him amma inaso ki dena kukan nan muyi mgn dake”..ba musu takai hannunta ta goge hawayen duk yana kallonta snn tace”na goge”..gyara zama yayi still idonshi kanta yace”tambaya nakeso inyi maki and i want u to be fair to yourself..idan da a Gombe kike gaban parents dinki would u do what u where doing now?..”girgiza mishi kai tayi a hankali alaman bazatayi ba…yace”then why kikeyi a nan sbd ba gabansu kike ba?..tsakaninki da Allah da ace wani abu ya sameki a hanya what do u want me to tell ur dad daya bani amanarki?..ko sbd kina ganin baki ta6a yin wani abu na sanar dashi ba?..”girgiza kai ta shigayi da sauri tace”sir wlh ba haka bane..gani nayi Lubna friend dinmu ce sosai and ko sbd besty bai kamata muki zuw…”bata karasa ba ya katseta cikin karaji yace”in your entire life karki sake mentioning min besty idan muna mgn..ina ruwana da wani besty ni ke na sani bashi ba and idan bakiji abunda na fada ba kuma you will see the other side of me”..ya karasa mgn har wani huci yake kaman tsohon zaki…Lamido dai kallonshi kawai take tana mamakin yanda yake changing forms within minutes..yanxun nan fa yake mata mgn a nutse kmr bashi ba within a second kuma ya dawo mata asalin proprietor data sani…kauda kanta tayi tana turo baki ita gara ma ya dingayi mata masifan kmr yanda ya saba ba yasata a gaba yanayi mata mgnr dake sa jikinta yana mutuwa ba…ganin yanda itama ta hade rai tana turo mishi baki ya danyi kasa da voice dinshi yace”wai meyasa bakijin mgn ne ke kam?..meyasa fitinanki yayi yawa?..”sake turo baki tayi tana gunguni kuma akan idonshi kawai sai ya rufe idanu tareda jingina jikin kujera yana karanta innalillahi a cikin ranshi…kamar yanda ya fada ne idan baiyi wasa ba yarinyar nan saita haifar mishi da ciwon zucia sbd abunda yakeji kanta is beyond his control…kawai yana ganin Allah ne ke jarabtarshi da ‘yar Gombe sbd tsananin kiyayyan da yakema ‘yan Gomben.